Showing 171001 words to 174000 words out of 235479 words

Chapter 58 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt

Janafty   

14 Jan 2025

16154

kwana Tanayi dukkansu suna Dakin gwanin ban Tsausayin Halin da Mami Asma"u ta saka yarta.
Daada ta aiko kiran Abba da Daddy suna zuwa tace maza suje a Daura auram nan da Abba ya kawo mganar Rashin Lafiyar Sajida sai Daada ta Saka Musu kuka,kan cewa in suma baza su yi mata Biyayya bane Sai su gayamata jin haka yasa suka Fice Daman Allah yasa da suka je Sallar asuba Daddy ya sanar da Liman akwai Daurin aure karfe 11am na Safe.
Haraban gidan suka Fice Daddy ya Kira Basheer da Yusuf ya basu kudi sukaje suka siyo Goro da dabino,Sha Dayan bata cika bama suka isa masalllacin Imran na Gida bai zo ba da Sagir yamai mgana kallonsa yayi kai Tsaye kafin yace"Ko naje ko ban je Inteesar Zata Zama matata so plz ka kyaleni..!
Sagir ya kada kansa yana Fadin"Kai dai Wlh baka da Tsausayi nan fa nazo Dazu ina Fadamaka Halin da yarinyar nan take ciki ammh kana ta jin Dadi anya kana da Zuciya a kirjinka..?
Imran ya kara Murmusawa kafin yace"In baka yarda bane ko Zamu saka Wuka ka fasa Kirjin nawa sai ka Duba kagani ina da Zuciyar ko bani da ita..!
Tunda ya Fadamai haka bai kara bi ta kansa ba to duk kowa bai da Natsuwa haka aka Daura auran Inteesar da Imran kan Sadaki Dubu Dari Daddy shi yayi ma Imran Waliyi Abba kuma ya bada Auran Inteeaar Mutanen anguwan suna ta yabon Ahalin Alkali Dukku marigayi suna Fadim bayan Ransa basu ya da Zumunci ba,Suna ta Hada ya"yansu auratayya Cikin Aminci,Kuma Daurin auran yayi jama"a matuka Domin kaf Anguwan ba wanda bai shaida karamici irin na Marigayi Hamisu dukku ba.
Daada bata ji Zuciyarta ta kwanta ba sai da Abba da Daddy suka dawo suka zube mata sadakin Inteesar da Goro da Dabino suka Tabbatar da sun cika mata Wannan Umarnin.
Daada na Sharan Hawaye tana saka musu albarka Tana fadin kamar yadda suke bin Umarninta Insha Allahu bazasu taba samu ya"ya wadanda Zasu bijiremusu ba Daada ta Bala"in basu Tsausayi Rauninsu ya bayyana sukaji suma kamar suyi ta kukan nan suka Taru suna Lallashinta Kafin ta Daina kuka ta koma Fara"a Da Dariya Lokaci Daya Tana Saka musu albarka.
Lokacin da Sagir ya shigo Dakin da Imu yake yana fadin an Daura mai aure Shi da Inteesar sai da ya Tsaya da aikin da yake yi gabadaya Jikinsa ya Saki yaji Wani irin Feeling mai karfi yana Tasomai yanzu Intee Matarsa ce ita din mallakinsa ne.
Baisan Sadda ya Furta"Alhamdullillah..!
Afili har Sagir ya jisa ba sai dai bi bi ta kansa ba Ya gama batamai rai ya kuma bashi Haushi Dauke kansa yayi kamar bai gansa ba ya Fara Shirya jakarsa Tunda yau zasu koma Imran na Kallonsa aransa yace kayi ka gama.
Umma kuwa Daman Tun jiya ta Kira Chan su Inno ta gayamusu komai suka Saka albarka da Fatan alheri,dukka yayyinta ta Kira su su Kawu Bala da kawu Salisu ta Fada musu sukace ba Domin bata gayamusu tun da Rana ba da sun samu Daurin aure tace bakomai suyi Zamansu Tunda anan kaduna za"ayi Bikin Tariyan Inteesar din.
