Showing 135001 words to 138000 words out of 235479 words

Chapter 46 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt

Janafty   

14 Jan 2025

16134

Umaima tana Tare dasu Munari Khamis kuma suna Haraban Gidan inda suke Walimar su nacin Abinci isu isu da sauran Mutane an Shimfida manyan Dardume suna zaune suna cin Abinci ga ababen sha nan Birjit sai wanda ka Zaba Imran ne kadai bashi a wajen kuma ba wanda ya Damu Dashi Sanin Halinsa.
Bangaran Amarya Sajida kuwa tana jin Gudan Inna Maimunatu Tana Fadin an Daura aure taji wani sukuni Tare da Salama ya Shigeta,abaya kafin Taga Imran tasha Mafarkin yadda Kayattacen Bikinta zai bar Tarihi a Nageria sai dai ganin Imran da Faruwar komai ya Sauya mata Duka Tunaninta Abunda ya Faru bai Dameta ba sai ma wani Salama Dataji na Zamo warta Mata ga Imran
Ya"yan Inna Bintalo ne suka zo suna ta Daukan Hoto da Sajida su Hamida,anan ciki aka kawo mata Abinci Tunda Daada ta hanata Fitowa Daga Dakin ballatana su Hadu da Mami Asma"u Alokacin ma ita kanta Sajidan bata kaunar ma taga Mamin Saboda tasan har yanzu da aka Daura bazata Daina adawa da wannan auran ba ita kuma ayadda Lokaci Daya Soyayyar Imran tayi mata kamun kazan kuku Tana Daidai da tayi Fito na Fito da wanda yace zai Rabata da Abunda take so..!
Bangaran Inteesar kuwa tun Safe tana Kwance gabadaya ayyukan da akayi da Ifacen ifacen da akayi ta yi acikin Gidan baisa ta Fito ba kanta Nauyi yayi mata Kirjinta na mata Zfi duk sanda ta Tuna da Imran zai auri Sajida ba yadda su Munari basu yi ba kam Tatashi Tayi wanka taci abinci tayi banza Dasu,gajiya sukayi suka kyaleta,su dai bayan sun gama aiki suka shaba wanka da kwalliya Har da Umaima Data shige Cikinsu suna ta Daukan Hotuna Munari ita ko ajikinta Domin ba wani Sanin Sajidan tayi ba,sai dai ta Tsausayamata Domin har ga Allah an bata aiki babba na Aura mata Ya Imu.
Inteesar tana daga kwancen Munari tazo tana Fadamata an Daura aure gasu Ya Basheer chan sun dawo Sai Inteeser taji kamar Zata Mutu sai Hawaye Sharr Hankalin Munari ya tashi ita taje ta Kira Umma Duk ta Rikice ta Rikita Umma itama ganin tana kuka yasa ta zata Jikin ne basusan Hakikamin me ke Damunta ba ita kanta bata sani ba Ballatana ta Fada musu sai dai Kirjinta nayi mata wani Zafi kukan datake yi shine kadai Salamanta.
Umma ce ta Lallabata tarakata Tiolet tace tayi wanka ta saka Munari ta Hado mata Tea saboda tasha Cikinta ya Warware,Inteesar na Shiga Tiolet din ta Zauna saman sit din Cikin Tiolet din ta Fashe da kuka yi take ba kakkautawa kamar wacce akace wani nata ya Mutu kanta yana Sara mata ga Nauyin Kirji,tana cikin kukan Wata Zuciya tace mata"To ke Inteesar kukan me kike yi..? Ina ruwanki Domin yayi auransa bai kamata kizo kina saka kanki acikin Damuwa ba Har kina kuka ba Tunda ba sonshi take ba..,!
Sai wata Zuciyar tace mata"Ko bana son shi ai dan"uwana ne bazan so mai abunda baida kyau ba..Sajida bata Dace dashi ba Shiyasa nake Damuwa..!
Tafada acikin Ranta tana jin yes wannan ne Dalilinta,Da wannan Tunanun ta Lallashin kanta ta yi wanka ta Dauro alwala ta Fito Umma da Munari na Jiranta,mai ta shafa kafin ta saka Doguwar Rigarta baka Kirar Armani,Munari ta mika mata Tea din tasha Umma ta balla mata mgani ta bata tasha ta Dora Tea din Daman tana jin yunwa Cikinta sai kuka yake,Tagama sha sai Zufa alamun dai ta Fara samuwa ganin haka yasa Umma ta Fita ta barsu,Munari ta Shimfida mata Darduma ta Fita ta barta Bayan ta Tada Sallah.
