Showing 141001 words to 144000 words out of 235479 words
Chapter 48 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt
bai damu yace dasu wani abu ba..
Ammh acikin Ransu suna Fata damai addu"an Allah ya sassautamai koma Miye ke Damunsa acikin Zuciyarsa.
Bayan Abba da Ya yusuf Inteesar ma tana Cikin Damuwa wannan yanayin da Imran ke Ciki Tunda suka Dawo bai kara yarda sun hadu ba Tayi ta Turamai sako zai gani zai karanta bazai bata amsa ba,Datagaji sai ta Fara Kiransa nan ma sai ta gaji da Ringing bazai dauka ba Daga karshe sai ya Kashe wayarsa Inteesar ta shiga Damuwa sosai na Rashin Sanin Halin Dayake ciki ga Karatun makaranta yayi Zafi sai ta fara Rama atsaye gata Daman ba wani kauri ba,Duk yadda taso su hadu hakan bai samu ba Zasu kwana su Wuni acikin Gidan nan ko Gilmawarsa bata isa ta gani ba Tunda suna Raba Raba ne,Yau su kwana a nan gidan Gobe gidan Mama saboda ta Saba da Inteesar tafiyarta zai saka ta ji Kadaici ya Dameta shiyasa suke Raba Raba ita da Munari da suka kara Shakuwa kamar wasu yan Biyu Daya bai iya Boyema Daya abu sai dai Inteesar ta Boyena Munari Damuwarta kan Imran ko dataga Tana ta Ramewa Data mata mgana sai ta ce saboda Stress din Karatu ne.
Inteesar Zuciyarta Zafi take tana da Raunin Data kasa Daukan Lamarin Imran yana bata Wahala batare data san Dalili ba Zuciyarta na Zafi Wani Lokaci Jikinta ya Dauki Dumi Zata iya Jure komai banda Fushin Imran Dafi ne gareta Ta zauna Tayi ta kuka ita Kadai in abun ya Dameta sai kuma Daga baya tayi wani Tunanin Kila ya Daina kula tane saboda Sajida yayi auransa me zai yi da ita yanzu..? Inteesar batasan Soyayya ba Domin bata taba yi ba ballatana ta gane itace ta mata Mugun kamu sannan bata karance karance Social median ma Bata wani Dameta ba,shiyasa ta gaza Fahimtar wani Hali take Ciki kamar yadda Ego din Imran yaki bari ya Fahimci Inteesar ta gama Mamaye Zuciyarsa da gangan Jikinsa ta yadda bazai iya Gudanar da komai acikin wannan Rayuwar ba sai da ita.
Abunda Inteesar bata sani ba Imran yafi ta Shiga Damuwa ya fita Wahala akanta,Sai dai shi Namiji ne kuma Shi din bamai Rauni ne bane ko Rauninsa ya bayyana baya yadda wani na Kusa Dashi ya Fahimta.
Atsakanin nan yadda yake azabtuwa da Rashin ganin Inteesar ko Abunda Daada tayimai baya Damunsa Saboda yagama da wannan Shafin Tuni Ransa ne yake bace tun Dawowarsu Daga yaji bayason kowa kusa dashi yafi son ya zauna shi kadai Daga shi sai Busa Hayakinsa,Bai taba Tunanin Rashin ganin Inteesar zai zama Cuta garesa ba sai alokacin,Fushi yake da ita Fushi mai Tsanani Saboda In ya Runtse idonsa ganinta yake Khamis rike a Hannunta sannan kuma yana Tuna kalamansa na ita din tashi ce in ya Tuna Hakan sai yaji har ita bayason gani kwata kwata..
