Showing 51001 words to 54000 words out of 85942 words
Chapter 18 - SO DA ZUCIYA COMPLET Hausa Novels by Nana Hafsat Mx.txt
kifiya tana mikewa tsaye. Suka hada baki wajen tambayar su,
"Namiji?"
Ai atuwa bata samu bakin magana ba, Sai guda data sake saki tayi waje tana nanata,
"Dole ne Ardo yaji Wannan dadd'adan zance. "Dan qundun uba, Kai Kai a hayye landantsan, shagali budiri wan dinner. Wabillahil lazi har gada zanje na sanar masa. "
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p
*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*
*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .
___________
2/4/22, 07:42 - Buhainat: *Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*
I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*SO DA ZUCIYA*
*NANA HAFSATU*
*29*
***Atuwa na ta zambad'a sauri a hanya tana kalle kallen lungu da sak'o wajen nemo Ardo. Don shelanta masa haihuwar Jammu .
Can gefen gada ta hango shi. Ya tsayar da zabbau me awara suna tad'i. Ta sauke bokitin awarar a tsakiyar su. Shi kuma Ardoo ya choge daga gefe yana zuba mata zance. Yayin da zabbau ke rike da gammon dora awarar a hannu tana jujjuya shi. Sun lula sosai a fagen zancen da suke. Sai ga Atuwa ta isa wajen su. Ta duk'a ta dau awara guda da daya ta cusa a baka.
"Ina kudin awarar da kikaci?" Cewar zabbau. Hade da mikawa Atuwa hannunta alamar ta chanke mata kudinta.
"Zabbau kenan. Ko Adaman shehulle (mahaifiyar zabbaun) na goya ta a baya bake ba."
"To ni meye ruwana aciki? Kawai kiban goma ta. Gaskia."
"Uban iyali. Malam Ardoo saurayin kawayen 'yayan sa. An gayda Ardo uban iyali. Nazo maka da daddadan labari. Amman kafin sannan biya mun goman awara dana ci ."
Harara Ardo ya dankara mata kafin ya zaro nera goma daga cikin nera 80 din dake aljihun sa ya mikawa Zabbau me awara. Atuwa taja guda tasaki hade da shewa.
" 'karuwa muka samu Ardodo."
"Ta mai fa? " Ardo ya tambayi Atuwa cikin kade kunnuwansa don jin daddadan labarin karuwar da suka samu.
"Jammu ce ta haihu."
"Jammu kuma? To meye garin gami na da ita?"
"Kayya bakacin ribar zance Ardo. Sai gani nayi abun atayaka murna ne tunda anyi zaman mutinci da kuma yalwar arzikin 'ya'ya a tsakanin ku. Gashi kuma garin ku 'daya"
"Ina sauraron ki. Wannan rawar kan da kike. Ko sunan ki aka sawa jaririyar ne?"
"Ka ji ka da wata magana. Na gayan ka abunda ta haife ne?"
"Yo ai nasan ba zai wuce hakan ba "
"Toh sanin ka bai fadi daidai ba "
"Toh uwar yan kanzagi. Ya akai?"
"Kai dai bari Ardodo. Sa goshinka bisa kasa ka fara yiwa Allah godia."
Ardo ya washe baki. Take zuciar sa ta hasaso masa kilan auren Dadaa ne ya mutu takeson jimmamman din ta roka mata shi. Ya mayar da ita dakinta.
Take ya goho ya duka yayi sujjada bayan ya dubi gabas. Wandonsa har sab'ulewa yayi. Ya janyo shi ya mayar come da jin dadi . Ya girgiza kai cike da jin dadi yace da Atuwa.
"Ai shika da nayi ba uku na shika ba. Idan ma ukun nayi ai tayi auren kisan wuta ko?Yo dama su Usmanu ne a dakin, Sai su futa daga ciki. Kice mata tadawo dakinta da zarar tagama id.."
Bai karasa fada ba. Jimmamman tasaki katuwar dariya tana jujjuya kai.
"Angon Rumalle mijin jimmamman. Na Atuwa bada kanka asare. Kaga uban iyali baban su Usmanu. Nifa du zancen nan ca zan maka Jammu ta haife 'da namiji charan chas Ardodo"
Ardo ya ware idanu. Cikin rawar jiki da baki yace da ita.
