Showing 189001 words to 192000 words out of 235479 words
Chapter 64 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt
na gani na Fada sai Wanda ya gani ba Ha"inci ba zamba cikin Aminci.
Mganar kayan Gida kuwa sun gama mgana da Kamfanin Marhaba Kudi kawai suke jira ya Tura musu zasu zo su Kawata gidan sai wanda ya gani Dagachan bangaran Umma kuma Tana Siyayyan yan abunda ba"a rasa ba,Mama taje ma tayi Sati a Wajenta suka gama Shawara bayan ta dawo ta Dawo da kayan wanka na Lalle da su margaya ta jikama Inteesar aka Zuba Ruwan Turaruka Kala kala Inteesar tana wanka Dashi Safe da Rana sannan ga mgungunan Infection na Gargajiya shima Maman ta Dake ma Inteesar din tana amfani Dashi.
Yan"uwa kowa yana ta zumudin Bikin banda Inna Bintalo da abun bai Dadata da kasa ba Dataji Labarin Abun Alherin Baffa Kabiru cewa Tayi bai da zuciya Tunda har za"ayi ma yarsa wannan Sakin Wulakanci kuma yazo yana Rawan jiki,Ba wanda yasan Tanayi bama abi ta kanta ba Itace ta Fara Kiran Mami Asma"u ta Labartamata komai,Jikinta yayi Sanyi ta kuma kara Tabbatar ma kanta Kabiru dai da gaske yake ya Rabu da ita Tunda gashi ya Shareta har yau bai nemeta ba kuma gashi ya Daidaita da yan"uwansa Har yaje yana Kashe kashen Dukiya saboda wanda ya Lalatama yarsa Rayuwa ya maidata Bazawara duk da Taji mganar Tarewar abakin Umaima bata Zata Lokaci kadan aka Saka ba Mami Asma"u da Inna Bintalo kadai take waya a Dangin Baffa Kabiru kowa ya kamasa kansa da ita da yawa ma basu san abunda ya Faru ba itama Inna Bintalo Ta Kira Mamin ne tana mata Tsegumin da Saninta Baffa Kabiru ke Kashe kudi haka Sai kuma taji Labari mara Dadi ita kuma ta Fadama Inna Maimunatu wacce ta Tabe baki afili ta Furta Ya kabiru yayi min Daidai Wlh..Allah ya kara mganinta kenan!
Ganin Bata samu Fuskar da Zata kawo Wata mgana ba yasa ta kama kanta Musamman ta Shirya taje Dukku Tana yima Daada mganar ita azatonta bata Sani ba Daada ta nuna mata Babba babba ne bata nuna mata ba Taji ba Sai ta Nuna mata abakinta ma take ji ballatana ta Fadamata yadda sukayi da ya"yanta nata taja bakinta ta Tsuke sanin Halin Bintalo akwai Daukan mgana sannan suna Dasawa da Mami Asma"u tana kuma da Tabbacin Mamin Asma"un ne ta gayamata yadda akayi ammh tasan Kabiru Ko Mustapha ko Malami ba wanda Zai kira Binta Domin ya Fadamata wata mgama shiyasa tayi mata abun nan da ake cewa ta yaro kyau take bata Karfo.
*******
Sajida Tana makaranta bata san Abunda ke Faruwa ba saboda ta yanke alaqa da duk wani abunda zai Karamata Mikin Dake cikin Ranta Da Umaima kadai sai Dad take mgana ta Sauke Duka Kafar sada zumuntar Dake Wayarta sun gama Test suna gabda Fara Jarabawa ammh bazasan Hakikanin Abunda ta Rubuta ba,Gadai Tanan nan kaawai Ta Rame Duk ta lalace kamar ba Sajida yar gayu bai ji da kanta da Takama da komai ba.
