Showing 6001 words to 9000 words out of 85942 words

Chapter 3 - SO DA ZUCIYA COMPLET Hausa Novels by Nana Hafsat Mx.txt

26 Oct 2025

357

zatayi Sallah.

“Angode Malam.”Ta Fada hade da sunkuya wa ta turawa yan biyun ta awarar.

Ficewa yayi bai ce mata komai ba. A zaure ya hadu da Modibbo babban’dan sa. Ya mika masa awarar Atuwa data ce bataso.

“Rike dan albarka.? Ya mik’awa Modibbo yana dashare masa baki.
Domin shi yakeso kawai kasancewar sa namiji ‘dan babbar matar sa data rasu.

Modibbo ya sa hannu biyu ya karba hade da yi masa godia ya shige Ciki. Shi kuma Ardo ya wuce waje. Dakin Dadaa Modibbo ya shiga ya gayar da ita. Su Zaraah ma suka gaishe shi. Awarar hannun sa ya mi’kawa Raheelah dake lasar ledar da suka lamushe. Suka Karb’a suna godia hade da kasafceta su cinye. Ya dan jima yana hira wajen Dadaa, Ya ajiye musu biredi dan 60 da madarar leda guda d’aya, Da sukari kullin goma, kafin ya musu Sai da safee ya shiga dakin Atuwa nan ma ya gayar da ita. Ya ajiye mata nata ledar, Ta amsa a dak’ile hade da juya masa kwakwidon gashin kanta. Batai masa godia ba, Domin kwarai matuk’a Atuwa nayiwa Modibbo madaukakiyar ‘kiyayyya saboda shakuwa da kaunar da sukayi da Dadaa data maye masa gurbin mahaifiyar sa data rasu....Shi kuwa mik’ewa yayi ya fuce dan dakin shagon sa dake wajen gidan.

<><><>

Wajajen k’arfe 9 na dare, Yan kawo bazawarar Malam Ardo suka cika layin su Atuwa da gud’a. Sai rera gud’ar suke yi. Suna shelar kawowar amaryar tasu. Yan layi dama wasu sassa na unguwar rimin kebe sai suka kawowa gidan ziyara don ganewa idanun su matar da Ardo aure aure ya ‘karo a karo na 9. Bakowa bace kuwa fyace, Jimmamman matar tsayyabu na lado dayayiwa shika 3 a baya. Kuma ‘ya ta farko ga Talle mai ‘data....


*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .
1/31/22, 18:28 - Buhainat: *_SO DA ZUCIYA_*

*_NA_*

*_NANA HAFSATU_*

*_ZAFAFA 5 (2022)_*
*_FREE PG:4_*

_ASSALAMU ALAIKUM BEAUTIFUL PEOPLE!! ZAFAFA BIYAR FAMILY💯💯🙌🏽❤️_

_MUNGODE DA ZABIN LITTAFAN ZAFAFA BIYAR. ALLAH YA KARA BUDI YA KUMA BAR ZUMUNCI_

_KAMAR KO DA YAUSHE, WANNAN KARON MA MUNZO DA KOKON BARAR YOUTUBE CHANNEL DIN YARON MU, SUDEIS MASOYI KUMA MAKARANCI, MAHADDACIN ALKUR’ANI MA GIRMA_

_WANNAN KARON MA DAN ALLAH A TEMAKA ADANNA WA CHANNEL DINSA KARARRWA DOMIN KASANCEWA DA MU A DUK SANDA MUKA DORA FEFAN BIDIYON SA, A TALLAFA A KALLA A KUMA DANNA MASA SUBSCRIPTION. HAKAN NA KARAWA SUDEIS KWARIN GWIWAR SAKE DAGEWA YA KUMA KARA KAIMI WAJEN YIN KARATUN SOSAI. MUNGODE KWARAI💯🙌🏽❤️_

_GA CHANNEL DIN DAKE YOUTUBE NAN👇🏾_

https://youtube.com/c/sudaiskura

_Sudais is a young boy who has passion in recitation of the Holy Qur'an at a very young age._

_Please help him grow his YouTube channel by subscribing and liking his videos to encourage the little boy. Jazakumullahu khairan🙏🏻_


••?. ••?. ••?. ••?.