Mama kuwa Daman ita ta Fara Kira ta fadamata Mama ta Saki Guda a waya Tana Bayyana Murnanta ta Tuna da Sanda tace ma Intee zata aurama Imran ita a wasa ashe dai Allah ya Hada al"amarin sai fatan Allah yasa su zauna Lafiya,Gari na Waye ana kuma Daura aura ta Kirkkira su Kawu Salisu ta shaida musu Nasara Kawar Inteesar sai da taji Labari kamar Daga Sama wai an Daura ma Intee Aure ita ta Fara Kiranta a waya tana Fata kwakwazon bata gayamata ba Inteesar tasha mamaki bata Taba Zaaton Auran zai zama cikin gaggawa haka ba tama kasa mgana Jikinta ya Mutu duk da kwanan Farincikin Datayi Zata Zama matar Imran jinta a Mtsayin Matarsa bayan a wanni kadan yasa komai ya Tsaya mata tama kasa gane wani yanayi take ciki.
Munari ta bari da wayar Tana ma Nasara Bayani har ta Fahimta Tana jinsu Suna Tsara yadda zasu gwangwaje alokacin Tarewar Bikin su Intee na Jinsu aranta tace badai da ba Ya Imu na aura ba shine zamu gwangwaje ammh wannam Dan ka"idan Allah yasa ma ya bari ayi Bikin.
Koda Anty Safiya ta shigo ta Fada musu Abun Farinciki sai ta iske ma Munari na waya da Nasara suna mgana Itama Yanzu Yusuf ya Kirata Rumgume Inteesar Tayi Lokaci Daya Tana Rangada guda,Munari na ganin haka tayi Saurin katse wayar Nasara bayan tace Zata Kirata Daga baya suka Hadu da Anty Safiya suna tayima Inteesar guda Da Wakar.


"Ke Kikace kina so..da baki ce kina so ba da ba'a baki shi ba..!
"Ta zama ta zama ta zama Dauko Riga ta zama Dauko wando..Ta zama Dauko Kofi...Ta zama..Ta zama..!


Kawai sai Inteesar ta saka musu kuka Hawaye Shabe Shabe Anty Safiya ce taci Girma ta koma Tana aikin Lallashi Tana fadin"yi shuru abunki..Amarya guda da kuka..?matar Imu guda a"a bar kuka Kada yazo yaga nasaka matarsa kuka yace zai Sauyamin kammanni..!
Gabadaya suka saka Dariya Harda ita Tana Hawaye,nan suka zauna da Anty Safiya da Munari suna Tsara yadda komai Zai tafi harda kirga ankon da Zasu yi lokacin Bikin Tariyar domin zasu Famshe Bikin yaya yusuf da ba"ayi Taro ba zasu yi gayya na kece Raini Taro sunan Taro ita dai Tana gefe Tana kallonsu Gabadaya Hankalinta da Tunaninta na kan Imran yana ina..? Wani Hali yake ciki..?
Kafin kace kwabo Labarin Daurin Auran Inteesar da Imran ya Zaga kunnen kowa a Dangi Ya Basheer ya Hau Whatapps ya sanar a Group Cikin Fahari da Farinciki a Mtsayinsa na Dan"uwan Intee yasan ta Gama Dacen Miji irn Imran irin su ne ake kira One in Million,Matan kuma su Anty Hauwa su Aneesa duka mazajensu suka kirasu suka Sanar dasu Inna Maimunatu ma ta kira su Zainab ta Shaida musu kowa yaji Sai yayi Murna yana Fadin Wlh Imran sun Dace da Inteesar Hadin yayi matuka.
