Showing 123001 words to 126000 words out of 235479 words

Chapter 42 - Gidanmu Book Complete Document hausa Novels by Janafty .txt

Janafty   

14 Jan 2025

16175

ki kulani kuma ki bani amsata Lokacin da nake Bukata..!
Abun nasa ma sai ya bata Yar Dariya Har sai da yajita da Sauri yace"Au dariya ma kike yi ko..? Ashe kina son Duka kenan ko..?
Da Sauri tace"Ban fa da lafiya..!
Tafada Cikin Shagwaba Har sai da yaji Hakan acikin Ransa Mirmishin Saman Lebe yayi kafin yace"Do as i say..!
Yes sir..! Tacemai tana yar Dariya shima Dariyan yaso yi sai dai bai bari taji ba ya Datse wayan ya koma ya Jingina jikin Motar Wani Nishadi na kara Shigarsa baisan Dalili ba In yana mgana da yarinyar yana jinsa kamar bashi ba Ya kasa Fassara hakan sai dai ya barsa ne a karfin jinin yan"uwantaka atare dasu,Shiyasa yanan nan Tsaye yaji Shigowar Sakonta,Da sauri ya Duba.
"Ban je ko"ina ba Ya imu..Ina Daki ina kwance ban lahiya..!
Sai kuma Dayan"Ehyyee..Ya imu ya Damu dani..!
Haka ta Rubutomai Dariya yayi afili ya Furta"Shagwabbiyar yarinya kawai..!
Yafada sanda Sagir ya kariso wajen yana Fadin"Kai kuma kai da Waye kake Dariya kai kadai..?
Dagowa yayi yana kallonsa Lokaci Daya ya maida Wayarsa aljihu yana Fadin"Ina Ruwanka banza Dan saka Ido kawai..!
Sagir yayi dariya daidai Lokacin da Sauran mazan suka Fito Harda su Abba domin zuwa masallaci an Kira Sallah da Sagir yama Imran mgana su Tafi cemai yayi shi Yaron sane da sai ya Tasa agaba...?
Yaje yasan Hanya zai zo Daga baya Sagir bai damu ba ya wuce,haka ma su Yusuf suka Fice abunsu sanin Halinsa kamai gwaninta ya Dizgaka
Ganin su Abba ne yasa ya wuce da Sauri bayaso ya gaida Baffa Kabiru shiyasa yayi saurin wucewa Abba yana kallonsa kuma ya Fahimcesa Sarai Mirmishi kadai yayi suma suka Rufa Musu baya zuwa Masallacin Dake kusa da gidan
Bayan an gama Sallah gabadaya suka Dungumo suka Dawo Gidan Imran ne abaya Shi kadai yaki ma yarda ya Jera da Kowa ko Sagir daya so ya Jirasa Cemai yayi yayi gaba basai ya Jirasa ba.
Bai damu ba ya Taka ya bi su Basheer ya kyaleshi yana Tafiya kamar bazai taka kasa ba.
Gabadayansu afalon suka yada Zango Domin cin Abinci Har da su Abba Daada ma ta Fito nan falon Imran yaso ya gudu ya koma Daki Daada ta Hanashi ta Kirasa tace yazo ya Zauna Kusa da ita bai da yarda zai yi Dole yaje kusa da ita ya Zauna,Yana cim mgani Irin su Mami Asma"u sai cika take tana batsewa,Ya"yanta na Gefenta Sajida da Umai,Sajida sai Satan kallon Imran take yi shi baima san Tanayi ba.
Tuwon Semo ne da Miyar kubewa Danya Dataji Naman Rago da Manshanu,sai Ci suke suna Sakin Santin su Anty Safeya dasu Aneesa suna Gefe suma cin na su suna Hira haka suma Mazajen nasu suna Waje Dayane,Haka ma su Abba suna Zaune dasu Daddy waje daya duka dai duk suna kan Katuwar Dardumam da Baba Asabe ta shimfidamusu ne.
Daada ne ta kalli Umma Dake gefen Inna Maimuna tana Fadin"Salaha ina Maryama..? Banganta ba..!
Tafada tana kallonta kafin Umma tace wani abu da Sauri Munari tace"Tana Daki batajin Dadi Daada..!
Daada ta jinjina kai kafin tace"Ayya..Meke damunta..? Taci abinci?tasha mgani..?
Tayi Tambayar Duka Lokaci Daya,Munari tace"Eh Daada tasha Tea dazu kafin na Fito..!
Daddy ya ijiye Spoon yana Fadin"Tun yaushe ne bata da lafiyar..!
Umma tayi Saurin Taresa Tana Fadin"Yanzu da yamman ne fa Abban Intee..Ni na bata mgani kasanta Raguwa ce gajiyan Hanya ne..,!
Kai ya kada bai ce komai ba Saboda Yasan meyasa Umma ta katsesa.
Khamis kuwa Hankalinsa ya tashi jin Inteesar bata da Lafiya Daman Tunda yazo ita yake songani Cikin nuna Alhini ya kalli Munari yana Fadin"Mai sunan Goggo jikin Inteesar din da Sauki ko..?
Kai ta gyadamai kafin tace"Eh Kamar ta samu barci ne..!
Kai ya jinjina duk ya Damu yama kasa Cigaba da cin Abinci,Mami Asma"u na Lura dashi Ranta ya baci ta kallesa Tana Fadin"Kacigaba da cin Abincika Tuwo ne fa nasan kuma Kan sonsa sosai..!
Dan Mirmishi yayi ya cigaba da cin Abinsa Imran kuma Cokali Daya yayi bai kara ba,wayarsa ya Fiddo ya Turama Inteesar sako.


