Showing 207001 words to 210000 words out of 235479 words
Chapter 70 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt
bata isa ta Sani Kaffara ba..!
Abba ya Bude baki kafin yace"Har nima ko..!
Cikin Dakuna Fuska yace"Ni fa Abba ban ce kai ba..!
Abba ya gyada kai yana Fadin"Ka dinga dai Hakuri kai Babba ne ka Girmeta..Ka Rika Tunawa sai ka Sadda kan ka wani Lokaci ita yarinya ce akwai kuruciya Tare da ita..!
Imu Hade rai aransa yana Fadin Wato ya Sadda kai ya Zama Sakarai Allah ya Tsareshi..!
Abba yace"Yusuf zai kawota..Zan mata Fada kada ka mata wannan Hargagin naka nasan Halinka..!
Imran ok kawai yace ya Katse Kiran Ransa na baci kokarin ma Daidaita kansa yake In yace abu baya so kuma ana Damunsa akai Abba fa da kansa yace kada su dawomai Gida nan kusa Shi mutum ne Dake Daraja Kalaman mutane masu Daraja awajensa Musamman Abba Shi bama da Wata Manufa yace mata kada taje ba ya bari ne sai Abba ya nemesu da kansu suma su Rama bacin Ransa Daya daya Dawo bai ganta ba wato ke je din Taje din Sai Taga abunda zai Faru..!
Abba Fada yayi ma Inteesar Sosai Tayi Narai Narai kana Abba ya Umarci Ya Yusuf Daya maidata Gida Tace Munari Tazota Rakata Munari tace Allah ya Tsareta Ta Rakata Ya Imu ya Hada da ita,Tana ma Rokonta Kada ma a bayaninta ta Kira sunanta
Inteesar dai Tasan yau sai ta sani da Fada Ya Yusuf ya Dauketa ya kaita Gidan ya kulle gidan ta Ciki sai da Ya Yusuf ya Kirasa a waya kana ya Fito ya Bude mata bai Shigo da Motar ba Daganan yayi musu Sallama ya Juya Imran yana wani Cin mgani aransa yace Yau Inteesar ta Zama nama kenan..
Shi ya Tsaya Rufe Gidan ita kuma Tayi Sadaf Sadaf ta Shige Cikin Gidan Tana Kokarin Shiga Dakinta ya Shigo Falon Cikin Dakiyarsa yace"Zo nan..!
Cak ta Tsaya gabanta na Fadi kafin ta Juyo bata iya Dagowa ba kanta na kasa Tana wasa da adon Gyalen dake Jikinta Daga sama Har Kasa ya Kalleta Kafin yace"Sagir bai baki Sako ba..?
Kai ta girgizamai Cikin Dakuna Fuska ya Danna ma Sagir Kira ta Wayar Dake Hannunsa Buga Daya ana Biyu ya Daga Yana Fadin"Ango kasha Kamshi..!
Imran yayi Tsaki yana Fadin"mallan ina Aikin da na baka..?
Sagir yace"Wani aiki kuma da Daddaran nan..?
Imran yace"Hijabin da na baka kudi a Dinkama MARYAM..!
Sagir yace"Au na manta kasan bani ke yi ba Kasuwa nakai Wajen wani abokina yana Dinkasu kala kala bari gobe zan Tabosa naji ko ya gama Hala Baka son Tana saka Mayafi ne..?
Banga Laifinka ba kada Maxa su kalle ma yar babynka..!
Imran Tsaki yaja ya Datse Kiran Yabar Sagir da Dariya Inteesar na Gefe Tana Sauraransa Zama yayi saman Kujera ya Dora Kafa Daya kan Daya yana Sanye da Riga da Wando Fari da baki.
Kallonta yake yi yana Kokarin Daidaita kansa Cikin Kaushinsa yace"Yaushe kika Fara rainani da Har Zan ce kiyi abu kiki yi..Sai abunda kika ga Dama Zakiyi..?
Yauahe muka Fara wannan Dake..?