Hafsah ma Dataji Labari ta Daka Tsalle ta Rangada guda Tana juyi Tana Fadin kano akwai Shagali Fareesatu namata Dariya,Kiran wayar Inteesar Tayi munari ta Dauka suka Dinga mata ihu suna Tsokananta da Amarya Amarya,ita dai tana jinsu bata mgana yau aure ya kashe bakin Intee Hafsah Har tafi Munari Zumudi Tana Fadin Taga wani less ko shi Zasu yi Ranar Dinner..? Intee Dariya suke bata da Tsausayi Sun manta wai Waye Imran ne Ta Rantse har ga Allah sai yayi Ra"ayi Duk abunda bai yi Ra"ayi ba ba wanda ya isa.


Hatta Baffa Kabiru Dake Abuja ya samu Labari inna Bintalo Gulma na cinta bayan ta gama Kiran ya"yanta su Siyama ta Tseguminta musu Duk Abunda ya Faru sukayi ta Zagin Imran suna Kuma cewa Daada bata kyauta ba tayi ta Kiran Mami Asma"u a waya ammh Wayar na Ringing bata Daga ba sai ta Kira Baffa Kabiru Lokacin ma yana Office Suna da wata Sharia mai Zafi ga Damuwa ga Abunda ya Faru jiya Wanda har suka iso Abuja bai ko kalli Barayin da Mami take ba har kuma yau din nan basu kara Haduwa ba Domin Tun bayan Dawowarsu kowa ya Shige Dakinsa Bai nemeta ba itama bata Nemesa ba Khamis ma yana cikin dakinsa yana Faaman da Raunin Zuciya na Rasa Inteesar gefe Daya ga Mtsalan da Mami da Dad,Umaima ce kadai ta Leka Mamin Sai tace mata batajin Dadi ta fita ta bata waje bata kawo wani abu ba,Ta koma Dakin Dad sai ta iske ya Fita bata Damu da Rashin Ganin Sajida ba atunaninta ta Wuce makaranta chan suka Fara maidata ita kafin su dawo gida batabi ta kan Khamis ba itama Tun Safe Direba ya kaita makaranta yan aiki kadai aka Bari suna ta Bidirinsu acikin Gida.
Lokacin da Binta ta Fadamai an Daura aure bai wani Damu ba Saboda ba Shakka Jiya ya kwana bai yi barci ba yana Nazarin Rayuwarsa Tun Daga Farkon yarintarsa Har Girmansa Haduwarsa da Asma"u zuwa auransu da yadda yake sonta ya kuma nuna mata Ya Tabbata Soyayyar Dayake ma Asma"u ce Weekness dinsa itace Silar Faruwar duk abunda ya Faru,ya sakar ma Asma"u komai nashi Rayuwarsa Rayuwar ya'yansu itace Take Tafiyar da komai Rayuwarsa ma shi da yan"uwansa shi ya bata Damar Tafiyar da komai saboda baya iya yin wani abu acikin Dangi sai ya Bata Labari kuma in tace kada yayi kaza ga yadda take so ayi haka ne zai Faru ne,Tana amfani da wannan Weeknees din nashi Tana yadda Ta gama Dama a Rayuwarsa gaskiyan Daada ne shi ya bata Komai da Tun farko bai bata Damar saka baki Cikin abunda ya Shafi Ahalinsa sa ba ita bata isa ta Ja da mganar Daada ba da Tun Farko bata Nuna Jajayarta kan auran imran da Sajida ba da Imran bai Saketa ba,da ya nuna mata bacin Ransa ya Nuna mata bata isa ba da haka bata Faru ba ammh Sai ya goyi bayanta yana ganin eh Daada batayi Daidai ba Yau ga abunda ya Faru Asma"u ta Ci Zarafin Daada bataji kunya ba..Itafa Ta Haifeshi Itace Uwa garesa ammh Asma"u bata Duba wannan ba kanta Kadai ta sani Shima son kansa Shi yajamai komai da ace bai da son kai da bai kyamaci Jinin Malami ba.Da Abunda ya Faru bai Faru ba,Da Daada batayi Fushi Dashi ba da Sajida ta Samu Abunda take so take Buri.
