Showing 144001 words to 147000 words out of 235479 words
Chapter 49 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt
take mai Wuyar Sha"ani
Tana da Tabbacin sun kamu da son juna basu sani ba,Soyayyar da ake Kira Makauniyar soyayya ta Tabbata Inteesar bata Fahimci Feeling dinta ba Shiyasa bata taba gayamata ba Gabadaya sai Tsausayinsu ya kamata Tuna ga Sajida ta shiga Tsakiyarsu,Ta Tabbata Duk da ya Hallata ya Hadasu Dukkansu ya aura ammh Hakan bamai yuyu bame Saboda Kishi kuma sannan su yan"uwan juna ne hakan zai kawo Tarin mtsaloli masu yawa Barinsa shine mafi Alheri.
Tana cikin wannan Halin ne taji Kiciniyar Bude Kofar Tiolet din yasa tayi Saurin maida mata wayar ta ijiye sai ta Dauki Tata tayi kamar Tana Latswa.
Inteesar na Fitowa bata Zargi komai ba Ta tambayi Munari ko Tayi sallah ne tace mata eh itama ta Dauro alwala tana gama Shafa Lotion dinta ta saka Dogowar rigarta baka ta Zurma Hijabi Ta Tada Sallah bata idar ba Daddy ya Kira Wayar Inteesar,Munari ta Dauka Jin ita ne yasa suka Fara gaisawa kafin ya bama Umma su tsinke da Hira,Umma ita yanzu ta zama mai ya"ya Biyu Inteesar da Munari suna wayar ne Imran yayi ta kira ita ko ji ma batayi ba,Har Inteesar ta idar da sallah suka zo suka Hadu suna ta wayar Har Umma ta gaji tace subama Mama wayar Lokacin har tatashi tayi Sallah suka Mikamata wayar ta cigaba da mgana da Ita.
Imran yana Tsaye ne ammh ya kasa Taka kafarsa Saboda Nauyin Datayimai cikin wannan Halin Sagir ya Fito Daga Shagonsa,Har da zai Shiga Gida,sai yaga Imran din yana nan Tsaye sai ya fasa ya Dawo yazo ya Tsaya agefensa yana Fadin"Mu shiga wajen Mama mu ci Abinci..Tunda bazaka Fadamin meke damiunka ba..!
Yafada Cikin kulawa Jin haka yasa Imran ya Dago Jajayen Idannuwansa yana kallonsa Cikin jin yadda Zuciyarsa ke suya Sagir daya ga Idanuwansa sun yi ja yace"Subhanallah me ke damunka Imu..? Kan mganata ce..? Am sorry bazan kara maka wannan wasan ba indai hakane..!
Yafada Cikin bayyana Damuwarsa Imran Ya Cije bakinsa kafin yace"Ni da wannan yarinyar ne.!
Ya fada kai tsaye saboda bai da wata Munafa Cikin mamaki Sagir ya Kallesa Kafin yace"Wata yarinya..? Sajida..?
Yafada Cikin Dariya Imran ya Saki katon Tsaki kafin yace"wacece kuma Sajida..? Nifa na manta da ita Saboda na Shafe shafinta Tun a dukku..Inteesar nake mgana kanwarka..!
Yafada yana kara jin wani Haushi ya kumesa Sagir yace"Kanwarmu dai ai kaima Takace ko..?
Imran ya kallesa Cikin ido kafin yace"Ta Raina ni ina Kiranta bata Dagawa kuma in na Tura mata sako bata bani amsana ba..? Wai kuma kasan Abunda yasa naji Raina na kuna..?
Sagir kamar gaula ya Girgizamai kai Cikin Bayyana Bacin Ransa Imran yace"Na kirata Call Waiting tun dazu..Kaga kenan tana gani..Ni ne ta Raina bazata Dauki wayataba ammh Tana chan tana mgana da wannan Dan"iskan yaron..!
Yafada yana Cizan Lebensa na kasa da karfi.
