Showing 93001 words to 96000 words out of 235479 words
Chapter 32 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt
da Lokacin kansu sam.
Ranar jumma"a Karfe 7:30am suke da Lecture tun 7:20am Inteesar ta gama Shiryawa ta Fito kofar gida Tana Jiran Munari sun yi mgana tace mata gatanan Fitowa Tana Sanye cikin Doguwar riga atamfa Gold,mai kalan Brown sai da ta saka Karamin mayafinta Sikiws,sai bakar jaka da Bakin Takalminta mai dan Dudu sai wasu littafai a hannunta.
Sakamakon Lokacin yayi Safe ne da yawa ba Mutane sosai sai Daidai ku ne ke Wucewa sai yara masu Haraman zuwa makaranta.
Tana nan Zaune Tana kallon Shashen da Munari Zata bullo Lokaci Daya Tana Kuma Duba agogon Fatan Dake Hannunta na kamfanin gucci.
Sai dai me..? Maimaikon Taga Munari sai taga yayan Munari yana Tahowa Cikin Kayan jugging Riga da karamin Wando duka Farare,sai Takalmin Kafarsa Booth shima Fari ne Tafe yake yana Jogging a Hankali ko'ina na Jikinsa na amsawa gabadaya Muscles dinsa sun bayyana alamun Karfi da Mazantaka.
Inteesar tunda ga Nesa ta Kuramai ido bata san ta Shagala da kallonsa ba,bata son haka yake da kyau da Zati ba Shan taba bai dace da Kamili mai Daraja irinsa ba,bakinta ta Saki da Hanci Tana kallonsa batare Datasan me take yi ba Shi kuma Tundaga nesa Daman ya Hangeta sai yayi kamar bai ganta ba sai dai Kallonta Datake Binsa Dashi ne yasa ya kasa Wuceta sai kuma Karamin gyalen Dake jikinta Haka kurum yaji Haushin yadda Zata Tafi makaranta Cikin Duban maza da wannan mayafin da bai Rufe mata jiki ba,,Har ya Tsaya sai wata Zuciya tace menene naka..? Sai kawai ya Kada kai ya wuce Kuma sai ya kasa Zuciyarsa sai ta Fara Zafi da kuna wanda yasa ya Juyo zuwa gareta batare da wani Tunani ba....
Shagalan Datayi da kallonsa yasa bata san ma yazo gabanta ba,Sai dai kawai taji Hucin Numfashinsa agabanta Da Sauri taja baya Tana Rarraba ido Binta yake da kallo Daga Sama Har kasa Bakinta ma yayi Nauyi ta kasa mai mgana sai kallon Zufar Goshiinsa Take wanda ke gangarowa zuwa saman Fuskarsa.
Sai da ya Kalleta ido Cikin ido kafin yace"Koma ki Cire wannan Mayafin ki Sako Hijabi..!
Yafada kai tsaye cikin bata Umarni a karkashin Zuciyarsa kuma yana Fadin ko bakomai kamar kanwa take gareni Tunda Kanwar Sagir ne,Zai kula da ita kamar yadda zai kula da Tarbiyan Munari duk da ta batamai rai ta yi mai alkawari kuma ta Sabamai.
Ita kuwa mamakin kalamansa Taji,sai dai kuma Kaifin Idanuwansa yasa bazata iyamai Musu ba Sai ta Rausayar dakai tana fadin"Ban fa da kalan Hijabin nan..!
Tafada Tana nuna mai Kalan Brown din Dake jikin Atamfan,Dan Hade rai yayi kafin yadan Mtsa baya yana fadin"bai zama Dole in an bani Umarni nabi..Ammh ya Zama Dole in na bada Umarni ni abi..!
Yafada kai tsaye Cikin Dakewarsa Bata isa ta kara cewa wani abu ba,Ganin yadda Girman Jikinsa duk ya Babbage ko"ina sai kawai ta Juya ta koma Cikin Gida yana Bin kowani Takunta da kallo Zuciyarsa na amsawa.
Sai dai Mama ta ganta ta Dawo Data Tambayeta sai tace Zata Sauya Mayafi ne,Wani Farin Hijabinta ta Dauko ta Sakamai hannu wanda iyakarsa Gwiwanta,Ta sagala Hannun ta Dauko Jakarta da Littafanta ta sake yi ma Mama Sallama ta Fice.
