Showing 99001 words to 102000 words out of 235479 words

Chapter 34 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt

Janafty   

14 Jan 2025

16125

kana suka Tashi zuwa Sallah Dakinta takai su tace suyi sallah ita kuma ta shiga Dakin Baban Waleed,waleeda Tana Manne dasu musamman ma Munari kamar ta santa.
Bayan ta idar da Sallah Kitchen ta Shiga ta Dora musu Dambun Cuscus na Zogala Cikin Lokaci ta gama shi suna Cikin Dakin suna Hira sai dai tazo tace su Fito suci suna ta mamaki.
Dambun yayi Dadi sukaci suna ta Santi,Sukace basu iya ba zasu dawo ta Koya musu Tace sai sun zo.
Bayan sun gama cin Abinci ne suka Dora da Zobon mai Dadi Data Hadamusu cikin su ya cika ammh Dadin Zobon yasa sai da sukaji ba Wajen Shiga kana suka Hakura.
Inteesar ta kunna Wayarta ta Kira Daddy tana Fadamai gata gidan Ya Sadam sai dai baya Gida sai Anty Aneesa Har ta bata suka gaisa Harda Umma,Daganan Ita Anty Aneesan ta Kira Anty Hauwa suka yi mgana da Inteesar ashe suna waya sosai Zumunci ya kullu Masha Allah.
Sai da sukayi Sallar La"asar kana sukayi Shirin Tafiya Tunda Ya Sadam shuru bai dawo ba,Aneesa nata Kiransa yace mata cikin wadanda suka ma aikin ido ne ya samu mtsala sai da suka kara komawa dashi su jiransa nan da Minti Talatin.
Sai dai har Ta wuce bai Dawo ba sai Inteesar tace bari su tafi Ranar Dayake gida Zata dawo ba yadda Aneesa ta iya sai dai taso yazo yaga Munari kila shima yaga abunda tagani ganin zasu tafi yasa tace su Tsaya suyi Hoto in ya Dawo Zata Nunamai haka kuwa akayi sukayi ta Daukan Hoto ta Daukesu Munari da Inteesar da yawa ta Dauka na Munari ita kadai itama Aneesan Inteesar ta Daukesu itada Munarin da Waleeda..
Kana ta Rakasu bakin Hanya suka Hau adaidaita zuwa gida ta basu 2k tace su biya mai adaidaita suka karba suna ta Godiya.
Gidan Mama suka yada Zango da suka Dawo sun gaji gashi Cikin su ya cika sun kasa Tafiya Munari bata koma Gida ba sai da Cikinta ya Sarara kana Inteesar ta rakata Gida,Koda suka je Abba ne kadai agidan Ya Yusuf da Anty Safiya basa nan Bata da Lafiya ashe Tun Safe take amai ya tafi ya kaita asibiti.
Jin haka yasa Inteesar ta zauna Har sai gabda mangariba suka Dawo Jikin nata da Sauki sai da Labari mai Dadi Tana Dauke da juna Biyu na kimanin Wata Uku Ba kunya Yusuf sai murna yake da bakinsa kuma ya Fada ma Abba.
Ana cikin Murnan sai ga Imran ya Fito Daga Dakinsa Da Sauri Yusuf ya Rumgumesa yana fadamai ya kusa Zama Baba sai alokacin Inteesar ta ga yayi Dariya Harwasu Daga Cikin Hakoransa sun Bayyana waje ya Bubbuga bayansa alamun Farincikin.
Su suka Rike Anty Safiya zuwa Shashenta suna mata Sannu Abunda yasa Inteesar ta manta da Abunda ya Faru da ita Jiya har ta kaiwa Bayan Mangariba.
Sai da su Abba suka dawo masallaci ta Tsorata ta tashi tace zata tafi Gida,Yana Dakinsa yaji Tana ma Abba Sallama Daman itace aransa yana Tunanin ta koma gida ko bata koma ba...?.sai yaji mganarta agogon Fatan Dake hannunsa ya kallah 7pm tayi Duhu ya fara Shiga Ransa ya baci ya Fito Lokacin har ta Fice Daga Falon Munari taso ta rakota tace mata ta Zauna Wajen Anty Safiya yau ma ba wayar nata agida ta barta.
