Showing 147001 words to 150000 words out of 235479 words
Chapter 50 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt
wayar taga Misssed calls dinsa ido ta Zaro kafin yace"Ai kuwa gashi..Allah ban gani ba ya Imu ka yarda dani..,!
Shi dai ya riga ya samu Salama Jin ba da shi take mgana ba Har sai da ya Sauke Numfashin Salama.
Kallonsa Tayi lokaci Daya tana kallon Taban Data gani a kasa Cikin mamaki Tace"Miye wannan..?
Tafada Tana nuna mai kasan yasan ko miye bai kallah ba ya Dauke kansa kafin yace"Meye..? Nima bansani ba..!
Dariya ta kusa kama Inteesar har sai ta Murmusa Tana kallonsa Dakuna Fuska yayi kafin yace"Kina son Duka ne..?
Dariyan nata sai da ta Fito da Sauri ta saka Gefen Hijabinta Tana Danne Dariyanta Hannunsa Daya ya Fito dashi Yana shafa kansa yana Mirmishi Cikin Dariyan kansa Inteesar ganin Fararan Hakoransa a waje ya Shagaltarta da ita tana ta kallonsa Tana auna irin kyan Imran He so nice.
Ganin Taki Tsayawa da Dariyan ne yasa ya Tallabi kanta ahankali Cikin Nishadi yace"yarinyar nan kin Rainani ko..?kinga gadon barci na..!
Yake Fada yana Kokarin Daidaita kansa.
Kanta ta sosa tana yar Dariya kallonta yake Cikin Sha"awa kafin yace"Yana kiran ki..?
Tsayawa tayi tana kallon cikin mamaki kafin tace"Waye shi din..?
Yana Dakuna Fuska yace"Yaron nan mana..Wanda yace yana sonki..A Dukku..!
Fara"arta ta Rage kafin tace"Yana kirana bana Dauka ko ya Turomin sako bana Dubawa..Tunda muka Dawo Daga Dukku yake Damuna..!
Tafada cikin bayyana Jin Haushinta Ransa yayi fari jin bata kulasa Sai dai bai kamata ya sakankance ba Hannu ya mikamata yana Fadin"Muga lambarsa..!
Batayi musu ba ta lalubo ta Daga Sama Saboda ya Kirata ma da Safe,Ta Haddaceta Duk da batayi Sarving ba Mikamai tayi ya karba wayar ya shiga ya Sakata Cikin Blook ya shiga bangaran Sakon nin yayi musu Delete all ya mikamata wayar yana Fadin"Ko kina son shi ne..?
Karban Wayar ta tayi kafin tace"Ni bana son shi..!
Tafada Tana Tura baki wani sanyi yaji acikin Ransa kafin ya kalleta yana Fadin"Gobe zamu tafi Lagos..!
Ido ta sakarmai kafin tace"Lagos..?ku da suwa..?
Imran yace"Ni da babanki da Abba da Ya Yusuf..,!
Baki ta Washe kafin tace"Daddy zai zo nan..Eyeee..,!
Tafada Tana bayyana Murnanta.
Kallomta yake yi yana jin Farincikin ganinta haka cikin dan Hade rai yace"Kina Murna saboda zan tafi..!
Bata rai tayi kafin tace"Ah"a nifa ina Murnan zan ga Daddy na ne ai kuma ba Dadewa zaku yi ba ko..?
Kai ya gyada mata kafin yace"Jibi zamu dawo..,!
Kai Tsaye yace"Chan zaka koma da aikin ka..?
Yana kallomta yace"Wayace miki aiki zan koma..?Gidanmu dake chan zamu je mu gani..!
Ajiyar Zuciya ta sauke kafin tace"Har naji Dadi..Bama so kayi nisa na Daina ganinka in ma zaka fara Aik plz Ya Imu ka yi shi anan garin kaji..!
Kamar wani gaula haka ya gyada mata kai Dariya tayi kafin tace"Zamu dinga mgana ta waya in kun je ko..?
