Showing 192001 words to 195000 words out of 235479 words

Chapter 65 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt

Janafty   

14 Jan 2025

16147

Alhassan bai da tacewa Saboda duk abunda ya Hada da iyalan Gidan su Imran bai da Karfin Gwiwan yin wani Motsi mai karfi Gabadaya ma Sha"anin Biki,Hajiya Mero da Danginta ne suke ta kaida kawo da gayya ma Hajiya Mero ke basa Labarin Wasu abubuwan Saboda ya Shaka.
Umaima bata samu zuwa ba sai Ranar Alhamis Ranar da zasu yi Bridal Shower dinsu,Ta jirgin kasa ta zo Baffa Kabiru yayi yayi Ta bari yasa Direba ya kawota tace ya siyamata Tiket na Jirgin kasa Zata iya kai kanta Har Kaduna Bazata gane gidan ba Zata Kira Munari a waya haka kuwa akayi Tana isowa kafin ma ta Kira Munari Baffa Kabiru ya Kira Basheer ya Fadamai yaje ya Daukota in ta Sauka.
Daman Tana da Lambar Ya Basheer din ta Kirasa ta Fadamai ta Sauka Daman yana Kusa shi yazo ya kawota Har Gidansa Inda su Inteesar din suke nan fa suka Hade suka Rungume juna Cikin Farincikin ganin Juna Umaima Babu Ruwanta Tana da kyakyawan Zuciya bata taba Duban Inteesar da Duba Ta auri mijin yar"uwanta ba,Tasani komai ya Faru Daga Allah ne SannanTa sani Mami bata san auran Shiyasa ita bata ga abun nuna Wata Damuwa ba ta shigo Cikin yan"uwanta wanda daman Tare suke Shirya komai..
Agidan Ya Basheer suka Shirya kayattacen Bridal Shower dinsu,Nasara ta gayyato Kawayen Inteesar sosai da suka yi makaranta Tare,sun kira mai Decoration yazo ya kawata Haraban gidan komai dai sun yishi Cikin Tsari da Wayewa Khalil da Sagir sun yi kokari Su suka basu 100k bayan Dinner da zasu Shirya Sagir fa gabadaya albarkar Dinki ya Fito Dashi Ana ta Hidima Indai akan Imran ne ko nawa ya Kashe bai Fadi ba.
Sun Kira mai Makeup Tazo ta Tsantsarama Amarya Kwalliya mai kyau ita da Zaratan yan"uwan nata Munari da Umaima da Hafsah da Nasara suna Zagaye da ita Kawayen su sunzo sun mata kara sosai Sun Kira Dj yazo sun Chase iya Chasewa Anty Hauwa da yan"uwanta duk sun zo Da kannenta dasu akayi komai Ga Cikinta ya Fito sai Fama Take yi ita da Anty Safiya ga Hidima suna Fama da Ciki agabansu Tiri tiri,Sun sha Hotuna sosai Inteesar tayi kyau matuka Sanye Cikin Red din Yadi Daman kusan Ja kalanta ne sai akayi mata Head da Bakin wani yadi mai kyau yana Daukan Ido Fitted ce Rigar ta kamata Daga kasa an Saki baza Rigar da wani Bakin Tazaran wani yadi mai Raga Raga,An Salaga mata Wani Yadin Fari mai Dauke da Rubutun BRIDE..!
Su Munari suma Haka akayi musu Dinkin Sai dai nasu ba"a Sake sa Daga kasa ba ammh su nasu Kalan Lemon Green ne sai akayi musu Kwalliya da Jan Flower suka Sirka suma sun sha Kyau Masha Allah,barin ma Amarya kamar ka saceta ka gudu Saboda yadda Inteesar tayi kyau sosai Sai dai ta Rame kadan Saboda Stress din Maakaranta da Zirga zirga da kuma Fargaban wannan Tarewar.
Sai 7pm na Dare suka tashi Daga Shagalin Tuni Hotuna suka Fara yawo a Social media barin ma Group din Marigayi Hamisu Dukku nan suka Turasu Kala Kala yan"uwana saiDauka suke suna sakawa a Status Intergram,Da sauransu suna Tayasu Murna sai dai Ba Ango ba wanda ma yaga Kyallinsa sai dai Sagir sai da ya Nuna mai Hotunan,yafa ga yadda Inteesar tayi kyau matuka sai dai ya kauda kansa bai nuna ma Kwalliyar nata sun Dakesa Har yaji yana son kallonta bai ko son Kiftawa.