Ta fito Gabanta sai fadi take tana ta Waige waige,Taji Tafiya a bayanta da Sauri ta Juya suka Hada ido dashi Sai taji wani Sanyi kamar an yi mata Gafara Tsayawa tayi tana Kallonsa yana Sanye da Riga da wando Baki da Fari,Ta lura blck and White kalansa ne Domin yawancin kayansa kalansu kenan sanan bata taba ganinsa da Manyan kaya ba Tunda ta Fara ganinsa bayan Jallabiya.
Ganin ta Shagala da kallonsa ne yasa ya Tsaya Hannayensa Cikin Aljihunsa yace"In kin gama Kallon nawa sai muje na Rakaki tunda ke baki jin mgana..!
Daga sama taji mganar sa Sai taji kunya ta Sadda kanta kasa Tana Fadin"Bansan Dare yayi bane..!
Da sauri yace"Oya muje..Bana son wata mgana kafin ki fashemin da kuka Shagwabbiya kawai..!
Yafada yana Kauda kansa dan Dariya Tayi kafin ta wuce yabi bayanta Sahu Sahu kafa kafa kamar wani mai tsa ranta Har Kofar gidan su Sagir Ita kuwa Gabadaya ta saka gane yanayinta jinta take kamar tana yawo Saman gajimare sai da suka iso kana yaja ya Tsaya ita kuma ta Waigo Tana kallonsa,Shima ya kallentan sai da ya Dauke kansa Mirmishi tayimai kafin tace"Nagode..!
Dahaka ta juya ta shiga Gida,dan Bakinsa yadan Cija kafin ya Juya zuwa Gida Aransa yana Fadin"Batajin mgana yanzu ba ban rakota ba wani abu ya Kara faruwa fa..? Da sauri ya Kauda wannan Tunanin jin har Zuciyarsa ta fara rawa.
Tana Shiga gida tama Mama sannu da gida ta Shiga Tiolet ta Dauro alwala tazo Tayi sallah bayan ta Idar ne ta Duba wayarta Taga Kiran Ya Sadam da Anty Aneesa,Da Mayen nan Khamis karamin Tsaki taja kaawai Ya Sadam ta Fara Kira ya dauka bayan sun gaisa ya Fara bata Hakurin rashin Dawowarsa tace bakomai kana ya bama Anty Aneesa ta yi mata ban gajiya Tana Tambayan Munari tace Yanzu ta Dawo daga Rakata Daga haka suka yanke kiran bayan Ya Sadam din yayi ma Inteesar Alkawarin sunan nan zuwa.
Aneesa Tayi ma Sadam mganar Munari tace"Honey ni kuwa naso ka Dawo dazu kaga wani abun mamaki..?
Yana kai Lomar abinci bakinsa ya Dakata yana Fadin"Mamakin me..?
Gyara Zama Inteesae tayi Tana Fadin"Kawar Inteesar da suka zo Tare take min kama da karamar yarinyar nan ta Hoton nan da Daada ta nuna mana adukku..!
Kallomta yayi kur kafin yace"Kina Nufin Hoton iyalan Kawu Malami..?
Aneesa ta Daga mai kai sai taga yayi Dariya yana Fadin"Daga ganin..Hoto sai kiga yarinyar mutane kice itace..?Ai da itane da Inteesar din ta Fara sanin hakan..!
Aneesa tace"To in ba itabace kamar har ta baci Wlh..Saboda haka nace muyi Hoto bari ka ganta..!
Cikin Halin ko in kula yace"Yauwa muga Hoton..!
Ta Lalubo Hoton Munarin kenan zata mikamai Waleeda Dake jikinta ta kwabe hannunta Wayar ta Fadi kasa ta Watse Ran Aneesa ya baci ta Maketa Ya sadam ya fara fada yana Fadin"Saboda Wayar banza zaki Daki yarinya..!
Cikin Kufulawa tace"in ta Lalatamin fa..? Banza yayi da ita ya Dauketa yana Lallashi ita kuma Aneesa ta Duka Tana Tattara Wayarta bayan ta Hadata Tayi tayi ta ki kawowa sai Ranta ya baci ta Shige Dakinta ta Jefa Wayar Cikin Wardrope shikenan ganin Hoto bai samu ba.