Dauke kansa yayi kafin yace"A"ah..,!
Bata rai tayi kafin tace"A"ah kuma..?
Tafada Kamar Zatayi kuka Karo Farko Dataji Sautin Dariyansa yana Fadin"Shikenan zamu rika waya..Kada kimin kuka Shagwabbiya kawai..!
Yafada yana kallonta da Dukkan Zuciyarta sai Lokacin ta saki Fuska Tana Buga Kafarta Tana Fadin"Kai Ya imu kaima zaka Biye ma Umma ne..Nice ma Shagwabbiyar..?
Kallonta kawai yake yi bai yi mata mgana ba,Yanayinsa ne ke Sauyawa ganinta ahaka yasa ya kauda kai yana Fadin"Shiga gida..!
Kai ta gyada mai kafin ta wuce Tana Waigensa,tana Dariya ta zata bai ga abunda tayi ba Sigarin nan Daya Wurgar ta saka kafa tatafi dashi Tana ja ya ganta yayi kamar bai ganta baa ya Kauda kai yana mirmishi Lokaci Daya yana shafa sumar kansa jinsa Cikin Farincikin da suka yi mai kaura Tun bayan Rasuwar su Anni sai da ya Hadu da Inteesar yake jinsa kamar ba shi ba.
Koda ta shiga ciki Abba ne kadai afalo nan ta Zauna suka gaisa suka Shiga Hira anan ma shima ya gayamata zasu je kaduna gobezasu tafi Lagos tayi musi Fatan Sauka Lafiya da Dawowa Lafiya,kafin tatashi ta nufi kitchen inda Taji mganar Anty Safiya da Munari Tana Shigowa Munari ta Fara Dariya saboda ta ga Ya Inteesar din Zatayi ta Kalleta Tana Fadin"Allah yasa ba wani Laifi kikayi mai ba..?
Ta fada Cikin Damuwa Inteear tace"Fada kawai yayimin..!
Munari ta Kwashe da Dariya a Fili ta Furta su Fada manja Inteesar bata gane ba tana Dariya Anty Safiya ma bata gane komai ba sai itama Dariyan take ta Zata Shakiyancin Munari ne.
Tare suka kama Girkin sai gabda mangriba suka gama kana suka shiga Domin yin wanka da Sallah.
Bayan sun idar ne Inteesae tace Munari tatashi ta Rakata Gidan Mommy ta Dauko mganinta na Ciwom mara Data zo dashi Daga Gida Jin maranta ta dan Fara mata Ciwo kadan kadan,Munari ta sako Hijabi suka Fito a Falo suka bar Abba da Ya Yusuf shima sai da yayi musu Fadan Fita duhu ya Shiga Jin Mgani zasu Dauko yasa yace suyi sauri ko kuma su Tsaya wajen Maman su kwana.
Sum sum suka Fice suna zuwa Haraban gidan zasu Fita suka kusa Cin karo da Imu ya dawo Daga masallaci ba Wutan Nepa sai dai Wata ta Raba gari Tar.
Lokacin da suka Fahimci shine Sai da jikinsu ya Dau rawa kallonsu yake Cikin mamaki kafin yace"Ina zaku yanzu da Daddaran nan..?
Yafada yana kallonsu Cikin Dakiyarsa
Cikin In ina Munari tace"Gidan..Ma...ma zamu je..!
Inteesar dai batayi mgana ba sai Morema kallonsa take yi yana Lura da ita sai dai bai bata Damar ma ta Fahimci ya ganta ba.
Hade rai yayi kafin yace"Yanzu da Daddaran nan..?
Yafada yana kara Duba agogon Fatan Dake daure a tsitsiyan Hannunsa.
Kafin ya Cigaba da Fadin"Ammh baku da Hankali ko..? In akace ku Fita iyanzu sai ku fita..?
Munari kanta na kasa tace"inteesar ce zata Dauko mganinta..!