Sagir Daya gama yin galala yana Sauraran Imran cikin son Tabbatar da Zarginsa yace"Kara kiranta mu gani..!
Imran ba Musu ya kara Doka ma Inteesar wayar har lau lokacin Call Waiting Cikin Hargagi ya nuna ma Sagir yana Fadin"U see..Na sani Dashi take waya..Ji na nake kamar yanzu na Bude ido na gansa agabana wlh in na Fara Dukansa sai ya Mutu uban wa yace ya Kirata..? Inteesar bazata taba Zama nashi ba Har Abada Ni Imran zuciyata bazata Jure ganinta da wani ba..!
Yafada Cikin Fitar Hayyaci da Bacin rai wanda yasa baima san me yake Fada ba.
Sagir Daya sake baki kawai yana jinsa Baisan Sadda ya saki wani kayattacen Mirmishi ba Kafin ya kalli Imran Ido Cikin Ido yace
"Imu U are in Love...KANA SON INTERSAR..!
da wani mamaki da Razana Imran ya ware idanuwansa masu girma akan Sagir Kalamansa suna mai yawa amsa kuwwa a kunnuwansa.
KANA SON INTEESAR..Wannan So ne..? Yana sonta ne Daman..?
Tambayan Daya Runtse ido yana yi ma kansa kenan.
*Janafty*
3/22/22, 23:14 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�10*
*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*
Kallonsa Sagir ya cigaba da yi yana Fadin"Ko ka yarda ko karka yarda Kana son Inteesar Dama ni Tuntuni naga alamun haka sai dai nayi Shuru ne Tuntuni ganin kai kanka ma baka san Ka kamu da soyayyarta ba..!
Ya karishe fada cikin son Tabbatar da mganarsa ganin yadda Imran din ke Girgiza kai cikin alamun zai musa mganarsa.
Imran kuwa mamaki ne ya cika shi yasa ya kasa mgana sai Girgiza kai kawai yake yi yana Tambayan kansa Daman haka so yake..? Shi yana sonta ne Daman..? Kai ina wannan ba Soyayya bane shi bai taba soyayya ba kuma bai santa ba kuma baya so ya santa ya Dauki Soyayya a mtsayin Shirme da bata Lokaci Da Takura shi kuma baya ciki da duka Daga ciki.
Kenan Saboda yana sonta yasa yake son ganinta..? Baya son kukanta..? Baya son tayi mgana da kowa yana jin Zafi acikin zuciyarsa Duk Sanda ya Tuna da Lokacin da Khamis ya Rike mata Hannu wannan ma So ne Imran..?
Acikin Zuciyarsa yake Tambayan kansa yaki yarda ya bama Zuciyarsa Daman karban Rauninsa da Feeling dinsa ya karyata kansa da cewa Imran wannan ba so bane,Kawai dai kana Tsausayamata ne saboda ita din yar"uwanka ce kuma mai kula dakai kaima ka kulasa to Khamis fa meyasa yake jin Haushinsa akanta..?Shima So ne..? Kai ina a"ah yana jin Haushin sa ne Saboda Son kai irin na Baffa Kabiru da Mami Asma"u sannan bai Dace da Inteesar ba ammh shi ba Sonta yake ba Sagir bai Fahimce shi Daidai ba.
Sai da yaga Duka nazarinsa kana ya Bude Dararan Idanuwansa da suka kala sukayi Jajir Saboda Halin Dayake ciki Sagir na kallonsa yana Nazarinsa Cikin Taunan Lips dinsa yace"A"a ba gaskiya bane..Baka Fahinceni ba..Ni ba Sonta nake yi ba..Ban taba son kowa ba..Ni ban yarda da Soyayya ba Abunda kake Tunani bashi bane..!
Yafada yana wani Dakuna Fuska Lokaci Daya yana kara Hade rai kada ma Sagir ya kara Fadin wata mgana.