Tafiyar Mama ya tashi Ana gobe Zata tafi Taje gidansu Munari da kanta Inteesar ta Rakata ta gaida Anty Safiya wacce ke fama da kasala,da Amai kana ta gayama Abba Zataje Biki Zata bar Inteesar Wajensu Abba yace bakomai bama sai tazo ta Taambaya ba,Inteesar kamar ya take a wajensa,Munari da Inteesar sun fi kowa Murnan hakan,Washegari Tun Safe Sagir ya Raka Mama tasha tahau Motan Kaduna,Inteesar kuma sun Tafi makaranta sai da suka Dawo Munari ts Tayata Debo kayan da Zatayi amfani Dashi kafin Mama ta Dawo,Sagir daman baya Zaman gida yana Shago Abinci kuma Siya zai rika yi Shima Ranar asabar zai tafi kadunan.
Imran baisan Inteesar ta Dawo Gidansu ba sai da Sassafe ya Fito zai Tafi jogging ya ganta Tana goge Dining Abun ya bashi mamaki har tsayawa yayi yana Kallonta baki sake Data gaisheshi Abun sai ya kusa saka Inteesar Dariya ta Rufe bakinta ta Shige Kitchen da gudu Munari Dake Feran Dankali ta bita da kallo.
Daman saboda ta gansa tace ma Munari bari ita ta gyara Falon ta Goge,Ita kuma ta Soya Dankali da kwai Kada su makara Karfe 8:30am suke da Karatu,Anty Safiya kuma Lafiyan sai Hankali bata Girki a asibiti ance ta Huta sosai kafin ta fara aiki.
Kuma ta gansa Taji sanyi acikin Ranta ita kanta akwanakin nan ta rasa meke Damunta jinta da ganinta Imran ne in bata gansa ba ta rika Shiga Damuwa kenan sai ta gansa take jin Sanyi,Sabida ta gansa tazo gidan ta Wuni bata tafiya sai duhu yayi Saboda ya Rakata tasan bazai taba barinta tabi Hanya ita kadai ba Kamar ma Dakonta yake yi Data Fito zata gansa yana Binta abaya koda bazai ce mata komai ba har sai ta Shiga gida zai koma ya Lura batajin mgana ga Tsoro ga Taurin kai bayason yayi mgana ta sakamai kuka ya Lura ta Fiye shagwaba Shiyasa Ya gwammace ya Rika gadinta Kullum in tazo takai yammah agidansu.
Har ya Dawo Daga Jogging yana Mamakinta Yana Shigowa Haraban Gidan ya gansu Yusuf ya daukesu zuwa makaranta Sai da ya Shiga Gidan ne ya Shiga wajen Abba yana so ya Tambayeshi ammh ya kasa sai ya bar Abun aranshi.
Sai dai ya samu amsar Tambayarsa Wajen Sagir Tunda ya fadamai Gobe Zai tafi kaduna Daurin aure Mama ma tana chan Tun jiya Shiyasa Inteesar ta koma Gidanku maimakon ada da bayason wani ya Rabesu,sai yaji Salama da wani Natsuwar da bai taba jiba.
Washegari Asabar da kanshi ya Raka Sagir tasha akan Mashin dinsa ya Daukesa Sagir yamai Tayin zuwa yace bazai jeba bai bar wajen ba sai da Motarsu tatashi kana ya koma Gida.
Kamar yadda suka saba kwana Biyun nan Suna Falo ita da Munari suna Kallo suna Hiramsu Anty Safiya na Barayinta ita da Ya Yusuf Abba ne Kuma yanzu yana cikin Dakinsa In suka gansa sai su Natsu suna Raba ido Da ya shiga Daki sai su Fara Dariya.