Ita kanta sani Tana da Cuta acikin Zuciyarta Har ta koma ga Allah Bazata Daina son Imran ba ba ita ta Dora ma kamta ba Allah ne ya Dora mata kuma bata isa tace Zata yaye ma kanta ba,Sai dai ta Dauki alhakin komai ta Dorama Mami itace Silar komai Sannan Daya Daga Cikin Ayyukan Mamin ne ita ta Girban mata Sakamako ne take gani ta Dauki hakan a Mtsayin kaddaranta Tunda Duk Zuwan da Dad zai yi wajenta ko ya Kirata a waya Nasihar shi da ita kenan yana Shiga Damuwa in ya ganta Ta Rame duk ta saki Ta Zama wata iri kamar ba Sajida ba
Bata da kuzari kamar mara Ishashen jini ajikinta ko Ruwa bata Farinciki Koda yaushe Cikin kunci in Ta gaji da Boye abun acikin Ranta tayi ta kuka Karatun ma bata Fahimtar sa kawai yinsa Take yi ba wai tasan ina Take ba ko ina Zata ba..!Jenefer kamta da suke Zaune Daki Daya tasan Sajida Ta Sauya haka ma abokan Karatunta da kawayenta Kowa Sajida What Wring..?me zata ce..!nayi aure ban Tare ba Mijin ba ya Sakeni..?kuma Duka Uwata Data Haifeni ta Ja Faruwar haka?bata da karfin Gwiwan bada wannan labarin amsarta Dayane bakomai ba abunda ke Damunta alhalin ita kanta ta sani Tana da Cuta acikin Zuciyarta Cutar da Sanadinta Mami Asma"u indai ta Fara Bin Ra"ayinta Tun Farko da ta Tabbata abunda ya Faru bazai Taba Faruwa ba.
Abakin Umaima take jin mganar Tarewar Inteesar din da Imran alokacin Sauran kwana Goma Sha Biyar,Ta zo Dubata tayo mata abinci da Miya Direba ya kawota Ranar asabar,ita kanta Umaima tayi ta ma Sajidan Korafin Ramarta Sai tace mata Stress din Karatu ne anan nema Umaima ke Nuna mata ankon da Munari ta Turo mata Guda Uku Less,na Dinner sai Wani Material na Bridal Shower sai Atamfa na Yinin Biki shi kuma za"a saka aje Lonching ta Nuna ma Dad yace ta zo ta nuna mata In tana Bukata sai a Daukan mata Sajida tace Bata Bukata bazata samu zuwa taron Bikin ba Saboda Lokacin sun Fara jarabawa Umaima bata Mtsa mata ba nan ta wuni Tare da ita akallah dai ta Debe mata kewa Umaima ta Tambayeta ko suna mgana da Khamis tace mata basa mgana Tun Dawowarta makaranta Cikin Damuwa Take sanar da ita basa samunsa ta waya Harta kuwa da Baffa Kabiru baya samun Khamis din Waya Sajida ta ce kila yanayin aikinsa ne kamar yadda Umaima ta Tambayeta Baffa Kabiru ma ya Kirata ya Tambayeta tace basa mgana bata Duba ammh Tana da Tabbacin shima yana chan yana Fama da Zuciyarsa kamar yadda itama take Fama anya Mami ZAta gama da Duniya Lafiya kuwa..?Tabar ganin Tana da Mtsayin Uwa a wajensu kamar yadda Take da Hakki a kansu suma suna da Hakki a kanta Sai dai bata Duba wannan ba Daga ita Har Khamis batayi musu adalci ba.
Umaima Tazo asabar Mami Asma"u ta shigo Cikin makarantar Ranar Lahadi,Daga Office take taje Duba Wasu Takardu shine ta Biyo ta makarantar su Sajidan Tunda ta Rufe Duk Hanyar da Zata sameta suyi mgana Mami Asma"u ta yanke Shawaran ta zo ta samu Sajidan suyi mgana Taji menene Nufinta..?ta sauya taa ne a Mtsayinta na uwa ko yaya..?