"Sharota kikayi ko Atuwa?"
"Wane irin sharota Ardo? Ba karya nake ba. Yanzun zuwan su Zaraah ai zancen haihuwar suka taho dashi. Kazo muje ku gaysa kaji da kunnen ka."
Ardo dake tsaye yana fuskantar Atuwa. Cikin manyan kaya, 'kirar riga Yar shara shudi'ya da wando . Duk kayan sun cukwikwiye saboda azabad chasar da Rumalle tayi akansa. Duk ya kara figewa ya jeme. Ya koma tamkar tsoho. Yace da ita,
"Allah dai ya kwashe miki albarka Atuwa. La'an"
"Karka soma la'ance mun. Da yardar Allah sai dai kaga kwashewar albarka akan ka. Aikin kawai." Ta karasa fada, Hadi da buga tsakiyar zaninta ta watsa hannu sama tana mai surfawa Ardo bak'ar magana.
Ardo ji yake tamkar ya fad'i kasa yayita birgima saboda tsananin yadda zuciar sa ke masa rad'adi. Wai Jammu ce ta be haife namiji?
Yaje ya dawo haka ya dinga safa da marwa akan gadar rimin kebe . Can ya samu gefen wani dakali ya zauna bayan ya zabga uban tagumi. Duk wanda ya wuce sai ya kalle shi. Ganin bayan tagumin daya zabga harda 'karin magana shi kadai. Yana nuna sama ya nuna kasa. Tamkar mai kirgen bulan gini.
Liman zai wuce yaga Ardo a zaune yana magana shi daya tamkar zaucacce. Fasa tafiyar yayi ya dawo gefen Ardo ya taba kafadun sa.
"Malam Ardo lapia kuwa?"
"Na'am jammu!"
"Jammu kuma? Malam Ardo."
Sai a sannan Ardo ya dawo hayyacin sa ya dubi liman dake mika masa hannu suka gaysa.
"Ya mutan gidan kowa kalau?"
Ardo ya sauke zuciya yana girgiza kai
"Ina cikin makauniyar kaddara liman "
"Toh pah! Ta mecece malam Ardo?"
"Mata ta dana shika a baya ce tayi aure wai harta haife da namiji yau."
"Shine kake zaune kana bayani Kai daya kamar sabon tab'i? Iyye?" Liman ya karasa fada tare da zama kusa da Ardo.
"Wacce matar taka. Ai wanda ka shika sunada yawa. Wacce daga ciki?"
Ardo ya daga kai zai yi magana sai ga Asabebiya kawar jimmamman data mata kitso. Ya zuba mata idanu yana binta da kallo harda lek'ar da kansa . Zai mike liman ya zaunar dashi cikin takaici.
"Meye haka?"
"Liman Asabebiya naga ta kara murjewa. Carkwadi. Yar na'innatuwa ce ko?"
Liman yaja dogon tsaki. Yasa hannun sa ya bige yatsun Ardo dake nuna Asabebiya .
"Mahaifinta aminin ka ne ko liman?"
"Buhun uban ka Ardon nace buhun uban ka. Asabebiya shekaran jia waccen aka daura mata aure da Ansari me kyamis a farin masallacin unguwar yan doya "
Ardo ya rafka uban salati yana jimami.
"Amma Allah ya kwashewa An.."
"Karka karasa. Kowa ma kwashe masa albarka. Dama inason zuwa wajenka zuwa na musanman. Amma tinda yauma mun hadu ai shikenan. Ina fatan kana saurarata!"
Ardo ya kada kai yana mai duban liman sosai
"Ina jinka yallabai."
"Yauwa dattawan rimin kebe na gada mai doyi dana yan farin masallacin unguwar doya. Da hayin yin bola dana yan dusar hayi. Sunyi zama sosai akan ka."
Ardo sanin ansaba hada masa kudi yasa ya mike ya zube akan gwiwoyinsa yana barbadawa liman godia.
"Godia nake liman. Karamcin ku yayiwa kalamai kadan wajen zayyano godia ta agareku. Ka ciri dubu aciki a siyawa iyali kukar miya. Akuma mikawa dattawan mu godia kafin nazo da kai na."
Liman ya yi murmushi yana kambama karfin hali da nakasar zuciya irinta Ardo.
