Showing 27001 words to 30000 words out of 85942 words

Chapter 10 - SO DA ZUCIYA COMPLET Hausa Novels by Nana Hafsat Mx.txt

26 Oct 2025

363

da bamu ambata ba_

_Akwai ragi na musanman ga yan zafafa fans❤️_

_Muna bada sari, Ko sayi ‘dai ‘dai akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*

_EMAIL:yerwaincenseandmore@gmail.com ko INSTAGRAM PAGE d’inmu:yerwaincense_and_more dama nambR mu:08095215215_

_MUNA TURAWA KAYAN MU KO’INA A FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN KETARE.
100% TESTED AND TRUSTED_

•••••••••?

**INTENSIVE CARE UNIT (ICU)**

***Alhaji Harith ne a gefen kujerar dake kallon luntsumeman gadon da Capt. Muhd yake jingine akai. Wani likita ne akan sa sanye cikin kananun kaya mai dauke da farar coat. Babban daki ne daya amsa sunan sa irin na masu farcinan susa. Sai ka kwaso rantsuwa ka dire kan tabbas ba dakin asibiti bane, Domin ‘d’akin shak’e yake da kayan more rayuwa mai dauke da parlor acikin sa da wata shirgegiyar talabijin da firij.

Rubuce rubuce likitan ya shiga yi. Tukun sannan ya zaro allura ya ‘dura mata ruwa, Ya mikar da hannun capt. Muhd ya yi masa allurar a jijiyar hannunsa. Sannan ya daga hannunsa ya dora bisaga goshin Capt. Muhd din. Tukun sannan ya saki tattausan murmushi yana kallon Alhaji Harith. Cikin harshen turanci ya shiga yi masa bayani.

“Alhamdulillah! Ba bu wata ragowar rashin lapiar data dangancita baya. Sai dai ciwon kai da zai dan yi na kwanaki. Tinda Alhamdulillah tunanin sa da komai ya dawo dai dai yadda akeso, Rik’e wannan takardar, Irin abincin daya kamata ya dinga ci kenan. Sannan kuma kada adinga bata masa rai. Abu na karshe shine mun baku takardar sallama, Nanda wata 8 Idan Allah ya kai mu sai ku dawo, Allah ya kai mu.?

“Yayi kwarai matuk’a, Mungode?

“Ni zan fita ziyartar sauran wards, Idan kun tafi Allah ya kiyaye hanya ya tsare. ?

“Tohm Insha Allah, Mungode Dr. Allah ya saka muku da alkhairi Kai da sauran yan uwa ma’aikatan lapia, Hakika kun kula da mu, Kun kuma bamu kulawa ga duk abunda ya danganci rashin lapiar sa, Mungode sosai.?

Sake yiwa juna bankwana sukayi. Capt. Muhd ya rike hannunsa suna musabaha lokacin da likitan mai suna Dr. Hamoodi ya rike hannunsa suna sallamar bankwana.

“Nagode k’warai Dr. Allah ya saka da alkhairi.?

“Allahumaa Aamin Capt. Allah ya baka lapia mai dorewa yasa karshen wahalar kenan. Aamin.?

Sake gaysawa sukayi, Sannan Dr. Hamoodi ya kara bawa Alhaji Harith hannu sukayi bankwana.
Bayan fitar sa Alhaji Harith ya dubi Capt. Muhd,

“Komai normal ko??

“Kalau ma kuwa! Alhamdulillah. Ai inaga Bappah idan akace muyi yar tsere da kai sai na wuce ka. A gafarce ni.? Capt. Muhd ya karasa fada yana sakin tattausan murmushi.

“Toh Alhamdulillah Capt. Ai haka muke so.?

“Tuba nake Bappah.?

Suka saki dariya baki d’aya. Tukun sannan alhaji Harith ya taya Capt. Muhd shirya kansa. Cikin sababbin kaya kirar riga da wando na kananun kaya, Ya dora babbar coat akansa. Kana kallon sa zakasan tabbas sun hada jini da Alhaji Harith saboda tsananin yadda suke kama.