Tana Fitowa Falon Lokacin su Abba na Shigowa nan suka gaggaisa dasu Inna Maimunatu suna ma juna Fatan Alheri da Fatan an kulla alheri kafin su Dunguma Zuwa Dakin Daada dake Cikin Dakinta taci kwalliya bakinta Har kunne Casbaha na Hannunta tana ta Lazimi ranta Fes Koyau ta Mutu Burinta ya cika.
Ganin Shigowar ya"yanta nata yasa ta Kira Hamida tace tazo ta kai Sajida wajen Mahaifiyarta haka kuwa akayi ita ta rike Hannunta zuwa Dakin da Mami Asma"u wacce bakin ciki kamar ya kasheta.
Saboda Takaichi takasa ma cema Sajidan komai kallonta kawai take tana kyafci tana Girgiza jiki da kafa,Wayace a Hannunta tana ta Kiran Baffa Kabiru bai Dauka ba suna Gaban Daada,bazai iya Daukan Wayanta ba yasan Rigima ce kwance a wajen Mami Asma"u.
Inteesar Dole yasa ta Fito Falo Tunda Munari sun mtsa mata sai ta Fito,ita kuma Ranta baya mata Dadi,sannan bata son ta Hadu da Khamis yana ta Damunta da waya da Sako ko ta kansa batabi ba..
Koda ta Fito duka an hadu a falon Mazan da matan su inna maimunatu dai suna Dakin Daada su Aneesa ne dasu Anty Safiya kowacce tana Tare da mijinta sai su Munari dake Hotuna,Khamis na Dakin Mami yana bata baki har ya gama mgana kanzil batace ba,har yagaji ya Fito nan yayi Tozali da Inteesar ya kafeta da ido yana kallonta Yarinyar nan tana bashi Wahala sosai gabadaya soyayyarta ya gama kasarashi sai dai tanayin wani abu kamar bata gane ina ya Dosa ba..
Suna Hada ido ta Hada rai ta kauda kanta kamar bata ganshi ba ta Dauko wayarta tana Dannawa ba Domin tana wanu abu ba Imran take Tunani bata gansa ba wata Zuciya tace"Ina Ruwan ki kumi dashi..Yanzu ai baida Lokacinki Tunda yayi aure. !
Tuna haka yasa taji zaman Wajen ya gagareta tatashi tana Shirin Tafiya Zainab din Inna Maimunatu ta jawo tace suyi Hoto bata da yarda zatayi Dole ta tsaya Khamis kuma yana binta da kallon Sha"awa da kauna ya Nufi wajen su Basheer dake zaune suna Hira gefe kuma Matayensu Sa"id ne sun ci gayu suna ta Hira gwanin Sha"awa.
Suna ta Hotuna Kada Munari da Hafsah suji Labari,Munari ce uwar kankaba tace afito musu da Amarya suyi hoto Hafsah tasan Hali bata je ba Umaima ce taje ita dasu Hamida suka Fito da Sajidan Daga Wajen Mami Asma"u wacce ke cika tana batsewa kala bata kara Furtama kowa ba Bata so tayi mgana saboda in ta Bude baki tace wani abu zata iya Fashewa da kuka kuma Faruwar hakan kamar Imran yaci nasara akanta kenan Baffa Kabiru take jira shine Zata saukema gabadaya Bala"in Dake Cinta.
Sun Fito da Sajida nan Falo waje ya Kaure da Gudan ga Amarya su Sa"id na Dariya Yusuf da Sagir suna kallon Sajida sukace masha Allah tayi kyau matuka,Inda Imran mai Wayau ne basu ga aibun Sajida ba mace duk inda ake neman takai,Khamis yazo ya Rumgumeta ganin Inteesar a wajen Har dashi ya Dinga shiga Hoton Bakinciki ya cika Inteesar tana so ta gudu Munari ta Hanata,Ga Waleedan Anty Aneesa ta makalemata sai ta Dauketa Kallon Sajida take tana mamakin ganin ta ko Damuwa acikin Idanuwanta Fuskarta bayyana wani Damuwa ba,sun kalli juna ido Cikin ido kafin kowa ya Dauke kansa,Abunda ke bama su Inteesar da Hafsah mamaki ganin Sajida tana mgana da Munari har da mata Dariya Inteesar Ranta wani kuna yake yi wato Saboda ta auri Dan"uwanta Ita tasan Darajanta,Inda ma mutane zasu Lura Hawaye ya cika kwarmin idanuwanta Tayi saurin Sharewa kada wani ya gani.
