Showing 66001 words to 69000 words out of 85942 words

Chapter 23 - SO DA ZUCIYA COMPLET Hausa Novels by Nana Hafsat Mx.txt

26 Oct 2025

375

tashi. Don haka ta daure kawai ta koma ta kwanta tana runtse idanu.

Ya sake rungumota yana shakar kamshin gashin kanta.

"Alhamdulillah Ala Ni'imatul Islaam" ya furta kasan makoshi yana jan numfashi.

Zaraah daketa tunanin yadda zata zame daga jikin sa. Tashiga tutture hannuwan sa. Maheer ya hanata ta hanyar janyo bargo ya rufe su baki daya.

Ganin karatun na neman canza salo yasa Zaraah zare hannunsa da karfi. Hakan yasa Maheer ya yaye bargon ya mike kamar wani roba roba ya fuce daga dakin.

Zaraah ta koma tabi lapiar gado ta kwanta. Tana sake tabbatarwa cikin zuciyarta lalle yanada ciwon sleepwalking din daya ce.

Shi kuwa Maheer koda ya koma dakin sa. Samun kansa yayi da sakin lallausan murmishi. Bai koma bacci ba. Bandaki ya shige ya dauro alwala ya tada sallar nafila. Ya jima a sujjada Yana kwararawa Allah godia a bisa auren da yayi. Da Kuma samun albarka acikin auren nasu hade da adduar neman zaman lapia da samun yara masu albarka.


×××××

WASHE-GARI


Zaraah ta jima tana bacci bayan sallar asubah da tayi ta koma. Koda ta farka ta Yi matukar mamakin ganin yadda rana ta dallare dakin. Alamun gari ya waye.

Da sauri ta mike tashige bandaki. Wanka tayo ta tsaya cikin bandakin tana yin turaren jiki dana lalle na dukkan na yerwa incense and more . Sai data kammala tsaf tukun sannan ta koma cikin daki. Ta shirya cikin wata riga da zani na atamfar Ghana mai launin ja da baki. Batayi wata kwalliya ba . Tadai shafa man baki da kwalli. Ta dakko katon hijabi ta saka

Parlorn ta bude kofa ta leka. Caraf ta hango Maheer. Ya zauna akan kujera yana daddanna laptop din gaban sa. Ahankali tashiga tura kofar zata koma. Maheer dake kallonta ta wutsiyar idanu ya kira ta da sauri

"Zo nan yar kanwata....!"
Ya karasa babu alamun daria a fuskar sa. Don karta gano wayo ya mata daren jia.

Ita kuwa dik a 'darare take. Jiya kawai take tunanowa. Gefe daya kuma tausayin sa ya shigeta. Na ciwon sleepwalking da yake da shi.

"Ina kwana?"

"Yana kwano! Ina zakije da hijabi ko sallah zakiyi?"

Ta girgiza masa kai alamun a'ah.

"To meya na saka hijabi...uhm? Ga abinci can a dinning je ki ci. Addayo ce ta Aiko aka lawo mana. Idan kin gama kizo mu Fara karatu."

Batayi musu ba. Ta mike ta nufi dinning din ta juya baya tanacin abincin ta ahankali . Kunya gaba daya ta lullube ta. Tana karasa ci. Takoma daga can gefe ta tsakure.

"Zo nan mu Fara. Dawo nan"

Zaraah ta matsa daga can, Tashi yayi ya koma kusa da ita .

"Yar kanwata. Zamu Fara da hadith"

ARBA'UNA HADITH (21) HADISI NA ASHIRIN DA DAYA


An karɓo daga Abu Amrin ko Abi Amrata, Sufyanu ɗan Abdullahi (R.A) ya ce, "Na ce, "Ya Manzon Allah (?)! Faɗa min wata magana a cikin addinin musulunci, wadda ba zan sake tambayar waninka ba game da ita." Sai ya ce, "Ka ce, "Na yi imani da Allah." sannan kuma ka daidaitu." Muslim (#38) ya rawaito.

Ya karasa fada, Hadi da saka kasan hannun sa ya goge labban Zaraah da karamun ketchup ya makale mata.