Yana nan Tsaye inda ta barsa Tana Fitowa Kaifin Idanuwansa yasa ta Fara Jin kamar Zata Harde Jikinta Duk sai ya Fara sanyi bata iya Jure Kallon nan nashi,Kanta na kasa ta Kariso gabansa Kafin tace"Kagani..! Na chanzo..!
Tafada Cikin Shagwababbiyar Murya,bai ce mata komai ba ganin Munari Tana Tahowa kawai sai ya Kada kai yayi gaba abinsa Inteesar ta Bita da kallo har ya bace ma ganinta afili ta Furta"Komai nashi na Dabam ne..!
Daidai Lokacin Munari ta iso Wajen Cikin mamaki take kallon Inda Imran ya bi ya wuce ta Kalli Inteesar Tana Fadin"Kamar Ya Imran na gani..?
Inteesar ta Kalli Munari kafin ta Waske mganar tana Fadin"A ina..?
Munari tace"Tsaye anan wajen kuna mgana ko bashi bane..?
Da Sauri Inteesar tace"Anya..? Baki lura badai..Wani dai ya wuce ta nan wajen ammh ba shi bane..!
Munari tayi Shuru tana Tunanin itafa Taga wani kamar Ya Imran,sai dai kuma Inteesar tace bashi bane,Ganin kamar Ta shiga Nazari ne yasa Inteeasr ta Duba agogon Hannunta Tana Fadin"Muje kin Sakamu makara..In kuma zaki zauna Dogon Nazarin ki ne shikenan..!
Munari ta Sauke Numfashi kafin tace"Shikenan Muje..!
Daga haka Suka bar mganar suka Fara Takawa zuwa Bakin titi Domin su Samu adaidaita sun kai Titin kenan suna Jiran abun hawa sai ga Ya Yusuf yazo da mota zai tafi Wajen aiki ya Daukesu zuwa Makaranta sai da ya ijiyesu har cikin makaranta kana yayi Kwana ya Dauki Hanyar ma'aikatan su.
Basu samu zama ba sai da weekend ta Zagayo,Ranar asabar suna gida Inteesar sunyi mgana da Ya Sadam kan in ta Shirya tamai mgana zai zo ya Dauketa saboda tafi Saurin gane gidan to tayi ma Munari Mgana Kan Zata Rakata ayau din Har Abba ta Tambaya ya barsu sai kuma Bayan ta Shirya Tana jiran Munari Ya Sadam din ya Kirata yace wani Emergency ya taso mai zai shiga cikin asibitin ko Zata Bari sai gobe ne ko kuma da yammah in ya gama abunda yake yi acikin asibitin sai yazo ya Dauketa sai ta kwana agidan sa Gobe sai ya Dawo da ita.
Ganin bata Shirya kwana ba kuma bata Gayama Mama ba,sai tace mai kawai ya bari sai gobe sai yazo ya Dauketa Da haka suka Rabu ganin haka yasa tace Ma mama bari ta je gidan su Munari tunda sun fasa Tafiyar sai gobe Mama tace sai ta Dawo Tana Fita suka Hade da Sagir ya Dawo Daga kasuwa ya siyo kayan Dinki Zai shiga tamai sannu da zuwa ya amsa yana Tambayanta ina Zata tace Gidansu Munari yace ta gaida su.
Daganan suka Rabu shi ya Shiga gida ita kuma ta kama Hanyar Gidansu Munari.
Yana Zaune Saman Motan Yusuf ya Dauko karan Sigari acikin Aljihun wandonsa ya sakata abaki ya Dauko Lether ya kunnata kenan Yana Shirin Maida Lether, Aljihun wandonsa yaji an Dauke Taban Dake Bakinsa Da Sauri ya ware idanuwansa akanta Cikin Mamakin ganinta Domin bai ga Shigowarta ba kuma yana dan jima awajen,Ya fito ya Busa Hayakinsa ne Saboda Abba ya Hanashi shan Taba,Shi kuma bazai iya bari ba sannan baya so ya zama Sillar Sabama Abba Shiyasa ya koyi shanta aboye.