Tafada tana Zungurin Intee datayi mgana ita kuma taki cewa komai.
Kallonta yake cikin Mamaki yace"Mgani bata da lafiya ne..?
Da Sauri Munari ta gyadamai kai Inteesar din yake kallo ita kuma taki yarda su Hada ido cikin Dakiyarsa yace"Oya ku koma gida in dai kunsan ba Chan zaku kwanaa ba....!
Munari tace"ai yau anan zamu kwana..!
Cikin gajiya da mgana yace mata"to bazaku fita ba..Ku koma ke gayamin Inda mganin yake naje na amso miki..!
Imteesar tq Fara Wiki wiki da ido kafin tace"Barshi ma gobe da safe sai muje na Dauko..!
Tabe baki yayi kafin yace"Better..!
Sum sum suka wuce yana Bin bayansu Har Falo ganin su haka yasa su Abba sukasan ya Korosu ne Dariya sukayi kawai su kuma suka wuce Daki suna Tura baki.
Washegari Daddy bai samu Biyowa ta nan Kano ba,Saboda zai yi baya Ya yusuf da Abba da Imran suka Samesa a kaduna,Su Munari suna ta Barci koda suka tashi Tuni sun kusa isa kaduna Domin 6:30am suka Fita Suna Dawowa Sallar asuba Tunda Tafiyan Motace zasuyi Dukkansu sun Tsani hawa jirgi Tun Faruwar Lamarin Daya Faru.
Da kwatace da komai sai ga Abba agidan Daddy farinciki kamar me Wajen Daddy ya kama Abba da su Yusuf ya Rumgume Umma kuma Tana ta ina ta saka dasu,Basheer ma yazo Dayake Har dashi Za"ayi Tafiya za"a Tafiyu iya Tafiya shiyasa Dole su nemi Wanda zai taimaka ma Yusuf da Driving Tunda Imu dai ya Dade bai Taka Mota ba.
Sai da suka karya kana suka Mika Hanya,Wajen 10am na Safe Umma ta Bisu da Allah ya Kiyaye Hanya Yusuf ke Tuki Imram na Gidan gaba Basheer da Abba da Daddy na Gidan Baya sai da suka Tsaya suka cika Tankinsu da mai suka Dau Hanya Da guzurin Abinci su da kayan Snak a bayan Booth Wanda Umma tayi musu tunda Tafiyace ba kadan ba kila su da isa sai Cikin Dare ko da asuban Gobe.
*Shakira*
3/22/22, 23:15 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�11*
*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*
Basu isa cikin garin Lagos ba sai Misalin 3:30am na Dare suka isa,Saboda Shigar Dare sukayi ga Gajiya yasa suka kama Hotel suka kwana suka warware gajiya sai da garin Allah ya waye bayan sun yi wanka sun yi breakfast kana suka Dauko Hanya zuwa Ainihin gidan su Imran wanda suka barsa Shekaru uku da wani abu.
Abba da Yusuf Rauninsu yafi bayyana ammh banda Imran wanda ba wanda ya isa ya bayyana wani Hali yake ciki.
Duk da sauye sauye ya karu a Birnin na Ikko basu manta kayattaciyar anguwan masu hannu da shunin da sukayi Rayuwa ba wato Victory inland ba.
Gidansu na nan yadda suka Barshi Katon get garkame da katon kwado Sai dai saboda Dadewa get din duk yayi kura yana sun Rufe wajen alamun dai ma mallaka Gidan sun Dade basa rayuwa acikinsa.
Ba wanda ma zai iya Tuna ina key din kwadon yake Lokacin da suka Rufe gidan suka Tafi suna cikin yanayin da ba baza su iya su iya gane komai ba.
Sai da Yusuf ya shiga Cikin gari ya samo mai yanke kwado aka zo aka yanke shi aka Bude gidan suka Shiga Ciki.