Fatan Alheri yayi Yana kokarin Dauke Hawayen da suka acikin Idanuwansa,Sai dai ya shiga Damuwa Sanda yaji Sajida na kwance ba Lafiya Batama san an Daura auran ba Baffa Kabiru yaji Takaichi Asma"u zata Kashemai ya saboda son kanta Wlh Shi Zai kaita kara Kotu in har wani abu ya samu Sajiya ya gane kuskuransa zai nemi Daada gafara zai kuma gyara Tsakaninsa da yan"uwansa Zai gayama Asma"u ta Shiga Hankalinta in kuma ba Haka ba Komai zai iya Faruwa.
Khamis ma ya Samu Labari ta waya Daya gani a group haka ya kwanta Saman gado yana kuka kamar karamin yaro ba Soja ba Mami Ta Riga ta Ruguza komai ba,Ta yi Sanadiyar shiga Tsakaninsa da abunda yake so Sai dai bazai yi Fushi da ita ba,uwa take garesa Sai dai Dole zai yi nesa da gida in ya Tafi baxai Dawo nan kusa ba so yake yayi nesa da Duk wata Hayaniya ko Damuwa ya yarda Imran yayi nasara shi kuma He is a Loser.


*****
Abba da Daddy shiryen Shiryen Tafiya suke yi sun yi mgana da Inna Bintalo da Inna Maimunatu zasu zauna su kara kwana Biyu har Daada ta Watseke Mganar Sajida kuwa sai da Abba da Daddy suka duka suna Rokon Daada Ta amince Sajida ta zauna in ta ji Sauki sai ta koma Abuja Kana Daada ta amince ammh da Farko cewa Tayi Sajida bazata zauna mata agida ba bata da Alaqa da ita ta koma Abuja gaban Iyayenta.
Kafim su Wuce sai da Daada ta kara Jadadda musu cewa Tarewar Inteesar kada ta wuce Wata Daya bata son jan Lokaci Tana son Ta dauki dan Imran da Inteesar da hannunta Jikan Mustapha da malami kafin ta bar Duniya Daddy ya tabbatar mata da Insha Allahu bazai Dauki Lokaci ba Da Daddy yace ma Daada ko nan Dukku Za"a dawo ayi Taron Bikin Daada tace a"a bata Bukatar ganin kowa su yi Taronsu chan wannan Tsakaninsu ne sai yadda suka Tsara.
Sai dai a turo mata Inteesar tana son ganinta kafin Lokaci sannan ayi al"ada kada ace baza"ayi wannan ba saboda na gida ne A"a Aure irin auren kowa ne abama Imran Wahala sosai yayi Duka al'adu kafin Abashi Inteesar su Abba nata Dariya Imran na wajen ya Hade rai yana cema Daada nima sai ta Wahala zan yarda na Tare Dariya su Sagir harda rike ciki,sai da suka sanya Daada Farinciki kana suka Wuce Motar yusuf su Sadam da Abba suka shiga sai Sa"id wanda ya Dauke su Imran zai ijiye su kano kafin ya wuce Jigawa,Umma kuma da Daddy ya Basheer ya Tuka su,a gombe suka Tsaya sukayi Sallar Azahar kana suka Dauki Hanya.
