Showing 3001 words to 6000 words out of 85942 words
Chapter 2 - SO DA ZUCIYA COMPLET Hausa Novels by Nana Hafsat Mx.txt
dake sunkuye tana daure sililfas dinta daya tsinke da leda. Sai Dadaan ce ta matsa gefe. Ita kuma ta tsaya tserere a bakin kofar dakin. Tana jefawa Zaraah dake kulle yan kayayyakin su data nunnunke a dankwali harara.
“Zaman ki a gidan nan bayada wani amfani..?
Zaarah da batasan da wa Sailuba take ba. Tacigaba da tattare komai na dakin. Hade da mikewa tsaye ta soka dan turaren tsinken kamshi data siyo jia a jikin hudar bango. Batabi takan Sailuba ba.
“Magana nake miki, Kin bawa iska ajiyata. ‘Karamar gaja.?
Sai a sannan Zaarah ta juya kanta tana kallon Sailuba, cikin zazzakar muryarta ahankali a kuma nutse. Kamar ko yaushe da bata biye musu ajikan su. Ta dan ‘kakaro murmushi hade da dan matsawa gaba.
“Me kika cewa ne yar uwa??
“Uwar ubanki nake cewa.?
Maganar sai ta bama Zaarah daria ma, Tadan dara sosai har hak’oranta na bayyanawa farare tas dasu a jajjere da wushirya. Kyakkyawan dimple dinta dake k’arawa fuskar ta kyau suka lotsa. Cikin sakakkiyar fuska da tattausan lafazi tace da ita,
“Kaka fa kika zaga, Allah ya jikan su. Ko da yake abokiyar wasa ce ai ko.??
“Oho miki uwar annamiman ci, canta matse miki da Irin kalaman ki marasa Kan gado. Nace ke yanzu ba zakisan yadda zaki yan Nepa karsu yanke mana wuta ba??
“Mezan yi wanda ya wuce na basu hak’uri yar uwa? Nayi nayi sun ki ha’kura, Banida abinda zanyi bayan haka. Wutar da ita da babu yar uwa duk d’aya ne. Mu ba abun kallo ne damu ba. Ba fanka babu komai da zamu more. To Meye na damuwa ko kuwa??
“Yar ciki da bak’i kawai...! Sailu babe rabu da ita dan Allah. Banzan bakin jininta ma ai ba zai sa su ki yankewa ba. Kullum jiya i yau. Sai tara samari masu tafiya tamkar iska zata kwakushe su dan yunwa.? Hajara ta karasa fada tana mai zazzage kayan da sukazo dasu a jaka akan tabarmar dake shimfide a kofar tsukukun dakin su.
“Gaskia ne ‘dayar biyu. Sailuba dawo nan ku nuna mun abubuwan arziki da kuka sassamo. Wannan kuma menene?? Atuwa ta fada tana daga wata leda mai dauke da sausage aciki.
“Abunnan ne fa, Ke Mama an cigaba fa, Hajara yama sunan sa?? Cewar Sailuba dake daga kai tana tunani.
“Sawsaji.. Naman gwangwani ko leda ba.? Hajara ta karasa fada tana mai jefa soyayyen sausage din a bakinta.
“Yauwa sawsaji (sausage) Soya shi ake Fa Mama. A mai Anti Hab’i ta soya mana da zamu taho. Sawsaji naman y’an gayu.? Sailuba ta ja kalmar sausage din kai kace dai dai take fa’da.
Haka dai Atuwa ta cigaba da tambayar su, Duk abunda tadakko sai ta tambayi menene shi? Su kuma suna amsata cikin zak’ewa da nuna su din yan gayu ne. Zaraah data karasa tattare dakin tsaf, Ta sauya kayanta zuwa daurin zani da hijabi. Ta sab’i sosan wankan su da sabulu ‘dan yanka ta nufi ban’dakin su na gidan dake can karshen kurya. Ta janyo langa langar da ake saya kofar bandakin ta rufe. Sannan ta koma ta dakko ruwanta dake rufe tun ebowar datayi da asubah ta shige bandaki bakinta dauke da adduar shiga bayi. Ta fyallo wankanta ta koma daki sam batabi takan su Atuwa dake yada magana ba suna tafa tafukan hannayen su.