Basu yi waya ba Tunda suka je Kaduna sun dai yi mgana Lokacin Tana Dukku Har tabama Daada sukayi mgana Inteesar din bama ta san ina Isalin Wayarta take ba Tana Hannun Munari Shi kuma Imran aiki yayi mai yawa ga Gida ya Fara cika da Jama"a Jiya ma Dakin Sagir ya kwana saboda baya son Hayaniya Mama ta na chan Gidan itama suna ta Hidima ya Kirata Sau Daya Munari ta Dauka yana jin Muryanta ya Kashe bai kara Kira ba ita kuma bata Nemesa ba sai da yaga Hotunan nan ya gane ga Shanshancin da suka Tsaya yi kenan Inteesar ta manta Dashi,Harda Videon da sukayi Rawa suka saka Inteesar a Tsakiya suna ta Rawa su Munari ita dai batayi Rawa ba Tana Tsakiya Tana Mirmishi Hade rai yayi yana mamakin yara kanana sun iya Iskanci haka..?
Shiyasa yace baya son Bidia a Bikinsa bazai Dauki wannan Shanshancin ba.
Washegari kuma Jumma"a A Kaduna aka tashi da Yinin Biki,yinin Bikin Gabadaya a Gidan Daddy zasu gudanar Harda Lonching din wanda Za"a Fara da karfe Biyu na Rana a tashi Shida na yammah kuma a Haraban Gidan zasuGudanar da komai.
Imran bai so yazo kaduna ba Daman yayi niyyar ba zo ba din Sagir yace saiyaje Ya Yusuf ma Haka Sadam da Sa"id ma sun iso sukayi mai Chaa suma Kadunanan zasu su Dagachan ne Gobe zasu Dauko Amarya da Tawaganta Imran yaso ya Zille sai dai bai isa ba Abba ya saka baki kuma Daga Wajen aikinsa Mr.Sulaiman ya bashi Hutu na Ranar yace yaje bakomai ya kuma Hada damai Fatan Alheri bai yi mamakin a ina yaji ba Tunda yana Tare da Katon Ameobe Sagir kenan.
Ai bai gama mamaki ba sai da Khalil ya Kirasa yace mai yanzu zai Hawo Jirgi ammh ta kaduna zai Sauka su Hade ta chan Tun jiya yaso tahowa bai Samu Dama ba Dr.Ali isa Argungu ne suka Taho jiya Hajiya Barira tazo Duba Innarta Dake Fagge bata jin Dadi Daganan zasu zo suyima Abba Allah sanya alheri kafin su koma.
Imran ya kasa mgana Lokacin da Sagir ya Fitomai da Sabuwar Bugaggiyar Shadda Gezner wanda taji Dinkin Hannu na Zamani Dinkin Riga Sharashara da Babbar Riga,Aikin jikin Shaddan Baki ne Haka ma Hula kansa baka ya sanya da Bakin Takalmi Rufaffe na Matar Damisa Agogon Hannunsa ma Baki ne shima na Fata ne mai kyau da yarari duka aikin Sagir ne shima Irinta ya saka sai dai Tashi ba Babban Riga Imran yayi kyau Har gaji da kyau kamar Wani Wata Dan Daran Goma sha Biyu yadda yake Walwalin Daga Kallon Farko zaka Fahimci Yana cikin farinciki duk da Fuskarsa bata wani Saki ba sosai.
Lokacin da sukaje yima Abba Sallama sai da yaja Dogon Tasbihi ga Allah Domin yadda Imran ya zama kamar Wata acikin Taurari ya Dafasa ya yi mai addu"aTare da sakamai albarka Daga Karshe ya Bisu da Allah ya kaisu Lafiya
Sagir da Imran Motar Yusuf suka Shiga Sa"id da Sadam suka tafi a Motocinsu tunda suna tare da abokansu ne suma,Karfe, 1pm suna cikin Garin kaduna a masallacin Sultan bello sukayi Sallar Jumma"a kana suka karisa gidan Daddy wanda dashi da Ya Basheer din duk sun gansu nan a Masallacin Tare sukayi Salla bayan sun idar suka Dumguma gabadaya
Koda suka isa an kawata Haraban Gidan da ado mai kyau an saka Kanofi da kujeru duka aharaban Gidan Masha Allah ga masu abinci nan kala kala Daga mabambamta Gidan abinci ga Moticin Ababen sha nan sai Wanda ka Zaba Falon Bakin Dake kofar Waje Daddy ya shigar da ya"yan nashi kana ya Kira Umma ya Fadama ta gasu Imran sun iso,Lokacin su Inteesar basa nan suna Shagon Sallon in da za"ayi musu wankin Kafa da Kwalliya Kunshi sunyi jiya da Safe,achan zasu Shirya ga kawayensu nata zuwa basu Dawo ba..