"Ba kudi bane Ardo . Atakaice dai dattawan sunce ba Kai babu Karin aure ba bu Kuma shika. Domin ka yiyyi na farko ka Kuma yi na karshe. Sannan dole ne ka tashi ka nemi Sanaa ardo. 'dan ka namiji daka laru akansa. Allah yafika kaunar sa ya karbu abinsa. Don haka dole ma tashi tsaye akan iyalin ka. Ka cire zancen aure ko shikar sa. Domin an shatale maka layi akansa ba zaka ketare ba. Kuma sunce idan kak'i aminta da dokokin su to ka tattara kabar unguwar rimin kebe.
"Sai a biyu na biyu. Wannan magana ce zan maka jan kunne akanta Ardo. Ka cire mayatar son haihuwar 'yaya maza a ranka. Kai lalle a dole Sai ka samu namiji ? Wacce iriyar rayuwa ce haka? Kai bakasan yawan haihuwar 'yaya mata bama alkhairi ce sannan Kuma arziki ne. Banda kai da gaulancin ka ai 'ya'ya mata sunfi jin'kai. Mazan me sukeyi ? Inada su har 5, Amma kafin su kyauta ta mun. 'ya 'ya matan dake gabana sun temakamu. Hakama wadanda ke gidajen auren su duk suna kyauta ta mun fiye da 'kartin mazan da nake dasu guda biyar . Saboda haka kayiwa kanka fad'a,
"Ka rungumi yaranka da iyalinka a matsayin taka kaddarar kenan. Sai kaga Allah ya yaye maka ya Kuma buda maka lamuranka Ardo. Yanzu kamar ayace kagani akanka. Ka shikata tayo wani auren ta haifi namiji. Don haka Wannan ya zama izina agare ka malam Ardo. Allah ya jikan Modibbo ya raya wanda suke raye da albarka. Allah Kuma ya buda musu su temake ka da al'umma baki daya. Aamin,"
"A,,,min" Ardo ya amsa a rarrabe. Zuciyar sa na matukar masa zugin hukuncin da aka yanke masa.
"Da kun kyale na shika rumale. Liman a ruwan ciki na ta zauna tana mun shakar mutuwa. Ga gand'ama gand'aman yara har 3 da ta dawo dasu. "
Liman ya hankalci dimuwae da Ardo ya shigaa , don haka ya shigaa tausasar zuciyar Ardo. Har sai da ya tabbatar damuwar Ardon ta ragu sannan ya zaro nera dari biyar ya mika masa
"A kula da iyali a sayo musu kad'in miya ko dan nama ne a watsa musu . Nima albarkacin 'yaya na mata naci. Zannirah ce ta aikomin da dubu biyar dazu."
"Masha allah! Allah ya saka da khairan."
"Amin Ardo. Tashi ka tafi gida dan Allah Kuma ka rika Jan girman ka kana kokawa da matan ka ko cacar baki shysa suka renaka. Ka ja girman ka don Allah Ardo."
Ardo dai tinda ya dafe kudin sa a aljihu ya mike. Ya dauki hudubar liman wata Kuma ya zubar da ita awajen. Kai tsaye ya wuce layin yan dusa wajen gaddafi me gurasa da nama. Yasa aka yanka masa gurasa da naman sa na dari hudu ya sayo leman roba na dari ya shigaa dannawa a baka yana korawa da lemon sa.
×××××××.
Zaman makoki sosai akeyi a gidan na Capt muhd. Anata kawo abinci daga makota da yan uwa hadi da abokan arziki. Ataya Capt jimamin rashin sudeis dansa a Kuma yi masa barka da samun baby sudeis.
Kusan duk wani makusanci ga ahalin capt muhd. Sai daya shigaa cikin rudanin babban rashin sudeis da akayi. Yaron kirki mai tarbiya da dimbin ilimi. Mutuwar lokaci daya.
Maheer ya shigaa matsanancin rudanin rashin sudeis. Tunda ya zauna akan runfar da ake makokin baya tashi sai dai idan zaayi sallah ya mike yabi jam'i ya koma ya zauna. Maganganun sudeis da suka zama tamkar wasiyya kwakwalwar sa ke tariyo masa duk sakanni.