Sagir yayi Mirmishi Sanin Daman mawuyacin Abu ne Imran ya yarda da Feeling dinsa da Zuciyarsa saboda Sanin Halinsa yasa yayi Mirmishi mai kayatarwa kafin yace"Nasan daman zaka ce haka..Bazaka taba yarda da Zuciyarka ba..Ammh ko kaki ko kaso kana son Inteesar Imu..!.
Yafada Wit Full Confident Imran ya kallesa ido cikin ido kafin yace"Wannan ma ai mganar banza ce..Taya ya zan fara son wannan karamar yarinyar..?Ai nayi mata Girma na tabbata Ko Rabin Kirjina na Dora mata sai ta suma ballatana Duka Mazantakana infact ma ni bana son Soyayya da yara kanana ni da nake Fama da kaina na dawo ina fama da wata..Ina ban yarda da mganarka ba kama Daina Fada Raina yana baci ne..!
Ya karishe Fada yana saka Hannunsa Saman sumar kansa Sagir yace"Naji baka sonta meyasa kake jin haushi in Tana waya da wani..? Meyasa kayi Fada da Khamis a Dukku Saboda ita..? Meyasa kake da lambarta ni a Tunani baka taba ijiye lambar wata mace a wayarka ba sai ita kagani kuwa ita din ta Dabam ne Kana Sonta ne ammh kai kanka baka sani ba kaki kuma yarda da mganata ballatana ka bata Damar fahimtar Feeling dinka..!
Tsaki Imran ya saki bai yi mgana ba kallon Sagir kadai yake yi yana Auna mganganunsa Sagir kuma ganin Imran bazai yarda dashi ba sai ya Sauya mganarsa Cikin Danne Dariyarsa yace"To naji ba sonta kake yi ba..Ammh kai sai ka bari Khamis din yayi nasara akanka..?
Imran yamai kallon bangane ba Sagir yace"Eh ina Nufin Cewa fa yayi yana sonta da aure kuma Daada ta bashi Dama ya nemi yardanta yanzu in ta amince fa ya nuna kai ne baka yi nasara ba shi yayi nasara akanka kuma Rashin Nasara ba Dabi"arka bace Imran..!
Ya karishe Fada yana kokarin Hana Dariyarsa bayyana ganin yadda Imran ya gama yadda da duka mganarsa Zuciyarsa da soyayyar Inteesar suna ta Rinjayansa bai sani ba.
Imran ya jinjina kai yana Tuna Sanda Khamis ke fadin Inteesar sai ta Zama nashi shi kuma ya Tabbatar mai da karyansa baza ta zama nashi ba kenan Gaskiyan Sagir ne In yayi shuru To Khamis yayi Nasara akansa Dole ne yayi wani abu akai ya zama Dole ya Dakarar dashi,In yama Tuna Sunansa Ransa Har wani Tafasa yake saboda Bacin rai da Kishi.
Cikin Bacin ran ya kalli Sagir yana Fadin"Ka Fadi gaskiya Sagir..Baka Taba mgana mai kyau ba sai yau..Lalle Dole na nuna ma mara kunyar yaron nan mganata kamar Saran Takobi take in na Sara sai tayi yanka..kuma Nine Imran wanda in nace Abu bana Barci kirki sai na aiwatar da gudurina..,!
Sagir ya kada kai yana Fadin"Yauwa Abokina..nuna masa Bakin Rijiya ba wajen wasan makaho bane..!
Yafada yana Bubbuga Kafadan Imran Lokaci Daya yana Danne Dariyarsa.
Imran ya wani Cije bakinsa yana Fadin"Na tsani yaron nan ban san Dalili ba..ga mata da yawa ammh yace sai ita..?
Sagir yace"Shi nagani..yanzu to ina Mafita ta ina zaka Fara..?
Imran ya kallesa kai Tsaye yana Fadin"Ta inda aka Hau ta nan za"a sauka...!
Sagir yace"Auranta zaka nema..?
Yafada yana kallon Imran ido Cikin Ido.
Imran yayi Tsam yana kallonsa Zuciyarsa na Bugawa ammh ta natsu da mganar Sagir Cikin wani yanayi yace"Nima ban sani ba..Ammh in dai ina Raye acikin Duniyar nan yaron nan bai isa ya sameta ba Har Abada..!