Duk da ya Rage shanta ba kamar baya ba Daya maida ita cinsa da shansa ba
Batare da yayi mata mgana ba ya mika mata Hannun alamun ta bashi Noke Hannunta Tayi Da kafadarta Lokaci Daya.!
Waro mata ido yayi Lokaci Daya Yana Mamakin Karfin Halinta Dakyar ya Bude baki yace mata"Bani..!
Kawai ya iya Fada Cikin Dakewa..
Kara Nokemai kafada Tayi alamun A"a
Dan Dakuna Fuska yayi acikin Ransa yana Fadin yarinyar nan akwai Shagwaba.
Saukowa yayi Daga kan Motan wanda yasa Inteesar tayi baya Da Sauri Tana Fadin"Plz kada ka Dakeni..ga abunka..!
Ta fada tana Mikamai Cikin Tsoro wanda ya bayyana acikin Idanuwanta.
Sai yaki karba ya gyara Tsayuwa Lokaci Daya yana Saka Duka Hannuwansa Cikin Aljihun Bakin Wandon Dake jikinsa yace"Bazan karba sai kin Fadamin meyasa kika karba Daga Farko..? Kuma yanzu kina so ki bani..? Bayan da farko nace ki bani kince A"a..!
Narai narai tayi da ido kafin tace"To bakai bane naga kamar Zaka Dukeni ba..?
Sai da Mirmishi ya Subuce Cikin Kaushin Muryansa yace"Kawai sai na Dake ki..?Me kikamin...? Aini bana Duka Haka kurum sai mutum ya batamin rai ya kuma Shiga Hurumina..!
Gyada kai tayi Tsoron ya Saketa Kafin ta Sauke ajiyar Zuciya tace"Ai kamin alkawarin ka daina sha ko..? Meyasa ka Saba..?
Kai Tsaye yace mata"Ni ban miki alkwari ba..Saboda nasan zan Saba miki. ni kuma bana Daga cikin mutanen Dake saba alkawari..Ina Matukar girmama alkawari sannan kuma bana Shiri da wanda bai daraja Girman Alkawari..!
Yafada yana kallonta ido Cikin ido Da Sauri ta Janye idanuwanta Kafin tace"Kana Jin Haushina Saboda na Saba maka alkawari ko..?
Daga Kafadarsa yayi kafin yace"Kinsani kema..!
Kanta na kasa Tace"Naso na dawo..Sai dai bani da Lafiya koda na koma Gida Hutun Ciwo nayi..!
Kura mata ido yayi kafin yace"Shiyasa kika Rame..?
Da mamaki ta Kallesan kafin tace"Daman na Rame ne..?
Cikin idonta ya kallah kafin yace"Eh..Ciwon me kikayi..?kuma meyasa baki gayamin ba..!
Sai da ya fadi hakane sai yaji kuma Mai ya kaisa cewa haka..?
Itama cikin Mamakinsa tace"Maleria ce Sauron kano ne da suka Cijeni..Kuma ai bansan ta ina Zan fada maka ba Sai dai Munari tasani dasu Abba.Lokacin ina asibiti ta Kirani muka gaisa da Abba ya gaisheni..!
Da sauri yace"Asibiti..?
Kai ta gyada mai kafin tace"Eh kwana na Shida a asibiti kafin na Dawo gida..Naso na dawo sai Daddy yace na Zauna sai na kara Warwarewa..!
Kallonta kawai yake yi yana jin Zafin Ciwon datayi baisan sadda yace"Kin ji Zafin Allura..?kinyi kuka..?nasan ki da Shagwaba..!
Yar dariya tayi kafin tace"Eh mana nayi ta kuka Daddy ne mai lallashina Umma Tayi ta fadan wai na cika Rangwanta..!
Imran ya Kalleta afili ya Furta"Eh mana ke raguwa ce..!
Ido ta waro kafin tace"Ni..?
Bai mata mgana ba inda ya Tashi ya koma ya Hau kafin ya zaro Wata karan Sigarin yana Fadin"Tafi ki barni..Kada kice zakiman amai..!