Yana ganin Sakonta kuma yana karantawa Domin sune suka Zamemai Tamkar Rigakafin Samun Saukin Wutar da Zuciyarsa ke ciki,In bata Turo ba Wuni zai yi yana Duba Wayarsa yana sakin Tsaki in bata Turo ba Haka zai ta maimata sakonta na Baya wani yayi Mirmishi wani yaji Haushi,in kuma ta Turo ya Dinga maimaitawa kenan kamar yadda yarinyar ta damu dashi matuka Sakonta Duka iri Daya ne.
"Ya imu kana lafiya ko..?
"Kaci abinci..? Don allah ka Rika cin Abinci bana so ka zauna da yunwa.."
"Fatana dai ba rashin Walwalarka Laifi nayi maka ba ko?
"Ya imu plz am sorry in wani Laifi nayi maka kada ka Hora kanka da Zaman kadaici.."
"Ok..Naji..Plz kada rika shan Sigari..bana son watarana na Rasaka I miss u.."
Iraren sakonta kenan sakon da sukasa Nishadi,Suke Debemai kewa Cikin Satin Dayan da yayi yana Boye mata kanshi,Ko Sagir bai kara yarda sun Hadu ba Tun bayan Dawowarsu ya Kirasa a waya yaki Dagaewa Kila Shima Fushi yayi bai kara Kiransa ba kuma bai nemesa ba Shima yafi son haka,Yafi so ya gama Da Kansa Tukunna kafim yazo kuma yaji da Damuwar wasu kuma.
******
*Abuja*
Labarin mutanen Abuja Hajiya Mami da ya"yanta wanda tunda suka koma bata barsu sun zauna Lafiya ba haka take ta fada Tana fadin Baffa Kabiru yayi Shuru Danginsa sun ci Zarafinta ita da ya"yanta tayi ikirarin wlh Sai ta Raba auran Sajida da Imran yarta bazata taba zama da Dan"iska ba.
Baffa Kabiru dai bai ce mata komai ba Khamis ne ke bata baki shima ta Hada dashi ta Balbale tare da Gargadi mai Girma kada ta karajin mganar Inteesar a bakinsa bata kaunar wannan Hadin kwata kwata,Ita ce nan Mahaifiyarsa ita Zata zabamai da matar Daya dace da shi.
Anan gabar kan Baffa Kabiru yayi mgana yace mata kada ta shiga Hurumin da banata ya yadda Imran bai Dace da Sajida ba,Ammh Inteesar bata da wani aibun da Zatace Khamis bazai aureta ba Kuma Diyar Mustapha ce suna da kyakyawan alaqan Jini da yan"uwanta da bazai ji Kyashin Hada Zuru"a dashi ba.
Mami Asma"u na jin haka ta Daka Tsalle tace bazai sabu ba bazata bari su hade mata kai shi da Danginsa ba,Sajida an mata auran kaskascin Auran da bazata iya Daga baki ta Fadeshi Cikin Dangi ba Ta tabbata masu mata Dariya suna da yawa sannan kuma shima Khamis din sai ya kara Zama nasu ta gama Wahala Dashi ya kawo yanzu sai ya zama Surikin Mustpaha da Salaha ita ta Zama yar kallo kenan bata yarda ba bata Amince ba kuma ba wai tace yarinyar nada Illah bane kawai Hadin ne bai mataba bata Ra"ayi kuma Tunda aka mata fim Karfi kan Sajida wannan karon bazata kara yarda ba.
Baffa Kabiru dai bai biye mata ba Sanin Halinta sai ya kyaleta,Sai ta koma kan Khamis tajamai kunne sosai na kada ya sake taji wata mgana kan Inteesar ta kara tashi Daliln Dayasa yaji Zaman Abujan ya isheshi kwana Biyu yayi ya koma Anambara Sai dai kafin Tafiyarsa sun yi mgana da Baffa Kabiru sosai ya bashi Daman Indai yana son Inteesar ya Nemi soyayya da yardanta yayi mai alkwarkn zai shigemai gaba sai ya aureta da wannan kwarin gwiwan ya koma Bakin aikinsa da yakinin zai samo kan Inteesar da yardanta Tunda Dad ya shigemai gaba Mami ba Damuwarsa bane in ta gama bambaminta shikenan.