Har Hostel din ta shigo Dakin da su Sajidan suke Sajida na kwance Tana Fama da Tunanin Data Saba a koda yaushe Karatu take yi ammh bata Fahimta Sai da ijiye ta koma Tana Tunani Zuciyarta na mata suya Hawaye suna Zubomata in ta Tuna da kalaman Imran akanta Son maso wani Take yi Domin a gabanta a gaban Kowa da kowa ya Tabbatar mata da baya sonta kuma bazai Taba Sonta ba Har Abada.
Duk Sadda Ta Tuna da Wadandan kalaman sai ta kwana kuka Kirjinta yayi mata Nauyi yana Suya yanzu din ma kukan take ita kadai acikin Daki Jenefer ta tafi gida Weekend bata nan Sai ga Mami Asma"u ta shigo.
Dukkansu sunyi Shock da ganin junansu Sajida tana kallon Mami yadda Ta koma duk ta wani Fige kamar ba ita ba,Idanuwa sun Zurma Daga gani bata Samun Cikakken Barci Ballatana Kwanciyar Hankali ita kuma Mami Asma"u ta Firgita sosai na ganin yadda Sajida ta Rame tayi baki ta koma kamar Wacce take cikin Wani Cuta.
Sajida ta gabatar ma da Mami Ruwa da Lemo Tunda suna da Fridge acikin Dakin,Mami bata iya ko shan ruwa ba Ta Fara Tambayan Sajida me ke Damunta..? bata da lafiya ne..?meya sameta..?
Sajida kallonta kawai take yi Lalle ne ma Mami Tambayanta ma take yi me ke Damunta..?ita bata sani bane..?
Ai tafi kowa sanin Damuwarta Tunda itace Silar Shigarta Cikin Wannan Halin batacemata komai ba illah Shuru Da tayi mata tana Binta da ido.
Ta Zata Sakin da Dad yayi mata zai saka ta Sauki ta gane kuskuranta Sai dai a kalaman Mamin Gabadaya ba Nadama Illah kara Kaucema Hanya.
Tunda tazo take Zagin Daada Tana Dora alhakin komai akanta
Sajida Tagumi Ta Zabga Tana kallon Mamin Sadda take Fadin"Sajida kema kin Gujeni ko..?kema Daada ta Rabani Dake kamar yadda ta Rabani da Babanku..Ga Yayanku shima Tunda ya Tafi ban kara Samunsa a waya ba..Sajida nasan kina jin Haushina ko.?miye Laifina na..?miye Laifina Domin na so ya"yana na Nuna ma Duniya kune Duniyata..? Sajida wannan yakin saboda ke nake yinshi Kalleki yadda kika koma da Kuruciyarki da komai an Bata Miki Rayuwa an maidake Bazawara da karfi Da yaji wannan wani irin Abun kunya ne..?in na Tuna wannan abun sai naji kamar na Kashe kaina Saboda Takaichi kuma na mike Zan kwatar Miki Yancinki Dad din ku ya Sakeni Sajida kuma kun juyamin baya,Nasan kan wannan yaron kike Rama Sajida ki Kwantar da Hankali kefa Diyar Asma"u ce da Kabiru Gangariyan Miji yana nan zuwa Miki wanda yafi wannan yaron komai da komai ki cireko aranki Domin bakya gabansa Bikin Tarewarsu ma da yar Wajen Salahan ya kusa Babanku na chan yana Kashe Kudi Kinga fa Bintalo ta gayamin Shi zai yima Mara Mutumcin yaron nan Kaayan Lefe Ita kuma Inteesar din shi zai yi mata kayan Gida Gabadaya shi bama ta ya"yansa yake ba yana chan yana Kashe kudin Inda aka ci Zarafinsa aka Sauke Darajan yarsa Sajida ina Cikin Damuwa bana iya barci Babanku bai Nemeni ba bai Nemeni ba Yana Nufin ya Rabu dani gabadaya kenan..?Umhm..Shikenan ai Barrister Asma"u bazatayi kwantamai ba Zan samu Mijin Dayafisa komai da komai Tunda shi Daada ta shiga Tsakanina dashi ita da su Mustapaha..!