Sagir Hafsah ya Kira ya Fadamata sun iso tace basa gida ammh gasu nan Zuwa su an gama musu Amaryace kadai ta Rage ana karisa Shiryata,Anty Hauwa ce da kannenta suka yi ta Hidima da su Imran ta Bangaran Abinci da ababen sha,Sai Wurga ido yake yaga ta inda zai Hango Inteesar bai ganta ba Sagir ne ya Fadamai basa Gida ga Inda suke Dakuna Fuska yayi yana Fadin Shirme.
To bama su Dawo ba Khalil ya Kira Waya yace ya Sauka,Sagir yayi yayi ya Tsaya azo a Daukesa yace su bashi address zai hawo Mota haka kuwa akayi Ya Basherr ya bashi Kwatancen Cikin Lokaci sai gashi nan suka Rumgume juna da Imran da Sagir da suka Riga suka Saba ta waya nan da nan Sagir ya gabatar mai da Nasa kayan ya Kwabe Shaddar Jikinsa shima ya Chakare Masha Allah abokan ango suma sun Fito Ras dasu Masha Allah.
Su Inteesar sai wajen uku saura suka Dawo Gidan,Anata jiransu Lokaci ya Tafi suna shigowa Cikin Gida Goggo Maimunatu ta Dauki Gudan ga Amarya nan saboda kyan da Inteeear tayi,Sanye Cikin Wani Ubansu Less cikin na Lefenta ne mai kalan Blue da Golden Dinkin Riga da Zani Ciki da alaku anyi mata Nadin Golden din Head a saman kanta kafarta Cikin Wani Takalmi mai igiya mai Tsini shima Golden haka Karamar pos din Dake hannunta,Tasha Kwalliya Tayi kyau Har tagaji da kyau su Munari kuma suna Sanye da Atamfar yinin Biki ne suma sunyi kyau har sun gaji da kyau.
Maman Nasara ta ta ja Hannun Inteesar din zuwa Dakin Umma,su kuma suka Nufi Falon Baki inda su Sagir suke suna Shigowa Kallo ya Dawo kansu Khalil na gefe ne yana kyalla ido yaga Munari ya Rude baki Bude yace Wow...Shima Sagir Hafsah kadai yake Kallo Domin ta gama Tafiya da Imaninsa.
Imran na gefe Kunya duk ta kamsa yadda Sagir da Khalil ke wani Rawan jiki kan kannen bayansu Hade rai yayi ya kauda kai,gabadaya suka gaida kowa da kowa har da su Ya yusuf Imran dai ta saman Lebensa ya amsa yana dan duba duben ta ina zai ga Inteeesar din..?
Waje Sagir da Khalil suka ja yanmatan suna mgana ganin Tuni mutane sun Fito an Fara Lonching din ba Amarya ba ango Tunda Lonching din Harda Manya su Umma kenan da gayyar Kawayenta.
Maman Nasara ta Fito da Inteeear ta Zaunar da ita inda aka Tanada Domin Amarya da ango guda na tashi da Kida mai Taken Aure ya Dauri sannan su Sagir suka shiga suka Fito da Imran Dakyar kamar Dole alhalin shima yana so ya Fito yaga Inteesar Rashin ganinta fa agaresa kamar Cuta ne.
Wow..Kawai Mutane ke Fadi sai tashin Flash din masu Hotunan da aka Kira Lokacin da Imran ya daidaita Zamansa kusa da Inteesar Khalil ya Harde Hannu a Kirji yana kallon Munari lokaci Daya yana Fadin"Wow...Wow..What a Perfect March...!
Haka yake fadi ita kuma Tana ta Daukansu Hoto Tana Fadin"Kai Ya Imu yayi kyau..Wow..Intee na Besty Wlh They are made for Each Other..!
Khalil kallonta kawai yake yi ammh Beb din ai ta gama Tafiya dashi Kowa Masha Allahu kawai yake Fada Na ganin Tsabar kyau Zati da Haiba Wajen Imran da wani Kwarjini Duk da Fuakarsa bata saki ba ammh yayi kyau matuka Inteesar bata iya Hada ido Dashi ba kanta na kasa tana Wasa da Zobon Dake hannunta na Gwal yana kyalli.
Imran dai yagama Hade Ransa Dole ya Karkace kai yana kallon Inteesar Baisan ya Kafeta da ido ba sai da ta Dagosuka Hada ido gabayansu sai sukaji kamar mayen karfe ya makalesu su Sagir dasu Munari suna ta Ihun Dariya suna Fadin kallon Love an kashe Hotuna cikin wannan yanayin ba adadi kafin Imran ya Fara Farga ya kauda kansa da Sauri yana wani Dakuna Fuska Inteesar ma kanta Ta maida kasa Tana Dariya.
