Showing 57001 words to 60000 words out of 235479 words

Chapter 20 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt

Janafty   

14 Jan 2025

16168

cafke Cikin Murna Tana Fadin"Shikeman Daman na Fadamiki..Haduwarmu Daga Allah ne..!.Inteesar tace"Na yarda da Mganarki..!
Daganan ssi Hira ta Tsinke kamar sun Shekara da Sanin juna,Haka kowanensu ke jin wani Farincikin na yau Kadai da suka Hadu,karin Farincikin Inteesar ma Da suka Tabo bangaran Karatu ta Fahimci Munari Tasan Abunda take yi Sosai,nan tace zata ari Wasu Notes dinta ta Kwafa Daga baya sai Munarin ta Koyamata Inda Bata gane ba Sai gashi Tare sukaje masallaci sukayi Salla Daganan suka Shiga Shago Inteesar ta Siya musu Freshyo,tazo da Cake suka Koma Suka samu wani Waje suka Zauna suka ci suka kora da Madara,Kafin su Shiga Lacture suka Duba littafansu Munari na kara yima Inteesar Bayanin karatun da akayi musu a baya Inda bata gane ba,har Lokacin Shiga Lacture yayi suka Shiga Tare suka kuma Zauna Waje Daya yan ajinsu sai mamaki akeyi Wasu acikin Ransu sukace sun Dace da juna ganin dukkansu Daman basu da kowa acikin ajin.
Ranar har suka gama Lecture dinsu na Ranar Suna Tare da juna 6pm suka Tashi,Tare suka Fita Bakin get suka Samu adaidaitan Gadon kaya Gidansu Sagir ne Farko kafin gidansu Munari ana Zuwa Inteesar tace zata Sauka Sai Munari itama ta Leko Cikin mamaki tace"Wai nan gidan kike Zaune..?
Inteesar na Shirin Bama mai adaidaita Kudin ta juya tana Fadin"Eh kinsan Gidan ne..?
Munari ta Fito Itama Tana Fadin"Sosai ma..Gidan su yaya Sagir..Ai abokin Yayana ne Ya Imu..!
Inteesar ta Washe baki ta ba Munari Hannu suka Tafa Tana Fadin"Abun mu Chas Wlh..,!atare suka Saka Dariya Bayan Inteesar ta Hada duka ta Sallami mai adaidaitan suka Nufo Gidansu Sagir Munari na Fadin"Ai Ni gidamu yana gaba kadan ne..!
Inteesar tace"Ayya Dayake Tunda nazo ban Taba Fita waje ba Daga makaranta sai gida..Bari mu Shiga mu Fito sai na Taka miki naga gidan naku..!
Sun Kariso Kofar gidan kenan sai ga Sagir ya Fito Yana yarfe Ruwa Daga Fuskarsa Kamar a mafarki ya gansu Tare bai Daina mamaki ba Har suka Gaisheshi ya amsa yana Fadin"Inteesar ina kika Hadu kuma da Munari..?
Inteesar na Mirmishi ta Kalli Munari sukayi Dariya kafin ta Kalleshi Tana Fadin"Makaranta yau muka Hadu..Ashe Course din mu Daya kuma ajin mu Daya..Ashe ma muna kusa sai da mukazo take cemin ai tasan nan Gidan kai abokin Yayanta ne..!
Sagir yayi Mirmishi yana Fadin"Eh Wlh..Nasan itama ta Fara zuwa makaranta To ban yi Tunanin Abu Daya kuke karanta ba Abu yayi kyau kin ga ke Inteesar kin samu kawa kema Munari kin samu kawa,sai ku Dinga Taimakama juna amakaranta Tunda kuna kusa..!