Allah Sarki suka baro Dukku Cike da Tsausayin Sajida da ita kanta Daada,Sai bayan Tafiyar su ta Farka Ta dan samu karfin jiki kuma Zazzabin ya sauka,Inna Maimunatu ta Taimakamata tayi wanka tadan Tsakuri abinci Inna Maimunatu ne ke ta Kula da ita Inna Bintalo kuwa Gulma kadai ta iya da Munafunci ta Girma bata san ta Girma ba ita ta Lallabo bayan Fitam Inna Maimunatu Zuwa Dakin Daada tazo tana gayama Sajida an Daura auran Imran da Inteesar nan da nan ta sake Rikicewa da kuka da Inna Maimunatu tazo ta ganta Cikin Wannan Halin Tasan Dalili Bintalo ce ai bata da Girma sai na Jikinta Kullum tana Girma Tana cin kasa
Ko ta kanta bata bi ba,Ta koma Tana Ta Lallashin Sajida,wacce ke kuka kamar Ranta zai Fita Idanuwanta Jajir take kallon Inna Maimunatu Lokaci Daya Tana Fadin"Goggo Shikenan Ya Imran ya sakeni..Shikenan Mami Ta Rabani da Mijina..!
Take Fada Tana kuka Rumgumeta Inna Maimunatu tayi kamar tayi kukan itama Tace"A"a ba shikenan ba Sajida kin ji ko..? Kiyi hakuri ki Daina kuka da yardan Allah zaki samu wani Mijin Dayafi Imran komai da komai..!
Girgiza kai take yi Tana Fadin"ko na samu bazan so shi ba..Imran nake so shi zuciyata ke Zafi saboda soyayyarsa..!
Tafada Tana Dagowa Hannun Inna Maimunatu ta kama ta Dora Saman Kirjinta Tana Fadin"Kin ji yadda take Bugawa ko..?to da soyayyar Imran take Bugawa kuma Tana gabda Daina Bugawa Saboda shi..!
Ta karishe Fada Hawaye na wanke mata Fuska Inna Maimunati sai ta kasa mgana Hawaye take share mata Acikin Ranta Tana fadin anya Asma"u zata ga Daidai kuwa..?
Hakkin yarta Sajida ta tabbata bazai barta ba
Dakyar ta samu Sajidan Tayi shuru ta koma ta kwanta Tana Shesshekan kuka,Ta fice zuciyarta Cike da Tsausayin Sajida ga Daada Tayi Fushi Sosai da Yaya kabirun da duk abunda ya Shafe shi ballatana taje ta gayamata Halin da Sajidan ke ciki Lamarin sai gyaran Allah kawai.


Su Imran suna Cikin Tafiya sun kusa isa kano,sai mirmishi yake shi kadai in ya Tuna shi fa yanzu Mijin Inteesar ne sai Nishadi yake ji in ya Tuna hakan,Yana ayyana yadda zai Rika Zuba Mulkinsa son rai,Kamar zai Tura mata sako sai wata zuciyar ta Hanashi da Cewa kul Imran wlh Ka kiyayi kanka Yanzu taji labarin komai sai ta Zata kana sonta ne Raini ya Fara shiga Tsakaninku abunda bazai taba yarda ya Faru ba Har Abada Balle da Munari Ta fara cewa wai suna Munafunci Yarinyar taci abinci in suka Hadu sai yayi kwallo da ita Tuna haka yasa kawai ya Share duk da har suka iso Tunaninta yake yi shi bai yarda yana sonta ba Imran naso ya rika karyata Feeling dinsa.
Tun da suka Taho Yusuf ya Kira Safiya ya Fadamata ta sanar dasu Munari,Munarin ta tayata suka Dora abinci Inteesar dai bata ma da Wani Kuzari bata san da wani ido Zata iya Kallon Imu ba wani Haduwa zasu yi akaron Farkon su na mata da miji..? Ga Abba ga ya yusuf gaskiya Tana jin kunya sosai bazata iya Hada ido dasu ba.
Tuna Haka yasa ta Lallaba ta Kwashi Littafan karatunta na gobe ta Gudu Gidan Mama koda Munari ta Laluba bata Gidan ta Gudu Data Kirata a waya sai tace Tana gidan Mama chan zata kwana Munari ta Rike baki Tana mata Tsiya.
