Showing 9001 words to 12000 words out of 46466 words

Chapter 4 - DA WATA A KASA BOOK COMPLETE BY BINTA UMAR ABBALE .txt

yakewa Titi na fitar hankali.














GA DUK MAI BUKATAR KARANTA BOOK D'IN ZAI TURA #300 TA WANNAN ACCONT DIN.....
0542382124.......BINTA UMAR GTBAN.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURO KI SAMENI TA WANNAN NUMBARS........07084653262......ZANYI MIKI BAYANIN YANDA ZAKI TURA




*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA DA BUKATAR LITTAFIN ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE*






*DAN ALLAH IDAN KIN SAN BA SIYAN BOOK DIN NAN ZAKIYI BA KADA KI KIRANI KO KI MIN WATA MAGANA*








*IDAN KINA BUKATAR SHIGA VIP GRUOP KIYI MIN MAGANA DA WANNAN NUMBAR*
WhatsApp
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*DA WATA A 'KASA!!*
Writing By
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~
*🌎Manazarta Writers Asso*
_'Kungiyar Masu Nazari da aiki da Ilimi._
~~~~~~~


*PAID BOOK!*




**Free Pege6*
Ganin yanda yake hak'arta yana bugunta da wani mugun 'karfi! ya sanya ta sare da al'marin sai ta soma kokirin kwatar kanta ihu!! takeyi azabah ta isheta, ya d'amke mata bakinta da tafin hannunsa guda daya yabi ya ma'kal'kaleta a jikin kujerar yana gurnani had'e da zufa sai sukuwa yake kan yarinyar mutane! Titi taga jaraba da masifa kuka takeyi wiwi tana bashi hakuri da fad'in kada ya yaga ta tsananin azabar da ta takeji a gurin ta sanya ma'kogwaronta bushewa, Hafeez kam! baya ji baya gani ya zama mayan 'karfe a jikin ta, kuka yakeyi yana fad'in "Dady ka cuceni ashe haka wannan al'amari yake da dad'i! Inaaa! sam! wallahi bazai yiwu ba kai kullum kana kwasar dad'i ni ka hanani.'! Sambatun surutan da yake yi kenan yana sake zurkudawa Titi jijiyarsa wacce takejin ta har cikin cikinta.


Sakatare ne tsaye a bakin kofar ofis din yana dan dubbugawa da Fadin " Sir ba'kin nan fa sun zo suna jiran su shigo ku tattauna." Shuru yaji yaja kofar yaji a kulle, sai ya koma ya zauna gurin zamanshi yana d'an kallon ba'kin dake zaune kan kujera, yace."Dan Allah kuyi hakuri mybe yana wani uziri ne ko yana toilet amma bari na sake kiran wayarshi." Daya daga cikinsu yace."Wai shin baka fad'a masa zuwan mu bane? duba fa munfi karfin awa guda zaune a gurin nan muna zaman jiransa, shiyasa kwata kwata bana so hurd'a ta had'ani da yaron sam bai iya mu'amulah ba."
Sakatare yace.",Afuwa Alhaji wallahi na fada masa ina tunanin dai ko bacci yake yi."
Daya mutumin yaja siririn tsaki yana fad'in" Okey bacci yazo yi kenan ba aiki ba, babu shakka watarana yaron nan zai rusa muku company mutukar yallabai zai dinga d'orashi kan harkokinsa." Sakatare dai shiru yayi yana cigaba da trying d'in numbar Hafeez d'in gashi tana shiga amma ya'ki d'agawa! Ya d'an dago kansa yana kallonsu jikinsa yayi sanyi saboda yasan sunji wayar na shiga amma ba'a dauka ba.
Alhaji Manu ya mi'ke tsaye ransa a 'bace! ya mi'kawa na kusa dashi hannu yace."Ni ina da abinyi alhaji yaron nan wulakanci yaso yayi mana dama ya an gama magana komai nasa hannu na biya kudi kuma azo a 'bata min rai! a ba kyauta nace a bani ba, saboda haka ni zan tafi harkokina dik sanda yaga dama ya bude ofis din shi ya sani." Alhaji Dantani ya mike shima yana bige babbar rigarsa yace."Nima harkokina na bari nazo domin cika alkawari saboda haka yanzu zan kira Yallabai din shaida masa abinda ke faruwa."
Sakatare yace." Kuyi hakuri mana ku dan jira Alhaji." Suka watsa masa wani kallo suka fita daga gurin ransu a mugun 'bace!
Sakatare ya koma ya zauna shima nasa ran a 'bace! Lallai babu shakka Hafeez idan haka yace zai dinga yi to kaf sai ya kori costumes dinsu dake rububin zuwa daukar kaya, shin wai me ma yake yi ne a ofis d'in.? Can ya tuno Ai Titi ta shiga ofis din tunda ta shiga kai masa Cofee bata fito ba, yayi jim yana tunani babu shakka biri yayi kama da mutum to amma ai yana zaune a gurin zaiga da idon da Titi zata kalleshi.