"Babban Yaya na baka amanar Zaraah na. Kai kadai na aminta da kai wanda zai rike mun Zaraah tsakani da Allah . Ka cire kiyayyar zaarah a zuciyar ka. Ka tarairayeta babban Yaya. Zaraah batada matsala saita zuciya. Dan Allah idan tahau kai ka sakko. Ka koya mata so da abunda ya 'kunsa."
Yana tunanawa Yana hawaye. Ashe wasiyya sudeis ya bar masa? Hawaye nata kwarara a fuskar sa. Dakyar ya mike cikin sanyin jiki ganin takwas harta wuce da rabi. Kai tsaye ya dau mota ya dauki hanyar rimin kebe. Wannan zuwan ma da temakon map ya karasa unguwar.
Almajiri ya tura gidan yace akirawo su Zaraah su tafi. Yaran ya shiga ya fito,
"Wai suna gidan gate. Gidan Haj Mari ."
"Kasan gidan ?"
"Eh"
"Muje ka rakani."
Almajirin ya shigaa gaban motar suka tafi har gidan Haj Mari. Yaci saa kuwa har sun fito zasu tafi.
"Zaraah...ku shigo mu tafi"
Ya fada Yana mai zuge glass din motar .
Gaban Zaraah ya fad'i don dadi, saboda da farko sai taga kaman sudeis ne. Don tanata jiran kjransa taji shiru. Ganin Maheer ne yasa tadan yamutsa fuska tamkar tamai shegen duka.
"Zaraah! Shigo mu tafi don Allah."
Ta bude gidan baya ta zauna. Yayinda raheelah tashiga gaba. Na'eelah kuma tazauna kusa da Zaraah. Ya hau titi yanata tafiya ahankali. Yanata sak'a yadda zaa sanar mata rasuwar sudeis. A haka suka karasa gidan .
An share makoki ganin dare yayi kowa ya tafi. Na gidah na gidah Kuma sun koma ciki. Yana gama parking suka fice ko kallo bai isheta ba.
Yanayin yadda ake shara adaren ne ga plates ma'aikata anata wanke wanke yasa Zaraah jin jikinta na bata wani abu. Suka shige sashen na Dadaa Kai tsaye. Yan biyu suka sheka wajen baby sunata kallon sa.
Dadaan dai tana zaune tayi jigum. Kallo daya zaka mata kasan ba lapia ba.
"Dadaa meya faru?"
Dadaa tayi shiru tana auna yadda zata sanarwa Zaraah. Harira dake gefe tayi caraf cikin azarbabi tace,
"Wannan ne ya rasu a jirgi sudens (sudeis )"
Zaraah ta saki wata gigitacciyar kara tafadi a kasa sumammiya.
"Gaskia harira an gayshe ki. Sam baki iya fadar mutuwa ba. "
Da sauri aka kwashi Zaraah sai asibiti. Likitoci suka shiga bata temakon gaggawa.. Ta farfado amma bata magana. Sai ambaliyar hawaye dake sharara a fuskarta.
Hakika zukatan mutane da yawa sun shiga rudani na halin da Zaraah tasamu kanta aciki. Ba cin abinci ba magana sai kuka kawai. Drip aketa durka mata sai allurori. Abinci ko ambata sai ta amayo dashi.
°°°°°. °°°°°. °°°°°.
Ranar suna ba'ai shagalin suna ba. Illa dai rad'in sunan da akayi a masallaci. An Kuma yi yanka. Kowa yabi jariri da addu'oin alkhairi. Allah kuma yasa ya gaji mai sunan sa.
An sallamo su Zaraah daga asibiti. Amman tamkar an sauya zaraahn baya zuwa ta yanzu. Duk wata walwala da take tadena. Kullum cikin kuka take. Da sallolin nafilfilim har abada hannunta rike da charbi tana adduoin saman aljanna ga sudeis mai kaunarta.
Kullum tana zaune a 'daki. Ba ruwanta da kowa da kuma komi. Dama sauran yan gidan sun debu Karan tsana sun dorawa Dadaa da iyalinta. Musanman yanzu data samu albarkacin haihuwa.
×××
Dadaa na zaune tana kallon baby sudeis dake saka hannun sa a baki. Yara duk sun tafi makaranta. Capt muhd ya shigaa parlorn bakinsa dauke da sallama.
Dadaa ta gayshe shi cikeda girmamawa. Ya amsa Yana mai daukar baby sudeis a hannun da.
"Su Maijidda sun shigo kuwa?"