"Sorry datti na goge miki. Afuwan! Kin hakura? Uhm?"

Ta samu kanta da daga kai alamun eh. Maheer yayi murmushi kafin yace,


"Zamu dora da SHARHI na hadisin da muka katanta' Kina sauraro. ?"

Ta sake daga kai. Don gani take tamkar an sauya shi lokaci daya . Shi Mai zafin rai da Bata rai yau shiketa tarairayarta?

"Zaraah! Kina sauraro na?"

"Eh"

"Wannan hadisi ingantacce ne, Imamu Muslim ne ya rawaito shi. Dangane da bayanin imani da Allah, wannan ya riga ya gabata a baya. A duk lokacin da aka faɗi imani, mun san
yana da rukunai guda shida, waɗanda muka yi bayaninsu a cikin hadisi na biyu, a jerin hadisan wannan littafi mai albarka. Sannan kuma da sauran abubuwan da imani ba ya cika sai da su, duk yana cikin, "Na yi imani da Allah...." Daidaituwa kuwa, a nan tana nufin daidaituwa a kan tafarki madaidaici: Kada ka ƙara, kada ka rage kan abin da shari'a ta dora ma, ka nisanci dangogin abubuwan da aka haramta maka, ka yi ƙoƙarin neman halal a cikin dukkanin al'amuran da za ka yi. Wannan shi ne daidaito. Duk mutumin da ya dace da waɗannan abubuwa guda biyu, ga imani ga daidaito, to shi kenan sai aljanna. Shi ya sa Annabi (?) da kansa, aka umarce shi da daidaito, aka ce masa (Ka daidaita kamar yadda aka umarce ka). [Hud 112]."

Ya karasa a hankali a Kuma nutse.

"Biya muji"

Karanto masa ta shiga yi. Inda tayi kuskure ya na gyara mata. A haka suka karasa. Zaman kurame yabiyo ba. Ba jimawa Yan biyu suka shigo Mata. Hakan yasa Maheer fita ya Basu waje.

Bai dawo ba sai dare. Lokacin Zaraah harta kwanta. Ya shige bandakin sa yayi wanka ya sauya kayan bacci. Kai tsaye ya sake koma dakin Zaraah. Ya zare bargon ahankali ya shige ciki.

Zaraah najinsa tayi shiru. Ahankali ya saka hannun ya fuskanto da fyskar ta zuwa tasa. A hankali ya saka tattausan labbansa cikin na Zaraah. Ya shjga Bata rantsattsiyar sumba. Wanda ya samu kansa cikin zirarar da hawaye daya rasa na meye. Da sauri ya mike ya fuce dakin sa. Don idan ya cigaba yasan Wasa zai canza.

Murmushi yayi byan ya kwanta akan gadonsa. Ya janyo paper da bjro ya shigaa rubutu Yana murmushi bayan ya saka kwanan wata da lokaci.

"At the first kiss I felt something melt inside me that hurt in an exquisite way. All my longings, all my dreams and sweet anguish, all the secrets that slept deep within me came awake, everything was transformed and enchanted, everything made sense. Zaraah. Ki temaka ki mallakamin ZUCIYAR Ki. Zan shayar da ke SO tacacce marar gauraye

Na gaskata cewa tasirin dake boye a cikin muryarki sinadari ne dake gusar da damuwa ga duk wanda ya saurareta Aduk lokacin da naji muryarki inajin tamkar a wannan lokacin aka Halicci farin ciki.

kallon farko da nayi miki na fahimci cewa kina da baiwar da Duk wani da namiji zaiji yana soki. baya ga haka ke kyakkyawace , na dade ina neman hanyar da xan furta maki soyayyata sai dai xuciyata tana jiye min wani abu, daxaki amince da syyyt da nayi farin ciki domin na dade ina fatan naga cewa mun xamo masoyan juna ni da ke, hakik babu wata makusa a gareki domin kinada kyawun da kowa zaiso yayi rayuwa dake.