Lokacin da suka fita masaukin da alhaji Harith ya kama musu suka wuce, Sukayi sallah. Capt muhd ya jima a sujjada yana addu’oi. Yasha kuka kwarai matu’ka lokacin da ya daga hannuwa yana mai yiwa Allah godia a bisa lapia daya bashi. Bayan tsawon lokaci daya dauka acikin rashin ta.

**WASHE-GARI**

A jirgi bayan sun tashi daga kasar Qatar zuwa Nigeria. Cikin hirar da suke yi ne. Alhaji Harith ya sako zancen gidan na Capt. Muhd.

Capt muhd ya girgiza kai kawai bayan ya karasa sauraron baffan nasa, Cikin faffadan murmushi yace,

“Ai Bappah... Banajin zan ‘karasa zama da matan nan, Domin bayana suke son gani tinda basason gudan jini na. Zanma fad’awa Addayo dana koma zan sauwake musu.?

“Kar kai haka Capt. Yadda kake da hakuri ka dubi girman Allah kabar komai ya wuce. Tunda abunda suke fatan bai farun ba. Kuma kai gaka nan Alhamdulillah! Allah ya yaye maka lalurar da sanadin shirin su ya jefa ka ciki. Sai dai mucigaba da yiwa Allah godia kawai..?

“Bappah! Ni da so nake kasa baki acikin maganar nan. Nagaji da TAKUN SAAKA’r da ake da matan nan. Ta temaka ta lamunce mun na sawwake musu. Bappah! Zama da irin shedanun matar nan hatsari ne. Gaba d’aya ZUCIYAr su sun ‘kisissima mata mugayen alkaba’i.?

“Kayi hak’uri dai, Mu kuma cigaba da adduar Allah ya zaba abunda yafu alkhairi kaji ko??

“Naji Bappah! Toh Aamin Yaa Rabbi.?

“Kasan an kusan kammala komai na islamiyar nan, Masha Allah ba abunda ya rage sai ‘karashen abun rubutu da za’a sassaka da signboard din da za’a sa ka akan layi. Shima ‘CAC? muke jira suyi approving sunan makarantar kawai.?

“Masha Allah Bappah! Sannu da ko’kari, Nagode kwarai, Allah yabar zumunci ya kuma kara maka lapia da nisan kwana mai amfani.. Allahumaa Aamin.?

“Aamin Yaa Rabbi Capt. Komai da nake ai da dukiyar ka ne, Sai fatan Allah ya kara maka yalwar arzuka.?

“Aamin Bappah! Kai kuma kanayi da jikin ka da jinin ka ba, Ai kaine mai yi gaba d’aya Bappah! Yanzu kenan Bappah Addayo ba zamu sanar mata ba sai dai tagan mu??

“Eh mana sai tafi farin ciki, Allah dai ya kai mu lapia.?

“Allahumaa Aamin.?

••?

Sun dau tsawon lokuta kafin su sauka a birnin kano dake k’asar ta Nigeria, Sudeis ne ya dakko su a airport?, Yayi matuk’ar Farin cikin ganin su. Musanman Capt da yaga ya warke kalau dashi. Rungume shi sukayi a tare. Dan dadi sai da kowannen su yayi kukan farin ciki. Kai tsaye sudeis ya kai su gidan na Capt. Muhd.

Babu kowa sai Addayo, matan gaba d’aya kowacce tatafi aiki. Mazan gidan ma sun tafi ofishin su, yammatan kuma wasu na makaranta. Sashen Addayo kawai suka zarce. Fadawa mai karatu adadin farin cikin da addayo ta shiga yayi kadan kalamai su zayyano muku. An Sha kukan farin ciki, Anyi raha hade da wasa da dariya. Addayon kuwa murna uku ce ta hade mata. Madaukakiyar murnar da tafi yi itace samuwar lapiar ‘danta Capt. Muhd. Da jikanta Sudeis. Da kuma gani guda d’aya da Allah ya albarkace ta dashi wato alhaji Harith. Dukkanin su ta dau tsawon lokaci kafin ta sasu a idanun ta. Sai yau da Allah yayi.

