Showing 42001 words to 45000 words out of 85942 words
Chapter 15 - SO DA ZUCIYA COMPLET Hausa Novels by Nana Hafsat Mx.txt
Dadaa ta sake bai wa Atuwa dubu biyar kan a sake yin abincin makokin saboda gidah yan uwa sun cika taf kuma ace babu abinci, Sai hammar yunwa mutane ke tayi.
Sai dare su Dadaa suka yi haramar komawa, Kowanne idanun sa jazir ciki harda yan biyu saboda tsananin sabon da sukayi da Hamman nasu. Zaraah kuwa dakyar Dadaa ta yakice ta daga makalkale rigar Hamman nasu da tayi dake ninke akan dan akwatun ‘karfen sa.Rayuwa kenan!
Ibrahim ne yazo daukar su Dadaan, Sai Haj Amina data bi yo shi don yiwa su Dadaan gaisuwa. Har ciki Dadaan tayi musu rakiya. Haj Aminan ta zube a kan taburma tanai wa su Atuwa ta’aziya.
“Amin dai Haj. Modibbo sa’i yayi.? Cewar Atuwa dake zaune a gefen dakin ta ta zubawa su Haj. Amina idanu tana musu kallon qurilla.
Haj Amina dake gefen Jimmamman ta amsa ahankali.
“Hajia baki waye ni ba ko??
Haj Amina ta juya tana kallon Atuwa da gaba d’aya ta mayar da ita kamar talabijin din kallo. Sam bata damuwa da kallon Haj Amina ba bare tsirarrakin mutanen dake wajen tasake cewa,
“Ni ce nan Atuwa da kika bamu kudi lokacin baya.?
Haj Amina ta’dan yi murmushi tana kada kai.
“Eh yaasin kika babbamu kudade charan chas sa’ilin nan ni da Jimmamman.?
“Okay nagane, Toh ya karin hak’uri d...?
Bata karasa tambayar ba, Idrisu dan Rumalle ya shigo da gudu Usmanu na biye masa a baya.
“Zo nan dan ‘kundin uban ka ka bani farantin nan. Idan ka cinye ni kuam fa? Mama mama kinga ya hana ni abincin ko??
Rumalle dake sosa kunnenta da guntun ice taja tsaki tana wurga musu harara,
“Kaci malafar kan uwar uban ka. Haba sai fitinar tsiya, Zaka bashi abincin ko sai na lakada maka na jaki.??
“Mama kadan ne nanfa, Wani mutumi ya bani, Shi ne nan wai sai munyi rabo dai dai.?
“Zaku matsa ko sai na zazzabga muku bari??
Ficewa sukayi dukkanin su, Yayin da Haj Amina ta musu sallama, Dada ta Kalli tsohon dakin ta a baya, Wanda hamamin kazantar su Idrisu ya sake munantar da dakin baki daya. Ya bade da kura. Tamkar yayi shekara da shekaru ba'a gyara shi.
Ta sauke ajiyar zuciya kawai. Hade da riko hannun Zaraah dake kuka shab'e shab'e. Domin idan ka tsame Dadaa agidan nan ba Wanda Zaraah tasu tazo daya Kuma suka fi kusanci irin Modibbo. Hakika Zaraah tayi babban rashi. Addu'oi tacigaba da yiwa modibbo ahankali saboda yanayin yadda labbanta ke motsawa.
Waje suka nufa don shigaa mota su koma gidan. Ardo dake zaune acikin jamaa Yan zaman makoki Yana ganin su ya mike tamkar dama sudin yake jira.
Idanun sa 'kur akan Dadaa dake tsaye da su Haj Amina suna yiwa wasu ta'aziyya a gefe
Cikin sauri ya yayibi takalmi wari da wari ya zura,Ashe tsabar rawar jiki warin takalmin Ladan ne daya, dayar kafar kuma na hannafi me shago, Hannafi dake shirin tafiya wajen aiki ya jawo rigar ardo da hankalin sa gaba daya yayi wajen su Dadaaa dake shirin shiga mota.
"Ban warin takalmina Ardo." Cewar Hannafi daya duk'a ya riko saman silipas din da kafa daya ke wajen Ardo.
"Karbomin nawa ma Hannafi" Ladan ya fada girgiza Kai. Domin gani yake mutuwar Modibbo ce ta susutar da Ardon. Ardon kuwa ganin Dadaa da yayi ne, Ta dawo kamar ranar daya faraa haduwa da ita ne yasa shi zuzucewa. Da sauri Ardo ya sab'ule takalman baki daya ya shigaa dokawa Dadaa kira, Kamar wata matar sa.
