Showing 168001 words to 171000 words out of 235479 words
Chapter 57 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt
shi da Sajida..!?
Tuni taji komai ya Tsaya mata Farincikinta ya gushe Allah na gani Tana matukar Kishin Sajida ko Sunanta ta Tuna amtsayin Matar Imran sai taji kamar ta saka kuka.
Achan Dukku kuwa Wayar na katsewa Daddy ya Dago yana kallon Daada kafin ma ya samu Zarafin mgana ta rigasa da cewa"Me muke son ji..? Ta bakinta ai mun ji komai Daga bakin mai sunan Autana..Sannan ita amsar mace Daman Shuru ne Mganar suna son juna Gaskiya ne Domin nima na Dade da ganin Alamun haka.!
Tafada Tana kallon Imran daya Dakuna Fuska aransa yana fadin"Lalle nema Daadan nan to Datake kallo na dawa take?
Falon yayi shuru Daada ta cigaba da mgana"Mustapha ku fara shiri..Malami baka ce komai ba..?kuma bana son naji kayi ma Imran Fadan abunda yayi duk da ba bamai kyau bane ammh Allah ya Hallata Saki kuma yayi shi a gabar Daya dace gabar da muka samu Masalaha..!
Abba kansa na kasa yace"Shikenan Daada mu masu bin Umarninki ne Da dukkan Abunda kikace..Allah yasa mu Kulla alheri..!
Yafada yana kauda kai Daga kallon da Baffa Kabiru ke binsa dashi kunya yake ji Wlh Imran ya basa kunya sosai da abunda ya aikata ammh bashi da ta cewa Daada ta mara mai baya.
Daada ta gyara zama Tana Fadin"Yau fa nake son a Daura auran nan ga ya"yanku nan zasu Taya ku shirya komai kuma bana son bata Lokaci nan da Wata Daya nake son ayi Taron Tarewarta Ayi komai a gama cikin Lokaci..!
Daddy ne ya karkace Kansa yace"Daada sai naga ko abar Daurin auran zuwa gobe ne..! Kinga yamma Tayi kuma ko Goro da dabino bamu siya ba da zaki mana lamini zuwa gobe da safe karfe Tara na safe sai a Daura auran zuwa 10 ko 11am na safe kowa ya Dauki Hanyar inda ya fito ko ya kukace.?
Yafada yana kallon su Abba da Baffa Kabiru wanda yake kallonsu kawai a bai ce ba,Inna Maimunatu tace"Eh hakan yayi Daidai daada..kiyi Hakurin Goben sai a Daura da yau kuma da goben duk Daya ne a wajen Allah..!
Daada ta jinjina kai Tana Fadin"Shikenan...Kai Kabiru..?
Tajuya bangaransa Dago kansa yayi yana Fadin"Na"am Daada..!
Daada tayi Mirmishin su na manya kafin tace"Naji tunda muka fara wannan zaman bakace komai ba..? Kai zaka biya ma Danka Imranu Sadaki ko..?
Tafada Tana tsareshi da ido Cikin Rauni da wani Takaichi ma yake kallon Daada Bai samu ma Zarafin mgana ba Mami Asma"u ta Mike da karfi kamar wata mahaukaciya Sabon kamu,Shock din Daya Riketa sai alokacin ya Saketa ta kara Tabbatar ma kanta Daada ta gama Tozarta ta Imran ya gama Tozarta yarta ya gama Wulakantata Saki..?ko Tareewa batayi ba auran da ko wata Daya bai cika ba Shine za"a yi ma yarta wannan Sakin Tozarcin da wulakancin.