Bangaran Sajida Mami Asma"u ta dawo kanta ganin Khamis ya koma bakin aikinsa,Ta riga ta kudura ma Ranta Tsarwatsa auran nan kuma ta Lashi Tokobin sai ta Wulakanta Imran Tana Fatan ya tako kafarsa zuwa Gidanta sai ya Raina kansa.
Tattara Sajida tayi tace ta koma makaranta Zasu fara Test,Daman A Hostel take zaune sai dai bayan 2 weeks take Dawowa Gida tayi weekend wani Lokacin har Sati ma Tana Dawowa Gida sai in Sun Fara Test ne ko jarabawa take zama acikin makaranta sosai wannan karon Mami bata ma barta tayi Tunanin makomarta ba ta Tarkatata makaranta da kanta ta kaita ta maidata bayan ta mata Fadan ta Cire komai acikin Ranta tayi Facing din Karatunta kamar wani abu bai Faru ba Sannan ta Gargade ta kada ta Sake ta fadama wani an mata aurre..Domin kaskanci ne sosai wani yaji wannan Labarin Sai ayi mata Dariya.
Sajida a makaranta bazatace ga Halin Datake ciki ba,Zuciyarta da Duka Tunaninta suna wajen Mijinta Imran ne bata San ta wata Hanya zata bi ta samesa ba,Ba mgana take da kowa ba Acikin Dangi ballatana ta saka ran Zata samu ko wajen wata ne,Bata kuma da lambar Munari Umaima ce ke dashi kuma tana gida bata san kuma ta Kirata Mami taji Labari ita ko bata Dama ta gana da Mijin nata ba"ayi ba abubuwa suka zo suka Faru ba Dadi ita dai koma Menene bazata yarda Mami ta rabata da Imran ba Tana son shi tana Kaunarsa ya Dace da Duka Zabinta bata damu da Hallayarsa ba shi take so kuma bata Damu da Rashin Jituwansu da Mami ba Ballatana Ya Khamis ba yare Daya take Fahimta Shine Son Imran mijinta Har wani alfahari take da hakan kuma bazata jura ko Ganin wani ya Shiga Tsakaninta da abunda take so ba, koda Mamin ne da kanta.
Haka take Sukuku bata da wani Karkashi Allah ne ma ya Taimaketa Kwakwalwarta naja shiyasa ta iya Tabuka wani abu a Test din da sukeyi ammh Rabin Hankalinta da komai nata suna ga Imran ne duka Mafarkinta nashi ne.
Ta bari ne su gama Test ta dawo gida Sai ta san yadda tayi ta mallaki lambarsa su rika mgana Kila jin Muryansa zai Rage mata wani Radadin ba ruwanta dashi bai Nemeta ba,ita din zata Nemesa saboda Shi din Mijinta ne nata ita kadai.
*******
*Kano..*
Yau ta kama Jumma"a ne a masallacin Jumma"a suka Hade tsakanin Sagir da Imran,Daman nan suke Sallar Jumma"a Shida Sagir,Abba kuma na chan Tsallaken Gadon kaya yake zuwa ,Tun ana Huduba Imran ya iso masallacin,shiyasa ya samu Shiga Cikin masallacin aka gama Huduba aka Tada Sallar sai da aka idar irin Tururuwan Fitowana nan sukaci karo da juna.
Tsayawa sukayi suna kallon kallon juna Sagir na sanye Cikin Sabuwar Shaddansa Fara Dinkin zamnii na Riga da wando Da Hulansa Zanna Bukar,sai Dardumansa Dake hannunsa yayi kyau sosai kuruciyarsa ta kara Bayyana da Samartakansa..