Professor Hankalinsa yayi masifar tashi da jin bayanin da Alhaji Dantani yayi masa, a hanzarce ya shiga kiran numbar Hafeez sai dai ya kira sau kusan goma bai daga ba, ya sauko 'kasa inda Mommy ke zaune ita da Farhana ya shiga sirfa bala'i ta inda yake shiga batanan yake fita ba, yana fad'a mata irin aika aikar da Hafeez din yaje yayi masa a Company. Mommy hankalinta ya tashi itama ta shiga kiran wayarsa sau ba'adadi bai daga ba. Professor yace."Kinga ni ko? kinga abinda nake fad'a miki ko? Hafeez ni zai kassara ya rusa min harkokina, kamar gaske ya shirya yace in zauna a gida zai kula min da harkokina ashe karya yakeyi muhiman mutane zasu zo a gana dasu ya yayi musu wulakanci yana cin ofis ya'ki sauransu, ai dama na fad'a miki yaron ba zai ta'ba hankali ba."! Murya na rawa Mommy tace."Yallabai kayi hakuri dan Allah ka kwantar da hankalinka kabi komai a tsanake mybe akwai wani abu da yake faruwa, ni nafi zargin ko ciwonsa ne ya dawo ya sanya bai sauraresu kaga ma ko waya ya kasa dauka dan Allah ka kwantar da hankalinka." Ai sai ya shiga bambami! yana fad'in" Ai dama tuntuni nasani duk wani abu da Hafeez keyi kece kike zugashi da har zakice na kwantar da hankalina kwata kwata yaron nan be da gaskiya, aure yake so nayi mishi billahillazi banza masa aure yanzu ba dan baiyi hankalin da zai iya jagoranta wani ba, ni ban haifi d'an da zai sauya min a'kidata ba." Mommy ta soma kuka tana fad'in "Ya zaka ce nice nake sanya shi yayi abinda ya ga dama, nice fa na haifeshi zanfi kowa son ya shiryu, kada kayi masa baki kai mahaifinsa, ne kuma ni banga laifinsa ba dan ya bukaci aure tunda ya kai munzali."
Tace."To ke dashi sai ku tursasani nayi abinda kuke so zan gani ni ko ku."!!!! Yana gama maganarsa ya haura sama a mugun fusace! Murya na rawa Farhana tace"Mommy dan Allah ki daina hawaye idan da sabo kin saba da wannan hayaniyar ta Daddy shi komai a laifi yake ni wallahi bana so naga yana miki masifa." Mommy ta girgiza kanta tana share fuska tace"Farhana Daddynku yayi lafiya ai da yafi zafi Kinsan duk mai suna Ali yana da zafi da a'kida." Kafin Farhana tace komai ya sauka, cikin shirin fita, yasha farin gilashi, ko kallonsu baiyi ba ya kama hanya zai fita, Farhana tace"Daddy a dawo lafiya." Ko kallonta baiyi ba ya fita daga palon.




Hafeez bai san iyaya a dadin kawowar da yayi a kan Titi ba sosai ya suburbudeta tamkar ba budurwa, sai da ya tabbatar da tayi gamsuwar da yake bukata sannan ya sauka daga kanta, Ita dashi duk sunyi wujiga wujiga, Titi fuskarta duk jirwayen hawaye kwarmin idanunta ya zurma sai kuka takeyi gabanta duk ya tsage! wannan wace irin masifa ce yau ta afka, da kyar ta jawo rigarta ta fara kokarin sakawa, Ya dinga kallonta yana tausaya mata shi kansa yasan ya azabtar da ita sai shima bada son ransa bane! Rigar ya kar'ba ya zura mata yana goge mata hawaye, miryarta na rawa tace"Sir zaka aureni."? Ya dago kansa da sauri yana kallonta, "Zaka aureni."? Ya sake maimaita tambayarta, shuru yay mata yana d'an tsuke 'karamin bakinsa, bashi da tacewa wai 'barawo a hannu mata, Tace" Nasan ba zaka aminci ka aureni ba, yanzu shikkenan na rasa abu mai mahimanci a rayuwata."! Sai kawai ta fashe da kuka." Yaji tausayinta sosai ya dan rungumeta a jikinsa, "Stop Crying bab, ki daina kuka kinji ko! nasan kinyi min adalaci a rayuwa kin farfad'o dani daga fad'awa wani 'kangi kuma nasan wannan abun naki da kika mallaka min mai daraja ne da girma, nayi miki alkawarin daukar dukkanin laluranki zan baki kudi sosai zan sauya miki mota duk abinda kike bukata ki tambayeni zanyi miki mutukar kudi na magani."