Daada ta kallah Ido na cikin ido tafara Fadin"Wlh ba"a isa ba..Ba wanda ya isa..Ni Asma"u aka shirya a Tozarta..Asaki ya'ta ko wata batayi da aure ba sakin Tozarci da wulakanci Sannnan agaban idon mu Daada kike cewa Baban Sajida ya sake biyama Wanchan mara Mutumcin yaron Sadaki..? Kai mustapha harda kai Ashe haka zaka ma Dan"uwanka ko Daada tace zata aurama yaron chan Yarka saboda Baban Sajida bazaka hanata ba? Kai kuma Malami Daman au nasani D'anka ai ya gagareka Duk Abunda yaga Dama shi yake yi ba kuma wanda ya isa yace don me to Wlh bazata sabu ba Bazan yarda akan Wannan al"amarin sai na shigar da ku kara akotu Wlh sai an bima ya'ta Hakkinta..!
Ta Karishe Fada Rauninta na Bayyana sai kuma ta fashe da kuka Tana kara Fadin"Wlh bazan yarda ba..Wlh bazan yarda ba..!
Take Fada Tana kuka har Gilashinta na Fadi kasa bata sani ba.
Daddy ya dago yana kallonta Cikin mamaki yace"wazaki kai kotu..Asmaa'u.?
Mami Asma"u ido na cikin ido take kallon Daddy da Jajayen idanuwanta Tace"Daada zan kai kara Kotu..Sai kuma wannan Tsagerin yaron.Duk Abunda ya Faru saboda ita ne Tsohuwa mai sonta kanta kawai ai ba Malami da Mustpaha kika Haifa ba Harda Baban Sajida meyasa baki nuna adalaci a kansa..? Kin cika som kai kuma baki da adal.!
"ASMA"U.......!!
Bata karisa ba Baffa Kabiru ya Dakatar da ita da karfin amon Murya yana Tsaye ne Ransa na Tafasa da abunda ya Faru da kuma kalaman da Ma"u take jifan Daada dashi ai duk Lalacewar Uwa ai uwa ce
Mami Asma"u bata Dagata ba ta Cigaba Da Fadin"Bazan yi shuru ba..Wlh bazan bari rashin adalci wannan Tsohuwar ya Rugamin gida da Farincikina ba..!
Wannan karon Daddy ne ya Mike cikin Fushi yana Fadin"Kar ki kara kiran mana sunan uwa kice bata da adalci..Uban waye mara adalcin in bake ba? Adalci me kike so Daada Tayi miki banda wanda tayi miki..! Inace anan wajen agaban kowa da kowa kikace sai bayan ranki wannan auran zai Tabbata kuma yau an cika Miki Burinki ga yar naki nan a gabanki an warware komai sai me..!? Nace sai me
? Bayan wannan adalcin kuma wani adalci kike so..?
Da kike Fadin Na yarda zan aura ma Imran Inteesar saboda ke sai naki yarda..? Miye aibunsa..? Jini nane dan Yayana Malami sai na gujeshi Saboda Rudin Duniya..? Ko kin manta Zaman mu na karshe da nayi mgana kan Hukuncin Daada cewa kikayi in adalci ne ni na bashi yata mana..?kin manta..? To ni ban manta ba shine yau na nuna miki adalci nan In kin Hanashi yarki bashi zai hana wani Uban ya Dauki tashi y'ar ya bashi ba nama Sauya mganata yau ba sai gobe ba zan biyama Imran sadaki na Dauramasa y'ata in kin isa Asma"u muga Barikin sojoji gabadaya ko kuma muga Duka kungiyar Lauyoyi acikin Gidan nan mara Mutumcin mata wacce batasan ana Raga mata ba..!
Ya karishe Fada yana Sauke Numfashi Daga gani Ransa ya riga ya gama Baci Umma ta saki karamin Tsaki a Fidi ta Furta Allah ya waddan naka ya Lalace.
Mami Asma"u idanuwanta sun Rufe Da kalaman Daddy cikin Fusata tace"Au haka kace..?to bismillah shege ka Fasa..kuma kada ka kara cemin mara Mutimci ai mara Mutumcin kun santa gata na...!
Bata kai ga karisa mganarta ba Baffa Kabiru ya karisa gabanta ya Daga hannu Zai kai mata mari cikin karaji yana Fadin"ASMA"U...!