Suka Hada baki Wajen Fadin insha Allahu Sagir ya wuce yana Fadin"Ke Munari kada ki Zauna fa ki Fito ki tafi Gida..Yanzu ma muka Rabu da Yayanki ya koma Gida su Taho Salla Tare da Abba..!
Inteesar ce Tayi Saurin Fadin'"Yanzu Zan Rakota Ya Sagir..!
Ya wuce yana Fadin"Kuyi Sauri kunji an Fara Kiran Sallar mangariba..!
Daga haka ya Shige Shagonsa su kuma suka Shiga Cikin Gidan suka Iske Mama a Tsakar gida Tana alwala ta Dago Tana amsa Sallamarsu itama Bakin ta Sake tana Kallonsu Daidai ta Idar da alwalan ta Mike Tana Fadin"Ikon Allah wa nake gani kamar Munari..?
Dariya tayi Tana kallon Inteesar Tace"Nice Mama..!
Mama ta Rike Haba Tana Fadin"Ikon Allah Maryam ina kika Samo ta..?
Inteesar tace"Makaranta Mama ashe ajinmu Daya bamu san muma kusa ba..!
Mama tace"Kaji wani ikon Allah..abu yayi Dadi ku shiga ciki ai nan kamar Gidane ga Munari gidansu na gaba Kadan,Imran yayanta ai Abokin Sagir ne na Sosai Ya kwana Biyu bai Shigo Gidan bane da kun Hadu..!
Suna gaba tana Bayansu Zuwa cikin Dakin,Sai da suka Zauna kana Suka gaisa da Munari Inteesar Tana ma Mama Bayanin Haduwarsu da Sagir akofar Gida da abunda yace Mama tace"Ya fadi gaskiya..Munari ga Kawa nayi miki Diyar kanwatace Salaha kema Inteesar ga Kawa nan munari Makota muke dasu..!
Suka Hada ido kafin su Hada baki Wajen Fadin insha Allahu Daganan Mama tatashi Bayan tacema Inteesar abincinta na Kitchen Itama kuma ta Shiga Ciki yin Sallah Inteesar Tayi ma Munari Tayin Cin Abinci sai ta Mike Tana Fadin"Nagode Kawas ki bari in na Sake Dawowa zanci..Yanzu Tafiya Zanyi in ya Imu yaga ban Dawo ba Wlh Zan ci kaniyata ne..!
Jin haka yasa Inteesar tamike tace suje ta Rakata,Kayan Hannunta Kadai ta ijiye suka Fice Tunda Mama ta Tada Sallah Tafiya kadan sukayi sai gasu Kofar Gidansu Munari ta Kalli Inteesar Tana Fadin"To kin ga GIDANMU..!
Inteesar ta Kalli Gidan Tana Fadin"Nagani Ai nasan Gidan yanzu..Da Zama ya Isheni in bamu Shiga Sch ba sai dai ki ganni..!
Munari tace"Shikenan sai na ganki..Bye sai gobe in mun Hadu..!
Inteesar tace"Gobe 10am muke da Lecture ki Biyomim mu Tafi tare..ko Kina da mai kai ki ne Kada na Takura Miki..?
Munari tace"Yayana ne Daman ke ijiyine in muna Karatun 8am Daganan ya Wuce Office in kuma ya Wuce Haka Dan Sahu nake hawa..Kada ki Damu Zan zo sai mu Tafi Tare..!
Inteesar tace"Yauwa..Kawo wayarki na Saka miki Lambata..!
Ba Musu Munari ta Daukota Daga Cikon Jaka ta Mikamata ta Saka mata Tana Fadin"Wani Suna Zan saka miki..?