Yayinda Imran ke sanye da Jallabiya mai Ruwan madara,bata da tsawo sosai sai ya Hada da wani bakin Wando kafarsa Cikin Takalminsa Sawu Ciki na Fatar damisa,kansa ba Hula sai dai yasha gyara Hannunsa kuma Agogon Fata ne baki na Fatar Damisa fuskarnan ko kadan ba Fara"a Ya wani Kara Dakuna Fuska da suka Hadu da Sagir.
Sagir bai damu ba Mirmishi yayi mai Lokaci Daya yana bashi Hannu alamun Musabaha bai yi gaddama ba ya mikamai suka gaisa Daganan suka jera har Wajen masallacin Mutane nata Xirga Zirga tafiya masu ababan Hawa nayi masu Tafiyar kasa nayi.
Sagir ya kalli Imran yana Fadin"Kazo da Mashin ne..?
Ko tankasa Imran bai yi ba Hanyarsa ya Dauka ya Fara Tafiya wanda hakan da yayi shi ya bama Sagir amsa sa bai Hakura ba ya taka ya Bisa suka Fara Jerawa Suna Tafiya Kafada da kafada ammh ba wanda ya kara ma wani mgana sai Sagir ne ya kallesa yana Fadin"Na kiraka baka Dauka ba..Hala wayarka Ta lalace ne..?domin naga baka Biyo baya ba..?
Imran ya wani kara Tamke Fuska Hannuns Daya Cikin Aljihun Jallabiyansa kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Bata lalace ba..Kawai bana Ra"ayin mgana Dakai ne..!
Sagir na Dariya yace"Nagane..Daman mai Amarya Danyan Sharaf irin Sajida ina zai yi ra"ayin mgana Damu..!
Kamar ya watsamai Wuta haka yaji mganarsa Da ace ba domin suna Bakin Titi bane da sai ya Daki bakin Sagir ya Fitar da jini sai dai yaci Daraja Daya suna Cikin Mutane ne da yau ya gane Kuransa na gayamai wannan mganar.
Kala bai kara cemai ba Sai ma kara Hade Rai da yayi yana wani Bude Hanci ganin ya kunnosa yasa Sagir bai kara mgana ba sai Kunshe Dariyansa yake yi.
Haka suka rika Tafiya kamar kurame har suka kariso kofar Gidan su Sagir din wanda yayi ya shiga ya gaida Mama yace bazai shiga ba kuma Shima Sagir din bazai shiga Gidan ba yanzu Sagir ya Tsaya yana kallon Ikon Allah ga Shagonsa yaronsa Auwal ya Rufe sun tafi masallaci Da alamun ya Rigasu dawowa.
Bai ce komai ba ya gyara Tsayuwa suna Tsaye kafada da kafada suna Bin Hanya da kallo kamar masu kirga wani Abu.
Ta bangaran Imran ba haka abun yake yau yaji ya gaza Inteesar kadai yake son gani,in bai ganta ba ji yake kamar zai iya Mutuwa gashi ta Daina Kiransa kwana Biyi bai ga Sakonta ba Ko ta Daina Damuwa dashi ne..?
Juyawa yayi yana kallon Kofar gidan Mama Tun jiya bai ji Motsinta ita da Munari agidan ba,kila Gidan Mama suka kwana kuma yau har yabar Gida bai gansu ba Abba da Anty Safiya ya bari agida Yusuf na wajen aiki.
Kallon Kofar gidan yake kamar yana so yaga Inteesar din ta Fito Sagir Dake Lura dashi Tun dazu ya Juyo yana kallonsa Cikin Nazarinsa kafin yace"wai wakake nema ne sai kallon Waje Daya kake yi..?Nace kuma kazo mu shiga kace A"a..!
Imran bai ce komai ba sai ma Mtsawa Da yayi gefe ya Fito da wayarsa Dake Cikin Aljihu Sagir na gefe Hannunsa Saman Kirjinsa yana kallon ikon Allah Cike da Nazarin Imran din.