Take fada Tana Hawaye kallo Daya Zakayi mata kasan bata cikin Hayyacinta Surutai kadai take yi bata san me take fada ba Damuwar take cinta ne take Furta batare Data sani ba
Ance Uwa uwace ko da kuwa Mahaukaciya ce,Tuni Tsausayinta ya Sarke Sajida duk da kuwa Tana Fushi da ita Tun bayan Faruwar Lamarin ammh ganinta Cikin Wannan Halin Tana kuka ya karya mata Zuciya Rauninta ya bayyana ta Rungume Mamin Tana Fadin"Mami u are not Well..Bakya samun barci muje asibiti a Dubaki plz..!
Mami Asma"u na kuka Share Share kukan da Tuntuni take son tayi bata samu Kafadan da Zata Kwanta Tayi kukanta ba,Tabbas Tayi Rauni ta kuma gaza Duk kuwa da Taurin kanta wannan karon ta gaza ta yardan ma kanta Mijinta da ya"yanta ne Duniyarta Da kuma su take Takama yau da basu Tare da ita Rayuwarta ta Zama cikin Wani Hali Halin kakanikanin da bata Taba Tsammanin Zata shigesa ba batama Dauka abubuwan zasu Dakule mata haka ba.
Sajida kuka Mami Asma"u nayi Kafin Sajida ta Tsagaita da kukan ta ta Share Hawayenta Mamin na Bukatarta a wannan Lokacin,Fiye da yadda ita take Bukatarta.
Mikewa Tayi Tana Fadin"Mami Tashi muje asibiti a dubaki..Bakya barci Idanuwanki sun kumbara..!
Mami Asma"u batayi gaddama ba bata Barci,Ga ciwon kai Datake kwana Dashi batayi ma Sajidan Musu ba ta Jirata ta sako Mayafinta Ta Riko Hannunta bayan ta Rufe Dakin...
Specialist Hop suka je inda suke da Fayel Dr.Barau ya Duba Mami Asma"u ya Tabbatar mata da jininta ya Hau Saboda Damuwa da Rashin Barci ya Rubuta mganguna sosai da Shawarwari ga Mamin,Bayan an dubata ta Mtsa Sajidan ta Zauna itama a Dubata ta ki yarta tace ma Mamin itafa bakomai Strees ne na Karatu kawai ba Domin Mamin ta yarda ba ta kyaleta sai da Mamin ta koma ta Maida Sajida makaranta Kana ta Tuka kanta zuwa Gida.
Da hajiya Turai ta ganta ta Dawo Cikin wani yanayi shine take Tambayanta tace mata Wajen Sajida Taje Daganan ta Rakata asibiti taga Likita Jininta ya hau.
Hajiya Turai ya kyabe baki Tana Fadin"Uhmm..Asma"u kenan kaza mai ya"ya..Ai kulafacin Kabiru da ya"yansa Kadai aka barki ba Jininki ne bane zai Hau ba har Bugawar Zuciya Zaki iya samu..yarinya kina Wahala kanta bata sani ba..Ta Debeke ta Watsar ke kuma kin kwashi jiki kin Bita kamar itace Uwar..Wannan Bakin Halin na Fulanin Dukku sun kwasoshi Wajen Ubansu shi kuma ya kwaso wajen wannan Kafaffiyar Tsohuwar..!
Mamin dai na jinta bata Tanka mata ba ta Shige Ciki gabobinta sungaji so take ta kwanta Maltina ta Dauko ta sha ta Sha mgani ta koma ta kwanta Tana Sauke Numfashi sai kuka Allah Sarki Rayuwa yau ina Brr Kabiru..?ina Khamis..?ina Sajida..?ina Umaima..?