Daga haka ya saka Lether ya kunna abarsa Inteesar sai ta Tsaya tana Binsa da kallo Lokaci Daya tana kallon Karan Sigarin Dake hannunta kai kawai ta Kada kafin ta juya Ta nufi Cikin Gidan gaskiyansa ne Zuciyarta har ya fara tashi,Kada tayi mai amai kamar yadda yace.
Acikin Fulawoyin Dake Haraban Gidan ta Cillar da Taban kafin ta Shiga Cikin Falon.
Dukkansu suna Falon Sun gama Cin Abinci ne suke Zaune suna kallo suna Hira Abba ke kusa da Ya Yusuf suna mganarsu kasa kasa Anty Safiya da Munari suna Gefe suna kallon Tashar Mbc2,Munari ta shirya Domin taci Gayunta tana ganin Shigowar Inteesar ta mike Tana Dariya Haranta Tayi kafin ta Duka tana gaida Abba da Ya Yusuf.
Abba ya amsa mata yana Fadin"Mamana..Har kin gaji kin biyo kawar naki yanzi nake cemata ba yau kika ce min Zata rakaki gidan yayan naki ba take zaune..Tacemin yanzu zata tashi Sai gaki kin shigo..!
Inteesar ta kalli Munari wacce ke Dariya Tana Fadin"Kyaleta Abba..Ai ma mun fasa tafiyan sai gobe..!
Abba yace"To..Allah yasa Lafiya dai..?
Inteesar tace"Lafiya lau Abba..YaSadam din da zai zo ya Daukemu Tunda banta zuwa Gidan ba Ya kirani Aiki ya tasomai a asibiti Shine kawai nace ya bari sai gobe..!
Abba yace"Eh hakane sai goben kuje da Wuri yadda zaku yi musu Wuni..!
Inteesar tace"Insha Allahu Abba..!
Daga haka ta Mike kusa da Anty Safiya ta Karisa suka gaisa Tana Tambayanta Tasleem.
Anty Safiya tace tana gidan Anty Saratu ammh tace mata ta nan zuwa Tunda yanzu jarabawa zata zana na Fita,ba sosai take zuwa makaranta ba.
Nan Inteesar ta zauna suna Hiransu suna Kallo Sama Sama Abba kuma suna Gefe da Ya yusuf suna mganarsu Duk akan samun Lafiyar Abba ne Domin Lokacin da sukaje asibitin da Abba an yi mai gwaje gwaje kuma Alhamdulillah komai Normal Likita ya Tabbatar da Samun Lafiyar Abba, hakan wani karin abun Farimciki ne Duk mganar Abba na Shiryann su Tafiya Dukku ne Yusuf yace ya bashi Lokaci ya Dauki Excuse a wajen aiki koda na Sati Daya ne sai su Shirya Tafiya Zuwa Lokacin itama Munari tayi Covering din Semester ta Kada su Tafi ta dawo ta samu wata mtsala kuma ba yadda zasu iya tafiya su barta.
Suna nan Zaune sai ga Imran ya Shigo zai wuce Dakinsa Abba ya Saka baki ya Kirashi ya Juyo yazo ya Durkusa gaban Abba,ta gefen ido yake Satan kallon Inteesar yana Fatan kada Abba ya mai Dizgi gaban yaran nan.
Sama da kasa Abba ya Kallesa Kafin yace"Kaje ka sha Sigarin kenan..?.ga mamakin Inteesar ta zata zai yi Karya ne sai taji yace"Eh Abba....!
Zaro ido Tayi tana kallonsa Abba ya Girgiza kai yana Fadin"Yayi maka kyau..!
Cikin Sadda kai yace"Saboda bana so in sha kagani ne Ranka ya baci..Am Sorry Abba..!
Daga haka ya Mike ya wuce saboda baya so mganar tafi haka,Baya son Rainin yara Yana Kallon Inteesar ta gefen ido Tana kallonsa.
Da kallo suka bisa dashi Har ya Shige Daki,Abba ya Girgiza kai kafin yace"Bazai taba maka karya ba ko da Kashe shi zaka yi..!.
Yusuf yace"Daya daga cikin Tsautsauran Ra"ayinsa kenan Abba..!
Abba ya gyada kai kafin yace"Allah ya Shiryesa..!