Sako ya Tura mata saboda yana son yaji ko Tana ina ne..?
'"Kina ina ne.."?
Haka kurum ya Turamata ya koma yana Jiran Tsammanin amsarta Sai dai Har wajen Shudewar Mintina Goma bai jita ba sai kallon Wayar yake yana Sakin Siririn Tsaki wata Zuciyar na Fadamai kila Fushi Take yi Dakai tana Kiranka baka Dauka Ransa ya kara baci Wato ita ce ma Zatayi Fushi ita bata ga abunda tayimai ba ko?
Kwafa yayi kawai yana kokarin Daidaita kansa Sagir Dake lura dashi ya matso kusa dashi yana Fadin"Wa kake ta kira ne haka..? Ko yaki Dauka ne naga sai Tsaki kake ja kai kadai..ko Amarya ce taki Dauka tana ja ma Ango aji..!
Ya karisa Fada yana yar Dariya wani banzan Kallo Imran ya Bisa Dashi kafin ya maida wayarsa aljihun Jallbiyan Dake jikinsa Kokarin Dunkule hannu yake yakai ma Sagir din Wani Naushin da Kila sai Bakinsa ya Zubda Hakora Lura da Hakan da yayi ne yasa yamtsa da Sauri yana Fadin"Daga mgana..? Allah ya Huci Ran angon Sajida ya Dade..!
Yake Fada yana Dariyan ganin yadda Fuskar Imran din tayi saboda Haushi Kwafa yaja kafin yace"Banza Dan saka ido..Ai daka Tssya Daka gane Ango yau..!
Yafada yana kara Sakin wani Tsakin ya koma gefe wayarsa ya kara Fiddowa Shuru bai ga Sakon Inteesar ba Ransa sai ya kara baci,Ga Sagir Sai Dariya yake yi mai Banza Dashi yayi bai bi ta kansa ba Duk da Sunan Sajidan Dayake ambata kamar ya Juya ya Watsamai mari da ashariya haka yake ji.
Sagir ganin Imran din bai kula sa ba sai ya Daina ya Matso kusa dashi ganinsa sai Bini Bini ya Duba Waya yana Sakin Tsaki ya Fahimco wani abu na Damunsa Cikin Lallami yace"Meke Damunka Imu..?na lura dakai kamar Miskilancin naka yau yafi na koyaushe..!
Imran yayi kamar bai jisa ba Sai chan yace"Ina Ruwanka..?
Sagir ya kada kai yana Fadin"Au Daga Tambaya..? Nima Allah karamin da nake kokarin jin Damuwarka kaga Tafiyama ka Dade damuwar bata Kashe ka ba Tunda kai baka son Abun Arziki ba..!
Yafada Lokaci Daya yana wucewa Shagonsa ya shige Daman Tun dazu suna Tsaye su Auwal din suka Dawo suka zo suka Bude shagon da kallo ya Bisa shifa bama Sagir ne agabansa ba..Damuwar Dayake ciki tafi karfin ya Tsaya yana bi ta kansa wanda yasan anjuma nan zasu Shirya kansu.
Ganin Shuru Shuru bai jita ba yasa ya yanke Shawaran Kiranta Duk da baya son Kiran nata ammh Zuciyarsa ta Rinjayi gangar Jikinsa Daya kasa Hana kanshi Sai dai ya gansa kawai yana Kiranta,Zuciyarsa Bugawa take da Sauri da Sauri so yake ji Muryanta ko ya Samu Salama,Sai dai me yana Kiran nata ta shiga yaji Call Waiting ma"ana Tana amfani da wayar kenan Wani Rugugin bala"i Imran yaji sun Saukomai acikin kansa Har wani Jiri Jiri yake gani bai Katse Kiran ba Sai da ta yanke da kanta,Kansa ya Dafe yana jin wani Daci Daga kasan Ransa Wato ma Tana ganin Sakonsa Tayi banza Dashi..? Da ganga taki kulasa..?kan Bala"i bata san Waye Imran ba Ya zama Dole Abunda yake so ayimai in kuma akaki yimai ba Zaman Lafiya.