Allh Sarki Rayuwa Duk mai Imani Dole ya koka ma wannan Ahalin Gabadaya Haraban gidan ya Cika da Kura kyakyawan Marbels din Dake Shinfide a Haraban gidan ya cika da Ciyayi duk sun bushe Flowers duk sun bushe sun mutu murus Yana duk ya Lullube ko"ina ga Motocin su na Zamani guda Hudu reras,Na Abba dana Imran dana Nura sai na Yusuf gabadaya sun Lalace sun yi kasa Saboda ajiya Tayoyinsu sun Faffashe ba kyan gani sun yi kura Har sun gaji sun Fara Kokewa saboda Zama Waje Daya,Domin kana ganinsu Zaka Fara Tunanin da wahala su tashi Har su iya Moruwa koma sun Morin sai sun Dade a gareji suna cin uban kudi.
Kuka Abba keyi Reras sanda suka Shiga Ainihin Falon gidan ba Kurar Daya bata gidan bane Damuwar ba yana Tuna each and Single Moment da suka gudanar acikin wannan kayattacen Gidan shi da iyalansa da Matarsa sai gashi komai ya Zama Tarihi.
Abubuwa Dadama agidan nan sun Lalace kama Daga kayan kallo Frigde da Sauransu kujeru ne sai gadaje basu yi komai ba ammh duk wani kayan Wuta ya gama aiki gidan yayi kura yana Duk ya Rufe ko"ina sai da Basheer da Yusuf suka rika saka Sanda suna Cire inda Zasu Taka.
Wasu Kofofin Dakunan ma Sun ki Budewa sun kame sai an kira masu Cire Kofa Imran ya shiga Dakinsa yana Kallon kowani kusuwar Ya Duba Cikin Wardrope dinsa da Gabadaya kura suka mamaye ka'ina kyawawan Suit dinsa na kamfanoni Dabam Dabam da ke shake Cikin Wardrope din Duk sun gama sauya kala Kama Daga Takalmansa na Kowani kamfani masu Tsada da yarari duk sun sauya kamanni da Dadewa da kura komai nashi acikin Perfect ne Lokacin yana amsa sunansa Banker Imran Abubakar malami ba yanzu da komai ya sauya ba shi kanshi yaji Tahowar kwalla yayi saurin kauda kai bai bari Hawayen ya Zubo ba yasa Hannu ya Dauke kwallarsa.
Haka bangaransu Yusuf da Abba Suna Bin ko"ina da kallo suna Hawaye Daddy da Basheer suna ta basu baki,Basu iya ko zama ba saboda ba Wajen zama suna dai Tsaye suna Zagaya Ko"ina na Gidan suna kallo Suna Tunawa da Rayuwar baya.
Daddy ya fara kawo shawaran bazasu Tafi su bar gidan nan hakan nan ba Zai kara Lalacewa Tunda ba su da Sha"waar kara Rayuwa aciki sai dashi Abba yace bazai Taba saida wannan Gidan ba Har Abada Ko ya Mutu ga Yusuf ga Imran ga Munari gidane mai Dimbin Tarihi zai barsa Kila ko watan Watarana Su rika zuwa Hutu ko kuma Yanayin Rayuwa zai iya maido da Daya Daga Cikin su Imran nan garin Tunda suna da Muhallin Abubuwan bazasu yi wahala ba Kowa yayi na"am da mganar Abba ammh sai aka Fara Tunanin yadda za"ayi Daddy yace Dole kafin su koma a samu wadanda zasu Zauna agidan nan da sunan gadi su kuma Rika gyarashi suna kula Dashi Domin barinsa ahaka shine Jidali.