Munari tace"Ki saka Besty Intee..!
Inteesar Tayi Dariya Tana Fadin"Au..Nima kuwa Da kin je gida ki kirani Zan saka Besty Munira..!
Dariya suka saka Gabadaya Daganan sukayi Sallama ganin Maza nata Haraman Zuwa Masallacin Inteesar ta Juya Zuwa Gida Tanajin Wani Farincikin in Tana Tare da Munari Sai take ji kamar Tana Tare da yar"uwanta na jini kamar Nasara,Dayake Daga Munari har Inteesar basu Taba gaanin juna ba Shiyasa bazasu Shaida juna ba sai dai Bond din Jini Dake Tsakaninsu ne yasa Sukejin kamar wani iri a Tsakaninsu hakama ta Bangaran Munari tana jin Intesar Sosai acikin Ranta.
Tana Shiga Haraban Gidan suka ci karo da Abba da Imran Harda Ya Yusuf ya Dawo Ganin ya Imu sai da gabanta ya Fadi tana gaishesu Abba ne kadai da Ya Yusuf ya amsa bandashi Daya wani Hade rai yana kallon Gefe.
Abba ne ya Kalleta yana Fadin'Munarin Abba ina kika Tsaya yau kin gota Lokacin Dawowarki..?
Kafin Tayi mgana Ya yusuf ya Rigata Da Fadin"Ni kaina na Damu yanzu Safiya ke Fadin Shuru bata Dawo ba Har 6:30pm ta wuce..?
Yafada Lokaci Daya yana Duba agogon Fata na kamfanin Rado Dake Daure a Tsitsiyan Hannunsa.
Da Sauri Munari tace"Ban samu Adaidaita ne da Wuri ba Ya yusuf Shiyasa..!
Jin haka yasa Dagashi Har Abba suka Kada kai Ya yusuf yace"Kawai Daga yanzu in na taso da Wuri Zan rika kiran ki naji in kun gama Sai na Biyo na Dauko ki..Kina mace bana so kina Yin Dare a waje..!
Kai ta gyada batare da tayi mgana ba ta Mike ta Wuce Sum sum ta wuce Ba Saboda kowa taki Fadan inda ta Tsaya sai Saboda Ya Imu ko kowa zai Fahimeta ban dashi ta Tabbata sai yayi kwallo Da ita bayan ya Fara Sauya mata kammin Dayake ikirarin Tun a Haraban gidan kafin su Shiga Ciki Shiyasa ta Rufama kanta asiri.
Cikin Gida ta Shiga su kuma suka Fice koda ta Shiga Safiya tana Shashnta Tana Sallah Domin ta Lekats sai kawai ta Wuce Dakinta Kafin ta Shiga wanka sai da ta Kira Inteesar sai taji bata Dauka ba sai ta Tura mata sako
Salam Besty nice..Munari..!
Daganan ta ijiye wayar ta Tube ta Shiga Tayi wanka,Ta Dauro alwala Tazo Tayi Sallah Ta idar kenan Tana Saka kaya Safiya ta Shigo Tana yi mata Sannu da zuwa Sai da Tagama Saka Kayan suka Fita babban Falo su Abba basu Dawo ba sai da sukayi Isha"i Lokacin Munari taci Abincinta Saboda yunwa Tea kadai ta Kara sha tayi musu Sallama ta Shige Dakinta ta Kwanta tagaji,Ta bar Abba da Ya yuauf da Safiya a Falo Abba da Ya yusuf Hira suke Safiya kuma Tana kallon Imu dai yana Dakinsa yau ko Tea din bai Sha ba Tun bayan Dawowarsu ya Shige Ciki,Sigari Ta Riga ta gama Cikamai Ciki in ji Abba Suna Dariya Shida Yusuf.