Ya Fada Cikin Tsawa da Daga Murya Inteesar da Tuni Idonta ya Ciko da Hawaye ta ce"Kai fa..kai fa kace naje..!
Cikin Hararanta yace"Yaushe nace kije..?cewa nayi ki je din Shine kuma Saboda Tsabar kin Raina ni sai kika je din ko..?
Inteesar na Sosan Idonta tace"Naji to kace naje kuma...!
Ransa ne ya kara baci ya daka Mata Tsawa yana Fadin"Shup up anan Wajen in kika kara mgana Kika Harzukani Zan tashi nayi kasa kasa Dake anan Wajen..!.
Jin haka yasa ta Toshe bakinta da Mayafinta Tana Hawaye bata son Fada a Rayuwarta.
Cikin Fushi yace"Bana so..Bana so..Ina mgana kina mgana Raini ne..Zaki cemin ke bakisan gatse bane..?da zaki kwashi Kafafu ki Tafi..?Kina Biyema wannan yarinyar ko..?munari Daya kuke da ita..?ke fa matar aure ce nan ne gidanki itama Chan ne gidansu Ammh baki da aiki sai Biyemata sai anyi mgana Kice Munari Munari kaza kaza..Munarin Daya kuke da ita nace..?
Yafada Cikim Tsawa ai Sai Inteesar ta Saki kukanta cikin kukan Tace"Ni bansani ba..Wlh bansan Gatse kamin ba..kana ta min Fada..Ni bana son Fada..!
Take Fada kafin ta Shige Daki da Gudu Tana kuka Baki ya Saki yana kallonta Wato ita batasan Fada..?to ya barta ta Cigaba da iskanci kenan bai Mata Fada ba,daya Daga Cikin Illan Auran yara kenan Yanzu in babba ce Taya ya Zaka Xauna ma kana mgana..?ai tasan abunda ya Dace da ita Soyayya batayimai adalci ba Data saka ya Fada soyayyar yarinya karama Datake Neman ta Sauya shi Daga Imran dinsa Zuwa Wani Imran din na Dabam
Yana Jinta Tana kuka yayi banza da ita In bai rika mata haka ba Watarana Da mganarsa Zata Rika ja tana yarda taga Dama Kwanjinsa bai Hana in Anyi ba Daidai ba ya magantu Soyayyat taci kaza kazanta alokacin in Komai ya Dawo Daidai sai a Tuna.
Yana Aiki Bisa Laptop dinsa yaji Har Tana jiniyan kuka kamar Wata karamar Yarinya.
Da Sauri ya Mike Ransa na Baci ya Shiga Dakin afusace kan gado ya ganta ta Dunkule Tana kuka kamar ya Daketa Cikin Fusata yace"Na Dake ki ne..?Kukan Dadi kikeyi kinsan Allah in baki min Shuru anan Wajen ba Na Tako Inda kike sai nayi kwallo Dake Nagani kukan Jini Zaki yanzu ko na Hawaye..!
Ai jin haka yasa Kaji Inteen Daddy Tsit Tasan zai aikata Kyafci yayi ya Fice Daga Dakin Ta rakasa da Harara Damam kukan Tabara ne afili Tace"Ko ma ya Lallasheni ina kuka.!.tafada Tana Tura baki Ranar Bai kara ganinta ba da Safe mahar ya Fita bata Fito ba aransa yace in na Nemeta zata Rainani ne gwara na Kyaleta ai itace Tamin Laifi da Wannan Tunanin ya Fita Batunta mai Dade a Office Dayake asabar ne wani aiki ma ya karisa Daganan Shagon Sagir yaje suka sha Hira bai bar Sagir yayi Salama ba sai da sukaje suka karbo Dinkin Hijaban Inteesar matar mallam Imu ce yadi Hudu Hudu ne Har yana jan kasa Mama Tayi Danwake ya Shiga Har Ciki Suka gaisa suka ci Danwake shida Sagir yana ganin Gidansu yaso kamar ya Shiga sai kuma ya fasa kada Intee taji tace Ita ya Hanata Shiyasa ya Fasa shiga ammh sun Hadu dasu Abba a Masallaci Ya Yusuf nata yimai Tsiyan mai Yaji ya Daka Borkunu Imun Abba..