Anci an sha a wannan Wajen anyi Rawa an Taba Bidi"a Umma ma tazo Tajawo Amarya da ango cikin Fili Ta Rika Sakar musu Mannin yan Dubu Dubu ita da Maman Nasara da Goggo Maimunatu da ya"yanta ganin haka yasa su Sa'id ma suka shige suna Rawa suna Manni Har da Ya yusuf da su Munari gabadaya Iyalan Daada ne sun Shige suna rawa suna Liki Imran na Tsaye kikam kamar Gunki ba Domin Umma bace da kanta da sai yace Umma abarma yara mana yana nan Tsaye yana Bin Inteesar da kallo kamar ya Lasheta haka yakeji ga wani Kamshi na tashi ajikinta Inteesar taji gyara soaai Umma ma bata Tsaya kunya ba ta gyara Diyar ta Ciki da baya.
Sagir ne yazo ya Hada hannunsa da nashi ya yafito su Ya yusuf suka zo suna ta Jansa da Rawa Hararansu yake yi ammh basu san yana ma yi ba Hayaniya ya ishi Imran ammh sai Mangariba aka Tashi Daga wannan Taron sai kuma Gobe in an isa Kano.
Gabadayan sun gaji Saboda Zirga Zirga,Ya Basheer gidansa ya kaisu Imran suka kwana Tunda gabadaya Matan suna Gidan Umma saboda Shiryan Shiryan Tafiya da Safe.
Sagir da Khalil dai sai chan dare suka Dawo suna gidan Umma Tare dasu Munari suna kara shirya Dinner Gobe Imran Harara kadai yake maka musu in suka Hada ido su kuma suyi tamai Dariya Allah kadai yaaan me suka Shiryamai gobe.
Garin Allah na Wayewa Daddy yace su Fara Harama Domin su tafi da Wuri,Masu Karatu zan so ku hangomin kukan da Inteesar tasha na Rabuwa da Umma da Daddy tana Sanye Cikin Nadin Lifaya,Gaban Umma Tana ta kuka Umma ma sai Hawaye tana ta sakama Inteesar albarka.
Ta Rumgumeta Tana Fadin"Umma ki yafemin..!
Umma na Sharan kwallah Tace"Na yafemiki Duniya da Lahira..Allah ya Zaunar daku lafiya..!
Dakyar Maman Nasara ta iya Raba Umma da Intee su Munari basasu iya gani ba Tuni suna Haraban gidan Tare dasu Sagir inda suka sanya kayansu Amota ai kuka sai Agaban Daddy ita da Imran ya Hadasu yayi musu nasiha sosai ya Hada hannayensu yace su Zama Bangon junansu Daga Karshe ya Bisu da addu"an Zaman Lafiya yadda Inteesar ta kamkame Daddy tana kuka ko shi Imran din sai da ya Taausayamata ya Rikota acikin Jikinsa yana Lallashinta Daddy kuma baya ya Juya yana Dauke kukansa.
Maman Nasara tazo ta kamata zasu Fara biyawa ta badarawa gidan su Inno Kafin su wuce inda Kawunanta ke chan zasu mata Nasiha.
Ya Yusuf shi zai Dauko Amarya a Motarsa Imran Motar Sadam ya shiga shida Goggo Maimunatu dasu Zainab,Suka Farayin gaba Su Sagir suna Tare da su Munari shi kuma baya son Harka da yara Shiyasa ya kama kansa akwai Motoci Tunda ga na Daddy da na Ya Basheer,sai nasu Goggo Bintalo itama da Mota tazo da Direba ita da ya"yanta Har Gidan Inno da ita aka je bata yarda ba sai taga Komai Saboda taji Dadin Kyankyasama Mami Asma"u gulma.
Achan gidan Inno ma Inteesar tasha kuka su Kawu bala sun mata Nasiha sosai da Inno da Mallam Babba Muda Yana makaranta chan ya koma sun Fara Jarabawa shiyasa bai Taho ba
Basu jima ba achan ba suka Dauko Hanya Maman Nasara na Rike da ita da Anty Hauwa Yusuf na Driving Anty Jamila Diyar Kawu Bala Tana gidan Gaba.