Chan din Mama ta sakata gaba da Tsokanan Abaya Lokacin Datace Allah ya Tsareta ta Zama matar Imran yanzu kuma gata mtsayin matarsa yake nan..?
Inteesar ta Tura baki Tana Fadin"ai bani nace ina sonsa ba..!
Mai mama zatayi ba Dariya ba Dawowar Sagir Bayan mangariba yasa Tasan su Imu sun iso kenan Shima ai yana shigowa gidan ya Ganta yahau Tsokananta da Matar Abokina Dan iska ko mai Shaye Shaye..?
Intee Tayi kwal kwal da ido kafin Tace"Kai ya Sagir..Mama kin gansa ko..,?
Cikin Shagwabarta kamar Zatayi kuka mama tace"Kyaleta Mana kada ka sata kuka..Ta gudu ne bata son Hada ido da Abba tana Surukanta dashi ba Uba ba..!
Dariya suka saakamata yasa ta Shige Ciki Tana Kukan shagwaba wanda bai da Hawaye Sagir yace ai su Abba sun Rigasu isowa su Sa'id ya Daukosu Ya kuma wuce jigawa Sadam kuma sai da su Abba suka ijiyesa agida kana suka Wuto nan.
Dakinsa ya shiga ya ijiye jakarsa ya Fito ya Dauki Buta ya Zagaya.
Yana Fitowa yayi alwala ya shiga Daki yayi Sallah Mama ta gabatar da abinci yaci yasha Ruwa yana bama Mama labarin kadan Daga abunda ya Faru a Dukku Harda Sakin da Imran yayi ma Sajida Mama ta nuna jimami sosai ammh fa akasan Ranta tasan Inteesar tafi Dacewa da imran.
Inteesar na Daki Taji komai Duk da bataji Dadin Haka ba sai dai Taji Sakayau Nauyin Kirjinta ya Ragu da Kishin Sajida sannan taji Haushi wai Da Sagir ke bama Mama Labarin Sajida tace tana son Imran Ranta ya Baci ta Tura baki tana Fadin"Ai sai ta yi ta sonsa..mara zuciya ba ya saketa ba..!
Ita kadai tayi ta Bata rai Sai dai taji Dadin yadda Mami Asma"u Taga Karshenta sai dai Baffa Kabiru ne ya bata Tsaisayi aranta tace Allah ya kara shima.
Mama bataji Dadi ba Salallami take,ko kadan abun bai mata Dadi ba Kiran Sallar Isha"i ya Fitar dashi chan masallaci suka hadu dasu Abba da Imran sai da suka idar suka fito Waje Sagir ya yafito Imran yana Fadin"Amaryanka na gidanmu ko zaka shiga ne ka rage Dare..?
Imran yayimai wani kallo kafin yace"Kaifa Dan iska ne a ina kasan ana Rage Dare Sangiru..La"ilahaillalah..Ka lalace na bani..
Dariya Sagir ke yi shima imran Dariyan yake yi kafin yace"Abun mata da miji fa..Allah ya shirye ka zan Tashi Tsaye na nemo maka matar aure kada ka Fara Leke gidajen Jama"a cikin Dare
Yafada yana Dariyan keta Duka Sagir yakai mai a Gefen Cikinsa ya kuwa Samesa shima Imran din ya Hambaresa yana Fadin"Dan iska karya nayi maka..!
Sai Dariya suke cike da Nishadi Daga ganin Dariyan da Imran yake yi na Tsantsan Farinciiki ne bai sani ba.
Ba yadda Sagir bai yi ba Daya shiga yaki shiga Cikin Dakuna Fuska yace"Bazan shiga ba Uban me zan mata..? Ai tasan muna Hanya ta Tafi gidan Mama kuma Dataga ganka meyasa batazo tamin Sannu da zuwa ba sai nine zan Bita Allah ya Tsari Imran..!
Daga haka ya wuce Sagir yabi sa da kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login