Bai ce komai ba ya Kara Hade rai kamar an aikomai da Sako mara Dadi a an anguwar yayi sallar Isha"i kafin ya Koma Gida Inteesar na Cikin Daki bata Fito ba ya Damu Yana so yaji Lafiyarta ya barta itaa kadai agida Tun Safe.
Ya Kirata bata Dauka ba ya Turamata sako.
"Kina lafiya..?.
Ta karanta Ta Sharesa Wata Zuciya Tace ka kama kanka Imran da Girmakka Yarinya na neman janka a kasa da wannan Tunanin ya Fita Batunta ammh fa Tana Ransa Ranar Lahadi ba aiki yana Gida yana Daki yaji Fitowarta da Safe ta Shiga Kitchen yana jin haka ya Fito Falo ya Zauna Saboda yaji kamar Girki take yi Sai da Ta gama ta Fito Dauke da Filet Shake da Indomie,Ko Gaisheshi batayi ba Bakinta agaba ta Shige Daki Dauke da Goran Ruwa ta kasan ido ya Kalleta Dariya ta kamsa afili ya Furta"Imu ka Tabo Autar Daddy sai Allah..!
Kitchen din ya shiga yaga iya Cikinta ta Dafa,Cikinsa ya Shafa ya Lafe sosai yana jin yunwa Inteesar Muguwa ce ko Ta Dafa dashi in bazatayi mai mgana ba ko acikin Kitchen din ta ijiyemai yazo yaci bakomai.
Hakanan ya Dafa Ruwan zafi yasha Tea sama sama ya Dawo Falo Laptop dinsa ya Dauko ya Fara aiki Domin ya Daukemai Hankali.
Ranar haka suka Wuni Inteesar Har Kai take kaudawa bata son kallonsa Imran shima ya Mazaye baya bari Ta gane ya ganta shima ya nuna mata ya Fita Zafin kai.
Washagari Monday Ranar ne Last Paper dinsu,Karfe 10:00am suke da Jarabawan Zai Rigata Fita Shiyasa da Safen ya Taka Har Dakinta tana Kudundune Cikin Bargo ta Rufe ido kamar mai barci batasan ya ganta ba Tana Danna Waya tana jin Sallamarssa Ta Tusa wayar Cikin Bargo Tana Barcin karya.
Bai bi ta kanta ba ya Ijiye mata Ledan Hijaban yana Fadin"Ki yi amfani dasu..Bana son na kara ganinki da Mayafan nan..!
Yafada Lokaci Daya yana Dora mata Dari Biyar saman ledan Ya kama Hanyar Fita yana gyaran Zaman Briefcase din Dake hannunsa.
Yana Fadin"Kiyi maneji ba kudi a Hannuna..!
Daga haka ya Fice ya Turo mata Kofar sai da Ta Tabbatar da ya bar Gidan kana ta Mike Zaune ta jawo Ledan Tana Dubawa ai data Gwada sai da ta Rike baki Tana Fadin"Tabdijam..Ni ce Zan saka wannan kamar wata Malama..!
Tafada Tana kallonta ta Madubi,Wata Zuciyar tace"Kuma ki ki sawa..Abu ya Zama Bala"i..Kila ma wannan karon Har da duka!
Tuna Haka yasa ta bata rai Hijabin kala Goma ne kala kala gashi an yi musu Dinkin Zamani.
Bata bar gidan ba sai ta Soya kwai tasha Da Tea da Buredi wanda sai da ma suna Hanyar dawowa Gida Ranar tagani tace su Tsaya su siya kana ya Tsaya ya siyan musu shi ba ci yake yi ba ballatana Yayi Tunanin siyowa.
Dakyar ta samu Daya daga Cikin Hijaban ta saka Kalan pick Zanen Material din Jikinta Har kasa ya kaimata ya Rufemata Diga digi ya ta iya Matar Imu take in batajin mgana Mganinta Zai yi a Dake ka kuma a hanaka kuka kuma aki Lallashinka sai dai ka gaji kabama kanka Hakuri..!