Sagir yace"Ita Sajidan fa..?ya zakayi da ita..?
Imran ya saki Tsaki yana Fadin"Tuni na gama da Shafin wannan yarinyar..Ni ba ajinta bane..ba ita ba Harta iyayanta sun sani nafi Karfin su..!
Sagir dai kallonsa yake yi bai ce komai ba Tsausayi kawai Imran ke basa ganin yana cikin Halin Soyayya ammh bai sani ba irin makauniyar soyayyar nan mai Wahalar da mai yinta.
Yana cikin wannan Tunanin yaji Imran na Fadin"Yara nan suna cikin gidan nan ne..?
Yafada yana Nuna Gidan su Sagir da Hannunsa.
Sagir yace"Eh basu dade da Dawowa Daga makaranta ba suna ciki indai ba bayan Tafiyata masallaci suka Fita ba..!
Imran kai kawai ya Daga kafin yace"Bari na shiga gida..!
Ya bama Sagir hannu sukayi musabaha kafin suyi sallama Sagir ya shiga gida Imran kuma ya kama Hanyar gida yana Tafe yana Tsara wasu abubuwa Daki Daki.
Gobe Baffa Mustapha yace Zai zo zasu Tafi Lagos jibi Lahadi su dawo da Farko yace bazai je ba ammh Daddy yace sai yaje Haka kurum yaji bazai iya mai Musu ba ko don yana Baban Inteesar ne..? A"a Saboda shi bai kullace shi kamar yadda ya Kullaci Baffa Kabiru ba Shiyasa
Ya riga ya gama Tsara komai suna Dawowa Ranar Litini Dukku zai je Zaima Daada Diran Mikiya Duk da yana jin Haushinta ammh Yanzu zatamai amfani Dole ya Danne komai yaje suyi mgana,ammh kafin nan sai ya bata ma Inteesar Rai ta fara Rainashi,kamar shi ya Kirata tana waya Ta sagale shi a Call waiting ya Tura mata sako ta karanta tayi banza Dashi..? Tana chan tana waya da wannan Khamis din ko..?lalle sai ta gane bata da wayau ranta sai ya baci.
Har ya isa gida yana Huci shi kadai yana Cika yana batsewa Shiyasa bai ma Lura da Bakuwar Motar Dake Haraban gidan ba,sai da ya shiga ciki ne ya iske Sadam ne yazo gaida Abba Daga masallacin jumma"a yake.
Bai da yarda zai yi Dole ya Tsaya suka yi musabaha yadan Saki Ransa kadan ba Sosai ba Har yana Tambayan Sadam din ya yara..?bashi ba hatta Abba yayi mamaki sai da yayi Dariya yana kallon Imran Daya kara Dakuna Fuska.
Daki ya shige baisan Tafiyar Sadam ba sai La"asar ya Fito Daure da alwala na Tafiya masallaci,ya riga ya gama Tsara Komai Tare da Abba suka Tafi masallaci suka kuma Dawo tare,Jin gidan Shuru yasa yasan suna Gidam Mama har yanzu,Yusuf ne ya dawo alokacin Yana jin yunwa ya Fita Chan Bakin Titi ya siyo kankana da Lemo daya dawo bai shiga gida ba aharaban gidan ya ci Burki saman Motan Yusuf ya Haye ya wani karkace kamar Wani Saraki yana shan kayan Lambunsa Hankalinsa kwance ya samo Mafita,Abu Dayane yanzu agabansa yaga Inteesar so yake yaji Dalilinta na yimai abunda tayi mai kuma yana so yaji shin dawa take mgana awaya Data sharesa... ?
Zuciyarsa zAfi take duk sanda ya Tuna da wani Khamis Shiyasa ya Kasa ya Tsare yaga shigowarsu yau in bai ganta ba zai taka Har Cikin gidan Mama yaji Dalilinta na maida shi Abokin wasanta saboda Taga yana mata Dariya.