Daddy ma ya yunkuro da Inna Maimunatu Ransu ya gama baci sai dai Daada ta Dakatar dasu Cikin Daga Murya tace"Kul..Kada wanda ya Tabata..Asma"u bata da Laifi ai ban Haifeta ba Laifin na wajen Kabiru shi da na Haifa bai nuna mata Ina da Wata Daraja ba duk Abunda Tayi shi ya bata Dama..!
Daada ta Fada sai ga Hawaye kuka Shabe Shabe.
Ran ya"yanta ya baci Hatta da Abba Harda jikokinta irin su Basheer da Sadam suna ta fadin wannan ai rashin Mutimcine gasikiya Baffa Kabiru ya gyara Rayuwarsa..
Inna Maimunatu na Huci tace"Gaskiya Yaya kabiru ka saki wannan matar taka ba matar kwarai bace ban ga Dalilin da zai saka igiyar auranka ta Cigaba da Zama kan wacce ta Zagi Daada ba kuma ta sakata kuka ba!
Khamis Dake duke yana ganin an kawo wannan gabar ya Mike da Sauri ya isa gaban Daada ya Duka yana Fadin"Don Allah Daada kiyi Hakuri ki Yafe ma Mami..!
Daada na Hawaye ta Kallesa tana Girgiza kai Lokaci Daya Tana Fadin"Batamin komai ba..Wlh ban Taba Rike Asma"u ba ko Zagina Datayi ai Tayi Daidai kabiiru na Haifa ba ita ba..In iyayenta ne ai bazata Zagesu ba..Daman ance dan kuka ke jama Uwarsa Zagi ni Ubanku yajamin da duk Abunda ya Faru..!
Ta karishe Fada tana kara Saka Kuka Daddy jikinsa Har rawa yake yana Fadin"Yaya kana gani fa? Agaban i don ka Ta Zagi Daada ta sakata kuka Kana Tsaye baka Dauki wani mataki ba..?
Baffa Kabiru ya Runtse ido yama rasa Madafa bayan Asma"u zai bi ko bayan Daada Tabbas an bata ma Asma"u sai dai bata kyauta ba abundaa Tayi Idanuwansa ya Bude yana Kallon Mami Asma"u cikin Kaushin murya yace"Ma"u ki Duka ki bama Daada Hakuri..!
Mami Asma"u ta tsaya kyam taki Dukawa Tana kallonsa Cikin Hawaye tace"Wlh bazan bata Hakuri ba ai ba wani Laifi nayi mata ba gaskiya na Fada..Saboda Hakkina sai nayi mgana Wlh..Na fada na kara fada bazan yarda ba..!
Ya sake yunkurawa Daada ta Daka mai Tsawa Tana Fadim"Kada ka Sake kamin Duka agabana gaban Sauran ya"yana da jikokina kabiru..Ranka zai baci..!
Tafada cikin bacin Rai kafin ta Mike Da karfi Ta kusa Faduwa ma sai da Inna Bintalo ta riketa.
Cikin Tsananin Fushin da ba wanda ya Taba ganin Daada dashi Tace"kaji kunya Kabiru yau na ce maka Kaji kunya..Yau ina ma Mahaifinka nada Rai Wlh shima sai yayi Tir da Haihuwanka..Komai ya Faru kai ne Sila banda kana Shashasha Sakarai ko Mahaukaci ne Imran na Tabbata zaka iya bashi yarka Saboda jini yafi Ruwa Kauri Malami fa Dan"uwanka ne Daka Saki nono ya kama ammh yau saboda Macen macen ma wacce kuka Hadu bayan ka samu iyaye da yan"uwa Saboda Bata Nuna amincewarta ba yasa kaima ka nuna ka kyamaci jininka Wlh ka bani kunya Tir da kai Tir da Hallayarka Ficemin agabana kafin Raina ya baci na Daga Maka NONO...!