RIMIN KEBE
KOTI MAI SHARIAH GALI BASHARI


" Yauwa. Ina malam Ardo da matar sa Rumalle? Ku shigo alkali zai saurari shari'ar ku." Masinja ya karasa fada ya koma cikin kotu

Yayinda Atuwa tayi gaba Kai kace itace Wadda zaai shari'ar akanta.

"Allah me alheri. Yau za a kafta. Jar ubancan kayya kai. " Sahun gaba ta samu ta zauna. Yayinda Ardo dasu Rumalle kowa Yana muzurai suka samu waje suka zazzauna..


*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar
2/17/22, 09:48 - Buhainat: ××SO DA ZUCIYA××

××NH××


××ZAFAFA2022 PAID BOOKS××


×××

   Mai shari'ah Gali bashari ya dawo daga ciki daya shigaa. Duk aka mike tsaye. Suka hada baki wajen fad'ar:

"Kottttt (court)"

Zama yayi . Bayan ya dan tsaya. Masinjan sa dake rike da wasu takaddu ya ajiye masa gabansa.

Mai shari'ah ya daga gilashi yana dan kallon mutanen dake wajen. Kafin ya mayar kan takardun. Masinja ya mike tsaye.

"Shari'ah ta gaba itace ta. Malam Ardo borkindo da mai dakin sa Rumalle.. Abisa kyautar da malam Ardo yayiwa mai dakin nasa acewarta ya bata gidan da suke ciki kyau...."

Bai karasa ba Ardo ya mike.

"Wabillahil lazi karya take ban bata gidah ba."

"Da girman Allah ya bani. Haka suke danginsu na borkindo . Wallahi karya yake ya bani."

"Zahiri 'kanzon kurege ne. Bai bata ba." Cewar jimmamman

"A hayye landantsan. Na rantse da gemun Ar" Cewar Atuwa dake daga hannuwa sama zata fara kwararo rantsuwa.

Bata karasaba. Mai Shari's ya mike saboda yadda suka gigita shi baki daya.

"Waya baku damar magana?" Cewar masinja. Da shi kansa sun hautsina shi.

Mai unguwa ya shigaa daga musu hannu alamar su dakata.

"Kai ne mai gidan? Malam Ardo ko?"

"Zahiri ni ne ya mai shari'ah"

"Wacece Rumallen acikin ku?" Mai shari'ah ya tambaya had'e da zama daga mikewar da yayi.

"Ni ce nan. Rumalle uwar su Usmanu ba. Mamallakiyar gidan Ardo baki daya."

Mai shari'ah ya danyi kasa da kansa saboda yadda dariya taso kufce masa. Ganin gaba tarin sakarmaru ne agaban sa.

"Ke kuma fa?"

"Ni ce nan jimmamman. Mai dakin sace ni ma."

"Sai ni Atuwa. Uwargidah kuma kujerar tsakar gidan malam Ardodo . Uwar su sailuba. Ranka ya dade suriki na ma anan yake aikin yamma idan ya taso. Yana auren 'yar waje na Hajara" Atuwa ta karasa fada bayan ko tambayar ta bai ba. Ta Kuma juya ta dallawa masinjan dake cewa tayi shiru harara.

"Masha Allah malam Ardo. Allah ya raya zuri'ah . Ya kuma hade kanku baki daya Aamin. "Mai shari'ah ya karasa fada hadi da kallon takardar gaban sa kafin ya sake cewa.

"Kafin sannan bari na danyi sharhi akan kyauta a musulunce. Kowa na wajen nan ya saurara ya kuma tsinci abin tsinta. Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika, kuma Ya sanya yin kyauta da kyauta-yi cikin kyawawan dabi’un Musulmi. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi, ya kasance jinkai ga talikai, kuma ya koyar da cewa kyauta da kyauta-yi ba ta rage dukiya; Amincin Allah ya tabbata ga halayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.

"Lallai, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, wanda kuma karshensa wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.