Yana gama Shanye kayan Lambunsa ya Zaro karan Sigarinsa ya kunna ya Cigaba da Fesa Hayaki iro megadi na Daga gefe kan bencinsa yana kallonsa aransa yana ayyana ga Mutum har Mutum ammh ya bata kansa da shan Sigari.
Yayi Nisa Cikin Duniyar Hayakinsa Kamar Daga sama yaji Dariyansu Sama sama da Sauri ya Bude Idanuwansa da suka Fara Lumshewa ya sauke su akansu suna Tafe Hannayensu cikin na juna ita da Munari daga alamu ma basu Lura dashi ba Munari ce ke nuna mata wani abu acikin Wayarta yasa suke Dariya Shagala yayi da kallonta ganin yadda Fararan kananun Hakoranta suka Bayyana..
Kara Ware ido yayi akanta Cikin Bugawar Zuciya gabadaya ta gama Tafiya dashi acikin Ransa ya Furta"Tana da kyau in tayi Dariya..!
Ganin bama su san da wanzuwarsa ba a wajen yasa yayi saurin Wurgar da Taban Dake hannunsa a kasa haka kurum yaji karo na Farko baya so Inteesar ta kara ganinsa yana shan Taba tunda yake bai taba ganin wani yaji kunyar shan tabansa ba Karo na Farko a Rayuwarsa ba sai yau.
Saukowa yayi Daga saman Mota yama gyara Farar Rigarsa data Tattare Saboda Zama ya sauya kaya Daga Jallabiya zuwa bakin wando da Farar Riga.
Daga Inda yake Tsaye ya Kausasa Murya yana Fadin"Kai ina zaku..?
Gabadayansu sun ji Faduwar gaba atare suka juyo suna kallonsa Munari ta Fara rawan jiki banda Inteesar data Kuramai ido wami sanyi na Shigarta Farinciki ya Cikata data gansa kamar Wacce ta warke makanta Shima ita yake kallo kai Tsaye sai dai ya san Takunsa Kauda kai yayi ya kara Daure Fuska Cikin Daga Murya yace"Da kuka Tsaya anan ni kuke so nazo na Same ku..?
Yafada yana kara Hade rai,Ai da Sauri sum sum suka kariso gabansa Suna Dukar da kai kamar Munafukai,Inteesar tace kadai taga bazata iya jurewa ba ta Dago Karaf suka Hada ido daman ashe ita yake kallo,Kallon juna suke Daga karkashin zuciyarsu suna jin wani Salama da Farinciki Imran Har boyayyiyar ajiyar Zuciya ya sauke saboda ganinta kamar an ce mai an gafartamai Zunubansa sai da yana kallonta yaga ta Ramemai ta idaanuwansa itama Salama take ji da Farincikin ganinsa Idanuwanta suka cika da kwallar ganinsa sai dai itama taga yayi mata Rama acikin Idanuwanta Dukkansu sun Jigata matuka da Rashin ganin juna sai dai Raunin Intee yafi bayyana Imran kuma yana Kokarin Boye Rauninsa ne.
Munari da kanta yagaji da Dukewa ta Dago ai sai ta ga an kure juna da kallon Soyayya sai ta Ware ido kawai ta na kallon Ikon Allah Dadi da Farimciki Lokaci Daya da matsanancin Tsausayinsu na Ratsata Har batasan ta shagala da kallonsu ba sai da taji Imran ya Daka mata Tsawa Domin ya ganta sanda ta kafe su da ido Da Sauri ta sadda kanta tana Kokarin Daidaita kanta
Hade rai yayi saboda kada taga Fuskar Rainasa cikin bada Umarni da Dakiyarsa yace"Tsayuwar Uban me kike yi..?Bace min dagani kafin na Sauya Miki kammani Nonsess..,!
Ai bai ma Rufe baki ba Munari ta bace da Sauri aranta Tana Fadin"basai takai ga Haka ba..!