Ta karishe Fada Cikin Tsawa da bacin Rai Lokaci Daya hawayenta na Zuba Baffa Kabiru jikinsa ya Fara rawa ya Zube gaban Daada yana Fadin"Don Allah Daa
"KA FITA NACE...KA FITA KABIRU BANA SON GANINKA AGABANA."
Tafada cikin Tsawan da sai da kowa ya tsorata Jiri ke Dibanta Tayi luu Zata Fadi Ya"yanta suka Tallbeta da Sauri suna Kiran sunanta kowa ya Mike harda Imran Dake tsaye yana jin Dadin Abunda ya Faru yau karyan Sonkai kuma ai ta kare
Daada Idanuwanta na Zubar kwallah Tana jikin Abba tace"Malami Ku fadama Kabiru ya ficemin Daga gida..Ya ficemin Daga gabana Dashi da matarsa Da Duka ya"yansa na Cire Hannuna akanshi da duka iyalansa Allah nagodemaka ina da wasu ya"yan kamar ku da yau bakinciki sai ya kasheni..!
Daada ta fada Tana kuka Shabe Shabe gwanin ban Tsausayi,Daddy ya kalli Baffa Kabiru dake duke yace"Yaya kuje kawai Tunda Daada tace kuje..Ku tafi din Kada ciwonta ya tashi Sakacin ya jawo mana Rasata gwara ka tafi kawai..!
Yafada shima kamar zai yi kuka,Baffa Kabiru ya kasa Mikewa saboda yadda Jikinsa yayi Nauyi,Sai khamis ne ya kamasa ya Daga sa Mami Asma"u kuma batayi Nadama ba ko ajikinta Wajen Sajida ta Nufa wacce Kanta ke kan Kafafunta Tana ta kuka ta Dago ta Tana Fadin"Ki daina kuka taso muje...Indai ni Asma"u na cika Mahaifiyarki sai na Daukan miki Matakin wannan Tozarcin da akayi miki Taso mu tafi da yau bamu da Muhalli da mun shiga uku..!
Tafada Cikin gatsali ba wanda dai ya Tankamata,Sajida kuwa taki yarda ta bita Tana Mikewa ta Turje taki Tafiya Mami ta juyo tana kallonta Cikin mamakin take kallonta kafin ta Samu Zarafin mgana Sajida ta Kwace hannunta Ta isa gaban Imran ta Zube Gabadaya shi baya ma yaja yana kallonta gabadaya sai kallo ya koma kansu.
Cikin kukan Fitar Hayyaci Sajida ta Hada Hannayenta Waje Daya alamun Roko Tana Fadin"kada kamin haka..Kada Laifin da ba ni na aikata ba ya Shafeni Laifin Mami da Dad bai kamata ya Shafeni ba..Kayi hakuri kada kace Zaka Rabu dani don Allah..!
Kowa sai ya saki baki yana kallonta Mami Asma"u da taji gabadaya Duniyar nan na Juyi da ita Cikin Fusata ta isa gaban Sajida ta Dagota Tana Fadin"sai me..? Nace sai me don ya Rabu Dake..? Wlh bai isa ya Tozarmu ba..Ke baki isa ki duka kina Bashi Hakuri ba sai dai ke ya Duka yana baki Hakuri..!
Dariyan Saman Lebe yayi na Kalaman Mami Asma"u Sajida kuwa Hannunta ta Fizge Tana Fadin"Ya isa Mami ya isa..!
Tafada Cikin Tsawa Lokaci Daya Hawaye na Shatatan mata.
Mami Asma"u ta Sandare Tana kallon Sajida cikin mamakinta.
Sajida ta Daga Ma Mami Hannu Tana Fadin"This is Enough Mami Enough..Ya isheki kin gama Lalata komai ammh duk da haka bazaki kama bakin ki ba..?
Kin Kashemin aurena auran da nake mafarkinsa..Kin Rabani da Mijina ne kuma kina kokarin Dora Laifin kan Daada Wlh duk Abunda ya Faru kece Silan komai to in baki sani ba bara na Fada miki Wani abu Wannan Da kike aibatawa kina Kiransa da sunanyen Banza Shine MAFARKIN YARKI..SHINE MURADINTA GINSHIKINTA..Eh Mafarkina Domin Ina SON SA..KUMA na shirya Mutuwa saboda shi kin taba Tambayanta Sajida kina son wannan auran..?ko kin Taba tambayata Sajida zaki iya zama dashi?kin taba jin Ra"ayina..?gaskiya ne kina da son kai..Baki son kowa sai kanki baki Damu da abunda Dad yake so ba ko yana so sai Ra"ayinki zai bi Baki Damu yayi biyayya ga Daada ba Kema zAi yi biyayya da Duka Dokarki Haka kike son adalci..? Ahalin kema bakya ma kanki adalci Wlh Tallahi kafin ki kai Daada kotu ni zan shigar Dake kara..Karar kan Uwa kamar Ki Barrister Asma"u Tafida ta kashema yarta aure Saboda Selfish dinki Ke din Wata irin uwace..?Nace ke din Wata irim Uwa c..!
Ai bata kai karshen mganarta ba Khamis ya Dauketa da wani Lafiyayyan marin da sai da ta Dukae Ta kara Fashewa da kuka.
Khamis Cikin Rawan jiki Alluran Soja ta tashi yace"Mamin kike Fadama Haka Saboda wani Sarakan Namiji..?ke wata irin Dabba ce acikin Dabobbi.?
Sajida da Idanuwanta suka Rufe ta Dago Tana Fadin"Eh naji ni Dabba ce..Indai akan Son Imran ne naji ni din Dabba ne kuma bazan Fasa fadin Mami Mai sonkai bace..!
Ya daga hannu ya kara kaimata wani Wawaan duka Mami Ta Taresa Da jikinta ke rawa Kuka take Kamar Idanuwanta zasu Fado yau bama Gilashin tuni yayi ta kansa Mami jiri Take gani Cikin Karfin Hali tace"Kyaleta Khamis...Kyaleta..!
Take Fada Jikinta na rawa Rikota yayi Daya Lura da Zata iya Faduwa yana kiran sunanta Cikin Duhu duhun Datake gani tace"Muje Mota..Muje Khamis jiri nake gani..!
Ai bai Tsaya ba ya Tallafeta suka fice bayan ya Bi Sajida da wani mtsayacin kallo,wacce ta Duke kawai Tana Kuka.
Ba wanda bai ji Tsausayinta ba afalon nan Hatta kuwa Daddy banda Imu da hakan yayi mai Daidai.
Dukawa yayi agabanta yana Fadin"Sorry fa..Ba Laifina bane..Gani nayi Dan Shaye shaye bai Dace da auran Diyar Lauyan lauyoyi ba..Ai hausawa sukace Babban goro sai magogin karfe,karamin goro sai ya nemi Daidaishi ke din matar Manya ce Diyar Barrister Asma"u sai Diyar Masu rike da madafin ikon gwamnati ba Imran da bai da komai ba Irina..!
Yafada Cikin Kwanciyar Hankali kafin ya Mike Tsaye Sajida kuwa kuka take kamar Zata Shida Baffa Kabiru ya kada kai shima Kwallar sun taru acikin idonsa ya Fice yana zuwa Mota gidan gaba ya shiga Mami Asma"u da Khamis suna gidan baya Tana ta kuka yana Lallashinta Fadi take Shikenan Nagama Tozarta ni Asma"u na gama Yawo..!
Baffa na jinta yayi kamar baya Motar Umarni ya bama Direeba kafin ya kwana yayi hon megadi ya wangale get suka Fice Daga Haraban gidan cikin su ba wanda iya Bude baki yace Ina Sajida domin ai idonsu ya Tabbatar musu da abunda ta aikata bata Bukatar bin su.
Suna Fita Dada jikinta ya Rikice Dole Daddy yayi ma Dr.Zubaida waya tace Gatanan zuwa Gabadaya Taron ya tashi Zucicyi ba Dadi banda Imran da Ransa Fes ko ajikinsa.