Hakaman yake jin Dadin ganinta a kusa Dashi koda bazai mata mgana bane baya ma son Mama ta Dawo ace ta koma Gida,Ranar asabar da yammh Tasleem tazo ita da Mommy da Anty Saratu suka zo Duba Safiyar basu jima ba Mommy da Anty Sarati suka tafi suka bar Tasleem Datace nan zata Kwana sai Monday Zata koma Taga su Inteesar.
Suka Hade su uku suna ta Bidrinsu Inteesar ne ke jansu zaman Falo Saboda Taga Giftawan Imran Munari kuwa bata so saboda Imran bayasom Hayaniya tafi son su zauna Shashen Anty Safiya yafi susha Hiransu kala kala bamai Takuta musu.
Adakin Munari suka Kwama Dukkansu Harda Tasleem Dataki kwana Shashen Anty Safiya.
Washegari Lahadi suka zage suka gyara Gidan
Inteesar ta matsa ma Munari su Zauna afalo su kunna Kallo,bayan sun Karya Abba na Samam Dining shi da Ya Yusuf suna Cin Abinci suna Hira su su kuma suna saman kujerin falom Sun kunna Arewa24,lokacin ana Maimaicin kwana Cha"asin suna ta Hayaniya Munari da Tasleem nata bama Inteesar Labarin Film din Tunda ita ba wani Kallo take sosai ba Daman Saboda Taga Imran ne yasa ta Mtsa musu su Zauna.
Yana cikin Dakinsa Hayaniyarsu duk ta Cikamai kunni Tun yana Sharewa Har Ransa ya baci ya tashi ya Fito a Fusace Jikinsa ko Riga babu Daga shi sai 3Quater,kamar Walkiya suka gansa gaban Kayan kallon ya Zare Soket din gabadaya ya yar a kasa ai kafin ya juyo Munari tayi ta kanta Tasleem ma ta mara mata baya Inteesar ne ta Tsaya tana Raba ido Hararanta yayi kafin yace"Bar nan Wajen..!
Da sauri ta Mike tana Kokarin Hana kanta Dariya yana kallonta aransa yace"Shikenan ta gama Rainani.!
Abba suna gefe suna kallobsu Abba ya Sa baki ya Kirashi ya Juyo yana kallonsa Cikin Mirmishi yace"kai da idon sani da bako Duk Dayane awajen ka ko Imran..?
Dakuna Fuska yayi kafin yace"Abba Hayaniya suke min akaina..!
Yusuf yace"Ai ba Dakinka suka shiga ba Ishasshe..!
Bata rai yayi ko mgana bai kara ba Ya shige daki har yana Bango Kofa Yusuf yayi Dariya yana Fadin"Na tabo Yaron Abba..!
Mirmishi kadai Abba yayi bai kara mgana ba.
Su kuwa Shashen Anty Safiya suka koma suna Sauke Numfashi Munari Ba bakin mgana Inteesar na Dariya ta Daka mata Duka tana fadin yau daya Daketa kanta zata rama ta kusa jamata masifarsa Ita dai Dariya kawai takeyi Burinta ya Cika Tunda ta gansa,sai da yanayin Data gansa ayau din ba Riga Gabadaya yasa ta jin wani iri Imran yana da Cikar Zatin da kowacce Lafiyayyiyar mace in ta gansa ahaka Taji wani iri hakan ne ya Faru da Inteesar wacce ta Wuni Tunaninsa bai bace mata ba.
