"Ki fito falo kici Abinci..,!


Ya turamata ya ijiye wayar a gabansa Daada Dake kallonsa Tace"Imrana kaci abincin mana..ko Baka cin Tuwon ne a sama maka wani abu..?
Da sauri ya Girgizamata kai kafin yace"Wannan ma is ok Daada Zan ci.!
Kai ta gyadamai Lokaci Daya Tana kara Nazarinsa Juya Cokalin yake yi Sai ya Dauki Lokaci kafin ya karaci yanayi yana kallon Wayarsa Zuciyarsa ta fara Zafin ganin bai ga sakonta ba,atsawon Mintina Hudu kafin yaji Sakonta ya shigo da Sauri ya Dauka ya Duba.


"Nasha Tea Ya imu..!


Da Sauri ya Rubuta mata Amsa da cewa"No..Do as i say Inteesar!!!..Kinsan bana son gaddama ko..?


Ya turamata kafin ya ijiye wayar Yana Sauke Numfashi.
Daga bangaran Inteeear kuma ganin Sakon Imu yasa Dole ta mike sanin Halinsa kada tayi laifi Dogon Hijabin Hafsah ta saka Ja,mai hannu Dama karamar Rigace ajikinta mai kama da Shimi shiyasa ta saka Dogon Hijabi,Allah yasa Munari ta tasheta Tayi sallar Isha"i ta matsa mata ta sha Tea.
Cikin Tafiyar kasala ta fito daga Cikin Dakin zuwa Falo lokacin data Fito ma Wasu sun gama cin abinci wasu ne basu gama ba Tukunnah,Tana yin sallama acikin Falon idanuwan Khamis ya fada kanta ya wani Kuramata Ido kamar zai lasheta,Imran ma ganinta yasa yaji sanyi shi kallo Daya yayi mata bai kara ba ya waske yaji dadi tanajin mganarsa,Bai ma lura da kallon da Khamis ke Binta dashi ba.
Ta gansa sai dai tayi kamar bata gansa ba ko barayinsa bata kallah ba Wajen su Abba ta nufa ta duka ta gaishesu suka amsa mata suna Tambayanta ya jiki ta amsa musu da sauki,Daddy ya Dafa kanta yana Tambayanta ya jikinta ta amsa mai cikin Shagwaba kamar ta Kwanta ajikinsa sai dai ba Hali tashi tayi ta koma wajensu Umma Tana gaida su goggo Maimunatu,ita kadai ta amsa mata cikin Sakin Fuska banda Goggo Bintalo Sama sama dai bata damu ba ta Lafe jikin Umma,Umma ta Tureta tana Fadin ta dagata Shagwabe afuska Tayi goggo Maimunatu nayi musu Dariya Daga Khamis har Imran kallonsa na kanta shi khamis irin kallon nan ne ma marasa aji yayinda Imran yake kallonta ta kasan Idanuwansa wanda ba wanda zai Fahimci yana kallonta ne.
Tashi tayi ta koma Wajen su Anty Safiya inda suke Hira dasu Munari Kafin taje ta gaida Daada Wanda Imran ke gefenta,Lamgwabe tayi jikin Daada Tana mata Shagwaba Daada na tambayanta jikinta ta amsa tana kallon Imran wamda ya Dauke kansa kamar bai ganta ba.
Daada ta Umarce da akwashe kwanunka da aka gama cin Abinci nan da nan kuwa su Munari suka Mike dasu Anty Safiya suka Tattara komai suka maida Kitchen Munari da Hafsah da Umaima suka Share Wajen suka Goge.
Daada ta Umarce ya"yanta su Matso kusa da"ita Inteesar tatashi ta koma Cikin su Munari yayinda Imran ya koma Chan karshen kusa da Sagir bai da yarda zai yi ya gudu saboda Daada bayaso yayi abunda zai bata mata rai.