Kamar ta Kifa wajen shigewa Cikin Falon Har Inteesar da ta bita da kallo ta Kusa Dariya yana kallonta Tana Juyowa suka Hada ido Harara ya sakarmata yana wani Kara Dakuna Fuska
Tasan Laifinta Narai narai tayi mai da ido kafin ta saka Duka Hannuwanta biyu,ta Rike kunnuwanta Dake Cikin Farin Hijabin Dake jikinta Cikin wata irin Sanyin Murya tace"Am sorry..Sorry..!
Tafada Idanuwanta na cika da kwallah Fuskarta yake bi da kallo yanayinta na Ratsashi cikin Dan kauda kai yace"Ashe kinsan kinyi Laifi ko..? Haka kika Raina ni ko..? Saboda kin ga ban taba kwallo Dake ba ko..?
Da Sauri ta Shagwabe Fuska Tana Fadin"To bana baka Hakuri ba..!
Tafada Tana Turo bakinta gaba Sha"awa ta bashi ya Tsaya yana kallonta ji yayi kamar ya kama Bakinta yayi ta tsotsa Shawaran da zuciyarsa ke basa kenan ammh yayi Saurin kauda wannan Cikin dan Hade rai yace"Ni kike Turama baki..? Shagwaba ko...?shagwaban ki zai Dawo kuka yarinya..!
Yafada kai Tsaye yana Tusa Duka Hannayensa Cikin Aljihun wandonsa yana More mata kallonta ji yake yana Cikin Farinciki gsshi ga Inteesar kamar bai taba jin kansa Cikin wannan Halin ba indai suna Tare sai yaji sa kamar yana yawo saman Gajimare saboda Farinciki.
Jin Abunda yace yasa ta Rufe bakinta Tana yar Dariya kallonta kawai yake kamar ya kamata ya Rumgumeta haka yake jin wani yanayi yana Shigarsa Tuna abunda ke Cinsa araina neyasa ya Hade ransa kafin yace"Shine na Turo sako kika gani kika ki kulani ko..? Kuma na Kiraki baki Dauka ba Saboda kina chan kina Waya da wannan D'an iskan yaron ko..?
Yafada yana bayyana Bacin Ransa Lokaci Daya yana kara Hade Girar sama data kasa
Inteesar ta waro ido Lokaci Daya Tana Fadin"Yaushe..!?
Hararanta yayi kafin yace"Ok nayi karya kenan ko..?
Da Sauri tace"Ni ban ce ba..!
Shima Cikin Saurin yace"U mean dat..!
Inteesar ta marairai ce kafin tace"Allah ban gani ba Ya Imu da yaushe..? Nima ai ina ta kiraka baka Dauka ba nayi ta Tura maka sako Shiru na Damu har kuka nayi ta yi..!
Tafada Cikin Damuwa Idanuwanta sun cika da kwallah
Kasake yayi yana kallonta baya so yayi mgana baisan me zai ce mata ba yasa ya kalleta Cikin Idanuwanta kafin yace"Meyasa kikayi kuka..?
kai Tsayen tace"Saboda kaki kulani ni kuma bansan Halin Dake ciki ba Shiyasa na Damu ina ta kuka..!
Tsigar Jikinsa Sai da ta tashi Haka yarinyar ta Damu dashi bai sani ba Wayyo Allah shima Data san irin Wahalan Daya sha Saboda ita da batace haka ba.
Kai ya Kauda kafin yace"Kada ki Sake kuka Saboda ni..kukan ki zai Hurting dina..!
Kallonsa Takeyi kai Tsaye kamar yadda Shima yake Kallonta kamar an ce su Haddace kamannin juna.
So yake yaji bada yaron nan take Waya ba yasa yace mata"Dawa kike ta waya Tun dazu..?
Inteesar ta Dago wayarta Dake hsnnunta Kafin tace"Daddy ne fa ya Kirani muna ta mgana ya bama Umma mukayi ta mgana dani da Munari Har Umms tace na bama Mama sun Dade suna mgana ni ban ma san ka kira ba..!
Tafada sai Lokacin data Bude