Lokacin da Munari taganta a makaranta Sai da ta Kusa Kaiwa kasa Saboda Dariya Inteesar sai kwal kwal kuka Cikin Shagwaba tace"Duk ban yi kyau ba ko..?
Ba yaya Imran bane ya kawomin wai kada ya kara ganina da mayafi..!
Munari na Dariya tace"Tab..Mrs Imran Abubakar Malami..!
Take Fada Tana Dariya wayarta ta Fito da ita Tana Fadin"Bari nayi miki Hoto naji Dadin Bama su Nasara Labari..!
Daman Kiris take jira sai ta sakamata kuka ganin haka yasa Munari ta Daina Dariyan afili Sai da Taga Inteesar din Idanuwanta duk sun kumbura alamun tasha kukabata Tambayeta ba sai da suka Fito Paper Course mate din su suna ta Murna Final Suka samu Waje suka Zauna Munari ta kalli Inteesar Dake Fama da Hajibi Tana Fadin"wai ya imun dukan ki yayi ne naga Idanuwanki sun Sauya..?in dai kuwa ya Dakeki Wlh Tashi muje office din Abba ki Fadamai kan me..?aure ai ya wuce wasa..!
Inteesar ta Dago tana kallonta kafin Tace"Wlh bai Taba Dukana ba..!
Munari tace"To me ya yi miki..?daga ganinki kin sha kuka wannan i don naki..!
Inteesar ta kauda kai batayi mgana ba Munari tace"Shikenan Tunda baki san Gayamin ammh Zan Fada miki gaskiya in baki Mike Tsaye ba Wlh Ya Imu Wahala Zai ta baki kafin ki gano kansa Kingama Jigata..!
Inteesar ta Juyo tana kallonta Kafin tace"Uhm..Naga alama..Ranar da naje gidan nan..!.,
Nan ta shiga bama Munari Labarin abunda ya Faru ta Karishe da Fadin"Haka ya dinga min tsawa da Fada ina kuka bai Lallasheni ba yace ma in na kara Damunsa yazo nan sai yayi kwallo Dani..Ni ba ance Miji na Lallashin matarsa ba ni Wlh Ya Imu bai Taba Lallashina ba Munari in ma Fushi zan yi baisan inayi ba sai don in nagaji na Hakura dakaina anya Yana Sona..?
Munari ta gyara Zama anzo Wajen Data ke son zuwa Cikin Hikima tace"Wlh yana sonki..So mai Tsanani ma Daya kai ku wannan Mtsayin in da baya Sonki ko sama da kasa Zasu Hade bazai Aure ki har ya Zauna dake ba Baki ga Sajida da baya sonta ba ya Saketa.ba..?haka Ya Imu yake Dan kafiya Dan Ra"ayi bamai Turasasa yayu abu Dole sai Abba ammh ko shi baya yarda yasakashi ya Zauna da abunda baya Ra"ayi..!
Inteesar ta jinjina kai alamun gamsuwa kafin tace"Ai bai taba Cemin yana sona ba..!
Munari tace"Ai bazai fada ba..Ke ce Zaki Sakashi ya Fada ma bai sani ba..!
Inteesar tace"Ta yaya..?
Munari tace"Baki gane ba..?tsaya ma wai Kun Fara amarcin ne ko kuwa Dai kina nan kina Jiransa..!
Inteesar ta Rausayar da ido Tana Fadin"Bama mu taba fa kwana Daki Daya ba Tunda muka yi aure..!
Munari ta Zare ido Tana Fadin"No Wonder shiyasa bai yi Laushi ba Har yanzu..ke kuma kika yarda..?baki cemai kina jin tsoro ba..!
Imteesar tace"To ya zanyi..?dakinsa yake Shigewa fa sai na Bishi..!?
Munari tace"Sosai ma.irinsu ya Imu sai da Tarko..Ki bisa ki Danamai Tarkon da zai kawo kansa da kansa yana Magiya..!