"Shin kafin mu tsunduma ga sauraron shari’ah, Na duba na kuma karanta shari’ar dake gaba dama abunda ta kunsa. Naga kuma ya kamata mu san shin za mu ga shi ma talaka ko yana da irin gudunmawar da yake iya bayarwa a karkashin tsarin na kyauta da kyauta-yi? Domin kowa yana da abin da zai iya bayarwa:

"Shi Musulmi na gaskiya yana da dabi’a da hali na kyauta da kyauta-yi komai talaucinsa, kuma komai kankantar abin da ya bayar, ana lissafe shi a wannan matsayi. Kai, ya ma dai ishe shi a ce yana da shauki a cikin zuciyarsa da tausayin wadanda suka fi shi talauci, saboda yakan yi tunanin irin halin da suke ciki na rashi da babu. Duk yadda mutum ya kai ga talauci, to yau da gobe, sai ya samu wanda ya fi shi, shi ya sa hadisai da dama suke kwadaitar da mara shi ya bayar da komai kankantar abin da ya samu don Allah, gwargwadon karfi da iyawarsa, lamarin da zai sa ya ji shi ma ya bayar da tasa gudunmawar wajen taimakon wadansu. Shi bayar da dan kadan saboda Allah, idan mutum ya gan shi a Ranar Lahira zai yi ta mamakin yadda ya kai haka don girma, saboda Allah Yana kiwata masa shi ne a wajenSa, matukar dai abin da ya bayar din ya same shi ne ta hanyar halal.

"Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Duk wanda ya bayar da wata sadaka (ko kyauta) daidai da dabino daya na halal ? domin Allah ba Ya karbar komai, sai mai tsarki (halal) ? Allah Zai karba da hannunSa na dama, kuma Ya kiwata (Ya tattale) shi, kamar yadda dayanku yake kiwon maraki har ya zama bajimi ? to Allah zai tattale shi har ya zama kamar girman tsauni a Ranar Lahira.? Buhari da Muslim ne suka fitar da Hadisin.

"Don ya kare mutane daga juya baya da kuma runtse idanunsu wajen bayarwa saboda Allah, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya bukaci su bayar da sadaka komai kankantarta. In sun yi haka, za a samu kyautatawa da tausayi da rangwame da shaukin juna a cikin zukatansu da kuma tsakaninsu. Ya gargade su da su guje wa rowa da kankame dukiya, a hana ta zagayawa tsakanin jama’a mabambanta, lamarin da yake haifar da jafa’i da bala’i a tsakaninsu, a yayin da ya ce, “Ku kange kawunanku daga Wutar Jahannama ko da da bayar da kyautar (ko sadakar) rabin dabino ne.? Buhari da Muslim ne suka fitar da Hadisin.

"Allah Yana son Musulmi ya zama na kirki, mai amfani ga al’ummarsa, wanda kuma yake taimakawa a samar da kyakkyawa kuma kwakkwarar al’umma, wadda kodayaushe tana cikin alheri, ko Musulmin nan yana da wadata ko talaka ne shi. Wannan dalili ya sa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya karsasa Musulmi ya kasance mai kyauta cikin kyauta-yi, gwargwadon iyawarsa da karfinsa, domin kowane irin aikin kwarai sadaka ne, inda ya ce,

“Kowane Musulmi lallai ne ya bayar da sadaka.? Sai sahabbai suka ce, “Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), to in mutum ba zai iya haka ba fa?? Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Sai ya yi aiki da hannunsa ya samu abin da zai biya wa kansa bukata kuma ya bayar da sadakar!? Sai suka ce, “To, in ba zai iya haka ba fa?? Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Sai ya yi kokarin taimaka wa wanda yake cikin halin kaka-nika-yi (wato yake cikin tsananin matsi)!? Sai suka ce, “To, in ba zai iya haka ba fa?? Sai ya ce, “Sai ya yi wani abin kirki, ya nisanci mummuna, wannan zai kasance masa a matsayin sadaka.? Buhari ne ya fitar da Hadisin. Musulunci ya yalwata da’irar kyauta-yi ta yadda ta hade kowane gefe na rayuwar Musulmi! Wato in ka rasa wannan abu, to da wuya ka rasa wancan! Wanda yake cikin talauci, ko kadan kada ya karaya ya ce ba shi da abin da zai bayar ko ya yi, wanda zai samu martabar mai kyauta ko sadaka. Matukar dai ya mayar da hankali wajen yin abin da za a kalla a ce madalla, to yana matsayin kyauta ko sadaka, wadda za a ba shi gwaggwabar lada a Lahira, saboda maganar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya fada, wadda Imamul Buhari ya fitar cewa, “Kowane irin aikin kirki, sadaka ne.?