“Wannan k’amshin fa daga ina??
Atuwa tafada tana kallon hannun Sailuba data jawo takardar da gasashen zabo ke ciki a jakarta.
“Nama ne Mama.?
“Iyye dakyau, Bara mu dandali abun arziki. Shima habin ce ta gasa muku??
“A’ah wannan tsayawa akayi a Kaduna yin Sallah, Shine mukayi wasu samari garori suka saya mana.?
“A hayye kun wanki garori.?
“Mun wanka Mama... Ke dai zakiji labari Idan muka shige ‘kurya. Nan akwai mahassada”Hajara tafada. Suka kashe hannuwa da Atuwa.
Ita dai Dadaa data karasa kauda komai nata, Ta shige cikin daki. Dai dai lokacin da su Na’eelah suka karasa sawun k’arshe na ruwan da Malam Ardo yasa su zubawa amaryar sa. Suna ajiye bokitan suka shige dakin su da sauri. Har cikin dakin Dadaa kana jiyo k’amshin gasashen zabon daya sha kayan hadi sai tashin kamshin tafarnuwa yake da kayan kamshi.
A dole Dadaa ta d’auke hankulan su Raheelah Da Na’eelah ta hanyar fara yi musu tatsuniya. Zaraah na daga can gefe tana yin aikin gidah (assignmnt) da aka basu a makarnta.....
••?. ••?. ••?.
Ana karasa kiraye kirayen sallar ishai sai ga Malam Ardo ya shigo gidan sanye cikin sabon yadi ruwan zuma. Ya dora hula kai kace yaron saurayi ne. Hannun sa rike da ledoji biyu farare na awara guda shida-shida an bad’e kowacce da yaji.
Dakin Mama Atuwa ya fara shiga ya ajiye mata awarar akan ‘ballallen benchin da suke daura jakar kayan su akai.
Atuwa dake kwance ta daga kai tana kallon sa shak’ek’e.
“Meye wannan Ardo...? Hum namiji hankaka. Wane salon munafuncin ne wannan harda leda. Ko mance dakin amaryar taka kayi ne. Jim’mam’man.??
Malam Ardo ya yamutsa fuska ya sake dakko ledar ya dire mata agabanta.
“Gashi nan awara ce.?
“Me hakan ke nufi? Ko awarar ce kayan fadar kishiya da kayo mana a karo na 9? Iyye??
“Idan ba zaki ci ba bani abuna.?
Ta wulkita idanu hade da galla masa wata uwar harara. Ta tattake ta dau ledar ji kake ‘kwas a k’irjin Malam Ardo.
“Allah ya kwashewa awarar albarka. Don bakin munafurci me zamuyi da awara guda 6? Ko ta uban uban mecece oho, Ba Za’a ci ba. Kai awara ta dama. Don kuwa mu yanzu muka sakushe hakoran mu da zabi.?
Sai a sannan Ardo ya juya ya Kalli ‘yayan nasa. Shi yama manta dasu. Dake gaba d’aya yaran sa matan ba’a gaban sa suke ba.
“Ai dole ka kalle su, kanada Iyali tamkar baka da su. Har sukayi tafiya suka dawo bakada masaniya kuma baka damu ba. Zaka fuce mun a ‘daka ko sai mun kwashi yan kallo da kai??
Ardo ya cije lebe yana girgiza kai. Kafin ya karkada yatsan sa tamkar zai mata magana sai kuma ya fuce. Dakin Dadaa ya shiga. Ya ajiye ledar awarar agabanta. Lokacin ta mike kenan zatayi Sallah.
“Angode Malam.”Ta Fada hade da sunkuya wa ta turawa yan biyun ta awarar.
Ficewa yayi bai ce mata komai ba. A zaure ya hadu da Modibbo babban’dan sa. Ya mika masa awarar Atuwa data ce bataso.
“Rike dan albarka.? Ya mik’awa Modibbo yana dashare masa baki.
Domin shi yakeso kawai kasancewar sa namiji ‘dan babbar matar sa data rasu.