Sai da kowa ya natsu kana Daada ta fara da Sallama ta Umarci Sadam daya Bude Taron da addu"a ya Bude aka Shafa Daada ba wani Dogon bayani tayi ba Abba ta bama Daada ya bama Kowa Labarin inda suka Shiga bayan barinsu Lagos.
Abba bai yi Nauyin baki ba ya gyara Zama ya shiga bada Labarin Abunda ya sani na Komawarsu kano daga Bakin ya"yansa dayasha ji da kuma Wanda ya sani ya Karishe da Fadin"Ya"yana sune garkuwata sune Duniyata..Musamman ma Yusuf gashi nan dan albarka ya Dauki Ragama da Nauyin daya kamata ni zan dauka ya kula dani..Ya kula da Kannensa Munari da Imran,ya Dauke komai a Wuyansa Imran ma ba"a barsa abaya ba Yana da kwanjin Kula da Ahalinsa Babu Abunda Zance musu sai Godiya da Fatan Allah ya basu masu Rama musu..!
Yafada cikin sadda kai Lokaci Daya aka amsa da Ameen.
Kafin Abba ya Dago ya cigaba da Fadin"Daada kiyi hakuri ki yafemin keda Sauran yan'uwana..Har ga Allah ba"a san raina Suka yanke wannan Hukuncin ba Lokacin bani da lafiya Sanda na Dawo Cikin hayyacina babu abunda zan iyayi saboda Ina neman Lafiyata ne kafin komai..!
Daada ta jinjina kai Tana Fadin"Bakomi Malami ban taba Rikon ka acikin Raina ba Tsakanina Dakai sai addu"a da Fatan Alheri..Ba kuma Laifinka bane ba kuma Laifin su Imrama bane Laifin Yan"uwanka ne da suka kasa Fahimtarka Musamman ma Kabiru..!
Tafada Tana nuna Baffa Kabiru Wanda ya Dago yana kallonta Hakama Ya"yansa da Matarsa suka Dago suma kallon Daada.
Cikin Muryan Tsufa ta Cigaba da Fadin"Da basu rika ganin Laifinka ba..da duk haka bata faru ba..Da sun jaka ajiki da duk haka bata faru ba..Ammh tunda kaga ka dawo Alhamdulillah kuma sun gane kuskuransu..Yanzu kai kabiru da Mustpaha ku juya ku bama Dan"uwanku Hakuri..!
Abba zai yi mgana Daada ta Hanashi Tana Fadin"Ku bashi Hakuri..nace..!
Daddy ne ya fara mgana inda ya kalli Abba yana bashi Hakuri Abba ya girgiza kai yana Fadin"Bakomai Mustpaha Wlh bantaba Kullatanku ba..!
Baffa Kabiru kamar bazai yi mgana ba Mami Asma"u sai Hararan Daada take yi Sajida ma ranta duk ya baci gani take kamar Daada ta Dizga Dad dinsu gaban Mutane bai isa ya Tsallake Umarnin Daada ba ya juya yana bama Abba Hakuri ya girgizamai kai yana Fadin"Wlh ko daya ban taba Rike hakan Araina ba..!
Daada ta murmusa Tana Fadin"Naji dadin jin haka..Daman fa"idan haka ku hada kanku Waje daya ne..Naji dadi sosai Allah ya kara Hada kanku..yayi muku albarka Gabadayanku ku da Zuru"anku..!
Dukkansu suka amsa da Ameen
Abba ya gyara Zama yana Fadin"Daada ina son na gayamiki wani abu kada ki gani kice ban Fadamiki ba..!
Da mamaki Daada ke fadin"Meya faru Malami..!?
Abba juyawa yayi yana kallon Imran Wanda kamsa ke kasa kamar baya jin Abunda ke Faruwa nan kuwa yana jin komai,Maida kallonsa yayi kan Daada kafin yace"Faruwar abunda ya Faru ya Sauya Imran sosai..har Sigari ma yana sha..Sai dai nasan Tunda komai ya Daidaita zai daina sha da Izinin Lahi..!