*Shakira*
3/22/22, 23:07 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*


*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty��*






       *🅿�29*


Har garin Allah ya waye Inteesar bata kara saka Imran a idonta ba duk da kuwa yadda taso ta kara ganinsa,Gashi yau din ta kama Monday ne suna Class da safe shiyasa suka Shirya da wuri Ya yusuf ya daukesu yakaisu kafin ya wuce wajen aiki basu kuma dawo ba sai yammah Tun suna makaranta Inteesar sukayi Mgana da Umma ta fadamata Su Mama sun kamo Hanya tun dazu shiyasa da suka dawo nan ta Tsaya tunda sun dawo gama Sagir nan a kofar Shagonsa shida Imran suna mgana.
Sun gaisheshi Sagir ya amsa cikin Fara"a yana Tambayansu karatu sukace Alhamdulillah,Inteesar na Tambayansa ya Kaduna yana Fadamata Hargidansu yaje Imran na Gefe ya Kauda kansa yau din ko sau Daya bai kalleta ba bayaso Zuciyarsa ta Saba da kallonta alhalin yau zata koma Wajen Mama,lokacin da Sagir ya Kirasa ya gayamai sun dawo bai ji dadi ba ko baya ganinta yana Samun Natsuwar Sanin Tabbas Numfashinta yana Kusa da nashi,yanzu din ma ita yake son gani yasa da Sagir ya kirasa yace sun dawo ya Fito suka Hadu Tunda yaga Munari bata dawo ba ya tabatar da suna makaranta in ma kuma sun dawo suna gidan su Sagir ya Tabbatar ma kansa zai ganta..
Har suka wuce cikin gida kansa na kallon wani waje,Duk da Satan kallonsa da Inteesar din Tayi tayi bata Samu Nasara Hada ido dashi ba.
Sagir na lura dasu acikin Ransa ya Dade yana mamakin wani abu Shi dai bazai ce soyayya suke yi aboye ba..?sai dai ya Fara Lura da wani abu ko Rakotan da Imran yake yi Sagir na ganinsu bai dai taba ma Imran din mgana bane sai shi kadai yayi ta mamaki yasan waye Imran ya Tabbata Baya abunda Ransa bai so ba Bamai sakashi yayi abu Dole duk abunda yayi ko ya aikata yayi Niyya ne kuma Ra"ayinsa ne Sai dai in ya Tuna Kaifin Imran sai yaga da kamar Wuya ace Soyayya suke shi da Inteesar sai dai yabar abun acikin Ranshi ya zura musu ido yana Bin Duka Takunsu itama ya Lura da kallon Data dinga bin Imram din dashi kallo ne na samun Salama da sukuni ya shiga Rudani shiyasa ya kasa Dora komai a inda ya dace ya bar Lokaci ya bayyana komai.