Basa Tare da ita Sai ita kadai Tayaya ko Zuciyar Karfe ce da Barrister Asma"u bazata Raunana ba Ya"yanta da Mijinta fa sune Duniyarta.
*******
Kwanci Tashi babu Wuya a Wajen Allah duk kuma abunda aka Sanyama Lokaci sai yazo,gashi yau Bikin Tarewar Inteesar da Imran Saura Kwana Shida a kuma Ranar ne Inteesar da Munari suka Sauka a Dukku Daganan zasu wuce Kaduna sai kuma an gama Taron Bikin.
Tuni Inna Maimunatu ta gama Hada kaya sai da aka kawoma Daada ta gani Ta saka Albarka Baffa Kabiru yayi kokari kuma ya Cika Uba wajen Imran akwatina Goma sha Biyu Tsala Tsala Cike da kayan Alfarma,Inna Bintalo da Inna Maimunatu ta Kira suka Hadu Gidan Daada Tunda Daganan Kaduna zasu kai kayan,Da Farko Baffa Kabiru yace afara kai su Kano Abba yace Dawainiya Zata yi yawa akai su kaduna Gidan Daddy.
Ganin irin Uban Dukiya sai da Taji Tsoro,Gulma na cinta Harda Vidoe tayi ma Mami Asma"u Ta Turamata Wacce Datagani Sai jiri ya Kwasheta ai ko Khamis Dansa Daya Haifa da Cikinsa sai haka Hawan Ruwa ne ya kusa kamata Data ga kayan.
Daga Inna Maimunatu sai Inna Bintalo sai Baba Asabe suka kai kayan nan Kaduna Dangin Umma suka karba su Mama da matan Bala da Salisu da su Anty Hauwa kowa yaga kaya sai barka ana ta ma Baffa kabiru Fatan gamawa da Duniya Lafiya Inteesar ma suna kano basu ga ko Kalar kayan ba sai dai ta Waya da su Zainab suka Dauka suka Dinga Turama Mutane Har Imran ya gani Yusuf ya Nunamai ya saka albarka Hae acikin Ransa ya yaba da Kokarin Baffa Kabiru a kansu.
Gida kuwa Tuni Anty Safiya da Mama da Matar Baba Manu Kaltume da Anty Saratu da Mommy da Anty Aneesa sukaje suka Tsabtace ko"ina washegari kamfanin Marhaba tazo ta jera kaya,2 Bedroom ne sai Falo guda Daya da Kitchen kowani Daki akwai Bandaki..
Falon Har Bedroom din Kalan Red and Black ne Zabin Amarya Inteesar,Bedroom din Imran kuma Kalan Baki da Fari ne kowa da Zabinsa Gida sai wanda ya gani.
Katin Biki kuwa kayattace Hadadde mai kyau na Zamani irin na ya"yan masu kudi Baffa Kabir ya Bugashi Copy 300,ya aiko ma da Abba 50,Inteesar da Imran 100,Yusuf 50,Daddy kuma y 50,Duk da Umma ma ta Buga nata Katin Anty Safiyama Ta Buga nata Katin Safiya Yusuf Hamisu Malami na gayyatan Kowa da kowa zuwa wajen Daurin auran kanin Mijinta Imran Abubakar Malami da amaryansa Maryam Mustapha Dukku(Inteesar)
gayyata Har Gidan Radio sai da Anty Saratu takai Safiya tayi gayyah Makota da yan"uwa da abokan arzuka Mama ma tayi nata gayyan Domin tace ita Uwar ango ce Tana Kaduna,Saboda komai Anty Safiya ita take sakawa a gaba ita da Anty Saratu.
Sagir ya sa an Buga Katin Waya wanda su Munari sukace suna so saboda Turama Kawayensu dake nesa yan Makarantar su,Sannan kati nan da Baffa Kabiru ya aiko Dashi Imran Ya Kirasa Inteesar ya bata bayan ya Tura mata 100k na gyaran Jiki Cikin kudin Albashinsa na Farko.