Modibbo ya sa hannu biyu ya karba hade da yi masa godia ya shige Ciki. Shi kuma Ardo ya wuce waje. Dakin Dadaa Modibbo ya shiga ya gayar da ita. Su Zaraah ma suka gaishe shi. Awarar hannun sa ya mi’kawa Raheelah dake lasar ledar da suka lamushe. Suka Karb’a suna godia hade da kasafceta su cinye. Ya dan jima yana hira wajen Dadaa, Ya ajiye musu biredi dan 60 da madarar leda guda d’aya, Da sukari kullin goma, kafin ya musu Sai da safee ya shiga dakin Atuwa nan ma ya gayar da ita. Ya ajiye mata nata ledar, Ta amsa a dak’ile hade da juya masa kwakwidon gashin kanta. Batai masa godia ba, Domin kwarai matuk’a Atuwa nayiwa Modibbo madaukakiyar ‘kiyayyya saboda shakuwa da kaunar da sukayi da Dadaa data maye masa gurbin mahaifiyar sa data rasu....Shi kuwa mik’ewa yayi ya fuce dan dakin shagon sa dake wajen gidan.
<><><>
Wajajen k’arfe 9 na dare, Yan kawo bazawarar Malam Ardo suka cika layin su Atuwa da gud’a. Sai rera gud’ar suke yi. Suna shelar kawowar amaryar tasu. Yan layi dama wasu sassa na unguwar rimin kebe sai suka kawowa gidan ziyara don ganewa idanun su matar da Ardo aure aure ya ‘karo a karo na 9. Bakowa bace kuwa fyace, Jimmamman matar tsayyabu na lado dayayiwa shika 3 a baya. Kuma ‘ya ta farko ga Talle mai ‘data....
*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*
*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .
1/31/22, 18:28 - Buhainat: _*SO DA ZUCIYA_*
*_FREE PAGE:3_*
_*NANA HAFSATU_*
*_ZAFAFA BIYAR PAID BOOKS_*

___________
****Dai-dai lokacin da su sameerah, Farillatu da kuma guggun yaran mak’ota suka fara ife-ifen yiwa su Sailuba da Hajara oyo-yo. Sai yauk’i suke suna baje hanci. Su ga yan hutu da sukaje garin Suleja wajen kanwar mahaifiyar su (Mama Atuwa). Su Sameerah sai gudu suke suna tsallen murnar dawowar yayyun nasu. Dandazon sauran yara na biye dasu. Kayan su duk’un duk’un. Wasu ma pant ne kawai ajikin su ba riga. Sai dai fatan Allah ya kare kawai.
Murnar ife-ifen shelar dawowar su Sailuba ne yasan ya Mama Atuwa tsaida maganar da take na Jimmamman (Jim-Mam-man) amarya kuma bazawara ga Malam Ardo mijin su. Ta kwasa aguje tana rangad’a gud’a, Kai kace sabuwar amaria aka kawo. Nan duk murnar dawowar ‘yammatan yayan nata ne. Sailuba da Hajara.
“Ahayye biyu kyautar Allah, An buga daku anbar ku ya zasuyi daku? Sai kallo. Kaf Rimin kebe baya ku ‘yayan Atuwa. Allah dai ya kawo muku mazaje masu motoci mai nishi su aure ku...?
Su kuma sai hura hanci suke, Suka ajiye jakar ghana must go din da sukayi kama kama da hannun ta.
Kamar su d’aya da Atuwa, Yanayin fad’adden bajajjen hancin ta daya kama gam a fuskar ta. Hakan suma suka dakko kamannin nata. Sai hasken mahaifin su da sukayi suka kuma ‘kara dana bleaching. Saboda tsananin yadda fatar su ke shekin kyallin yellow yellow, Da kuma bak’i bak’i a kafafuwan su da hannayen su.
Kana ganin su kallo d’aya zakayi musu kasan yan biyu ne. Suna kama da junan su ainun. Sai dai tsayi daya bambamta. Hajara tafi Sailuba tsayi. Suka zube akan tabarmar Atuwa dake shimfide a dan tsukukun kofar dakin ta. Duk ta huhhuje taji jiki ainun tabarmar. Sai ‘daga kai take tana leka jakar kayan su.
“Wai ba wuta ne har yanzu..?? Cewar Sailuba hade da tankwashe k’afafunta. Tana mai latsa lambobin jikin yar Nokia wayar hannun ta mai chocilan (3310).