Shuru falon yayi Imran kuwa ko Dago kai baima yi ba,Kamar ma bai ji ba Haka ya nuna,Mami Asma"u ta tabe baki tace"Ai wanda ya fara ShayeShaye..Da wahala kaga ya iya barinta..!
Tafada kai Atsaye ba wanda yabi ta kanta Sajida kuwa Gabanta ne ya Fadi Imran ke Shaye shaye..? Gabanta ya kara Faduwa ta fara Wurga idnuwansa nemansa Cikin Falon sai chan ta Hangosa kansa na kasa ta na kara Nazarinsa taga Yayi mata kama da mai Shaye shaye ko A"a..? Sai dai bata ga wata alama ba.
Inteesar kuwa Mami Asma"u ta kallan Tana Mamakinta ita meyasa bata kama Girmanta ne..!
Daada kuwa Mirmishi tayi kafin tace"Ai ya gayamin ma Malami Dazu da safe..!
Gabadaya kowa ya Kalleta Cikin mamaki kai ta gyada tana kallon Imran kafin yace"Eh da kansa ya Fadamin..Halinsa iri dayane da na Mahaifinku Alkali baya karya komai zai Fada iya gaskiyansa kenan..Bakomai Allah yayi mana mganin komai..!
Suka amsa da Ameen Tabe baki Mami Asma"u tayi ba Haka taso ba taso ne Daada tayi fada sosai.ta zageshi sosai ta kuma ji ta tsaneshi sai dai hakan bai samu ba Daada ta nuna ko ajikinta ma.
Imran kuwa yana Duke dan Mirmishi kawai yayi bai ce komai ba acikin Ransa yana auna wasu abubuwa.
Kwatsan yaji Daada tace"bayan haka akwai wani abu da nike son gabatarwa..Wanda na zauna na yanke Hukunci ni kadai da Zuciyata Kuma ba Shawara bace Umarni nake so na baku koda shi kadai ne abu na Karshe da zan gudanar ina da Rayuwa..!
Kowa Hankalinsa ya maida kanta Domin karin bayani.
Daada ta gyara Zama Kafin ta Cigaba da fadin"Mustpha,Malami da kai Kabiru kune Maza manya..Ina son ku Hada Auran Imran Dan wajen Malami Da Sajida yar Wajen Baffa Kabiru Saboda Dalilina na kara Hada kanku ya"yana da Jikokina waje daya..!
Gabadaya Falon sai da kowa yaji mganar Daada kamar Daga sama Baffa Kabiru ya zaro ido yana kallon Daada Abba kuwa Daddy ya juya ya kallah Shima shi yake kallo cike da mamaki.
Zuciyoyi uku kuma sun Buga Lokaci Daya Zuciyar Imran data Sajida sai ta Inteesar wacce ta kwalalo ido Tana kallon Imran wanda ya Dago kansa Cikin mamaki yana kallon Daada yayinda Sajida ta rasa gane yanayinta Farinciki ko bakinciki.
Munari da Hafsah suka kalli juna cikin mamaki haka su Yusuf su kansu mganar tazo musu a bazata.
Inna Maimuna kuwa jinjina abun take ita da Umma suna Hango Tashin Tashina kan wannan mganar.
Mami Asma"u kuwa kamar ma bataji Daidai ba Idanuwanta kan Daada kafin tace"Sajida fa kikace Daada..?
Wata Sajidan..?
Daada kai Tsaye ta kalleta Tana Fadin"Wata Sajida kika sani..? Sajida dai Yar wajenki Asma"u..!
Ai da sauri Mami Asma"u ta Zabura ta Mike Cikin Hargowa take fadin"Na Rantse da Allah Daada bazai sabu ba..Arasa wa za"a bama Dan Shaye Shaye Tsageri fitsararre mara kunya sai Ya"ta..?
Ina wannan mganar bama mai yuyuwa bace Sajida bazata taba auran Dan iska ba wanda baida Sana"a sai Shaye Shaye..!
Tafada Cikin bacin rai Lokaci Daya tana Tada Jijiyan Wuya da nuna Rashin yardanta kan mganar.