Tare da Munari suka shiga gidan tayi ma Mama sannu da zuwa,bata wani jima ba Inteesar ta Rakota Kofar gida,Sukayi sallama da cewa sai gobe Inteesar zata zo ta kwaso kayanta Leda baka karama a hannunta cike da Goriba da gyada Tsaraban Mama ce ta bata ta kai gida,Lokacin da ta rako Munari Daga Sagir din Har Imran din sun tashi Daga wajen har Leke tayi bata Hangosu ba ajiyar zuciya ta Sauke Ranta duk ba Dadi yau data bar Gidan su munari batasan meke damunta ba ita kanta abunda ta sani Shine Imran yana cikin Ranta da Tunanin wanda komai take sai ya Fado mata arai ganinsa kuma Tamkar karin kuzari ne da Farimciki agareta Rashin ganinsa kuma sai taji gabadaya batajin Dadin jikinta da Zuciyarta tarasa Dalili sai dai ta Danganta haka damai kula dakai kaima ka Kula dashi ko bakomai Imran ya mata komai arayuwa Tunda ya ceci Rayuwarta.
Sai washegari da suka dawo makaranta taje ta kwaso yan kayanta ta Dade agidan saboda Tasleem na nan Har yanzu bata koma ba,Anty Safiya Taji sauki sosai Sai dai Rashin cin Abinci komai taci sai ta dawo dashi Sai dai zuwa in an kwana Biyu Laulayin yabi jikinta.
Tasleem da Munari suka rakata Har gida da kayanta,tayi ta waige waige agidan su Munari bata ga Imran ba Shi kuma ya ganta Saboda yana Haraban Gidan Lokacin da suka Fito bayaso su Fahimci ya tsayane kallon Inteesar yasa Lokacin datake waige waige ya Boye jikin Motar Yusuf har suka Fice daga gidan yana Kallonta,yana jin kamar yaje ya Riketa Kada tatafi karamin Tsaki yaja acikin Ransa ya rasa Meke damunsa..? Abubuwansa bama raguwa sukeyi ba sai ma Karuwa kan baya.
Haka suka cigaba da Karatunsu cikin maida Hankali Tasleem Sati Daya tayi ta Koma gida Tunda Anty Safiyan ta Warke sosai har tana aiki ma da kanta,Munari kuma basa zama sai Weekend tun safe in suka Tafi makaranta sai yammah basu da wani Ishashen Lokaci.


******


*Bayan sati daya..*!


Yau Alhamis tunda sai 6pm suka Dawo Daga makaranta tun safe sun Wahala daga Newsite suka tafi Class Oldsite,gabadayansu sun dawo jikinsu na Ciwo shiyasa yau kowa ta wuce gida.
Inteesar sai dai tayi wanka ta gasa Jikinta kana ta iya shan Ruwan Tea domin Karatu bai barsu sun Tsayama cin wani abu yau a makaranta ba.
Kwance take kan gado Tun bayan data idar da Sallar Isha"i take nan Zube kamar kayan wanki tagaji kafafuwanta Ciwo suke mata sosai inda zata samu mai mata Tausa da taji Dadi sosai ido kawai take Lumshewa ga barci Tana ji ga gajiya data Lullubeta ta Saukar mata da kasala.
Wayarta ta Dauko Data Tuna da wani abu Dazu suna makaranta ta Dauki Wayar Munari ta saci Lambar wayar Imran Bata sani ba Kwanakin nan bata ganinsa koda gidan taje ballatana ta Rage zuwa saboda Wuni suke Zungur acikin makaranta..
Haka kurum take son ta adana Lambarsa acikin Wayarta ko bazata Taba Kiransa ba Zuciyarta ta aminta da Hakan sai dai me..! Yadda ta kurama Lambar ido haka take ganin Gilmawar Fuskarsa ta cikin Wayarta,Kurama Fuskar wayar ido Tayi kowani Dakika jikinta na kara Saki Cikin yanayin kasala..? Meke Faruwa dani ne..?
Bata samo amsar tambayanta ba Hannunta ya kubce ta Danna ma Imran kira batare data ankara ba da Sauri ta Mike tana Shirin kashewa sai dai me...? Kiran Tuni ya shiga har ta fara Ringing gabanta ya yanke ya kanta ta Dafe kanta Dayake Saramata Jikinta ya Fara rawa bata da kwanan Amin taji ya Daga Kiran duk da kuwa Bai Taba Daga Bakuwar Lamba ba.
Yadda take kwance Tana Tunaninsa Haka shima yake kwance yana Tunaninta Sai dai shi yana Rage ma kansa wasu abubuwan in ya Busa Sigarinsa yanzu ma Tabance a Hannunsa yana Busawa cikin kwarewa yana Kwance ya Kishingida da Filo,Dagashi sai bakin dogon Wandojikinsa bako Riga kwantancen Gashin Kirjinsa mai Santsi ya kwanta Sai kyalli yake..
Yayi mamakin ganin bakuwar Lamba Tana Kiransa shi ba wanda ya sani masu Kiransa Daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login