"Musulunci ya bayar da tabbaci ga kowa cewa yana da gudunmawar da zai iya bayarwa wajen gina al’umma, ya karfafe ta, ya ciyar da ita gaba a harkokin yau da kullum ta yadda za ta kasance natsattsiya kuma tabbatacciya, wadda kowa zai yi alfahari da ita, alhali a karshe zai zama ya ci kyakkyawar riba. Allah Ya sa mu dace!

"Musulunci adalin addini ne mai rangwame ga matsayin kowane Musulmi. Bai dora wa kowa, sai abin da zai iya dauka. Bai cewa mutum ya bayar da dukiyarsa ma, sai dai daga abin da ya ci ya rage. Ba ya zargin mai kadan. Ya ma fi son kowa ya samu damar biya wa kansa bukatarsa, domin hannun sama ya fi hannun kasa (wato mai bayarwa ya fi mai karba matsayi)! Amma dai duk abin da ya yi saura, to (Musulunci) yana kwadaitarwar a yi kyauta da shi cikin kyauta-yi, saboda shi Musulmin kirki ba ya kankamewar abin hannunsa, ya yi rowa, domin ya koya daga addininsa na Musulunci cewa bayar da sadaka (da kyauta), abu ne mai kyau, alhali kankamewa da rowa, abu ne mummuna, kamar yadda Hadisin da Imam Muslim ya ruwaito ya fada cewa:

“Ya kai dan Adam, idan ka bayar da abin da ya yi saura na dukiyarka, abu ne mai kyau gare ka; idan kuma ka ki bayarwa, ka rike abinka, to abu ne mara kyau gare ka. Babu zargi a kanka don ka rike abin da kake da bukatarsa. Ka fara bayar da kyautar ga wadanda suke makusantan bukata gare ka. Ka sani, hannun da ke sama ya fi hannun da ke kasa (wato ya fi kyau ka bayar da ka karba)!?

"Musulmin kirki ba ya mantuwa wajen yin kyauta cikin kyauta-yi, musamman wajen bayarwa daga cikin abin da yake saura a hannunsa, bayan ya fitar da bukatun kansa da na iyalansa, ko da cikin irin ajiyar nan ta shirin ko-ta-kwana, ko kuma ajiyar da za a ce an kirga shi cikin mawadatan al’ummarsa.

"Toh wanan duk romon fashin baki ne kan kyauta da kuma kyaauta yi a musulunce. Saboda shari'ah da zamu yanke tagaba akan haka taken ta yake. Sai mu dawo Kan shari'ar ku. Na gidah da malam Ardo miji ga Rumalle. Yayi kyautar gidan sa kacokam ga Rumalle. Inda Malam Ardon ya musanta zahiri lallen gaskia bai bata kyautar gidansa ba. Hasalima shi bayada masaniyar sanda yayi kyautar bare tabbacinta. Duk kunyi alwalar ai ko?"

"Allah me alheri. Yau ana kwal landantsan. Kan balastin kayya kai. " Cewar Atuwa dake zaro idanunta kur akan mai shari'ah.

"Duk wanda ya sake magana cikin ku zai yi waje. Ku kamar kananun yara." Cewar masu tsaron kotun.

"Yauwa. Bazan iya yanke hukunci kai tsaye ba. Saboda nan kotu ce ta musulunci. Don haka kowanne cikin ku Ina nufin Ardo da Rumalle. Zakuyi rantsuwa kan tabbacin bayarwar ko akasin haka. Daga nan sai mu yanke hukunci. Domin zama daya za'ayi wa shari'ar ku. Tunda abune na cikin gidah. Sai ku sasanta sauran a tsakanin ku. Basu qurani Anas."

Anas ya dakko da hannu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login