*Kuyi Hakuri Don Allah yau nayi Fama Da rashin Chaji ne,Bamu da wuta nakai wayata Chaji ban karbo akan Lokaci ba afuwan..*












*Shakira*
3/22/22, 23:14 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�5*




*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*


Mamakin Mami Asma"u ya kama Ilahiran wadanda ke cikin Falon,Barin ma Abba da Daddy da suka ga yadda Mami Asma"u take nuna Hannu tana so taja da mganar Daada wanda ko su basu isa su ja da Umarninta ba.
Imran manyan Idanuwansa ya Zubamata da suka Fara Chanza Launi Saboda bacin rai bai ce komai ba sai dai ya kara Ware idanuwansa kan Yarinyar da Daada takira da Sajida Duk da bai san ko itace ba a mganar Mami Asma"u ya tabbatar da Zarginsa sai akaci sa"a itama Sajidan shi take kallo da dukkan Tunaninta Shima sai Lokacin yake kare mata kallo Cikin kaskanci da bacin rai Billahil Azim Ko Dauramai wannan yarinyar akayi a Kafarsa sai ya kwance ko mata sun kare a Duniya babu abunda zai yi da ita ballatana Har Uwarta ta Nemi gayamai mganar Banza Daada kamar Tayi kuskure ne Wajen Fadan suna.
Sagir kuwa Tsabar mamaki ya kasa mgana Shi da Yuauf Imran kadai suke kallo suna Fatan kada wani Hargitsi ya Faru a wannan zaman sun sansa sun san Halinsa bayason ka Shiga Harkansa ka batamai rai yanzu zaku samu mtsala.
Khamis kuwa bai ce komai ba Ammh Shi kansa Hadin ai bai yi ba ina Sajida ina wannan Muradadden Mutumin wanda baisan yan"uwansa ba sai dai yana da Tarbiya bai saka baki cikin mganar da ba nasa ba.
Inteesar gabadaya Jikinta taji yana Rawa Zuciyarta na Bugawa Fat!Fat.Kamar wacce tayi Gudun Fanfalaki Kanta ya Fara wani Sarawa da Karfi Har Jikinta na kasa Daukanta Daga inda take Zaune Hannun Munari ta Damke Lokaci Daya tana Runtse Idanuwanta ta sauke kan Imran wanda ya Kauda kansa Daga kallon Sajida yana maidawa wani barayin yana Kokuwa da bacin Ransa ne bayaso Ransa ya baci ya Hargitsa wajen Wanda kuma ya Tabbata bazai ma kowa Dadi ba.
Munari da Hafsah cike da mamaki suke Bin Inteesar da kallo wacce ke Hada Uban gumi duk da Sanyin Fanka da A.c dake cikin Falon ammh bai isheta ba Lokaci daya Jikinta sai karkawa yake yi Har suna jin haka a Hannuwansu data Damke cikin nata.
Cikin Firgicin da suke ciki Munari tace"Intee meya faru..?Ciwon kan ne ya tashi..?
Haka suka Shiga Jera mata Tambaya Ita da Hafsah sai dai ita kanta Baxata iya Fasaara Halin data Shiga ba Tun Lokacin da Taji Daada tana Fadin Umarninta ne Imran ya auri Sajida Taji komai nata ya Tsaya Cak ta kasa gane gaba ballatana baya.