Ya amsa da Ameen Inteesar Dake gefe aranta Tana ayyana bata Taba ganin Mutun irin Imran ba komai nashi Dabam ne.
Kiran Sallar La"asar ya tadasu Daga Falon su Abba sukayi alwala suka Fice zuwa Masallaci Anty Safiya ta Shige Shashenta Ita kuma Munari da Inteesar suka nufi Dakinta sukayi Salla suka Cigaba da Hira Rabinta duk na Karatu ne.
Suna cikin hakane Hafsah ta Kira Inteesar suka gaisa,ta bama Anty Faree itama suka gaisa kana Hafsah ta kara Karba Tana Tambayan Inteesar meyasa bata mgana a Famiy Group..? Inteesar tace haka kurum Hafsah tace ko Zasu Bude nasu isu isu Yan"mata..? Inteesar tacemata Shikenan daga haka sukayi sallama..
Bayan sun gama wayar ne Munari ke Tambayanta take gayamata Munari sai taji Tsausayin kansu aranta Tana Tunanin da itama Yau tana cikin Dangin da yan"uwa kanar Inteesar ganin Kamar munarin Fuskarta ta Sauya ne yasa Inteesar ta Tambayeta ko Lafiya..? Munari tayi Saurin Waskewa Tana Cemata bakmai ita kuma bata matsa mata sai taji ko menene ba,sai dai ita duk atunaninta Yan"uwansu Munari basa nan garin suna chan garinsu ne shiyasa bata taba Damuwa ta Tambayeta ba.
Inteesar nan ta shantake Munari na bata Labarin Tayi wani Saurayi a Sahad Store Ranar data Raka Anty Safiya da Ya Yusuf siyayyah ya nace nata sai da ta bashi Lambarta
Yayi ta Damunta da kira da mgana ta Chart Munari ta nuna ma Inteesar Hotonsa tana mata Dariyan Budurwan gajere Tunda gajere ne Munari na jin Haushi Tana Kai mata Dundu..!
Basu an kara ba sai da Anty Safiya ta Leko tana fada musu ana Kiran sallar mangriba,Suka Mike cike da mamaki,suka Dauro alwala suka zo sukayi Sallah kana Inteesar tayi Shirin Tafiya Munari ta Rakota.
Sun kawo Haraban gidan sai ga Abba da Ya yusuf sun dawo Daga Masallaci Abba nata Fadan meyasa tabari Dare yayi mata yace tayi Sauri ta koma Gida
Munari bata yi nisa ba Inteesar tace mata ta koma sai gobe zata Karisa Sukayi sallama Ta koma ita kuma Inteesar ta cigaba da Tafiya Ganin akwai Duhu Lokacin Wata bata Raba ba kuma yanayi ne ya Sauya ana mganriba Duhu ke shiga sai ta Fiddo Wayarta Tana Haskawa.
Wasu maza biyu ne dake Biye da ita Tunda suka Rabu da Munari irin yan iskan Gari ne masu kwacen waya Tunda suka ganta ta Fito da waya suka Fara Bin Bayanta Dayake Hanyar bata da yawann Mutane ba wanda ya Lura dasu,ga kuma Mangariba tayi Kowa yayi Salla ya shige gida.
Bata san suna Binta ba sai Daga baya Dataji Takun Sawunsu Daga bayanta Tana waigawa sai suka Tsaya Tundaga Lokacin sai Tsoro ya kamata bata yarda Dasu ba ta Fara Sauri sai da suka ga Hanyar ba kowa kana suka Fara Sauri suna so su cin mata ganin haka yasa Inteesar ta Fara gudu batayi nisa ba Daya yasha gabanta Dayan kuma yana Bayanta.
Gabadaya Inteesar ta Tsure Jikinta Sai rawa yake abunga gamai Tsoro tsayawa Tayi tana kamkame jikinta Cikin Muryan Tsoro tace"Su waye ku..? Lafiya kuke bina..?
Tafada Hawaye na cikamata Kwarmin ido...
Dayan ne wanda yasha gabanta ya Kece da Dariya kafin ya Mikamata Hannu yana fadin"Ba Dole bane kinsan ko suwa ye mu..? Ki bamu wayar Dake hannunki Salim Alim..Sai mu Rabu Lafiya in kuma kin ki..!