***GIDAN MALAM ARDO(AURE-AURE)***

**Safiya ta zama rana, Rama ta zama yammaci, Yammaci ya zama dare. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha’u, Watan bikin Ardo ya shigo, Tuni ya azalzali Jimmamman ta kwashe kayanta daga ‘dakin mai sarari ta komar da kayanta ? dakin girkin da ada shi ke amadadin parlorn ta. Kujerunta uku da wardrobe dik ta sayar dasu, Saboda bazeyiwu ta sanya suba sunyiwa ‘dakin girma.

Kullum sai Ardo yace ya shikata, Ita kuma tace wallahi saki d’aya ne. Tana da igiya biyu awajen sa, Yakan jera tsaki ba adadi aduk lokacin da ta isheshi kan bazata ko’ina ba, Takance ita taga gidan zama babu inda zataje, Ai kuwa kullum Sai tasha shika shikan rashin mutincin Ardo. Itama tabi layin su Atuwa sam bata gaban sa.

Dadaa kuwa kullum cikin adduoi take, Da neman zabin Allah abisa abunda yafi alkhairi a rayuwarta, Tarasa wanda zata nema ta gayawa damuwar ta. Gashin kusan kullum Sai sunyi waya da Hajia amina ta wayar Modibbo. Sam bata taba gaya mata halin da take ciki ba, Bare dan uwanta dake k’auye guda d’aya ne dama yayi ragowa kuma shidin makaho ne.

Wasu zafafan hawaye ne suka shiga mata reto a fuskarta, Hango mata na shige da fice a dakin amaryar Ardo da za’a kawo. Tabbas yayansu basuyi sa’ar uba ba. Domin Ardon duk wacce zai aura sai ya kashe mata kudade a dan banzan bashin dayake ciwa kansa, Kowacce kuma data shigo zai rabu da ita. Tarasa meyasa matan ke amincewa auren sa, Sarai bayan sunsan adadin yawan sake saken auren da yake. Sai dai zucia kowa da irin tasa, Wasu matan akan kudi idanunsu rufewa yake.

“Toh Allah ya kyauta, Ta mu qaddarar kenan... Allah ka musanya mana da mafificin alkhairi.? Ta mike ta tada sallar da zatayi istikhara na kwanaki 3 chas. Aranar ta kammala. Ta karkade yar katifar Zaraah tayi kwanciyar ta bayan ta rufe yan biyunta da adduoi. Ta saya kofar dakin nata. Lokacin data jiyo ife ifen gudar amaryar Ardo ta 9!!! Tuni zuciar ta ta yanke mata barin gidan shine mafi alkhairi..!!

Ango Malam Ardo ya gwangwaje da amaryar sa Rumallen Nababa mai ice, Bazawara ce yar kauyen su Dadaa (unguwar kuka fanda)!! Dadan sam batada masaniyar wacece, Cikin dare dai ihun Ardo ya karade cikin gidan da unguwar baki d’aya;

“Wayyo Allah na! Kai garin dadi na nesa, Rumalle Allah ya miki albarka, Qur’anin Ubangiji na baki gidan nan halak malak, Takardun na cikin dakin Modibbo a jakar kayana. Wayyo Rumallen Nababa, Na baki kai na gabaki d’aya sai yadda kikayi..? Sambatun da Ardo keta sakarwa amaryarsa kenan yayinda suke nunawa juna farin ciki🔥

Cikin kirsa ta rad’a masa a kunne; “Dankwali yaja hula kenan??

“Yaja mana Rumalle tah, Billahil lazi dankwali yaja hulunan Ardo da gangar jikin sa hade da zuciar sa baki d’aya. ?

Atuwa dake kwanciyar bakin ciki ta jiyo su, Cikin jan tsaki hade da nanawa cinyarta da sauro yaciza duka tace,

“Bankadaddu! Yan gaba da iska, Allah ya kwashe muku albarka.?


*AL-MADRASATUL SHUHADA'I LI TAHFEEZIL QUR'AN*


***Tunda driver ya sauke ta, Sanye take cikin uniform din islmiyar, Mai dauke da kalar amber orange da white jilbab sai niqab bak’i, Da socks baka.

Yana tsaye daga barandar ajikin sa dake sama, Sanye cikin jallabiya, Baisa hula ba , Gashin kansa ya kwanta luf gwanin sha’awa. Manyan idanun sa ya sake zuba mata ya kasa dauke su daga gareta.

Zuciar sa ramkar Zata faso kirjin sa ta fado. So yake ya tabbatar wa ZUCIYAR sa, Itace ba gizo bane. Yanayin bakon lamarin daya shige sa ne ya sashi sauke idanunsa ahankali daga kanta. Yana fatan shigowar ta cikin makarantar, Don tabbatarwa idanun sa itace. Domin bai manta da manyan idanunta Dake dauke da kwayar idanun coffee color.

Tabbas sudeis ya kamu da SO DA ZUCIYAr Zaarah Ardo Borkindo... Saura kadan ya ci tuntub’e ya fado lokacin dayaga tashigo ciki ta nufi ajin da zai koyar. Wata katuwar bahaguwar zucia ya sauke mai nuna hamdala ga samun abun bege.

#unedited 🏃🏽‍♀?
#ALHAMDULILLAH MUN KAMMALA SHIMFIDA, YANZU ZAMU SHIGA GUNDARIN LABARIN, TAWAN TA UNCLE ABDULL (BILLY TAHH)❤️ TAKANCE YANZU WASAN ZAI FARA🔥
••?

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ci3ao6233sn3&utm_content=6k8ur6p

*WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉🏾 Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉🏾hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉🏾billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉🏾miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉🏾huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ƊAI ƊAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*

2👉🏾400
3👉🏾500
4👉🏾700
5👉🏾1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽
#team zafafa biyar .


___________
1/31/22, 18:40 - Buhainat: _*SO DA ZUCIYA._*

_*NANA HAFSAT_*

_*17*

_*Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*


*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb


*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS


*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw


_________________________


*_MACE SAI DA GYARA_*💃🏻💃🏻
_GYARAN MA NA KAMFANIN TURAREN:_
*YERWA INCENSE AND MORE*

*Ƴar uwa ta hanyar gyara ne kawai zaki cigaba da amsa sunanki mace hamshaƙiya a wajen miji ba tare da ya ga kin tsufa masa ba.*

_Maza garzayo ki gyara jikinki da kayan ƙawatattu kuma nagartattu irin namu na gida da suka sami haɗi na musamman da babu cutarwa a ciki. hadin bornu/chadian na kamfanin turaren YERWA INCENSE AND MORE_

*_Muna da haɗin_*

_Turaren wuta kala kala na gidah_
_khumrahs_
_Kullaccham_
_Turaren wanka_
_Turaren Kaya_
_Turaren wanki_
_turaren mopping_
_Dukkanil al’ajab (Turaren tsugunno na Matan aure kad’ai)_
_khumratul al’ajab (khumrah ta jiki ta matan aure_

_Muna Gyaran jiki_
_Na amare_
_Da masu jego_
_Da sabulai masu gyara fata_
_Turaren tsugunno_
_zumar goran tula_
_Scented hair cream and spray (man kamshin gashi da gyara gashi_

_Akwaisu kujeran tsugunno
_Dilke and halwa set_
_Burners da igniters da tong_
_turaren fesawa dana ruwa._
_wardrobe balls_
_scented pebbles_
_cotton wooly oudi incense_
_kabbasas_


_Da sauran kayayyaki da yawa da bamu ambata ba_

_Akwai ragi na musanman ga yan zafafa fans❤️_

_Muna bada sari, Ko sayi ‘dai ‘dai akan farashi mai sauƙi da rahusa. Ga mai buƙata sai ya nememu tanan 👇🏼_*

_EMAIL:yerwaincenseandmore@gmail.com ko INSTAGRAM PAGE d’inmu:yerwaincense_and_more dama nambR mu:08095215215_

_MUNA TURA KAYAN MU KO’INA A FADIN NIJERIYA DAMA KASASHEN KETARE.
100% TESTED AND TRUSTED_

•••••••••?

*AL-MADRASATUL SHUHADA’I LI TAHFEEZIL QUR’AN*

**FASLUN SALMANUL PARIS**

(AJIN SALMANUL PARISA/AJIN SU ZARAAH)

***Zaraah na shiga da sallama yan ajin da baza su wuce 20 ba daga su har sashin maza dake gefe kowanne yana kujerar sa. Ajin a tsare yake tamkar makarantar boko. Harda abun matso ruwan sha na zafi ko sanyi (dispenser) Ga locker nan kowanne dalibi da sunan sa ajikin locker din da take a matsayin tasa.

Cikin haba-haba kamar yadda Aunty Amina ta sanar da ita, Haka Zaraah ta mimmika wa matan hannu suka gaysa, Mazan kuma ta musu sallama. Kafin ta nemi kujerar dake can baya mai dauke da sunan ta a jiki taja ta zauna.

Tunda ta shige cikin ajin, Sudeis ya samu kansa da kasa dauke idanun sa agareta. Yadda take tafiya cikin nutsuwa da yadda ta babbawa matan ajin hannu suka gaysa, Shi ya sake narkar da kaunarta a zuciar sa. Ya samu kansa da jan kasan leben sa taune kana ya saki lallausan murmushi. Dai dai lokacin da ya aza kafar sa bisa kofar shiga ajin, A kuma lokacin ne Ustaz Naseem ya dosa wajen yana daga wa Sudeis hannu,

“Barka kadai ustaz.?

“Barka ranka ya dade..?

Sudeis yayi murmushi, Ya fasa shiga cikin ajin ya tsaya akofar ajin.

“So nake dan Allah ka rike ajin ustaza heekmah, Wai ba yanzu zata karaso ba sai 4:30. Na musu fiqhu, Zan rike naka ajin mu fara karatu da su. Sai ka musu fassarar kaji? Ka amince??

Sudeis ya daga kai kawai, Ya wuce ajin ustaza heekmah, Zuciar sa tamkar zata fashe. Can yaje ya fara Karanta musu surar da zasu fara, Kafin ya isowar malamar tasu. Tana zuwa kuwa yamike da sauri bayan ya kai ayah.

“Godia nake...Ustaz Sudeis!? Ustaza heekmah tamasa godia tana dashare masa baki.

Murmushin shima ya ka’karo yayi, Ya wuce ajinsa kai tsaye, Yana mai duba agogon hannun sa, Yana zuwa ya tarar Ustaz Na’eem ya kai ayah saura fassarar kawai.

**FASLUN SALMANUL PARIS**

Ustaz Na’eem ya mike ya fita, Musabaha sukayiwa juna, Sudeis ya shige cikin ajinsa, Farkon abinda ya fara yi shine sauke idanun sa akan Zaraah dake sunkuye da kanta a kasa tana karanta farkon Suratul baqra.

Cikin harshen larabci ya fara musu magana, Idan yayi sai ya fassara da turanci ya kuma ‘kar’kare da hausa.

“Sai a karshe sunana Sudeis Ibn Harith. Kuma ni ne zan kasance malamin ajin ku. Sanda bana nan Ustaz Na’eem zai wakilce ni. Zan dinga koyar daku AlQur’an da fassara da tajweed, Sai hadisi da kuma littafin bugyatul muslimin da sauran littafai, Sai wasu littafan da sauran malamai zasu koya muku. Ana fahimta??

“Ehh...?
Suka hada baki wajen amsa shi.

Dai dai lokacin da idanun su shi da Zaraah suka sarqe dana juna, Ta janye nata da sauri tana kallon bango. Gyaran murya yayi ya zauna akan kujerar sa dake fuskantar ajin.