Sauran Katin kuma ya bama Sagir Tunda dai ba wanda zai bama wa Sagir kuma Daman sun Buga wani Shida Khalil na Events.
Imran bai sani ba bai da Labari sai dai yaga Kati Da programme of Event Daya so yayi ma Sagir hauka sai ya Hasada sa da Abba shi kuma yace kul Imran din ya Kyalesu suyi abunda suka Shirya Tunda shi bai da kara Dole yaja Bakinsa yayi Shuru.
Sagir yayi kokari sosai ya D'inka musu Shadda Kala Daya da Boyel Kala Daya shi da Imran da Khalil Duka kuma shi ya Dinka sannan su suka Shirya Dinner,Lonching da Bridal Shower a Kaduna za"ayi Dinner ne za"ayi a Kano Ranar asabar in aka kawo Amarya,Ranar Lahadi kuma agidan Inteesar Za"ayi Walima Tunda Ranar Jumma"a Umma Zatayi nata Taron Nan kano kuma Ranar asabar gabadaya Dangi kaduna zasu je Daganan ne zasu Dawo kano,Aneesa ce kadai take Kano suna ta Shirye Shirye ita da Anty Safiya,Anty Fareesatu kaduna zasu Sauka dasu Inna Maimunatu kuma Duk kowa yayi ankon Fitar Bikin na Kaduna dana Kano,Su Sadam ba"a barsu a baya suma duk zasu ce kaduna Daganan su kwaso Tawagan Amarya Zuwa Kano.
Imran bai sani ba Duk Sagir ya gama Satan Lambobin su Mr Tunde da su Mr Sulaiman duk ya Tura musu Progrmme of Event da Code din Dinner maza deep Blue din Shadda Mata kuma Deep blue din Head Leess din kuma Sky blue ne,Sai code din Bridal Shower material ne Red,Sai Atamfan Yinin Bikinsu itace ta Lonching.
Kwana Biyu sukayi a Dukku Suka Wuce Kaduna bayan Inteesar tasha Nasihu Wajen Daada,Sannan Baba Asabe ta Dafa mata Zabbin Amare da gumba mai yawa wanda Daada tace ta Rika sha da Nono,jaka guda suka Tafi dashi Kaduna na Nono,sun gama Test amakaranta sai jiran Jarabawa.
*Shakira..*
3/28/22, 18:34 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�23*
*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*
Ranar talata da yammah suka Dira a Kaduna sun iske gida acike da yan"uwa da abokan arziki,Inna Maimunatu da ya"yanta Tun Ranar Monday suka iso,Inna Bintalo ne bata Riga ta iso ba ammh Dangin Umma sun Cika gida ana ta Hidima
Nasara Daman already sun yi mgana ta waya tasan da zuwansu,Dayake gabadaya Dinkunansu na ankon da suka Fitar Kudin suka Turama Anty Hauwa gabadaya ta siya musu Nasara tazo ta karba ta kaimusu Dinki Gabadayansu Harda Umaima da Daddy ya siyamata itama Munarin da Hafsah Daddy ya siya musu Tasleem kuma Ya yusuf ya Tura nata kudin Duka ankon,Kayan Lefen Inteesar kuma Umma ta Diba ta Bama Nasara ta Hada da kayan su takai Dinkin Shagon Telan da suke kai Dinkunansu ita da Inteesar tun Tana Kaduna kafin ta tafi kano Karatu.
Washagari Laraba Hafsah da Tasleem Suka Dira a kaduna,Hafsah jiya Da Daddare suka iso kano ita da Anty Fareesatu da yara gidan Abba suka kwana nan ita zata Tsaya tayi Bikinta Ita da Anty Aneesa a kano ita kuma Hafsah Damansun yi mgana da Tasleem In tazo zasu wuce Tare haka kuwa akayi,Tare da Tasleem suka Dira Kaduna Alhaji