Cikin wannan Halin ne Muryan Inna Maimunatu ya Karade falon Inda ta Mike Cikin bacin rai Tana Fadin"Haba Asma"u ai banzata Tsaurin Idanuwanki yakai Har Daada tayi mgana ko gama Sauke Numfashi batayi ba ki mike kice bazai sabu ba..In kin manta bari na Tuna Miki Daada Uwa take ga Yaya Kabiru kuma Kaka take wajen Sajida kamar yadda kike da Iko da ita muma muna dashi..kuma Dangin Uba sune Kan gaba Wajen zaba ma ya"yansu Mazajen da suka Dace dasu ba ke ba..!
Ta Karishe Fada Cikin bayyana bacin Ranta da yadda Daman take Cike da Mami Asma"u da Raininta.
Mami Asma"u da idanuwanta suka Rufe ta Fara Tafa Hannu Tana Fadin"Eyye Ahhye..Wato saboda ba yarki bace shiyasa kikacewa haka..?in adalci ne meyasa sai yata..! Ba yar Muatpaha ba yar wajenki..Ko ba yar Wajen Binta Dole sai yata.?oh saboda kowannenku anan yasan Zafin nashi kuma Ko Mahaukaci nasan abu mai kyau da Nagarta,Shiyasa ba wacce Zataso a Dauki yarta a Hadata da Mai Shaye Shaye kuma Dan iska..!
Daddy ne yaji abun ya isheshi yana Daga Zaune ya Daka ma Mami Asma"u yana Fadin"Ya isa haka Asma"u..!
Jin haka yasa ta tasomai Tana Fadin"Ba zan yi shrun ba..?Saboda kada na Fadi gaskiya ko..?To wlh ba wanda ya isa ya Dinkemin baki sai nayi mgana In adalci ne ka Dauki Inteesar ka basa mana Sai ka Shiga maganar in kana so na Rufe bakina nasan kuma adalci ne za"ayi anan Wajen ba son kai ba..!
Tafada Tana kallon Daada Datake kallonta batayi mamaki ba Sai dai Tana kara Nazarin Wasu Hallayar Asma"u da ta dade da karantarsu,sai dai bata taba Nuna mata agabanta ba sai yau.
Kowa mamakinta ya cikasa da mamakin yadda take Fadar mgana son Ranta Baffa Kabiru ya kasa Dakatar da ita Daddy ya kallesa Cikin Takaichin ganin yayi Shuru ko Uffan baice ba Ballatana ya Dakatar da ita Cikin bacin rai ya Maida kallonsa kan Mami Asma"u yana Fadin"Wlh Tallahi ba Domin Umarnin Daada bane da yau na Nuna Miki iyakarki Asma"u Da yau na Nuna Miki Da Imran da Inteesar duka Dayane awajena anan Wajen ba sai gobe ba zan Biyamai Sadaki a daura musu aure..sai ki jika Taki yar kisha..Domin ba ita kadai bace ya"a ki duba Fadin Falon nan Cike yake da ya"ya da jikoki Saboda ya"yanki kadai Daada bazata ji Tayi wani Maraicin Rasa Jika ba..!
Yafada cikin Bayyana Bacin Ransa Imran kuwa jin Abunda Daddy yace ne yasa dago kansa ya Kalli Barayin da Inteesar take zaune karaf kuwa suka Hada ido Itama kallonsa take Cikin zuciyarta Tana jin Wani Rauni na shigarta,Hawayenta Datake ta Tarewa suka samu nasaran Zubomata Sharr saman Kuncinta shi kuma Imran sai yaji Ransa na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login