Washegari kamar yadda Inteesar Ta bukata Bayan Munari ta Shirya Gidansu Sagir ta Fara Biyawa Inda Allah ya Taimaketa Imran yana Gida bai Fito ba koda tazo Inteesar ta Shirya ita take jira basu Bata Lokaci ba Sukayi ma Mama sallama Suka Fito Ta bisu da addu"an Allah ya Tsare,Suna Fitowa suka Tsaya Bakin Shagon Sagir ya Fito suka gaisa Shi Kanshi ya godema Allah Imran baizo ba Kila da anyi wani karamin Shirin Film,500h ya basu suka ki karba yace sai dai in sin Raina Shiyasa Munari ta Karba Daganan basu Samu Abun Hawa ba sai da suka Taka da Kafarsu suna Hira Har bakin Titi kana suka Samu suka Hau zuwa Cikin makaranta,Koda sukaje ana Ta Shiga ajin Dole suka bi ayarin yan ajinsu suka Shige suma Domin yin Abunda ya kawosu.
Ranar ma Tare suka wuni,Basu Je Cafteria ba sai da sunje Shago sun Siya Lemo Inteesar tazo musu da Biskit da,Donut sukaci suka Koshi Suka Tsinke da Hira Ranar Munari ta Sha Labarin Daddy da Umma da ya Basheer Har gaisawa sukayi da Daddy Daya kira yaji Inteesar Cikin Fara"a yake Tambayanta tace Besty ta samu Tabana Munari suka gaisa yana ta Saka mata albarka Munari Taji muryan Daddyn Intee kamar na Abbanta Sai dai bata yima Inteesar din mgana ba Shi kuwa Daddy Daga Barayin Yasan Munari ta Musamman ne Tunda Har Daga Haduwa Suka Kulle da Juna yana Fatan Allah yasa kawancensu ya Zama alheri ga juna.
Ranar 4pm suka Tashi Daga makaranta Daganan gida suka Taho,Munari bata Sauka Daga gidan su Sagir ba,Saboda Tana Tsoron Haduwa da Imran illah kamar ta Sani yana Cikin Shagon Sagir,suka Rabu bayan Inteesar ta Karbi Wasu Note Hannun Munari Zata kwafe Tunda Gobe suna Gida bazasu Shiga makarantar ba.
Lokacin Data Sauka Imran da Sagir na Fuskantar Kofar Shagon Sagir kadai ya ganta Shima bai Dade da Dawowa Daga cikim makarantar ba,kanta na kasa ne Tunda Shago ne na Dinki akwai Dandalin Maza awajen Har ta Wuce batama Dago Kanta ba,Imran kansa na gefe yana kallon Wani Atamfa da yaron Sagir ke yankawa Shi bawai yana son koya bane No sai dai yana Kallom komai Dake Gudana a Shagon kuma yana Dauke sa acikin Kwakwalwarsa Batare da ya bama Abun Muhimmanci ba.


******


*After 10Days..*
Bayan kwana Goma da Haduwar Inteesar da Munari Sosai kawancensu Yayi nisa wanda yasa Kowa bai iya Boyema Daya Labarinsa,Har takai Abba da ya Yusuf da Safiya sun san Sunan Inteesar Besty Munari a bakinta Abba yaji Dadin jin Diyar kanwar Mama ce Mahaifiyar Sagir Hakama Ya yusuf,Shima bai Hanata ba jin na Gidane Tunda yanzu suna Kokarin Daidaita komai nasu ya Dawo kamar Baya ne.
Haka itama Inteesar din Daddy da Umma da Ya Basheer sun san da Zaman Munari Tunda In suka kira a makaranta indai suna Tare da Munari sai ta basu sun gaisa sun santa da Murya Sosai Harta da Nasara ma ta san Labarin Munari sun ma Taba gaisawa Watarana Datakira Inteesar din suna Tare da Munarin ta bata suka gaisa.
Inteesar ta Taba Zuwa Gidansu Munari sau Biyu bata Hadu da Ya Yusuf ba Imu kuma yana Dakinsa Shi a labarin ma bai sani ba Domin Munari bata yarda ta Furta Indai Labarin Zai kaimai ba.
Sai ta Hadu da Abba ita kanta Inteesar ganin Farko Datayi ma Abba sai da Tayi Shock Ta Dinga kallonsa Tana so Ta Tuna ina ta Taba ganinsa ta kasa Shekarun Dayawa Tana karama ne,Sannan kuma yanayin da Muryansa kamar ta Daddynta,Sai dai itama abun na Ranta bata iyama Furtama kowa ba,Sai ya Yusuf da suka Hadu Rana ta Biyu Data Dawo Shi kanshi Taso ta ganesa Domin da Girmanta Tataba Raka Daddynta Dukku suka Hadu dashi yazo Shida Marigayi Nura alokacin Sai dai kamaninsa ya bace mata Tunda ya Kara Girma aure yasa ya Zama wani Budede Sai kawai ta Watsar da Abun acikin Ranta ko Zencen batayi ma Munari ba.
Tana jin Dadin zuwa gidansu Munari Sabida Abba da Anty Safiya Suna da Matukar kirki Haka Abba zai ta janta da Hira yana musu Fadan su maida Hankali ga Karatu,ita kuma Anty Safiya ta jasu Shashenta suyi ta Hiransu,Ta maida kanta Sa"arsu Ranar ma da Inteesar din tazo Suna Shashen Anty Safiya sai gasu mommy sun zo ita da Anty Saratu da Tasleem Dama Tun jiya Mommy tace Safiya tasa Idonsu Dayake ta Dade ta Tura musu Kwatancen Gidan basu sha Wahalan gane Gidan ba Tunda ba yana Lungu bane.
A falo suka Fara ganin Abba yana Zaune yana kallo Suka Gaisa Dashi,Kafin Safiya ta Fito ganinsu Mommy yasa ta Murna ta Rumgumesu Cikin Farimciki nan take Fadama Abba Mamartace da yayarta da kanwarta suma ta gabatar musu da Uban Mijinta Suka kara gaisawa Sosai Abba ke ta Godiya sai da Mommy da Anty Sarati suka ji wani iri.
Sun zo Da kaya sosai a manya Ledoji Safiya tajasu Zuwa Shashenta sun ga abun mamaki kayan arziki haka,Ba ko sisinsu,Nan inteesar da Munari suka gaishesu Tasleem ma suka gaisa da Munari ta gabatar mata da Inteesar,Nan suka barsu suka Koma Dakin Munari suka Cigaba da Hiransu Daga Baya nan Tasleem din ta Dawo suka Hade su uku suna Shan Hira Tasleem na Fadin itama Buk Zata Cike Taje chan su Hade tare.
Safiya kuwa Ta Dinga ina zata saka da Iyayenta,Daman ta yi girki Dazu ita da Munari,Farar Shinkafa Miyar Kaza Sai Kunun aya da sukayi shi ta Zubo musu sukaci suka saka albarka suka Leka ko"ina suna yabawa Anty Saratu ta Kada baki tace"Ni kam ai banga aibun da Alhassan ke Fada akan wannan Gidan ba..Ga Baban Mijinta Dattijon yasan Karamci ji yadda yake mana Godiya mu da muka kawo musu ya ba komai ....Ji Abun arziki Mero..Ji Safiya tayi kiba kamar ba ita ba ai wannan gida..Tabbas Gidan Aure ne Wlh..Allah ya Zaunar Lariya..!
Hajiya Mero Tana ta Dariyan Farnciki,Sun zo mata da kayan Kitchen,da Turarun ka Daki Dana Jiki sai Speciess na girki da Garin kunu da Zogale Bushashiya,da su Kubewa,kuka Da Sauran abubuwa sai Kayan gyara,Da kayan gara irin su Mangyada da manja da Kwalayen Indome da Taliya da Macaroni suka Gyara Kitchen din suka Jera komai gwanin Sha"awa Basu Tafi ba sai yamma da Yusuf ya Dawo suka gaisa,Lokacin Inteesar tatafi Gida Tasleem da Munari suka Rakata Gida suka Dawo suna Dawowa Suka Tafi su kansu suna ta yima Yusuf Godiya Shi kuwa aransa yana Fadin ai Shi ke da Godiya Safiya ai Kamar Zinare ce a wajensa Bayan sun Tafi ta Nunamai kayan da suka kawo mata ya gani ya saka albarka har Abba ta Fadamawa Shi ma ya saka albarka
Sun Tafi sun barta Cikin Farinciki Suma sun koma Cikin Farinciki suna Yabon Irin Gidan da Safiya tayi aure aciki.
























*Shakira.. *
3/22/22, 23:05 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*