"A'ah! Amman inajin basa nan don na je dazu kofofinsu a rufe."
Capt muhd ya girgiza kai kawai yanawa baby sudeis wasa. Kafin yace,
"Ki rabu dasu. Dama zaman TAKUN SAAKA nake dasu ai. Kema Kuma ba zasu so ki ba saboda kina kaunar su Maheer da marigayi sudeis . Kinsan meyasa?"
"A'ah"
"Saboda basa kaunar ci gabana. Sun so su halaka matata wadda tarasu. Wato mahaifiyar sudeis . Yayar babar Maheer me rasuwa. Sun so su halaka ta saboda tasamu albarkacin 'da namiji. Suna cewa wai nafuson ta. Da Kuma abunda ta haife. A shekarun baya suka shirya wani tsari da zai zama anyi hatsari gaba daya daga Jamila da Maheer da Sudeis din duk su mutu.
"Dake Allah adali ne. Sai gashi naje fandan. Ta roke ni Kan zasu kara kwana. Ashe direba an kunce notocin cikin motar anan fandan suka aika wani ya tsara komai. Washegari muka shirya Ni da ita da yaran biyu wato sudeis da Maheer. Muka dakko hanyar gidah. Wanda nayi waya dashi a karshe kawu na ne Harith. Lokacin da hatsarin ya taho mana muna waya dashi. Ya jiyo sanda motar ta kwace muka fada wani kurgurmin rami. Kai na ya bugu. Airbag takare su Maheer Allah yayi sunada kwana a gaba. Ta murfin mota ashe ya bude Jamila ta fada ramin ta rasu. Ni daganan bansake sanin inda kai na yake ba. Ashe take na shigaa coma aka kaini asibiti a Qatar. Da taimakon kawu na da muke waya shi ya gano komai.
"Maijidda da Iklima ba matan kwarai bane Jammu. Ba wai Ina gaya miki bane don kitsane su. No ki barsu da halin su kamar yadda Addayo ke fada. Badan Addayo ba wabillahil lazi dana sakesu duka. Tunda har sun san su had'a Kai suyi kokarin kashe mun mata da yara. Wadda sukazo suka same Ni da ita. Yar uwace agare Ni. Gari daya da komai. Akan kaunarta gare ni da yadda na dora raina akan Maheer saboda rashin mahaifiya da yayi. Ashe zagwan kasa suke su kashe su. Yaran su su gaji gado ko? Saboda yaransu su girma su rike companies dina ko? Saboda haka daga yau Ni da Addayo da yaran mu zaki aminta dasu. Babu ruwan ki da sabgar wa'incan. Inaso a karshe ki bani dama na aurar da Zaraah ga Maheer domin zumuncin mu ya sake kulluwa Jameelah. Banason Zaraah ta sani Kuma Kinji? Kin amince?" Ya karasa Yana mai fashewa da kuka.
Dadaa ta mike ta koma kusa dashi tana hawayen itama,
"Insha Allah bappan su . Da yardar Allah komai yazo karshe. Allah Kuma ya cigaba da kareku baki daya. Allah Kuma ya jikan su da rahama baki daya. Bappan su Zaraah ai 'yace awajen Ka. Don haka kanada dama da Kuma girman iko ga duk abunda ka zartar akanta ya halasta...."
Ya Kai mata runguma mai ratsa jiki. Dadaa na kashe shi da salo kala kala. Sai dayaji zuciyar sa ta Sarara tukun sannan ya mike ya nufi sashen maheer. Ya same shi da maganar zaraahn. Maheer bai turje ba. Don shi kansa so yake ya cika amanar sudies duk kuwa da bayason zaraahn
×××
Cikin sati na gaba, capt muhd ya tashi da kansa bisaga jagorancin Maheer suka nufi rimin kebe da Alhaji dangoje. Suka zanta da Ardo dake dama an karbi kudin sudeis don haka atake awajen bayan anyi sallar la'asar. Aka daura auren'
Maheer muhammad muhammad da amaryar sa Zaraah Ardo borkindo, akan sadaki mafi daraja💯❣️
#unedited 💯
2/7/22, 09:08 - Buhainat: _SO DA ZUCIYA!!_
_30_
_ZFF2022__
_(PAID NOVELS)_
_NANA HAFSATOU❣️_
I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p
*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune