Showing 219001 words to 222000 words out of 235479 words

Chapter 74 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt

Janafty   

14 Jan 2025

16137

ta kara mgana ya Rufe bakinta da nashi Intesar bata isa ta Kauda kai ga Imran ba Itama Cikin Zumudi ta Tarbesa Lokaci Daya ta Tallafesa Tana kara Taimakamai Wajen Samun Natsuwa Cikin so da kauna da Muradi mai girma Shudewar Mintina Talatin kafin su Samu Natsuwa suna Manne Cikin Bargo Dukkansu ba kaya ajikinsu Inteesar ta yunkura Tana Fadin"Ya Imu mu je muyi wanka..!
Tafada Tana shafa Sumar kansa Daya Kara Taruwa ita tace kada ya aske Sumar tana yimai kyau kuma Tana jin Dadin wasa da ita.
Yana jinta bai ce komai ba Tana Cikin Jikisa ne ya Tusa kansa Tsakanin Wuyanta kamar mai Barci nan kuwa yana ta Sauke Numfashi ne Inteesar bata Isarsa bai Koshi ba Kari yake so..!
Jin sa yayi Dif yasa ta Motsa Tana Lekansa Ta kara Fadin"Ya Imran..!
Tafada Cikin Shagwaba dan Motsawa yayi kafin yace"Uhmmmm...!
Baki ta Tura Tana Fadin"Ka tashi muyi wanka kaifa kake min Fadan ba kyau Zama da Najasa..!
Ta karishe Fada tana Mintsininsa a Gefen Cikinsa D'an Kaucewa yayi Yana Rikota sosai Cikin Jikinsa yana Sauke Tagwayen Numfashi Tunda taji haka tasan Kwanan Zencen sai ta Fara Kokarin Zillewa Ta Mike Zaune shima ya Mike ya Rumgumeta ta baya yana Fadin"Uhm...Uhm...I need More Mah..!
Inteesar ta Kallesa Tana Fadin"Nidai A"a ka kyaleni..!
Imran ya Shagwabe mata Fuska yana Fadin"Ta ya zan kyaleki..?kin Taba jin inda Masoyi ya kyale masoyiyarsa..?kedin ce kin cika Dadi Dadin baya isata Anty Inteesarr...!
Yafada Har yana wani Juya mata Ido Dariya tayi kafin tace"Ni yaushe na Zama Masoyiyarka..?kuma wato Tunda Zakamin wayau Kai ne yau kake cemin Anty..!
Karan Hancinta yaja yana Fadin"To ke din in ba Masoyiyata ba macece ke..?
Duk Duniya ban da kamarki Kece Matata kuma Sirrina in ban miki Wayau ba..Wazai miki..?
Yafada yana mata Dariya Shagala Tayi da kallonsa Kafin tace"Ya Imran kana SONA..!?
abazata yaji mganarta sai kawai ya Tsaya yana kallonta Idonsa take kallo Kafin tacigaba da Fadin"Ban taba jin kace kana sona ba..!
Imran ya Lumshe ido kafin Yace"Nima ai baki Taba cewa Kina Sona ba..!
Inteesar tace"Ai ba sai na Fada ba Tun afarkon Fara mganarmu Na Fara Sonka..!
Imran yace"Nima ai ba sai na Fada ba..Na Fara sonki ne Tun Ranar dana Fara ganinki ban sani ba Inteesar..Sonki yayi min kamun da ni kaina bansani ba..Sagir ya Dade yana Fadamin ina sonki naki yarda da Hakan sai dai abu Daya na sani na Tsani naga wani Namiji Tare Dake bana so kowa ya Rabeki sai ni..Bana son kukanki ballatana Fushinki Rashin ganinnki Azaba ne a wajena Inteesar kin bani Wahala sosai kafin ki Zama mallakina..!
Ya Karishe Fada idonta na Cikin nashi Inteesar da gabadaya kalamansa ya Sanyayamata rai ta kasa mgana sai Binsa take da kallon Kauna kafin tace"meyasa baka Taba Fadamin ba..!
Imran yace"Kauyanci ne na Tsaya Ina I Love u..Kawai ayyuka na akanki Zai sa Ki Fahimci haka kuma ni kinsan ban wani san ya kamata ba abubuwa masu Muhimmamci Ina ganinsu a Shirme sam ban kawo Tunanin ya kamata na Sanar dake ba..!
Inteesar ta Fada Kirjinsa ta Rumgumesa kamkam Cikin Farinciki Tana Fadin"Nima Ina Matukar Sonka Ya Imu..Nima na Fara sonka Tun Farkon Haduwarmu banfara yarda ina sonka ba sai da ka kwaceni hannun yan iskan nan masu Kwacen Waya Nima ka bani Wahala..!
Take Fada tana Dukan Kirjinsa Riketa yayi yana Dariya yace"Naji An buga wasan daidai duka min bama juna Wahala..Ni dai yanzu ki bari na kara..?
Ido ta waro Tana Fadin"Ka kara me..?
Cikin Karya wuya ya shafo Kirjinta da suke kallonsa yace"Allah sau Daya zan kara..!
Inteesar tayi mai wani kallo Kafin tace"Kai fa sai kace sau Daya kana min Wayau in na yarda Allah wajen sau Uku kake karawa kayi ta yi..!
Tafada Tana Tura baki Rumgumota yayi yana Fadin"Yanzu Daya zan kara My Sweeeet Intteee..Na kara..!?
Yafada yana kallonta Kai ta Dagamai kafin yace"Kayi alkawarin D'aya..?
Kai ya daga kafin yace"Kai Intee meya kawo mganar alkawari..?
Tana Dariya tace"Ai nasan sai ka Zarce ne..!
Shima Dariyan yake yana Fadin"Ai nasan Matata mai adalci ne in na kara ma Zata yafemin..!
Da wannan Dadin bakin Imran ya Samu suka kara Komawa Ruwa Sai da ta Hada da kuka da magiya kana ya Sauraramata sukaje sukayi wanka Tare achan ma Tiolet din Tabara kawai sukayi tayi Kafin su Fito tare suka Shafa ma juna Mai suka ka kuma koma suka Kwanta suna Nane da juna Adaran dai bai kara ba ammh da Asuba bayan sun gama Sallar asuba sai da Imran ya kara kafi Siga Dadi.
Haka Rayuwarsu ta Cigaba da Tafiya Imran shi haka Salon nashi Soyayyar take mai Zafi ce sosai,bai iya Fadinta abaki sai dai a aikace Inteesar Tana ganin Abu Salo Salo A aikace ta Zama yar gata Wajen Imran ta kuma kara yardan ma kanta Shi din na Dabam kamar yadda yake na Dabam acikin Ranta..
Inteesar Ta ji Dadin Hutun Makarantar da suka samu Saboda yadda suka samu Ishashen Lokacin da suka Murje amarcinsu Imran bai so ma suka koma ba Hutun Wajen Wata Daya da kwanaki kana suka koma makaranta,Kudin Rigistration din su Ita da munari duka shi ya Biya musu na Shiga Aji Biyu,ba yadda ya iya ne kamar yace abar karatun Tunda da suka koma Lectures sosai sukeyi sai Yammah suke dawowa shi yake zuwa Watarana ya Daukosu ita da Munari ya Fara kai Munari gida kafin su wuce Wani Lokacin kuma kusan atare suke Dawowa Gabadaya dan kiban datayi na amarci Duk ta fara ramewa Ga gajiyan makaranta in ta dawo ga Girki da Laluran Miji Imran ba Daga kafa ya Saukar da gajiyan Dare ya Saukar da ta asuba to yata iya yasan Lagonta ko Ta Hanasa sai ya Lallabata ya ji Dadinsa ba ruwansa.


*****


*After 2 Month*


Bayan Wata Biyu da Daidatawar abubuwa Tsakanin Inteesar da Munari Daada ta Zame a bandaki Tayi Gocewar Kashi da sai da aka Dangantata da asibiti,Hankalin iyalanta ya tashi sosai da duka Jikokinta,gabadaya kowa da kowa sai fa sa yaje saboda jin Halin da Daada ke Ciki,ga Jikin Tsufa ga Kashi ya Tabu Baffa Kabiru da Abba da Daddy tun da abun ya Faru suka bar komai nasu suka Tafi Chan An gyara Kafar Kwananta Hudu aka Sallamota su Goggo Maimunatu ne tare da ita,Jikokinta duk sun zo su Sadam da su Sa"id ya su ya Basheer Ya Yusuf ma yaje Imran dai sai Weekend suka Tafi da Inteeear lokacin Harta su Abba sun koma Goggo Bintalo ne ke Zaune da ita Har Lokacin.
Daada kamar bakinta zai yge Saboda Murnan ganin Inteesar da Imran Cikin Farimciki da annushuwa Daman abunda take Fata kenan tayima Allah godiya ta kuma kara Godemai da ya Hada kan Iyalanta Waje Daya Kwana Daya sukayi suka Juya Inna Bintalo kam ga Gulma abakinta ba wajen Fada Tunda Mami Asma"u da Rayuwa ta gama ma kullin Goro ta Daina Daukan Wayanta Tun bayan Bikin Imran da Inteesar Data Kirata Tayi mata Tas tace kada ta kara Nemanta indai ba Alheri Zata Fadamata ba in kuma ba Daidaita abubuwa Zatayi ba ta barta da Halin Datake Ciki Tundaga Lokacin bata kara Sauraran Inna Bintalo ba.
Mami Asma"u ta gama ganin Rayuwa ta kuma Sarewa da al"amarin ta Tabbatar ma kanta ta riga ta rasa komai,ita ba Miji ba ya"ya ba Khamis ma bata samunsa kwata kwata awaya Sajida kuma ta Zama sauran Cutar Namiji Baffa Kabiru ya gama Toshe duk Wata Hanyar da zasu hadu ballatana ta saka ran in suka Hadu yaga Yadda ta koma zai Tsausayamata ta Rame ta Fige kamar ba Mami Asma"u in lissafinta yayi Daidai Tama Fita Iddanta Kenan Aure ya Haramta Tsakaninta da Kabiru sai in har ya Sake yarda an Daura musu aure gashi Tun tana Boye abun har ya bayyana yan"uwanta sun gane Sakinta Mijinta yayi mgana har wajen abokan aikinta ana ganinta ana Gulmaanta a kawayenta ma duka sun samu Labari Harda wadanda suka Tareta suka mata mgana Mami Asma"u Wlh ta yarda Duka Kuskuranta ne ammh bata san ya Zata gyara abunda ta Riga Ta gama batawa ba.
Bata da wata Hanya Hatta Hajiya Turai ta Sare tace Mami ta Kira Baffa Kabiru ta basa Hakuri Mami kunya ya Sata kasa Kiransa sai dai ta bama Umaima Sako ita kuma Data Fadamai bai ce komai ba Saboda ai bata gama Nadama ba In ta yi Nadaman da gaske Tasan yadda Zata gyara komai,Shi kanshi baya Cikin Natsuwarsa kan Rashin Sanin Halin da Khamis yake ciki,Yaso yaje tun sanda sukayi mgana da Imran sai dai wani Case ne ya Rikesa yasa ya kasa Tafiya yana so sai sun yi Covering din komai Tukunnah ya Shirya yaje Har Chan Anambara ya gani ko Lafiya..?shiyasa ya Share Mamin Asma"u yasani akwai Watarana da Zata gane Duka abubuawn Data aikata kanta suka Dawo,Shiyasa ya Kyaleta sai Ta Fahimci Kuskuranta da kanta.




Su Inteesar na Tsaka da Karatu Anty Hauwan Ya Basheer ya Ta Haihu Ya mace Murna wajen Inteesar ba"a gama sai dai Murnanta ta koma Ciki Tunda sai ana gobe suna Imran ya bari suka tafi Tare da Anty Safiya da itama Cikinta Haihuwa ko yau ko gobe da Munari da Anty Aneesa da Fareesatu da Hafsa,suka Tafi Kaduna suna shima din Inteesar sai da Abba ya Saka baki ya barta tayi kwana Biyu,Yarinya Takwaran Inteesar ne Domin taci sunan Maryama ne kuma Itama Inteesar za"a rika Kiranta ai ko Auta Tayi bajinta ita Goganta Imran sun Siyama Mejego da Baby kaya na alfarma,Domin duk wacce taci sunan Inteesar abar karramawarsa ce a zuwan su suna ne kowa yake jin Labarin Soyayyar Hafsah da Sagir da na Munari da Khalil kuma kowa yayi Na"am Tunda Sagir yaje Dutse sau Biyu,kuma ya Sa"id yayi Na"am Dashi Shi Sagir din bai gayama Imran ba Shi Sa"id din shi ya Kira Imran din sukayi mgana Anan ne yaji Sagir din yaje har Dutse Imran aransa yace Uhm da gaske Yaron nan yake Shiyasa yadda bai Gayamai yaje ba Shima bai Numamai ba Kowa yaji Abun sai yace Hadin ya kayatar Ita ma Munari Khalil din yana nan tafe Kafin Iyayensa su suzo shima ya gabatar da mganar awajensu Dr.Isa Ali Argungu
A kuma Lokacin ne aka kara Tattauna Lamarin Mami Asma"u da Baffa Kabiru,Tunda Labari ya bayyana acikin Dangi Auransu ya Mutu kowa sai Fadi yake ai mganinta keman Taga Karshenta goggo maimunatu bata zo ba ammh ya"yanta su Zainab da Karima sun je Daga Kwana Biyu sai ga yan suna da kwana Hudu Imran ransa ya Baci Inteesar sai ta Saki jiki ta Rama mai Kwanakin da bata nan ya Kwashi Dadinsa Shine yasa ya Dan Hakura Kadan Daga baya kuma sai da yayi mata Fadan nan nasa ta gama Tura Bakinta ta Hakura tunda itace bata da gaskiya.
Tsakanin Haihuwan Anty Hauwa da Anty Safiya Kwana Hamsin ne Itama Allah ya Sauketa Lafiya a asibitim Murtala,Danta Namiji kyakyawa mai kama da Imran kamar shine Ubansa yana Kama na Jini da Mahaifinsa da Mahaifiyarsa.
Haihuwan nan Kamar wani karin Haske ne a wannan Gidan Tun a asibiti Yusuf yayi mai Huduba da Imran,Masha Allah Imran baki yaki Rufuwa Ya Yusuf yamai Takwara Yaji Dadin har yakasa Boye Murnansa Inteesar sai rawan kafa Take Takwaran Gwarzonta Anty Saratu ke Tare da Anty Safiyan har suka Dawo Gida Mama Ya yusuf ya kira Tazo sukaje asibiti tare,Suna Dawowa Gida ta Saka Ruwan Zafi tayima Maijego wanka Ta kuma Gyara mai sunan Imran,nan da man gida ya Cika da Dangin Anty Safiya Abba kuma baki yaki Rufuwa Anyi jika Daddy da Baffa Kabiru sun kira sun yi barka da Fatan Alheri.
Tunda akayi Haihuwan Inteesar chan take wuni Sai Dare Imran ke Daukanta su koma Gida,da sun Dawo Makaranta nan suke yada Zango,Alhaji Alhassan da kansa yazo Har gida yayi barka ya bama mejego 50k Amtsayinsa na Uba bayan kuma akwatin Kayan Daya shako Cike da kayan Bby da Na uwar,Alhaji Alhassan ya Riga ya gama yin Nadama ya Zama Mutumin kwarai yana so ya gyara Halinsa ya Roki Hajiya Mero Gafara ita da Danginta da nashi Dangin.
Inteesar Taci Darajan mai sunan Imran da kuma Darajan Ya Yusuf yasa Imran ya Sakarmata kafa sosai tana Wuninta agidan,Shima amtsayinsa na Wanda Jariri yaci sunansa yayi rawan gani Shima akwati guda yayi na kayan yaro Inteesar kuma ta siya mai Jego atamfofi.
Anyi suna Taro sosai an tashi Lafiya Mama ita ke zuwa Tana ma Safiya wanka da Imran junior safe da yammah Mommy Taji Dadin haka Daman ta Fara Tunanin wacce zata Zauna da Safiyan sai ga Mama Abba ma Kyautar Dubu 100ya yi ma Jikansa na Farko Duniya kuma mai sunan Dansa Gabadaya Ahalin Daada sun Hadu Hatta da inna maimunatu sunzo sunan da su Inna Bintalo,kuma sai da sukayi kwana Biyu kana suka koma,Raguna uku Yusuf ya yanka ma takwaran Imran an sha Shagali sosai kam sai Fatan Allah ya Raya Imran karami.
Bayan suna kuwa Inteesar ta Gayama Aya Zakinta Domin Imran sai da ya Famshe kwanakinsa Inteeear ta Jigata sosai a Hannunsa Sai ta Fara Hadamai da kuka da magiya yake kyaleta Tunda yanzu ta Fara Zama Raguwa Tun Sunan Anty Hauwa bata jinta Daidaita Tunda suka Tare bata Taba Jini agidan ba sai dai Kafin Tarewar ne tayi period,Bata Dauka komai ba Saboda yana mata haka Shiyasa bata Damu ba,sai bayan sunan ne na Anty Safiya ta Fara Zazzabi da Amai Ta Rame duk ta Tsurr har da kwanciya asibiti lokacin da aka Tabbatar da Inteesar nada Cikin Wattani biyu da wani abu Murna wajen Imran kamar Zai Shide bai Taba Zaton Watarana zai Zama Baba ba sai gashi da kanshi ya Kira Sagir da Khalil ya Fada musu ya Kusa Zama Baba suna nan a yara Su kuma sukacemai Suna kan Hanya da yardan Allah
Samuwar Cikin Inteesar ya Zaga Dangi Har kunnen Daada,Sai Jin Dadi Take Tana saka albarka,Inteesar kuma Cikimta mai Laulayi ne ga makaranta Dole Munari ta koma Gidan Tana Taimakamata Tana ganin Abu Su Ya Imu asan ya"ya Wato na wasu ne bai Damu dasu ba ya Damu da nashi Tana kallon Rayuwa yadda Inteesar ke Zuba Shagwabanta Dama gata mai Raki Baban Urborn kuma na Tarairayanta,kuma bai jin kunyar Munari Ko ajikinsa ammh da sun Hadu ya Hade rai yana Hura Hanci Munari tace aranta Daman ai nasan Watarana Mace Zata sauya ya Imu ko bai gama Dawowa Daidai ba Watarana in ya zama uba zai dawo Daidai yanzu ma Shan Taba ya Ragesa Saboda Intee abun ya Zame mai jiki ne yasa yake sha asati sau Daya wani Lokacin balle yanzu Data samu wannan Cikin Inteesar ta kara Lalacewa Tsurfa kala kala batacin komai Daga Goriba sai tuwo sai su Fante da sauransu Imran shine da baisan Hanyar kasuwa ba ya sani yanzu Tunda zai zama Baba Munari kuma ke ta Wahala da tsurfan Inteesar Umma Daman dataji Labari tace Imran ya shiga Uku Daddy na Dariya yace ai Daman sun Hadu da sun Dace ne Dagashi har Inteesar din.
Allah ya Taimaki Inteesar basu Fara Test da wuri ba sai da tadan samu kanta Kana Munari ta koma Gida Bayan sun gama Test suka fara Jarabwwa Lokacin Laulayin yayi Sauki aman ya Tsaya suka samu hutu na Sati uku Imran yaji Dadin haka ta koma Gida tana Hutawa.


******


Baffa Kabiru ya samu zuwa Anambara Har gidan Khamis inda yake Zaune gidansa Daya mallaka Halak malak,Halin da Baffa yaga Khamis sai ya Dawo Abuja yana kuka da Idanuwansa yana Durama Mami Asma"u Allah ya isa.
Yaje yaga Khamis ya Kazance ya koma Cikin Wata Rayuwa,Shaye shaye ga Shan Giya shi yaci Uban Taba,harda Wiwi yana sha,ga Harkan mata Koda Baffa Kabiru ya isa gidan cikin maye ya iskesa ya Tara Kasumaba Duk yayi kazanta Harda mace ya gani agidan,Baffa Kabiru kuka Shabe Shabe Bai iya kwana agarim ba,Har ya baro garin Khamis baya Cikin Hayyacinsa bai san ma yazo ba tun a Garin ya Daga Waya ya Kira Mami Lokacin Tana Hanya Zata Dawo makaranar su Sajida da aka Kirata Bata da Lafiya har an kwantar da ita a Clinic din makaranta Tayi kuka sosai Data ga Halin da Sajida Take Ciki sai dai Sajidan ta nuna ma Mamin Ulcer ce ke Damunta Saboda Tana Zama da yunwa ba komai ba ta Boyemata yadda Take Tarin jini wani Lokacin Achan makaranta ta wuni sai da Taga Sajida ta koma Hostel Tayi Tayi ta Bita Gida Taki ta Fake da Sun kusa Fara Jarabawa Bata so tayi Loosing abunda bata sani ba Mami Taje ta Duba result din Sajidam sai da taji Tsoro ta kuma Tabbatar ma kamta Sajidan Rabuwanta da Imran ya tabata Gabadaya Tayi kasa sosai G dinta Low,Kowa kuma yasan Sajida da Kokari ammh Yanzu Har an yi mata Warning din Kora Daga Deparmnt Mami Asma'u ta baro makaranta cikin wannan Damuwar Tana Tafe tana Driving Tana kuka Har ta kusa Bugama wani Mota ya leko yana ta Zagimta Dayasan Halin Datake ciki Da bai Tsayama bi ta kanta ba Da yayi mata Uzuri.
Bata kai ga isa gida ba Kiran Baffa Kabiru ya shigo wayarta karo na Farko Bayan Abunda ya Faru Wata Shida Cikin na bakwai.
Da farko ta Zata gizo idonta ke mata Har ta katse bata Dauka ba sai da ya kara Kira kana ta Zabura Tana Dauka Tana Sharan Hawaye sai Fuskarta ta Cika da Alhini da Kuka Data barke da shi bayan jin Abunda Baffa Kabiru yake Fadamata Cikin Kaushin Murya"Asma"u me zan ce miki..?in nace na barki da Allah Kamar nayi miki adalci Gwara na Miki Allah ya Isa Allah ya isa Asma"u ko naji Sanyi a Raina Kin Zama Silar Tsarwata Rayuwar ya"yana da bani da kowa sai su..kin ta aibanta Imran kina Kiransa Mai Shaye Shaye Dan iska To Shi Taba Kadai yake sha D'anki gashi chan yana Kora Giya da Wiwi yana Budema Mata Rayuwarss gabadaya kinga Illah aibata D'an wani da Mugun bakin ki ya kamaki me zaki ce..?Kin Ruguzama Sajida Duka Rayuwarta Kin saka Tayi Sallama da Farincikinta In ban yi miki Allah ya isa ba Me zan ce miki..?
Wlh bazan yafe miki ba Asma"u yadda Kika sani kuka Insha Allahu kema sai kinyi mafiyin nawa..!
Ko Cewarta bai jira ba ya Datse Kiransa yabar Mami da kuka Allah yasa Kafin ta amsa Wayar sai da Ta Faka Motar agefen Hanya da Allah kadai yasan Irin Hadarin da Xata Hada kanta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login