Ya fada yana nuna ta da Hannu kafin ya kara Sakawa Dariya na Bayan ne ya zuro Hannu zai karbi Wayar Inteesar ta Tsorata Ta kamkame jikinta da wayarta ta Fashe da kuka Tana fadin"don Allah ku kyaleni..Wayarnan wayatace bata ku bace..!
Tafada Tana waigen waigen ko Allah Zai kawo wani sai dai ba kowa..
Na gaban ne yace"Jika aiki Taurin kai Zata nuna mana jika mata aiki..!Hannu ya Daga Daga gefen Wandonsa ya Zaro Wuka Inteesar na ganin Wukan ta Kara Tsoracewa ta Zaro ido ba Inda Jikinta bai Rawa Cikin Rawan jiki Tana kuka Ta mikamusu wayar Tana Fadin"Ga..Gashi...Don...Allh kada ku tabani..!
Take Fada take gabadaya Zufa ya gama wankemata Hijabin Dake jikinta.
Dariya suka kwashe dashi a tare kafin na gaban ya karbi Wayar yana Juyata yace"Kin san da hakane kika faramana gaddama..? Jika aiki bata Mari koda guda uku ne ladan batamana Lokacin Datayi..!
Bai gama mgana ba ya Daga hannu Zai wanke Inteesar da mari wacce Har ta Runtse ido Tana makyarkyata tsoro Taji shuru Lokaci Daya Da tsayawan Wata inuwa agabanta Da Sauri ta Bude idanuwanta Duk da Bayansa Tagani jikinta da yadda Zuciyarta ta amsa ya Tabbatar mata da Imran ne
Bayan sun idar da Sallah ya Tsaya Kofar Shagon Sagir suna mgana Duk da Hirar duk Sagir keyinta sai dai gabadaya Zuciyarsa ta kasa Natsuwa yana jin Wani abu na Faruwa Domin gabansa ne ke Bugawa Fat..! Fat!
Wanda ya Rasa Dalili ganin haka yasa kawai yama Sagir Sallama ya biyo Hanya Tunda Daga nesa ya Hangosu,Da fitilan Wayarsa yayi amfani ya Haska kasa Da Zai wuce sun Shagala da aikata barnan su basu lura dashi ba.
Zuciyarsa ta kusa Bugawa Daya Fahimci Inteesar ce Maza Biyu suka Zagayeta Daya na Shirin kaimata Duka Cikin Zafin nama ya Dira gabansu Lokaci Daya yana Rike Hannun wanda zai kaimata Dukam Cikin Bacin rai da Zafin Zuciya.
Cikin mamaki suke Binsa da kallo na Gaban ne yace"Mallam lafiya..? Kada ka shiga abunda ba ruwanka ka barmu muyi aikinmu mu gama in ba so kake yanzu Jikin ka yayi Lahani ba..!
Bai ma tsaya Sauraransa ba ya yarfar da Hannunsa Cikin Fushi wanda sai da ya Ja baya kamar zai fadi cikin mamaki suka Dago suna kara Kallonsa.
Inteesar Data ga haka cikin Sauri ta Taso ta Rumgume Imran ta baya tana Mkarkyartan Tsoro da kuka Tana Fadin"Ya Imran sun karbemun waya..Sun fito da wuka zasu kasheni..!
Gabaadaya ta Rukumkumesa Kukanta kuwa ji yake kamar wani Dalma na Shiga Cikin kwakwalwarsa.
Ransa na baci Zuciyarsa na Zafi kamar Zata kama da Wuta Jijiyoyin kansa sun tashi Radau.
Mai Wukan ne yace"kai jika aikin zaka Ma haka..?lalle ka kira Ajalinka yau..!
Yafada Lokaci Daya yana Ciro wuka dake jikinsa ya Nufi Imran da ita yana zuwa ya daga zai Chakamai ya Damke hannunsa da Karfi Har sai da Wukar ta Fadi kasa ya murde hanun ka ya Saka Gwiwan kafarsa ya Daki bayansa sai da ya Fadi kasa,Dayan na ganin haka ya ja baya Cikin mamaki.
Imran ya