Sun cigaba da yin Hotuna har Da su Sa"id da suka taso ana ta Family Picture,Khamis sai da yasan yadda yayi ya dawo kusa da Inteesar ya Riko Hannunta bata zata ba da Sauri ta Dago tana kallonsa Gira ya Dagamata Lokaci Daya yana marairaicemata kamar zai yi kuka kwace hannunta tayi tana Hararansa Haushi Rike mata Hannun da yayi taji Har Cikin zuciyarta.
Mtsawa tayi daga kusa dashi ta koma Kusa da Hafsah ganin munari na kusa da Sajida,wacce ke ta wurga ido tana Neman inda zata ga Imran bata gansa ba bata so kuma tayi mgana aga Zakewarta sai tayi shuru da bakinta.
Kiran Sallar La"asar da Fitowarsu Abba ya Dakatar da Hotunan suka ce mazan su fito su tafi masallaci matan kuma suma suyi sallar acikin gida.
Baffa Kabiru sai Lokacin ya Shiga Inda Mami Asma"u take tana ganin Shigowarsa Rauninta ya bayyana ta Mike ta isa gabansa Tana Fadin"Yanzu Kabir kana gani aka Daura ma yarka aure da wannan Dan iskan yaron.?Kana ji kana gani aka yi ma yarka auran kaskanci ammh ka kasa cewa komai ko Kabiru..?
Tafada tana Fashewa da kukan Takaichin Dake Cinta acikin Zuciyarta Saman kirjinsa ta fada Tana Dukansa Riketa yayi yana jin pain din Datake ji Cikin Lallashi yace"Ma"u ya zan yi..?Ni ban isa na Tsallake Umarnin Daada ba..Kada kuma ki manta Abubakar Dan"uwana ne Dana saki Nono ya kama Taya zan nuna ina gudin hada jininsa da nawa..?ya zai ji acikin Ransa..? Ammh wlh ni kaina Ma"u banso wannan Hadin ba Tunda kikaga ban yi mgana ba bani da Mafita ne acikim al"amarin..!
Ya karishe Fada yana riketa acikin jikinsa bata iya cewa komai ba sai kuka Bakimciki ya cika ta gani take Cika bakinta ya zama na banza Daada ta gama Cutar da ita cutar da bazata manta ba Har Abada.
Dakyar ya iya Lallashinta Tayi shuru da cewa bari yaje suyi salla su dawo zasu yi mgana kana ta yarda ta sakeshi ya Fice ta koma ta zauna tana Sharan kwallah jira take yazo suyi mgana Gobe goben nan bata kaunar ta kara Kwana agarin Dukku Har Daadan bata kaunar gani Zata Tarkata ya"yanta ta tafi dasu Sai taji kuma ta gani wanda ya isa yazo ya Dauki Sajidan Wlh sai dai ya gaji da auran ya Saketa tana Fatan Tsautsayi ya sa ya kwaso kafafunsa zuwa Abuja A nan ne Zata nuna mai ikon Barrister Asma"u..!
Imran sai bayan da kayi sallar La"asar kana ya Farka Daga Barcin Daya kwasheshi cikin kasala ya Mike ya Fada Tiolet ya Dauro alwala yazo ya saka Riga da wando baki da Fari,kana yayi Sallarsa acikin gida tunda an riga anyi Sallar,sai Lokacin ya Fito Daga Dakin Falon ba kowa duk suna Dakuna suna Sallah Hafsah kadai ya gani Data gaishesa Sai da ya juyo yana kallinta asaman Lebensa ya amsa kafin ya kada kai ya Fita Haraban gidan Inteesar yake son gani bai ganta ba Tun dazu din nan Daya hangota ta Boye kanta.
Yana Duba wayarsa su Basheer suka shigo gidan sun dawo Daga masaalaci
Ganin su yasa ya koma Chan gefe yayi kamar yana waya saboda bayason mgana da wani suna ba wanda yabi ta kansa Harta kuwa da Sagir suka Shiigewarsu cikin Gida sai da yaga Shigarsu kana ya Sauke Wayar Daga kunnensa ya Lalubo lambar Inteesar ya Tura mata sako.