***Dadaa dake cikin dakin ta ita da yara, tana jiyo hayaniyar masu kawo amarya tai saurin kashe fitilar shekarau ya gaza din da ta kunna musu dan suga haske. Tayi haka ne dan mutane suyi zaton sunyi bacci dan gudun kar ayi mata habaici da yawa. Gwaggo Lami ce ta shigo gidan da gud’ar ayyirrrrrrriri tana cewa.

“Amarya ta shigo gidan masoyinta, Jimmamman tako kafarki da hannun dama saboda kore asirin kishiyoyi.?

Gabaki daya mutanan da suka yo rakiya suka kwashe da dariya tare da hada baki wajan furta.

“Ahayye!! Nanayeeee casss...!?

Mama Atuwa na daki sai faman kwafa take, ji take kamar ta harbe daga su har amaryar saboda kishin da yake damunta. Kai tsaye kuwa suka nufi dakin ta zasu kai amarya a hada su tare da yi musu nasiha. Sai da suka fara shiga ta mike a zabure tana wani irin nishi tace dasu tana nuna su da yatsa manuni.

“Aradun Allah duk wace ta kuskura ta shigo sai na balla mata kafar baya bakaken munafukai. Daga ku har Ardon a karkashin kafata kuke babu uban da nake tsoro billahillazi.?

“Heeee caras-cas! Ardo dai ya yi sabon zubi, kuma dole yadda ya dama haka za'a shanye a gidansa.? Cewar wata kanwar Jimmamman daga can bayan Gwaggo Lami.

“Aikin banza aikin wofi BZ din? Har bazawara tana da wani daraja da kima a gurin miji? Mune nan aka aure mu a yan mata yan shila ba wai ragowar wani ba.?

Mama Atuwa tai maganar cikin cusa musu haushi. Sai dai babu wanda yaji din sai ma wata gud’a da suka sake yi kamar sun zo gidan gala.

“Haba ke kuwa Hafsatuwa, wannan auren fa ba haramun bane. Annabi Muhammad S.A.W ya auri bazawara, dan me zaki dinga aibata makamancinsa? Kiyi istigifari dan kinyi sabo babba.?

Gwaggo Lami ta fada tana kamo hannun Jimmamman suka juya dan shiga wajan Dadaa, wacce tasa duk suka kwanta tare da yin kamar sunyi bacci. Duhun da suka gani ne yasa su haska fitilun dake hannuwansu, nan suka tarar da Dadaa kwance tayi ‘dai-dai tamkar mai baccin gaske. Gwaggo tace a rabu dasu a kai amarya dakinta. Jimmamman na yafe da mayafi cikin ranta tana ta sak’a yadda zata zauna a gidan, musamman zama da Atuwa dan taga itama ba wai mutunci gare ta ba.

Sai da suka gama habaice-habaicen su kafin su tattara kowa ya kama gabansa, aka bar amarya ita kadai a daki tana jiran shigowar angonta.

••?.

Sai da kafa ta dauke ya rage daga yan dakin Dadaa sai dakin Mama Atuwa da kuma amarya. Cikin daga murya suka ji malam Ardo ya yi sallama kai daga jin muryarsa kasan cewar yana cikin farin ciki kamar wani saurayin ango. Mama Atuwa tai saurin fitowa daga daki har tana take kafar Farilatu kuma ko a jikinta bare ta bata hakuri saboda tsabar masifa tana cinta. Kicibus suka yi dashi zai shiga dakin jimmamman hannunsa rike da wata karamar kula da leda baka sai murmushi yake yana lasar lebe. Ganin Atuwa gabansa yasa shi hade rai tamkar be taba dariya ba a rayuwarsa dan yasan fitowa tayi dan tai masa tijara.

“Toh malam kasan dai yanzu yara sun dawo gidan uban su ko??

“Sai kuma aka yi me dan sun dawo? Ai ni ban ma san basa gidan ba sai da kika fada dazu?

Haushi da bakin ciki ya sake cika Atuwa, ta buga cinya tare da sake matsawa kusa dashi dan ta gano meke cikin kular. Kamshin tafarnuwa da kanumfari ne ke ta tashi kadan-kadan saboda an kulleta sosai. Malam Ardo ya kuma rike kular yadda ko kwata tazo yi ba zata iya ba duk masifarta. Atuwa ta kama kugu da yake akwai hasken farin wata ta ciki ana ganin komai, tace dashi.

“Eh! Daman ya za ai kasan suna nan ko basu nan? tunda kwan su kawai kake ajiyewa baka san yadda muke kyankyashe su ba bare kasan yadda muke kiwon su. Babu abinda ka sani malam sai aure, da anyi magana kace sunnah kake rayawa. Toh wallahi yanzu bazan dauki rainin hankali ba. Menene wannan kazo dashi bayan mu ka hada mu da kwayoyin awara.??

“Ina ruwanki dako ma menene? Hafsatuwa bana son sa ido, ki fita daga cikin sabgogina idan ba haka ba wallahi tallahi zan saba miki.?

“Kai tafi can, ni fitowar da nayi shine. Kafin ka shiga gurin waccan BZ din ka fara bani kudin karin kumallon gobe, nasan kana da kudi tunda gashi har aure ka sake jajibowa mutane muna cikin rashin abinci. Wannan dubu goma ta sake jajibo mana bala’i bayan ko shekara ba’a rufe ba na shikar Zabba’un mai koko da kayi.?

“Bani dasu, Ina ruwan ki kuma? matsa ki bani guri."

“Aikuwa baka isa ba sai ka bani abin karin kumallon safe, ai nauyin a kanka yake bani ba.?

Malam Ardo ya kalleta ya kalli dakin amarya jimmamman, ya kagara ya shiga ciki amman Atuwa ta kasa ta tsare. Ya daddage tare da sa gefen hannunsa ya bangajeta da sauri ya shige dakin jimmamman yana faman baza yar shararsa.

“Zaka fito ka same ni wallahi, ba dai a gidan zaka kwana ba? Banyi niyar shigowa dakin ba dan ban sani ba ko sunyi barbade a bakin kofar. Amman Allah ya kaimu safiya duk masifarka sai ka bani abin da zamu ci, banda mugunta ba zaka tsaya ka gina mu ba, sai dai daka samu kudi kace aure sai kace wani jaki.?

Malam Ardo yana jin ta amman da yake ba ta ita yake yi ba duk maganganunta babu wanda ya d'ad'arasa a kasa, burinsa kawai ya farantawa amarya Jimmamman dake zaune tana ta murmushi cikin mayafi, dadi kawai takeji miji na sonta. Ardo ya ajiye kular a gaban Jimmaman da ledar ya zauna a kusa da ita baki a wangale kamar shine farkon auransa.

“Amarya ta.? Ya fada kamar zai shiga jikinta.

“Na'am na Jimmamman.? Ta bashi amsa babu ko kunyar nan.

“Dan bude min fuskar mana, ai yanzu babu maganar boye wani abu ga junan mu.? Kamar yana kallanta, ta saki fari da ido ta cikin mayafin tare da cewa.

“Sai ka siya baki.?

“Hahahaha amarya ta kenan, yo maganar siyan baki ai ta kare. Maza bude fuskarki farfesu ne nasa aka yi mana na kaza.?

Yana magana yana bude kular, shi kansa ya kagu ta faraci yawunsa gaba daya a tsinke yake. Jimmamman ta bude mayafi dai-dai lokacin da Ardo ya gama bude kular kamshi ya bud'ad'e cikin dakin. Tai saurin janye kular daga gabansa tana wani yauki kamar wata karuwa tace dashi.

“Idan har ta siyan baki ce ai babu kai zamu ci. Wannan tawa ce ni kadai na Jimmamman.?

Ardo ya ware ido tare da tunawa da yayi bashi yasa aka bashi kazar guda daya ta hausa, ya kuma sa aka dafo masa gashi ta dan kaciya ce. Amma ya zai yi tunda amarya tace ba zai ci ba. Ya goge hannunsa yana ta sakin fara'a yace mata.

“An bar miki kiyi yadda kike so da ita, ai ke amarya ce duk yadda kika ce haka za'a yi.?

Yana magana yana janyo leda mai dauke da lemon kwalba Pepsi guda daya tal. Ya fara laluben mukullinsa mai dauke da keyholder na bude murfin kwalba. Nan ma da sauri Jimmamman ta karbe tare da lakuce masa hanci tana faman murmushi tace.

“Haba na Jimmamman wai duk bani ka kawowa ba ne??

“Du naki ne mana amarya ta.? Ardo ya fada cikin gigita ganin ta kwace komai zata handame.

“Toh ka bar min kayana ba yanzu zan ci ba sai gobe.?

Ardo ya jinjina kai tare da shafa hannu kamar me goga man shafawa. Yana ji yana gani ta tura karkashin gadonta daga nan ta kwanta. Ganin tana neman hanashi raya daren yasa shi saurin bin bayanta suka kwanta. Bata hana shi ba domin ita kanta ba ta da juriyar da zata hanashi dan tayi mu'amala da kayan mata daban-daban kafin ta shigo gidan.

Dadaa kuwa bata rintsa ba saboda tasan wata gwagwarmayar Ardo ya sake jajibo musu, takan ce shi kuma kaddarasa ta auri saki ce. Duk da yasha gaya musu cewa yana yin aure ne saboda ya mori kuruciyarsa ya kuma samu yalwatar ‘ya’ya maza tunda bashi da ‘ya ‘ya mazan sai Modibbo kad’ai ba sauran maza da zasu gajeshi ko su taimaka masa nan gaba. Yaransa duk mata ne da zasu zame masa wahala aganin sa, ya gama rainan su da kulawa dasu a karshe wani katon yazo ya aure su shikenan bashi zai more su ba. A cewar sa mace wahalace shi kuma ba zai wahalar da kansa ba wajan kiwata su a karshe su tafi gidan wasu babu ko na buhun shinkafa bare kudin cefane.

Fitilar da ta kashe shigowar kawo amarya, ita ta kunna. Abin da ya bata mamaki shine ganin Zaraah a zaune ta zabga uban tagumi ga alama kuma tunani ta fada dan ko motsawa ba ta yi daga inda take.

“Zaraah! Zaraah!! Ke Zaraah...!!!”Cikin firgita da zabura Zaraah ta dago tare da cewa.

“Na'am Dadaa?

“Haba tunanin me kike yi haka??

Babu zato bare tsammani wasu hawaye Dadaa taga Zaraah na fitarwa, kuma cikin sanyin muryarta mai dadi da babu hayaniya tace.

“Dadaa ina jin tsoran lokacin da zai zo a yi mana wulakanci akan irin wannan abun da Bappah yake yi. Ance duk abinda mutum ya yi sai an yiwa nasa. Yanzu Bappah baya gudun muma muyi aure miji ya dinga wulakanta mu??

Wani irin zafi ya daki zuciyar Dadaa, kuka take son yi amman tana gudun kar Zaraah ta kuma karaya da samun rahamar duniya. Ta dade cikin shiru bata samu amsar da zata bata ba, wanda hakan yasa Zaraah ta kuma tsorata, zuciyarta ta kuma shiga cikin tashin hankali, tasan shirun da Dadaa tayi tabbaci ne na cewa suma idan suka yi aure mijin su zai mai da su banzaye...

Dak’yar Dadaan ta iya saita kanta, Cikin ikon Allah da buwayar sa kuwa ta shiga magana da Zaraah cikin nutsuwa hadi da kwantar mata da hankali, Ta yadda ta goge bak’in Ardo dake zuciar ta Zaarah. Domin uba ne agurin su. Don haka duk abunda yayi idan har ba sab’awa mahalicci yayi ba. Dadaan na k’ok’arin wanke Ardon agurin yaran nasa. Sam bataso su tashi da jin haushin sa da kuma ‘kullatar sa a zukatan su. .

Tas Dadaa ta wanke Ardo kamar ko yaushe tasamu suka shiga wata y’ar hirar daban. Kafin Dadaan ta juya tayi addduar bacci ta tofe yan biyu da addu’oi don tuni bacci yai awun gaba dasu. Ta tofe lungu da sako na dakin da addu’oin kariya. Kana ta umarci Zaraah data matse hasken fitila idan zata kwanta.

Zaraah ta rage sautin rediyon da Hamma Modibbo ya saya mata kwanaki. Tashiga neman tashar da bata wuce ta duk daren Allah. Sannu ahankali ta nemo tashar. Kamar ko da yaushe gidan rediyon sun saka sautin qira’ar bakin bahaushen balaraben mai tattare da nutsuwa, ‘kima da kuma kaifin tunani, Dimbin Ilimi da kuma sautin qira’a ba kowa bane fyace matashi kuma mahaddacin AlQur’an dake k’asar ta Mecca, inda yake karo karatun sa akan fannin islama. Matashin malamin dan kano ne wanda makarantu dama manyan manyan kasashe ke san kasancewar sa a tattare dasu. Sai dai shid’in na dabanne, Baya shiga harkar kowa da komai idan har bai shafi bangaren sa ba. Karatu ne kawai agaban sa. Indai ba yan uwa na kusa da kuma wanda suka san shi tun yana karami ba. Ba wanda zai iya ce maka ga yadda fasalin sa yake, Sai dai sautin ‘kira’ar sa.

Sannu ahankali haka Zaraah tak’arasa jin sautin kira’ar matashin saurayin. Ta lumshe idanu bayan ta kashe rediyon. Ta jero adduoi ta tofe jikin ta. Ta matse hasken fitilar sannan ta kwanta da dama. Kunnuwanta ba abunda suke tariyo mata sai sautin daddad’an karatun, Sudeis Ibn Harith.. A haka bacci ya dauke ta. Dake bata sallah bata, futsari ne kawai ya tasheta da asuba takoma ta cigaba da baccin ta. Ihun shekowar kururuwar Atuwa ce tasa Zaraah ta tashi daga daddadan mafarkin muryar, Sudeis Ibn Harith. Da sauri Zaraah ta mike ganin Atuwa na shirin fad’owa kanta.

“Ke Atuwa lapia?? Cewar Dada dake tsaye tana gyara dan yargalallen labulan su da Atuwan ta yago shi daga jikin ‘kusa da k’afarta.

“Ina fa lapia Jammu, Ardo nagani da fulas na shayi dayan hannun kuma da lafceciyar leda dauke da soyayyen kwai, Sai kamshi yake. Gefe d’aya kuma biredi mai yanka yanka Jammu. Mai yanka yanka biredin....Da tuntub’e yai saurin shigewa cikin dakin bankadaddiyar. Lalle Ardo, Biredi mai yanka yanka. Murtala 10 ne fa..?

Atuwa ta karasa fada tana kambama shayi da kwai da kuma biredi mai yanka yankan da Malam Ardo ya sayowa Jimmamman amaryar sa. ...


#pls follow/like and refer my scented product to your beloved ones🥰🔥💯🍓

Instagram:yerwaincense_and_more
Muna sales. Tun daga 4 ga December zuwa 10 ga watan sabuwar shekarar 2022 watan janairu/January Insha Allahu. Mun cire kaso 30 na kudin kayayyakin mu. Akwai kuma kyauta ta musanman ga wanda suka saya kaya daga dubu 7 zuwa sama.

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .


___________
1/31/22, 18:28 - Buhainat: *_SO DA ZUCIYA._*
_(A LOVE SO BEAUTIFUL)_

*_NA_*

*_NANA HAFSATU_*

*_ZAFAFA 5 2022_*
_(PAID NOVELS/LITTATTAFAN KUDI NE)_

*_FREE PAGE:5_*
_(SHAFIN KARSHE NA KYAUTA)_

*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login