*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty��*


      *🅿�18*


 Yau din Takama Ranar Sati ne Wato Asabar ce Tun Safe Inteesar tatashi da ayyuka,Da wankin kananun Kayanta ta Fara Iners dinta da bata ba dasu Wanki,Daman Tun tana gida ta iya kowani aiki banda wankin kaya sai Dai tana wanke Inners Dinta Sauran kayanta kuma Wanki a ke kai musu Nataa da na Umma sai dai a dawo Dasu a goge tas dasu.
Hakama Datazo Gidan Mama Tana Kowani aiki in Tana Gida banda Wanki,Itama Maman bada kanta Take Wankin nata ba kaiwa akeyi Sai da Inteesar din tazo ake Hadawa da kayanta Sagir ke kai musu Suma sai dai adawo dashi agoge.
Tana yin girki Duk Ranar Datake Gida kamar asabar da Lahadi,In bata nan Tana makaranta sai Mama tayi.
Yau ma hakan ce ta Faru bayan ta gama Wankin Kayan nata ta Share Daki ta gyara tayi mopping ta kuma Wanke Bayin Daki Da kuma na Waje ta Share Tsakar gidan ko"ina Tayi Tsaf, Da Mama tace ta bar Girkin ta Dora sai tace Maman ta barshi Ita Zatayi Shinkafa da Miya da wake ta Dafa musu,Da Salat Bayan ta gama tayi wankanta ta Saka Wata Doguwar Rigar atamfarta Gold mai kalan ja da Brown Anty Hauwa Matar Ya Basheer ta Dinkamata shi,Ta kashe Daurinta na Zara Buhari Fuakarta Tayi kyau Sosai Duk ita ba ma"abociya Kwalliya bace.
Sallaya ta Shimfida ta Tada Sallar Azahar Daman Daga Tiolet ta Dauro alwala,Bayan ta Idar da Sallar ne taje Kitchen ta Dibo ma Mama Abinci Ta kawomata Zobon da Tayi Jiya da Daddare Bata Taba gwadawa ba Ko tana gida sai dai Tana ganin Talatuwa mai aikin Umma nayi Shine jiya Dataga Mama nada kayan Hadin Zobon Tace bari ta gwada sai gashi kuma Yayi Dadi,ammh Sai da Munari Tazo ta Taimakamata.
Sannu da aiki Mama Tayi mata Tana Daga kan Darduma bayan ta Idar da Sallah Tana Lazimi.
Inteesar ta amsa mata Cikin Jin Dadi Domin Tana bala"in jin dadin Zama da Mama Tana ganinta kamar Umma abaya ta Zata tafi Kowa Kewar Gida sai gashi Tana jin Dadin Zaman Gidan Mama,Sai dai kewa ta iyaye kuma gashi Suna mgana ta waya Kusan kullun sai sunyi Waya Daddy Fiye da Sau Uku Rana Umma ce ma sai Bayan an kwana Zata kirata taji ya Karatun ko Bata kirata ba Takan kira Maman su gaisa.
Ganin Zata Koma Cikin Uwar Dakin ne yasa Mama ta Daga baki Tana Fadin"Inteesar ina zaki kuma..? Ke banga kin Debo abincin Kinci ba kuma kin gama Dafa Abinci da kanki..!
Inteesar ta Juyo Tana Fadin"Mama ba yanzu Zanci ba sai anjuma..Dambun Namam da naci da Safe ya Cikamin Ciki..!
Mama tace"Ina Dai Lura Dake baki san cin abinci sai kayan kwalama da Shan Zaki Shiyasa gaki nan Har yau bakya Kiba..!
Dariya Inteesar Tayi kafin Tace"Kai Mama Allah ina ci..Rashin kibata kuma wlh ina jin Dadin kaina ahaka Sam bana son kiba..!
Mama tace"ai shikenan nayi Shuru..!
Yar Dariya Inteesar Tayi kafin Tace"Mama zan Dan kwanta In ya Sagir ya Shigo Abincinsa na Kitchen..!.da kai Mama ta amsa mata Tana cigaba da Laziminta ita kuma Inteesar ta Juya ta koma Ciki kan gadon Datake kwana ta yada kanta Lokaci Daya Ta Dauki Wayarta Ta kira Munari har Sau Biyu bata Dauka ba Lokaci ta Duba taga Har 1:30pm Tayi,Sai tayi mamaki Rashin Zuwan Munari alhalin sun Rabu ajiyan kan cewa yau Zata zo da Wuri suyi Karatu Tare suna Taimakon juna inda Daya bai gane ba in Daya ya gane sai ya Tada Dan"uwansa haka suke yi Duk Karshen Sati basa yarda su Zauna haka ko suce sai Test yazo ko Jarabawa Zasu Fara karatu a"a su Tuni suke Karatun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login