Basu yi gudu Bisa Hanya ba sai 12 suka iso kano tuni su Imran sun Dade da isowa kuma Gidan Sadam din suka yada Zango,Ya Damu yana so yaji ko Inteesar ta iso yana ta Kiran wayarta Bata Dauka ba sai daga baya aka Dauka yaji Muryan Sagir na Fadamai sufa suna Hanya kuma wayar Amarya Tana Wajen su Munari Tsaki yaja ya Datse kiran wai meyasa bata Rike wayanta ne sai ta Rika bama Shashanshan yaran nan Ya ja Tsaki yafi a Kirga kafin ya Kira Ya Yusuf shi yake Fadamai sun iso har su Maman sun zo Taran Amarya zuwa Cikin Gidansu Gida ya Cika Makil suma Haraban Gidan Cike da Mutane an saka Kanofi da kujeru Hajiya Anty Safiya yayar Ango mai Masaukin baki Taci Gayunta kamar Wata Amarya.
Taro Ta Hada itama gagrumi sai wanda ya gani Hajiya Mero da Danginta sun yi kara soaai Mama itace Uwar ango ita da Kaltume Matar Baba Manu,Abba dai Dole ya bar Gidan zuwa Cikin makaranta Saboda Gida ya Cika ba Mtsaka Tsinke..
A Shashen Anty Safiya aka Sauki Amarya Inteesar Wacce ke ta kuka Cikin lifaya Gefe da gefenta Maman Nasara da Antya Uwani matar kawu bala,Anty Hauwa Tuni ta shige Cikin su Aneensa an hadu ana ta Shewa da Hiran yaushe gamo bata ga su Munari ba Tadai san tun a gidan Daddy ta barsu kila suna Hanya gashi ba Waya a Hannunta Ballatana ta Kirasu.
Sai 2pm na Rana suka iso wai Mai ne ya Tsaya musu a Hanya Motar Sa"id suka Shigo matan mazam kuma Motar Basheer Gidansu Imran suka ijiyesu tunda nan ma akwai yinin Biki suka wuce gidan Sadam koda sukaje Tuni su Imran har sun yi Sallah sun Wuta sun ci Abinci suma Sallar sukayi suka ci binci suka Zauna Zaman Hira da Labarin yadda Dinner anjuma Zata kaya.
Imran na gefe yana jinsu to me zai ce..?bai isa yace komai ba yadda Khalil da Sagir suka Hada kai ai sun fi karfinsa sai dai ya Bisu da ido
Gidan su Imran kuwa Biki fa yayi Biki Anty Safiya ta Kira dan Asharalle yazo Yayi kida Mata sun chase Har da ita ga Ciki ga komai ita dasu Anty Hauwa Ko Nauyin Jikinsu basa ji,Harda Inteesar duk sun Fito Haraban gidan suna kallon Rawan manya mata Goggo Mainunatu tayi rawa itama ta Kira Bidi"a Sosai kowa kagani yayi anko Tabbas Anty Safiya ta yi gayyah kuma an Mata kara sosai Tunda Shagali ne Wanda ba"a taba yi ba Duk Tsawon Shekarun da suka Shude Dole abiya bashi.
Chan na hango yan Dandalin GMB2BANDGROUP,Suma sun cakare cikin ankonsu sun sha kyau har sun koshi sai hotuna suke da Amarya Inteesar bakinsu yaki Rufuwa Yau gasu ga inteen Imu duk da basu samu ganin Imun ba sun Rage Zafi.
Sai yammah aka tashi Wannan Rawar Makota da yan"uwa wadanda baazasu kwana ba sukayi Haraman Tafiya masu Shirin Tafiya Dinner kuma suka Fara Shirya Daman already Munari sun Dauko mai Kwalliya wacce Zatayi musu na Tafiya Dinner kawayensu na Buk abokan arziki suma duk zasu je Wajen Dinner maza da mata.
Pass dinka shine Code din Dressing din Dinner din shine pass din Shigarka.
Amarya ko kafin 8:00pm Tayi an gama Shiryata kuma 9pm za"a Fara Dinner din,an Shiryata Cikin Less mai kyau Skya Blue itama an mata Nadin Head Deep blue,sai Daga baya an yafa mata Wani yadi mai Santsi Sya blue yana da Kwalliyan Deep blue na Duwatsu yana Daukan Ido Har kasa yanasharan kasa haka Jakarta ma Deep blue pos sai Takalmin kafarta ma Haka mai Tsini Shima Deep Blue Wata Kwalliya akayi mai mai kyau da Yarari Cikin Lokaci kamar ba ita ba kafin a Fara Shirya Sauran kawaye Tunda Sagir ya kira suma Kadan ya Rage su karisa Shiryawa zasu zo su Dauke su.
Ango Imran yasha Shadda Deep Blue da Babbar Riga da Hulansa Zanna Bukar mai Zanen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login