"Jammu, Jammu, Jammu"
Dadaa da har ta bude murfin mota zata shiga taja ta tsaya tana mai sarautar Allah idanu. Hakama hajia Amina data saki baki tana jiran cewar Ardo. Da sauri ta zagaya tana dan murmushi kadan.
"Malam Ardoo mun gaisa ko? Ya Karin hakurin rashi?"
Ardo ya bude idanu yanawa Dadaa wani irin mayataçcen kallo.
"Jammu!"
Dadaa dake binsa da kallo shak'ek'e tace,
"Na'am Ardo"
Ardo ya hadiye wani 'dacin daya tokare masa a wuya. Na jin sunan sa data Kira gatsal yau babu ma sirken Malam din da take joganawa a sunan sa. Ya kada kai yana kokarin 'kakaro murmushi. Idanuwan sa nata karakaina a jikin tah
Haj Amina ta sha gabansa hade da wangalewa Dadaa kofar motar ta shige.
"Ardo Nace ya Karin hakuri?" Haj Amina ta sake cewa dashi,
Ardo ya zura Kai Zai sake lek'a Dadaa,
"Alhamdulillah Hajia. Jammu nace ki dakata muyi magana ko?"
"wacce magana zakuyi Ardo? Ai bakin alkalami ya rigada ya bushe. In Sha Allahu. Jammu tamaka nisan da har gaban abadan ba zaka iya cinma taba. Yara ne dai Allah yayi zaku samu a tsakanin ku. Kuma har abadan da sunan ka zasu amsa a matsayin mahaifin su. Zumuncin ku ba zai samu tangarda ba Kai da yaran ka. Jammu kuma albarkacin 'ya'yan dake tsakanin ku dole zaku dinga gaisawa. Baya ga haka Kar ka ma kulla wa zuciyar ka wani abu ga me da jammu. Domin yanzun ta maka ni sa. Allah ya musanya mata da mafi alkhairi. Allah ya jikan Modibbo Mai gidana na maka ta'aziyya. "
Haj Amina na gama magana ta shige cikin mota. Yayin da Ardo ke tsaye motar su Haj Amina ta bula masa kasa ta yi kan titi. Yatsan da yasa a baki ya chiza yana auna karshen zancen na hajia Amina datace Allah ya musanya Mata da mafi alkhairi
Dakyar yaja sanyayyun kafafun sa da babu takalmi acikin su. Sunyi furu furu saboda rairayin kasar dake wajen.
Hakama Dadaa anata bangaren tashiga mamakjn kalaman na karshe da Haj Amina tace da Ardo. Batace komai ba har suka karasa gidah.
××DANGOJE's××
Koda suka karasa gidah Haj Amina bata yi wa Dadaa maganar komai ba, Su Dadaa suka cigaba da alhinin mutuwar Modibo. Sai bayan sati biyu da rasuwar Modibbo . Haj Amina ta sami Dadaa da maganar Capt. Muhd, Saboda tsananin yadda ya takura musu da zancen Dadaan. Ciki harda Addayo datazo gidan a bazata taga Dadaan. Wanda Dadaan da su Zaraah sam basuda masaniya. Kallo daya da Addayo tayi wa Dadaa da yaran ta gaba daya taji kaunar su ya kamata. Tabbas Dadaan zubinta kwarai yayi kamada su marigayi ya Jamila da Jamila.
Dadaa fafur tace bata raayin kara wani aure, Zatayi zaman tarbiyyar 'yayanta dai. Haj Amina ta kada ta raya. Dadaa tace sam ita ta wuce shekarun aure.
Haj Amina takanyi murmushi duk sanda Dadaa tafadi haka takance,
"Kalli baya na . Na goyaki a baya yafi sau nawa Jammu. Shikenan tinda haka Kika zaba. , Kin nu na ban isa dake ba, Baki dauke ni tamkar Iyami ba kenan. Nagode"
Takarasa tana goge hawayen data 'kakaro shi. Nan jikin Dadaa yayi sanyi. Ta yanke hukunci take awajen tana hawayen itama,
"Na amince Hajia. Dan Allah kibar zubar mun da hawayen ki na amince."