Inteesar tace"Ta yaya hakan zai Faru..?kamar fa baya son abun ne ni ko irin Romance din nan bamu taba ba..!
Tafada Abun na fitowa Daga Karkashin Ranta Munari tama kasa mgana Inteesar ta Cigaba da Fadin"Ina Fadamiki sirrina ne saboda Ke Kawatace kuma yar"uwata wacce banda kamarki..ki bani Shawaran ya Zanyi..?
Munari tace"Insha Allahu Inteesar Zan baki Shawara kamar yadda Zan bama kaina..!
Nan Munari ta Zauna Tana ta karanta mata Yadda Zatayi da Dubarin mata Inteesar tayi Kasake tana ji kafin tace"Kina ganin...kin fa san Ya Imu..!
Munari tace"Ai shima Mutum ne kamar Kowa kuma Namiji mai Lafiya Wlh karyansa ya Ture Kiran wannan Majalisar Dinkin Duniyan in kuma ya Fara Dandanarta To zai so kullum ya Dinga Ninkaya aciii ina nan Zaune Zamu gani Ya Imu yayi Laushi sai yadda kikayi Dashi..!
Inteesar tace"Allah yar"uwata..!
Munari tace kina wasa ne Dariya sukayi lokaci daya suna Tafawa Inteesar na Fadin"Khalil ya Shiga uku..,!
Munari na Fadib"Ai yama shiga Goma ne..!.
Dariya suka saka gabadayansu sun dan jima acikin makaranta bayan sun gama Sallama da Course mate dinsu suka Tafi Office din Abba suka gaisheshi bayan sun gama shan A.c da Lemo suka Mai Sallama suka Tafi Daga Bakin Get suka Rabu kowacce ta hau adaidaitan da zai kaita inda zata suka Rabu Da Inteesar kan Zata gwada Shawarwarinta.
*Shakira..*
3/29/22, 14:31 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�27*
*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*
Inteesar ta koma gida da Kudiri Tare da Niyyar gwada Shawarwarin Munari da kuma amfani dasu.
Tana komawa Gida bata Zauna ba Bayan ta sha Complex tayi alwala Tayi Sallar la"asar Domin sunyi Sallar Azahar a makaranta ita da Munari.
Daganan ta Fara gyaran Gidan bata gyarasa Koda yaushe sai Ranar Datake Gida shima Daga Falo sai Kitchen sai Dakinta ko Hanyar Bedroom din Imran bata Taba kallah ba.
Sai da ta kal kale ko"ina Har Bedroom din nashi ta shiga ta gyaramai Duk da ba wani gyara saosai bai da kazanta Duk Abunda yayi amfani Dashi yana Kokarin Maidashi Muhallinsa Har Tiolet sai da ta wankemai Tas yana Tashin Kamshin Turaran Dakunan Data Turara Gidan dashi a Burner.
Tana gamawa Ta Fada Kitchen ta Fara Sarrafa abunda Zata Dafa Saukkan Abinci Tayi Farar shinkafa da Miyar ganye Da Kifi sai ta Soya kaza Tayi mata Pepe Chicken da yaji albasa da kayan Kamshi,akwai Fruit a dayawa a acikin Fridge Saboda Imran baya bari ma ya yankemai Wani Lokacin da yawa yake siyowa Tana sha ammh ita dai barta Da Cin kayan Fulawa da Zak'i.
Kayan Lambun ta yayyanka tayi Fruit Salt ta saka afrige Lokacin Data gama an Fara Kiran Sallar mangariba Bata Shiga Daki ba sai da ta Jera komai Saman Dining kana ta shiga Ciki.
Wanka Ta Farayin kafin ta Dauro alwala ta Fito Sallar ta Farayi kafin ta Shafa Man shafawarta na Olive Ta Fara kokarin neman kayan da zata saka Wadanda zasu ja Hankalin ogan akanta.