"Kina ina ne..? Ki fito na ganki..!


Ya tura mata Ya koma ya Coge yana Jiranta,Inteesar kuwa Ta idar da Sallar kenan tana zaune kan Sallaya taji Shigowr sako Ta zata Khamis ne yasa batabi takai ba sai da mike Daga Kan Sallaya ta karisa bakin gado ta Zauna ta Dauki wayar kana taga sunan Imran har jikinta na rawa wajen Budewa abunda tagani ne ya Kara bata mata rai Baki ta Tura kamar Yana ganinta afili tace"Ina ruwanka dani..Kaje kaga matarka..!
Haka tafada Har sai da Munari Dake Zaune ta waigo tana kallonta ganin haka yasa Inteesar din ta Mike ta koma chan kusa da Tiolet ta turama Imran Sako.


"Ina daki ban ji dadi.."


Daman jiran sakonta yake yi yasa Yana Shigowa ya Duba Shuru yayi yana wani Tunani Jikinsa yayi sanyi bata da lafiya Har yanzu..!?
Haka ya Tambayi kansa da Sauri ya Tura mata sako.


"Ki fito naga yanayin jikin naki yanzu..Bana son gaddama do as i say malama..!


Ya tura mata Dataga sakonsa Sai da tayi yar dariya Imran bazai taba Sauyama ba.
Tura baki tayi kamar yana kallonta ta Turamai.


"Kana ina ne..?


Kamar yana jiranta ya Turomata.


"Ina Waje..ina jiranki..!