“Babu Sailuba! Yo wa zai gyara aganin ku. Sati biyu cir kenan tun tafiyar ku har wa yau baa gyara ba. Malam ya ‘karo kud’i da dubu goman da Nomau kansila i bashi. Yau aka daura auren sa da Jim-mam-man dai ta karshen layin yan tumaki. Ko bai karo aure bama kunsan sarai Sai dai mu dawwama ba wutar. Modibbo kuwa ai sai Allah ya saka masa. Da uwar data haifeshi tana nan ai datayi kukan bakin cikin ‘danta da aka mayar Kamar tandan waina.?
Nan suka hau yada maganganu. Kafin Sailuba ta mike ta karasa kofar dakin Dada. Tamkar zata bige Dadaa dake sunkuye tana daure sililfas dinta daya tsinke da leda. Sai Dadaan ce ta matsa gefe. Ita kuma ta tsaya tserere a bakin kofar dakin. Tana jefawa Zaraah dake kulle yan kayayyakin su data nunnunke a dankwali harara.
“Zaman ki a gidan nan bayada wani amfani..?
Zaarah da batasan da wa Sailuba take ba. Tacigaba da tattare komai na dakin. Hade da mikewa tsaye ta soka dan turaren tsinken kamshi data siyo jia a jikin hudar bango. Batabi takan Sailuba ba.
“Magana nake miki, Kin bawa iska ajiyata. ‘Karamar gaja.?
Sai a sannan Zaarah ta juya kanta tana kallon Sailuba, cikin zazzakar muryarta ahankali a kuma nutse. Kamar ko yaushe da bata biye musu ajikan su. Ta dan ‘kakaro murmushi hade da dan matsawa gaba.
“Me kika cewa ne yar uwa??
“Uwar ubanki nake cewa.?
Maganar sai ta bama Zaarah daria ma, Tadan dara sosai har hak’oranta na bayyanawa farare tas dasu a jajjere da wushirya. Kyakkyawan dimple dinta dake k’arawa fuskar ta kyau suka lotsa. Cikin sakakkiyar fuska da tattausan lafazi tace da ita,
“Kaka fa kika zaga, Allah ya jikan su. Ko da yake abokiyar wasa ce ai ko.??
“Oho miki uwar annamiman ci, canta matse miki da Irin kalaman ki marasa Kan gado. Nace ke yanzu ba zakisan yadda zaki yan Nepa karsu yanke mana wuta ba??
“Mezan yi wanda ya wuce na basu hak’uri yar uwa? Nayi nayi sun ki ha’kura, Banida abinda zanyi bayan haka. Wutar da ita da babu yar uwa duk d’aya ne. Mu ba abun kallo ne damu ba. Ba fanka babu komai da zamu more. To Meye na damuwa ko kuwa??
“Yar ciki da bak’i kawai...! Sailu babe rabu da ita dan Allah. Banzan bakin jininta ma ai ba zai sa su ki yankewa ba. Kullum jiya i yau. Sai tara samari masu tafiya tamkar iska zata kwakushe su dan yunwa.? Hajara ta karasa fada tana mai zazzage kayan da sukazo dasu a jaka akan tabarmar dake shimfide a kofar tsukukun dakin su.
“Gaskia ne ‘dayar biyu. Sailuba dawo nan ku nuna mun abubuwan arziki da kuka sassamo. Wannan kuma menene?? Atuwa ta fada tana daga wata leda mai dauke da sausage aciki.
“Abunnan ne fa, Ke Mama an cigaba fa, Hajara yama sunan sa?? Cewar Sailuba dake daga kai tana tunani.
“Sawsaji.. Naman gwangwani ko leda ba.? Hajara ta karasa fada tana mai jefa soyayyen sausage din a bakinta.
“Yauwa sawsaji (sausage) Soya shi ake Fa Mama. A mai Anti Hab’i ta soya mana da zamu taho. Sawsaji naman y’an gayu.? Sailuba ta ja kalmar sausage din kai kace dai dai take fa’da.