Cikin akwatin kayanta na Gida Wanda Nasara ta Hadamata,gabda Biki ta Bude Tasan Tana da wanduna da Riguna Lokacin Tana Gida da Zata Taho kano ne Umma ta Hanata Tafiya Dasu Taji Dadin ganinsu aciki Batasan Umma ce ta saka su ba,Domin ai Tasan Zasu yi mata amfani Tunda Gidan Miji Zataje Daman ko Gidan Maman abunda yasa Umma ta Hanata Zuwa Dashi Saboda ba kamar nan bane Da ba Kowa Daga ita sai ita sai Daddy Ya Basheer na Gidansa ba Kullum yake zuwa ba,gidan Mama kuma akwai Sagir kuma shi ba Muharraminta bane Shiyasa ta Hanata tafiya da Wandunan datake Sakawa su Lameta sosai suna Fitar da Surar Jikinta.
Wani Wando ta Samu Red Colour Daga Kasa ya Tsuke sosai iyakarsa kuma daga gwiwanta Kadan ya Wuce sai Wata karamar Riga mara Hannu Itama Ja ce sai dai Tana da Zanen Baki a Jikinta an yi Rubutu kanana daga gaban Riga Data Sanya kayan Ta Tsaya gaban Madubi sai ta Fara Tunanin Anya Zata iya Fita gaban Ya Imu haka..?kayan Tun Tana gida bata cika sakasu ba sun kamata sosai Wandon ma Dakyar ta saka Gabadaya Shafaffan kugunta ya Bayyana Kirjinta ya Cika rigar ta kamata sosai da Har Shatin Cibiyarta ana gani sannan kuma Da kadan ta Wuce Cibiyarta Data Daga Hannu Lafaffan Cikinta Zai Bayyana Waje ne.
Sumar kanta Da bata Kitse ba Ta Tattara ta Daure Daga kasa ta Sakamai Band kafin ta Samu Wata Hula red itama mai adon kamar Love ta gaba ta saka bayan ta Saka wani Saukakkan Dan kunnen da bazai Dameta ba kara kallonta Take ta Madubi kafin Wata zuciya tace mata"To ke Intee keda zaki burge Miji ai bakya Bukatar wannan Hular..!
Tafada Tana Cire Hular kanta Sake Sauya yanayin Band din Tayi ta maidashi ta Tsakiya duk da ba wata Doguwar suma gareta ba Tana da Cika da na Zaman Falo.
Karan Bude get taji Tasan ya Dawo kenan Tanaji ya Shigo da Motarsa ya koma ya Rufe get din Wanka Ta Fara ma kanta da Hunra da Turaruka masu Kamshi Da Fitar ma da Duk wanda ya Shake su Hankali yau akwai jan mgana.
Kugu ta Rike Tana Sauke ajiyar rai a Fili ta Furta"Zan Burgesa..?
Allah yasa ma ya Kalleni Nasan Halin Wanda na aura ba komai ke Burgesa ba..Zan so Tarkon na ya kamashi Can"t Wait naji Ya Imu ya Kalleni yana Fadin I Love u Inteesar..Bazan iya Rayuwa bki ba..!
Tafada Hartana Kwakwaiyon Salon mganarsa Kafin ta Tsintire da Dariyan Farinciki Bakinta Ta Rufe jin Motsin Shigowarsa ya shiga Dakinsa kana ta Sauke ajiyar Zuciya gefen gado ta Zauna Tana Kara jiran Fitowarsa kamar yadda ta Tsara sai ta Fita Ta ja Fada daman ai basa mgana suna Fada ne.
Yayi matukar mamakin ganin Dakinsa Tsab yana Tashin Kamshi Sai dai yasan Intee ce ta gyaramai Daki Mirmishi yayi yana Fadin"Allah Sarki..Yarinyar Tana da Hankali..Allah yayi miki albarka..!
Yafada kafin ya ijiye Briefcase din Hannunsa ya Sabule kayan Jikinsa ya Shiga Wanka Har ga Allah yaji Dadin Ganin ko"ina na Tashin kamshi Sosai yayi wanka cikin jin Dadin Da Annushuwa aransa yana Fadin Ta Daina Fushin kenan..?
Bayan ya Fito bai Tsaya