Wani Tunanine ya shiga kansa Kodai da wannan Banzan gayen take waya ne..? Domin ai yaji Daada ta bashi Umarnin ya Nemi yardanta in ta Amince shikenan Tuna Haka da yayi sai da Idanuwansa suka Sauya Launi Kirjinsa ya Fara tashi yana komawa da wani bakin Kishi da shi kanshi baisan yana da shi ba Tana Waya dashi Shine tayi banza Dani..Ina Bata isa ba..Shima khamis din bai isa ba Inteesar bazata taba Zama nashi ba Har Abada.
Abunda bai sani ba Sakon Daya Turama Inteesar ba ita ta gani ba Munari ce,Domin yau din da Safe suka Shiga School shima Assigment suka yi Submitting,suka Dawo gidan Mama suka kwana Daman bayan sun Dawo kuma suka yi Girki,Da Niyyar da sun gama zasu je gidan su Munari,To bayan sun gama ne Duka aikin su ne Mama tana Falo ta samu Barci Saman kujera ita kuma Inteesar ta shiga wanka Munari tace bazatayi wanka ba sai anjuma Tunda Tayi da Safe Inteesar tace sai ta karayi bazata iya Fita hakanan ba Tayi kaurin Kitchen Munari ta tabe mata baki ta shiga wanka tana mata Dariyan kazama Tana jinta bata tanka mata ba..
Tsakar gida Munari ta Fita ta Dauro alwala tazo ta shimfida Darduma tayi Salla Ta idar kenan tana kan Sallahya Tana Lazimi taji shigowar sako Daga wayar Inteesar wayar tana kusa da ita ne Daga bakin gado sai ta saka Hannu ta Dauko Tasan Passaword din Inteesar yasa ta saka ta Bude Tana Budewa ita bama da Niyar ganin wanda ya Turo sakon ba sai dai ganin Sunan YA IMU�� Da Love agaba alamun Shi ya Turo Sakon ya bata mamakon da batasan Sadda ta shiga Sakon ta karanta ba Mamaki ya kara kamata ita dai Ya Imu Daya ta sani..Kuma in shine yaushe suka Fara haka da Inteesar bama haka ba Shi yana da Lokacin Tura ma mace Sako ne..?kodai wani ne bashi ba..? Bata gasgasta ba sai da ta jawo wayarta ta Kwafe lambar Imran ta Saka awayar wata Tana Danna Wajen Kiran Sunan Daya Fito ya kara bayyanar mata da komai Batasan Sadda Dariya ta kamata ba Ya Imu da Inteesar What a pecfect martch,Bata Tsaya sanya ba ta koma Cikin Masages din ta Rika karantawa Tunda Daga Farko Tana karantawa Tana Tsintsiran Dariya ita kadai Ganin irin yadda Imran din ke Rubutoma Inteesae sako kamar Dole?Wannan wani irin Soyyyace..! Lalle ta yardan ma kanta Ya Imu ne na Dabam ne taga duka Sakonnin da Inteesar ke Turamai yaki bata amsa Duk Sai taji bataji Dadi ba Har ga Allah Zata Fi kowa Jin Dadin wannan Lamarin Sai dai Tana Tsausayama Inteesar Zata Sha Wahalan Soyayya da Imu saboda Baya bama Masu zama dashi Damar Saninsa in yau yazo da wannan kalan gobe wani ne,Ta fara Tuna duk Abubuwan da suka Faru da yawan mganarsa da Inteesar ke mata da yawan Damuwa dashi dashi kanshi Yadda yayi Fada da Khamis a Dukku Saboda ita Allah Sarki su kuma irin su haka Salon Soyayyarsu