Sajida Inna Maimunatu ta kamata zuwa Daki Tana ta lallashinta da bata Nasiha ammh bata Daina kuka ba Su Abba basu samu natsuwa ba sai da Dr Tazo ta Duba Daada Jininta ne ya Hau ta bata mgunguna Tace data samu Barci Shikenan kuma adaina Tuna mata da abunda zai sakata Damuwa,jininta ya hau sosai su Abba suka amsa da ba komai zasu kiyaye dukkansu suna Dakin Daada sai da ta Samu barci suka Fito sukayi Sallar La"asar data Subuce musu, kowa ka gani ba Fara"a Saboda Halin da Taron ya tashi da abubuwan da suka Faru ba masu Dadi bane.
Banda Imran Dake cikin Daki yana aiki Bisa Laptop dinsa Ransa Fes ko ajikinsa Sagir na kallonsa yana ayyana Imu karshe ne Shi ko ajikinsa Daga gani ma Dadi yake ji to me zai Damesa...? Abunda suka aikata ne suke Girba.
*Shakira..*
3/24/22, 14:21 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�17*
*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*
Aranar dai ba"a samu Daura Auran Inteeasar da Imu ba kamar yadda Daada taso,saboda yanayin Motsawar Jikinta da yadda Zukata suke babu Dadi,Allah ya taimaka da Daada ta Farka taji Sauki sosai shi ya kwantar ma dasu Abba Hankali.
Ranar gidan na Daada kowa kadaha kadaham banda Imran Daya kusa Raba Dare yana aiki Saman Laptop dinsa ko irin agefen Kwalan Rigarsa.
Sajida kwana Tayi kuka kafin Safe Zazzabi ya Rufeta duk mai Tsausayi ya ganta sai ya Jimanta mata Umma da Inna Maimunatu ne ke ta kula da ita Ita Taje ta Fada ma su Abba Hankali Tashe suka Rankayo Dakin suka ga Halin Datake ciki,Sajida ai tasu ce koda Daada tace ta cire Hannunta akansu Bacin rai ne ammh Hanunka baya taba Rubewa ka yankeshi ka yar Daddy ne bai Damu ba gwara Da Daada Tayi ma Yaya kabirun haka ko ya dawo Cikin Hayyacinsa ammh har ga Allah yana Takaice da Mami Asma"u kuma da jin zafin yadda ta Ci ma Daada Mutumci bata gama ganin komai bama yanzu ta fara gani.
Abba kuwa Daman Dan Sanyi ne gabadaya ya shiga Damuwa bai so yayi ma Daada mgana ne ta Birkice mai ga kuma Dokar Likita Lura da hakan da Daddy yayi ne yace ya bar mganar kwana Biyu sai su dawo su samu Daadan su zauna su Lallasheta ta yafe ma Yaya Kabiru,Kada Fushinta ya Shafesa a mtsayinta na Uwa a garesa ammh awannan Lokacin sun fi Bukatar Natsuwar Daada da kwanciyar Hankalinta.
Da wannan mganar Abba yayi shuru bai ce ma Daada komai ba ammh Hakika Lamarin ya Tabasa yana ganin kamar shine Silan komai da Imran bai Saki Sajida ba da haka duk bata Faru ba sai dai abun nan da Hausawa kan ce Ka Haifi yaro ne baka Haifi Halinsa ba.
Da Dr.zubaida tazo duba Daada da Safe Daddy yace ta Duba Sajida ta Wahala Zazzabin ya narkemata Jiki ga Ciwon kai ga Nauyin kirji Allura Tayi mata ta Rubuta Drip da mganguna ABBA ya Umarci su yusuf da Basheer sukaje suka siyo suka kawo tayi mata amfani Dashi ta Dora mata Drip din bayan ta saka wasu Allurai aciki ba Dadewa Sajida ta samu Barci Duk ta jeme ta Lalace Fuskarta sai Sauran Bushewae Hawayen kukan Data