Ganin sakon sa yasa ta Dauki Mayafinta ta yafa Munari ta kalleta Tana Fadin"Ina zaki Kuma?
Tana yamutsa Fuska tace"Nan waje zani yanzu zan dawo..!
Hafsah da Munari suka kalli juna kafin su tafa suna fadin"In tayi wari zamu ji..!
Kallonsu tayi taja karamin Tsaki ta Fice,suka Bita da kallo suna Dariya su azaton su da Khamis suke mgana ta Messages kuma Wajensa Zataje shiyasa suke mata Dariyan sunsan komai.
Bata bi ta kansu ba ta Fice Taso ba wanda zai ga Fitarta sai dai duka suna Zaune acikin Falon Har dasu Abba Baffa Kabiru ne baya nan yana Dakin Da Mami Ta Sauka Sajida kuma tana Dakin Daada.
Wajen Daddy da Abba ta nufa ta Rankwafa ta gaida su,suka amsa mata Cikib Fara"a Abba ya Dafa kanta yana saka mata albarka Duk Khamis na Lura da ita Tun Fitowarta Mikewa Tayu tace Abba da Daddy bari ta zo yanzu zata dawo basu damu ba sanin ina Zata ba ta fice Daga Falon zuwa Haraban gidan.
Tafara Waige waigen Neman Imran kenan Khamis yasha gabanta da Sauri Har yana neman gugan Jikinta da Sauri Taja baya tana Binsa da kallo mai kama da Harara Cikin sanyinta tace"Lafiya?
Lamgwabe kai yayi yana Fadin"Kinsan ai me ya kawo ni wajen ki ko..? Look inteesar na gaji da Horan da kike min na Tabbata ke ba yarinya bace kinsan Abunda nake nufi kada mu bama junanmu Wahala..I love u Tun Ranar dana Fara ganinki sonki yana bani Wahala kuma da aure nake sonki ina so ki bani Dama mu Fahimci juna kafin iyayanmu suji mganar Daga Baya Plz.!
Ya karishe Fada yana narka mata wani irin kallo na Kauna Taso ta Yi mai Tsaki ne sai kuma ta fasa Tsuke bakinta tayi kafin tace"Ni ba yanzu zan yi Aure ba am sorry Karatu nake yi..!
Tana gama Fadin haka ta juya Zata wuce Caraf ya saka Hannunsa ya Damki Hannunta Wajen ta Waigo da Sauri gyalenta ya Zame daga saman kanta zuwa Kafadanta Gashin kanta ya bayyana wanda ke Tsife sai dai ta Nannadeshi Cikin band dinta
Juyowar da zatayi suka Hada Ido Hudu da Imran Dake Tsaye ta gefen Khamis Hannayensa goge a kirjinsa Zuciyarsa tana wani bugawa Tun Lokacin da Inteesar ta Fito ya ganta ya taka zuwa Wajenta ne sai ga Khamis yana bayansa Duk abunda ya Fada a kunnensa Bai taba jin Bakinciki ba irin na yau da Khamis yace wai yana son Inteesar yana kokarin Controling din bacin Ransa ne yaga ta juya shi kuma ya Riko mata Hannu gyalenta ya Zame gashin kanta ya Bayyana Agaban Wani katon Namijin yana kallon Hannunta Daya Rike ga kuma Mayatacen kallon Dayake Bin Inteesar dashi Kamar Zai Lasheta Tuni Imran yaji kirjinsa na Harbawa Jijiyoyin kansa sun mike Idanuwansa sun Rufe radadi ya cika Ransa na ganin wani rike da hannun Inteesar kuma yana kallon surar jikinta.


















*Shakira..*
3/22/22, 23:14 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�8*