Suna cikin Hakane sukaji Sallama Daga Kofar Falon gabadayansu sun ji mamaki Abba ne da Daddy suka Fita Haraban Gidan Ikon Allah Abba kawai ke Fadi na ganin Abokinsa Amininsa Dr.Isa Ali Argungun Abokin aikinsa ne shima Lecture ne a nan Lagos Universty,Sai dai shi yana Shashen Kimiya da Fasaha ne Wato Computer Science sannan kuma Makota suke da juna Domin gidansa da Gidansu Gida Dayane Tsakani sun yi Zaman Amana sosai da Amintaka Duk garin Lagos Abba bai da aboki kamar Dr Ali argungu Matarsa Hajiya Barira Kawar Anni ce Lokacin tana Raye,Sannan karamin Dansa Ibrahim Khalil,ma"ikacin Banki ne shima Tun alokacin da shi kadai Imran ke gaisawa Sama sama abota dai wacce bata Zama Takura ba yayinda shi Khalil ke aiki da Firstbank nan Reshen Jahar Lagos shi kuma Imran yana aiki da GT bank suna Haduwa Lokaci bayan Lokaci in Bankunansu ta Tura su wata Seminar Tunda dukkansu Zakwakurai ne abangaran da suka karanta ma"aikatan su na matukar ji dasu,yanzu ma Tare da Khalil suka shigo Abba suka Rumgume juna da Dr.Ali Argungun suna masu Hawayen Farincikin ganin juna jin shuru ne yasa su Yusuf suma suka Fito Haraban gidan nan suma suka ga Abun mamaki nan fa aka Shiga gaisawa Cikin Tambayan juna bayan Saduwa Dr.Ali argungun yaja su zuwa Gidansa Tunda nan yayi kura ba wajen Zama basu yi gaddama ba Sanin sa ai shakiki ne ga Abba ko su Daddy sun san Tunda Lokacin Rasuwar su Anni Har Dukku ya Taka Daga baya daya samu Labari shi da Iyalansa.
Alokacin da Abun ya Faru bai sani ba Har Suka zo suka tafi da Abba chan Dukku sai daga baya yaji Labari kuma garin Dukku ba boyayye bane sannan Gidan Marigayi Alkali Dukku ma haka da Tambaya da komai suka isa Dukku Lokacin Abba yana Halin Rashin Lafiya baya gane komai sai sambatu Dr.Ali argungu ya Dawo da Tsausayin Abokinsa matuka acikin Ransa kuma yasha zuwa Dubasa Har Dukku kusan Sau Uku Daga baya da suka Dawo Lagos kuma basu Dade ba aka nemesu aka Rasa ya Zata sun kara komawa Dukku ne sai da yaji Shiru ba waya ba komai Achan Jami"a ma ba wani Labari yasa yaje Dukku da kansa nan ya iske Labari mara Dadi an nemi Dr.Abubakar malami ko sama ko kasa Shi da Sauran yaransa ba'a gansu ba Lokacin ya gana Daada Tana ta kuka Tana Bayyanamai Damuwarta ya Dawo Lagos shima da Damuwar Abun kuma shima yayi ta Bincikensa ba wani Labari sai dai ba Cire rai ba
Suna da Lambar juna shi da Daddy yana Kiransa Lokaci bayan Lokaci yaji ko an ji Labarin Malami sai dai Shuru ne,Shima Daddy yakan kirasa yaji ko da wani Labari Lokacin da Abba ya Dawo Wasu abubuwan sun Doke wasu Shiyasa bai samu Damar Sanar da Abba komai ba.