“Zamu fara da fassarar surah-Al Fatiha, Zuwa ayoyi goma na suratul baqrah..?

سورة الفاتحة (1) ص 1
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ {1}
الْحَمْدُ للّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ {2}

الرَّحْمـنِ الرَّحِيمِ {3} مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ {4}

إِيَّاكَ نَعْبُدُ وإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ {5} اهدِنَــــا

الصِّرَاطَ المُستَقِيمَ {6} صِرَاطَ الَّذِينَ أَنعَمتَ

عَلَيهِمْ غَيرِ المَغضُوبِ عَلَيهِمْ

وَلاَ الضَّالِّينَ {7}

?1-Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai.
2; Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu; 3; Mai rahama, Mai jin kai; 4; Mai nuna Mulkin Ranar Sakamako. 5; Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa. 6; Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya. 7; Hanyar wadanda Ka yi wa ni´ima, ba wadanda aka yi wa fushi ba, kuma ba batattu ba,

Ya cigaba da fassara musu har i zuwa ayoyin da yace zasu na suratul-Baqrah. Ya kai ayah tukun sannan ya juya ya dube su bayan ya ajiye qur’anin hannun sa.

“Anan zamu dakata..Insha Allah rabbi, Gobe da yardar Allah zan karbu haddar ayoyin da kuma fassarar dukkanin su? An gane ko??

“Eh! Ustaz.?

Suka hada baki, Ciki harda Zaraah dake jujjuya abin azuciyar ta. Sam ba zata taba mancewa da sanyayyar muryar mai ‘dandanon dadi da sanya nutsuwa Irin ta sheikh sudeis ba. Matashin malamin da bata gajiya da sauraron karatun sa Kullum da daddare a atashar Quran and sunnah dake gidan rediyo. Yau Gashi agabanta tana sauraron muryar sa. Ashe rana irin haka zata bayyana agareta.

Sam batasan ta lula duniyar tunani ba, Sai ganin sudeis tayi agabanta, Ya zuba mata idanu. Gaba d’aya yan ajin kowa ya tsaya yana kallon ta.

“Meke...me ke far...Faru..faruwa ne bakya tare da mu...? Tunanin me kike? Uhm?? Ya fadi uhm din tahanyar jan kalamen,

Wanda har sai da hucin iskar bakin sa mai kamshin mint ta daki hancin Zaraah. Dadda’dan turaren Calvin Klein ya gauraye ilahirin cikin ajin da wajen sa.

“Ba.Bakomi.?

“Kin tabbata?”Ya rankwafo yana sake tambayar ta. Wanda shi kansa yakasa sanin dalilin hakan...

Daga kai tayi alamun Eh. Ya ja da baya yana mai ajiye littafan hannunsa agaban ta.

“Kizo mun dasu gobe Insha Allah, Kuma kece zaki zama matemakiyar shugaban dalibai.? Ya karasa yana mai tafiya gefen mazan ajin. Ya nuna wani katon cikin su,

“Kai ne shugaban daliban ajin nan, Class representative kenan, Ke kuma zaki zama assistant dinsa, Ya sunan ku??

“Sunana Zaraah Ardo Borkindo...? Ta fada a nutse, Cikin muryarta mai dadi.

Sudeis ya daga kai alamun Toh, ya dubi dalibin Shi kuma ya amsa sunan sa da,

“Ibrahim Ali Ibrahim?

“‘Masha Allah!! Zo class rep ka kira malamin da zai koyar da ku karatu na gaba. Ke kuma Fadimatu kizo da wuri saboda littafai na na wajen ki.. Kin...kinji ko??

Daga kai tayi alamun Eh. Shi kuma ya fuce bayan ya musu sallama, monita ya bishi a baya.

**GIDAN MALAM ARDO**

**Da sassafe Ardo ya tafi bakin kasuwa sayowa amarya Rumalle abincin karin kumallo. Yana ficewa ta je

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login