Haka dai Atuwa ta cigaba da tambayar su, Duk abunda tadakko sai ta tambayi menene shi? Su kuma suna amsata cikin zak’ewa da nuna su din yan gayu ne. Zaraah data karasa tattare dakin tsaf, Ta sauya kayanta zuwa daurin zani da hijabi. Ta sab’i sosan wankan su da sabulu ‘dan yanka ta nufi ban’dakin su na gidan dake can karshen kurya. Ta janyo langa langar da ake saya kofar bandakin ta rufe. Sannan ta koma ta dakko ruwanta dake rufe tun ebowar datayi da asubah ta shige bandaki bakinta dauke da adduar shiga bayi. Ta fyallo wankanta ta koma daki sam batabi takan su Atuwa dake yada magana ba suna tafa tafukan hannayen su.
“Wannan k’amshin fa daga ina??
Atuwa tafada tana kallon hannun Sailuba data jawo takardar da gasashen zabo ke ciki a jakarta.
“Nama ne Mama.?
“Iyye dakyau, Bara mu dandali abun arziki. Shima habin ce ta gasa muku??
“A’ah wannan tsayawa akayi a Kaduna yin Sallah, Shine mukayi wasu samari garori suka saya mana.?
“A hayye kun wanki garori.?
“Mun wanka Mama... Ke dai zakiji labari Idan muka shige ‘kurya. Nan akwai mahassada”Hajara tafada. Suka kashe hannuwa da Atuwa.
Ita dai Dadaa data karasa kauda komai nata, Ta shige cikin daki. Dai dai lokacin da su Na’eelah suka karasa sawun k’arshe na ruwan da Malam Ardo yasa su zubawa amaryar sa. Suna ajiye bokitan suka shige dakin su da sauri. Har cikin dakin Dadaa kana jiyo k’amshin gasashen zabon daya sha kayan hadi sai tashin kamshin tafarnuwa yake da kayan kamshi.
A dole Dadaa ta d’auke hankulan su Raheelah Da Na’eelah ta hanyar fara yi musu tatsuniya. Zaraah na daga can gefe tana yin aikin gidah (assignmnt) da aka basu a makarnta.....
••?. ••?. ••?.
Ana karasa kiraye kirayen sallar ishai sai ga Malam Ardo ya shigo gidan sanye cikin sabon yadi ruwan zuma. Ya dora hula kai kace yaron saurayi ne. Hannun sa rike da ledoji biyu farare na awara guda shida-shida an bad’e kowacce da yaji.
Dakin Mama Atuwa ya fara shiga ya ajiye mata awarar akan ‘ballallen benchin da suke daura jakar kayan su akai.
Atuwa dake kwance ta daga kai tana kallon sa shak’ek’e.
“Meye wannan Ardo...? Hum namiji hankaka. Wane salon munafuncin ne wannan harda leda. Ko mance dakin amaryar taka kayi ne. Jim’mam’man.??
Malam Ardo ya yamutsa fuska ya sake dakko ledar ya dire mata agabanta.
“Gashi nan awara ce.?
“Me hakan ke nufi? Ko awarar ce kayan fadar kishiya da kayo mana a karo na 9? Iyye??
“Idan ba zaki ci ba bani abuna.?
Ta wulkita idanu hade da galla masa wata uwar harara. Ta tattake ta dau ledar ji kake ‘kwas a k’irjin Malam Ardo.
“Allah ya kwashewa awarar albarka. Don bakin munafurci me zamuyi da awara guda 6? Ko ta uban uban mecece oho, Ba Za’a ci ba. Kai awara ta dama. Don kuwa mu yanzu muka sakushe hakoran mu da zabi.?
Sai a sannan Ardo ya juya ya Kalli ‘yayan nasa. Shi yama manta dasu. Dake gaba d’aya yaran sa matan ba’a gaban sa suke ba.
“Ai dole ka kalle su, kanada Iyali tamkar baka da su. Har sukayi tafiya suka dawo bakada masaniya kuma baka damu ba. Zaka fuce mun a ‘daka ko sai mun kwashi yan kallo da kai??
Ardo ya cije lebe yana girgiza kai. Kafin ya karkada yatsan sa tamkar zai mata magana sai kuma ya fuce. Dakin Dadaa ya shiga. Ya ajiye ledar awarar agabanta. Lokacin ta mike kenan