Dr.Is Ali Argungun Koda yaushe zai shiga gida ko zai Fita sai ya kalli get din gidan nan ko zai ga an Budesa Shekaru uku da wani abu bai Taba ganinsa a Bude ba sai yau daya Dawo Daga Wajen aiki yaga Gida a Bude mamaki ya kamasa haka ya Shiga Cikin Gida yana Fadama Hajiya Barira Ita ma tayi mamaki suna cikin mganar ne sai ga Khalil ya shigo shima Dai zencen yake musu shine Dai Hajiya Barira tace su leka su gani ko yan"uwanshi Daga Dukku ne kila zasu samu wani labarin suna zuwa kuma sai suga Abba sai Sabon Labari ya tashi anan Falon gidan Dr.Isa Ali Argungun Abba nata bashi Labaran bayan Rabuwa shima yana gayamai Faculty dinsu tayi rashinsa Wlh kuma yana mai Tabbatarmai ko yau ya koma Zai koma da aiki Jami"ar Lagos bazata yi sakacin rasa Zakwakurin Malami kamarsa ba,Nan sukayi Lunch Cikin Farincikin kara Saduwa da juna Hajiya Barira ta Fito suka gaisa Jin cewa su Abba kano suka koma da Zama yasa Dr.Isa Ali argungun yace ma Abba ai kano gida ce Hajiya Barira yar Fagge ce dake kano ne suna zuwa kano Sosai Rashin Sani sun gaisa ta karamai gaisuwan su Anni ya Amsamata Cikin Jin Dadin karamincinsu yana ta godiya.
Hajiya barira bata da wani D"a gabanta sai Khalil shi kadai ne bai yi auree ba kuma shi kadai ne Namiji Sauran duk matane suna gidajen Auransu,Shiyasa Gidan Daga ita sai yan aikinta da Mijinta da Danta Khalil.
Sai da suka yi Sallar Azahar anan cikin Gidan Yusuf yayi musu Limanci,bayan sun idar ne kuma suka kara Tsinkewa da Hira Khalil ma da Imran Cikin Ikon Allah suna ta mgana kan abunda yashafi aikinsu Yusuf da Basheer suna ta mamaki duk da Daga Khalil din Har yusuf din Daya ne bama su son Hayaniya bane da yawan mgana ba.
Daddy shi yayi ma Dr.Isa Ali Argungu mgana kan wanda za"a Samu ya rika gadin gidan Abba,Dr.Isa Ali argungu yace Faduwa tazo Daidai da Zama Megadinsa Buba Dan BAuchi ne Bahaushe ne nan suke Xaune dashi Shi da iyalansa suna BQauters,Daman kaninsa yazo kwanakin nan Wajensa yake yana ta neman Aikin gadi bai samu ba in hakane sai ya koma Gida ya Dauko iyalansa su zauna a BQuatre suna Kula da gidan Allah barshi Duk wata sai arika Biyansa Abunda ya Sauwaka Duk da yaso Abba ya baro Kano ya Dawo Lagos kamar baya su Cigaba da aiki Tare Abba ya nuna a"a Shi Zaman Lagos ta Fitarmai arai kwata kwata bai mtsamai ba Tunda Daddy yace A Buk kano zasu neman ma Abba aikin su gani ko Za"a Dace Tunda Lokacin aikinsa bai Wuce ba..
Ba bata Lokaci akayi ma Buba Megadi mgana Shida kaninsa Lurwanu sun ji Dadi Matuka Abba yace yaje ya Dauko iyalansa su zauna agidan su Rike Amana su kula da gidan sannan Yusuf ya Dau alkawarin Biyansa Kudi mai Tsoka Duk wata wannan abun yayi Musu Dadi suna ta Godiya.
Aranar basai da aka kwana ba aka Fitar da komai na Gidan Daya Lalace aka Zubar Motocin kuma aka Saida su aka Karbi kudadensu kalilan ba masu yawa ba Aranar basu koma Hotel ba agidan Dr.Isa Argungu suka kwana Washegari da Safe Lurwanu ya dau Hanyar gida zai je ya Dauko Iyalansa Kudin Motan da komai Dr.Isa Argungun ya basa,Yana Tafiya shida Abba da Daddy da Ya Yusuf da Basherr suka tafi Jami"ar Lagos inda Abba yayi aiki Shekaru ashirin abaya Abba yaga Tarin Sauye sauye yaga wadansu wanda sukayi aiki Tare Lokacin wasu kuma sun bar Wajen wasu kuma sun Rasu,Shugaban Jami"ar da kansa ya Nemi Abba ya dawo ya Cigaba da aiki da inda