Haj Amina cike da farin ciki ta rarumi Dadaa ta matseta ajikin ta. Suka fashe da kuka baki daya, Wanda nake da tabbacin na farin ciki ne.
Haj Amina ta 'kara da
"Ina dattijuwar data zo kwanakin baya? Mahaifyar sace. Shi da ita sun kafe don inda gaban matsuwa ma wallahi sunyi Jammu. Sunason ke da yaran ki baki daya zaku koma can gidan. Ciki harda Zaraah. Yadda suka nuna kaunar su akan ku hakan yasa na aminta da zancen na Kuma kara da doriyar mu zamu dinga daukar nauyin karatun Zaraah harta kare makaranta izuwa jami'a. Da yardar Allah har ya zuwa aurenta. Don Addayon ma catayi ita kam tayiwa Zaraah miji. " Ta karasa tana daria
Dadaa dai murmushi tayi kawai don tarasa bakin magana. Haj Amina ta kirawo su Zaraah da Yan biyu ta sanar dasu komai dangane da auren da Dadaar su zatayi. Da Kuma zaman su da zai koma can baki daya
Kwarai matuka dukkanin su duk kuwa da kankancin shekarun su. Sunyi matukar murna sun Kuma amince da sabuwar rayuwar da zasu shiga. Dadaa dai tana gefe kawai. Kunya duk ta lullube ta.
×××××
Sati daya da sanarwa Dadaa zancen Capt muhd. Ranar jumuah ya sanar dasu Haj Amina zuwan da zai yi wajen Dadaa da daddare bayan sallar ishai.
Tun safiyar ranar Haj Amina dakanta takai Dadaa saloon and spa aka yiwa Dadaa wankin Kai aaka kitse yalwataccen kan da kitson shuka. Aka mata gyaran jiki da su kunshi.
Dadaa dai tafito ras kamar sabuwar budurwar amarya. Kyanta ya tsatso. Karancin shekarunta suka bayyana.yankwanewar datayi na gidan Ardoo data koma tamkar babba. Yanzu duk komai ya baje. Takoma Jammu ta baya. Kai ba kace tayi aure tanada babbar 'ya kamar Zaraah.
××CAPT. MUHD's××
A bangaren na Capt muhd shidin ma hakan take. Tun kafin a sanar dashi amincewar Dadaa tuni yafi mai Kora shafawa. Yasa an gyare sashen daya ware shi daban a gidan. An zuba furnitures da komai. Kamar sabuwar amarya Zai 'bare a leda.
Jikin su Haj Iklima yayi sanyi kwarai matuka. Kuma Addayo Kai tsaye ta sanar dasu auren da mijin nasu Zai Kara. Sun tashi hankulansu kwarai matuka. Wanda hakan da sukayi ya jefa zukatan su ga dimuwa.
Domin 'barau 'barau capt muhd ya futo musu a mutum ya nuna musu ya san abunda suka aikata a bayan . Yana Gama fada ya fice kai tsaye ya wuce gidan ALHAJI Dangoje cikin shigar sa ta alfarma. Sai kamshi ke tashi ajikin sa
Bayan sun gaysa dasu Haj Amina da kuma Alhaji Dangoje dake tsokanar sa. Hajian tayi masa iso zuwa ga parlorn baki. Nan ba jimawa Haj Amina ta raka Dadaa parlorn inda Capt muhd yake .
Tun da tashiga parlorn yake binta da kallo. Kallon ta ya shiga yi tamkar saurayi yaga budurwar sa.
Wanda hakan da yake yi ya jefa Dadaa fadawa kogin kunyar sa. A 'darare ta zauna nesa dashi. Ta zuba kyau cikin dogon jilbab din dake jikin ta. Maroon color wanda ya karawa kyakkywar fuskarta kyau.
Shi Kuma capt. din yayi shiga cikin manyan kaya shudaye. Ya dora hular zanna bukar. Kamshin turaren sa ya gauraye parlorn baki daya.
Gaisawa suka fara Yi Da Dadaan. Cikin nutsuwa da kalama. Gwanin sha'awa Capt muhd ya fara yiwa Dadaa bayanin kansa ya 'karkare da,
"Sai abu na karshe Kuma muhimmi shine a yanzu Ina da mata biyu da yara 9. Matata ta uku Wanda a yanzu itace ta kasance ta farko tanada yara 4. Sai mai biye Mata tanada yara 3, Sai maza biyu Wanda iyayen su duk sun rasu. Jamila da Jamila kenan. Ya da kanwa ne. Yayar na Fara aura muka samu albarkacin 'da namiji. Sai tarasu. Aka bani kanwar ta mai suna Jamila itama. Duk suna daya ne dasu. Kowanne cikin su ya ci sunan kakannin su ta uwa da uba. Jamila ta farko ana ce da ita ('Bingel) kanwar ta Kuma jamilann ake CE Mata, Toh dai itama kanwar sai Allah ya mata rasuwa bisaga wani hatsari shiryayye da aka Mana cinne dashi. Wanda Nan gaba Zan sanar miki komai. Itama kafin rasuwar ta, Alah ya azurrta mu da albarkacin 'da namini.
"MAHEER shine 'da na na farko a duniya, Wanda ya kasance 'dan Jamila data rasu wajen haihuwa ko!? Ina fatan kina ganewa?"
Dadaa ta 'daga Kai. Capt muhd yayi murmushi kafin ya cigaba da cewa,
"Toh anan bayan wani lokaci sai aka auramun kanwar ta tacigaba da shayar da yaron Bingel dayaci suna MAHEER. Bayan wani dan lokaci sai na Karo aure. Wani oga na daya samamin aiki a lokacin sai bayani 'yar sa na ayra bayan shekaru budu da yin auren matata ta uku kenan. Toh dai bayan na auro Maijidda sai Jamila ta haihu. Muka samu albarkacin 'da namiji muna ce dashi SUDEIS.
"Wanda insha Allah nan gaba Zan sanar miki komai. Amma kafin sannan Maheer yana kasar Egypt acan yayi karatn sa da komai. Ya kanzo Nigeria. Amma iya Ikko (Lagos) yake sauka gidan kawu na kanin mahaifya.tah. Wanda Matar sa Haj. Laila ke rikon dukkanin su a baya. Kafin a mayar da sudies zuwa kasar saudiyyah.
"Shi Kuma Maheer Yana kasar Cairo Egypt. Gaba daya dangi musanman mahafiya ta ma muna Kiran sa da na Ikko........" Ya karasa fada hade da daukar ruwan robar gaban sa ya kurba....
2/1/22, 10:21 - Buhainat: ×SO DA ZUCIYA!!×
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p
*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*
*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .
___________
××25××
×××Dadaa dai tayi shiru tana sauraron sa, Hadi da jujjuya kalaman da yake fada a kwakwalwar ta.
Sai daya sha ruwan sosai, Tukun sannan ya zare robar ruwar daga bakin sa. Ya saki katuwar ajiyar zuciya mai dauke da hamdala. Yanayin yadda ya sauke zuciyar tasa zaka gano tabbas ya sauke wani boyayyen nauyi dake addabar zuciyar sa.
"Jameelah! Baki ce komai ba" Ya karasa hadi da zuba mata manyan idanun sa akanta dake nuna tsantsar kaunarta a zuciyar sa.
"Allah ya jikan su da rahama." Ta samu kanta da fadin haka.
"Amin Aamin! So duka dai. Kamar yadda na gaya miki,' Yaya na 9. Maza bakwai mata 2. Sai matan da igiyar aure na ke akan su. Maijidda ita likita ce dake aiki a asibitin kwararru na murtala muhammad, Sai ikhiima ita kuma babbar ma'aikaciyar banki ce. Yara kuma wasu na aiki wasu na karatu , Ban aurar da kowa cikin su ba. Amman ina fatan aurar dasu da zarar lokaci yayi. Tamkar dai yadda neman kowane aure yake, Zaki ga kowa da sanadin dayaa sa yayi 'karin, Ni dai a nawa bangaren zan kara aure ne saboda zucia ta ta aminta da wadda zan auro, Mahafiya ta ta amince fiye da kalmomi, Sannan dalili na biyu zan kara aure ne saboda gazawar da ke cinye zucia ta ta farfado. A yanzu ba abunda nafi bukata fiye da akula da ni. Wannan shine dalilin dayasa zan aure ki Jameelah. Ina kuma fatan zaki tallafe ni ki amince ki aure ni. Insha Allahu zaki same Ni mai rike amana da kuma kyauta tawa.. Ko?"
Yadda ya karasa maganar yana langabar da kansa tamkar wani matashin saurayi ne hakan ba karamun dariya ya bawa Dadaa ba. Ta danyi murmushi kawai
'kasan zuciyar ta kuwa cike yake da fargabar irin ilimin matan sa. Taya ma ya yanke hukuncin auren ta. Bayan ita din batada ilimin boko sai na arabi. Sam ba zata iya gogayya da su ba. Tunda su din gogaggu ne da suka shak'i ilimin boko suka 'koshi.
"Ba ki ce komai ba"
Ba tare da masaniyar labarin zuciyar ta yafito ba Dadaa tace,
"Bani da ilimin da zan iya gogayya da matan ka."
Yadda ya zuba Mata idanu ba ko kyaftawa yasan ya Dadaa gano baranbaramar da tayi. Kafin tace wani abu tuni ya rigata.
"Haba Jameelah Kar ma ki sake dakko maganar nan. Ke kuwa ki me da ishasshen ililin da zaki tafiyar da gidana da ni kai na baki daya. Banason auren mu ya dau lokaci Jameelah . Ni da son samu na ma a daura gobe da yardar Allah...."
Dadaa ta sauke ajiyar zuciya tana lankwasar da yatsun ta dake dauke da maroon color lalle
"Kinji? Idan har ban takura ki ba. Don inaga babu wani abu da zai dau lokaci. Mu ba yara bane,So ba wani hidindimu da zamuyi Wanda zai ja lokaci. Yanzu dai ga wannan ba yawa idan da akwai abunda kike bukata sai a saya."
Ya karasa maganar hade da ajiye wata leda bak'a mai dauke da bandir din kudi.
Dadaa dai tayi shiru tamkar ruwa ya cinyeta. Zuciar tace ta shiga tsananta bugu. Gaba daya jj take tamkar mafarki take
Wai yau itace babban mutum Mai cike da Kamala da dattako yazo Yana neman aurenta? Babban mutum gogagge wanda ake damawa dashi a yankin masu farcinan susa. Ga matan sa masu dimbin ilimine. Da gayu . Wai yau ita Dadaa matar Ardo a baya, Yar kauyen kayau. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha'u .Ta 'daga idanunta ta sauke akan bakar ledar daya ajiye a gabanta.
Da sauri jiki da bakinta na rawa na tsoron ganin himilin kudin dake cikin ledar gaban ta tace.
"Ba abunda nake bukata yallabai. Mungode kwarai." Ta karasa hade da 'dan janye ledar daga gabanta.
"Yallabai?" Ya tambaye ta yana sakin tattausan murmushi.
Itama murmushin ta danyi tana maida kanta kan 'kofa.
Ya kalli agogon hannunsa kafin ya mike tsaye Yana mai gyara zaman hular kansa
"yalla...."
"Karki karasa don Allah. Wai yallabai kamar wani alhajin kauye, Dole acanzamun suna da zarar an daura."
Tamkar wata yar budurwa haka Dadaa ta samu kanta da rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta.
Murmushi ya sake yi. Kyakkyawar fuskar sa mai 'dauke da annurin kamala ta fad'ad'a da farin cikin Jammu dake gaban sa.
"idan har ba renawa ki Kayi ba. Dan Allah kada ki sake cewa na daukàa. Zan koma gida, Kinji ko?"
Dadaa ta samu kanta da daga masa kai alamar eh.
"Ina yan biyun mu da Zaraah?"
"Suna ciki "
"A kirawo su mu gaysa sai na wuce "
Mikewa Dadaan tayi ta hau saman. Gaba daya kunya duk ta kamata. Ai kuwa tana ganin Na'eelah tace da ita.
"Kira su Zaraah kuje ku gaysar da bakon su Abba (Alhaji Dangoje) a parlorn baki."
Da sauri Na'eelah ta juya ta shige dakin Zaraah inda suke baki daya. Gaya musu tayi umarnin Dadaa suka wuce parlorn kai tsaye.
Cikin faraa da nuna kaunar sa gare su Capt muhd ya shigaa amsa gaisuwar su Yana wa yan biyu Wasa . Lokaci daya yaji kaunar yaran sun shiga can cikin zuciar sa.
Sarai ya gano Dadaa ba zata dawo ba. Don haka ya dau ledar da damun kudin yake ciki ya bawa Zaraah yace takai wa Dadaa
Ya kirawo alhaji Dangoje a waya. Ashe har ya dawo Yana parlorn sa . Can yaje suka shigaa hira. Nan Capt din ke shedawa alhaji Dangoje auren Dadaa da yake