*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*




Khamis da baisan da wanzuwar Imran Daga bayansa ba ya shagala da kallon kyakyawan Surar Inteesar da gashin daya kwanto ta saman Goshinta ya tafi dashi har baisan Sadda ya Furta"Wow..Beatifully.!
Yafada Cikin wata Murya mai cike da Muradi mai girma.
Imran Dake bayansa wani Takaici ne ya kara kamasa Tuni naman Goshinsa ya Tattare ya koma Waje Daya Inteesar yake kallo wace ke kallonsa Cikin Wani yanayi Dayake kara Wutar bacin Ransa.
Kokarin Daidaita kansa yake shi yasa bai yi mgana ba Hannu kawai ya Saka Cak ya Dauke hannun Khamis dake Rike da Inteesar Cikin ZAfinsa har sai Da wajen yarfar da hannun Khamis yayi baya Ya fadi kasa Dabas Saboda Imran din da karfi ya Wanchakalar da Hannun nashi,Shi kuma ya saki Jikinsa ne saboda baisan Haka Zata Faru ba Shiyasa ya kasa Rike kansa Har Sai da yakai kasa.
Da mamaki ya Dago suka Hada ido da Imran Dakemai wani kallo na rainin Wayau da kaskasci.
Saurin Mikewa yayi shima Ransa ya baci Cikin Bacin rai yace"Mallam Lafiya kazo ka Tureni na Fadi kasa..?
Imran ya Kara Hade rai bai yi mgana ba Ganin haka sai Ran khamis ya Fara Tafasa yana ganin Karshen Rainin Hankali Imran ya gama Rainasa shiyasa yakarisa gabansa ya saka Hannu ya Daki Kirjinsa yana Fadin"Mallam ina mgana ka kyaleni..? Wa ya baka izinin Tabamin hannu Har kana Tureni..?
Yafada Shima Fararan Idanuwansa sun Fara Juyewa zuwa Jajaye Alluran Sojojin shima sun Fara aiki ajikinsa.
Imran Dayake Cije baki Yana kokarin Daidaita Bacin ransa yaki cewa komai illah Inteesar ya kalla wacce Ta Fara Fiki Fiki da ido tana neman yin kuka ganin Abunda ke faruwa.
Cikin Dakiyarsa yace"Ki koma Cikin Gida..!
Tsayawa tayi tana kallonsa bata tafi ba Khamis ya kalleta yana Fadin"Tatafi ina..?Ina Ruwanka da ita ai bakai ka Kirata ba..Inteesar ba inda Zaki ok..?
Yafada shima yana bata Umarni Sai kawai ta Tsaya ta kasa gaba Ballatana Baya,Ran Imran sai ya kara Baci Zuciyarsa ta Fara Tafarfasa Cikin Daka mata Tsawa yace"Nace ki bar nan..!
Yafada Cikin Dakakkiyar Muryansa Cikin Fushi Daya Tsorata Inteesar ta Juya Zata Koma Cikin Gida tana Kokarin Boye kukanta da Hannunta Bayan ta saka Mayafin jikinta Ta Rufe bakinta dashi saboda kada kukanta ya Fito Khamis na ganin haka yayi Saurin Riko Hannunta again yana Fadin"Ba inda Zataje..Zan gani in kai ka Kirata in kuma Zaman ka takeyi Acikin gidanan..Haba rainin wayau ka ya Isa haka..Kana ganin cewa tsoron ka Kowa yake ji shiyasa kake yin Abu ba"a Tanka maka..? Wlh ina Daidai da Duk Abunda kake takama dashi Inteesar ba inda Zataje sai kayi abunda Zakayi in ka Isa..!
Ya Karishe Fada Cikin Bacin Rai yana kuma Rike da Hannun Inteesar wacce take kokarin kwacewa ganin yadda Imran yake kallon Hannun nata kamar Zuciyarsa Zata Buga ya mutu gabadaya Cikin Kokarin Daidaita kansa yake fadin"Sakar mata Hannu..!
Khamis ya kallesa yana Fadin"In naki fa..?Ko kana Tsammamin zaka Dakeni ne..?
Imran ya Taune Lebensa na kasa Kafin Cikin Tsawa yace"Nace ka Sake mata Hannu Kafin Raina ya baci..Nayi maka Biji Biji anan wajen..!
Khamis ya taresa Shima Cikin Tsawa yana Fadin"Naki na saketa din kayi Abuda zakayi..Ina Ruwanka in narike mata Hannun..?Au sonta kake yi..? Lalle baka da Tunani Shaye shayenka sun gayamaka karya in ka manta bari na Tuna maka Yau aka Daura maka aure da Sajida kanwata Ko agarin gaba gaba muke ana barin Halas ko don kunya..Ko kana so baka so Inteesar mallakina ne ina sonta kuma Zan aureta ita din Tawace..!
Ya karishe Fada yana kara Riketa wannan karon harda Kafadunta duka Biyu.
Ai Imran sai yaji wani Tukikin Takaichi acikin Raina Duhu ya mamaye idanuwansa na ganin yadda Khamis

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login