Girgiza kanta ta shigayi tana goge fuskarta tace"Ni daina nafi so ka aureni." Yaji wani fad'uwar gaba sam! baya so tana wannan furucin D'an had'e rai yayi yace."Baby kin manta addinina da naki ya bambanta bana jin zan iya auranki."! Tace."In dai zaka amince ni zan muslunta saboda kai ina sonka sosai shiyasa ma na mallaka maka jikina." Jim! yay yana nazari yace."okey zanyi tunani kada ki damu, sannan ka bana so kowa yasan mu'amular dake tsakaninmu." Titi tayi murmushi tana jin sanyi a ranta ta amince mutukar zai aureta zata musulunta koda kuwa kaf danginta zasu gujeta.....Tace"Yanzu zanje gida in huta in gasa jikina ne." Mikewa yayi yana fad'in "Bari nayi wanka na fito ko." Ta daga masa kai, tana kallonsa ya shiga toilet a gurguje yay wanka ya fito ya goge jikinsa ya mai da kayansa,
Lokacin itama ta dan 'kokarta ta kimtsa jikinta, ya bud'e 'kofar ofis d'in suka fito a tare, wanda yay dai-dai da shigowar Professor gurin.........Kafatanin ma'aikatan dake gurin suka mi'ke suna masa barka da zuwa, hankalinsu duk ya dauke a kansa, hakan ya bawa Titi damar silalewa ta fice da saurin gaske! dama tana ta tunanin ya za'ayi ta fito su ganta, Professor hankalinsa na ofis dinshi bai wani tsaya sauraran su ba, ya nufi ofis d'in Hafeez ya bishi da kallo cikin tsananin rud'u da tashin hankali, a duk sa'ilin da yaga irin wannan fuskar daga gurin mahaifinshi to babu shakka yana cikin tsananin 'bacin rai! Bayansa yabi da sauri! sai suka buga karo, Yace."Daddy da kan........! Kafin ya 'karasa ya wanke shi sa lafiyayyan mari! Allah yasa ba'a gaban jama'a bane cikin ofis din ne.
Yana huci! yace."Kayi dai-dai! nace abinda kayi yayi kyau! kuma yayi dai-dai! ashe kai munafiki ne Hafeez."!? Yakarashe maganar yana nunashi da yatsa.
Hafeez ya sunkuyar da kansa 'kasa, yana tunanin abinda ya janyo wannan tashin hankalin! da sauri ya d'ago kansa yana kallon mahaifin nasa dan ya tuno komai, saurin mayar da kansa kas yayi ganin yana idanun Mahaifin nasa sukayi jajawur jijiyar kansa tayi rad'a!-rad'a! Professor Ali mugun masifaffan mutum ne.!!!! A hankali yace."Daddy kayi min afuwa dan Allah wallahi tunda na shigo ofis din nan jikina ya sake rikicewa kwanciya nayi bayan na d'an sha magani bacci me nauyi ya daukeni ,sai yanzu na farka naga miss call dinka."
Ya nuna shi da yatsa yana fad'in" Bana son rainin hankali Hafeez ni bazan dauki wannan shashancin naka ba wallahi! wato dama bacci kazo kayi min a ofis ba aiki ba? kamar gaske ka dakatar dani da zuwa kace zaka tsaya min kan al'amura sai kazo ka kwanta bacci!? Kullum idan na kiraka, mara hankali da iya mu'amula ka nuna 'bacin ranka, kana shigowa ofis din nan Sakatare ya shaida maka abinda keda akwai, mutanan nan da mutukar mahimanci a garemu kuma tsofaffin abokan cinikayyarmu ne, manyan mutane kaiwa irin wannan wulakancin ka ajiyesu ayi ta kiran wayarka ka'ki d'agawa."!!


"Daddy bani da kuzarin d'auka waya a lokacin ni bacci ma fa nake ka dubi yanayi na da kyau ban jima da tashi ba wallahi." Professor yaja wani matsiyacin tsaki ya juya ya nufi kujerar zamanshi wayarsa ya dauko ya shiga laluben numbobin su Alhaji Dantani.....Hafeez ya dan ta'be tsukakken bakinsa a sace ya kalleshi ya d'aga kafad'arsa ya juya ya fita daga ofis d'in, yana fita yaci mur! ya daure fuskarsa sosai Sakatare nata so yayi masa magana yaga babu fuska, sai yaja bakinsa yay shuru yana fadin "A sauka lafiya." Hannu kawai ya daga masa wuce.






*****
Washe gari Asiya ta tashi da wani irin ciwon kai mai tsanani hakan bai hanata yin duk wani aikace aikacen da takeyi a gidan ba sai da ta gama ayyukanta tukkuna Gaje ta mi'ko mata wani karamin kofi da ruwan kunu a ciki tsalala! babu sugar.
Asiya ta kafa kai kur'ba uku tayi masa ta shanye tasa hannu ta katse ragowar ta sud'e, taje ta d'auraye kofin ta kife a kwando, da sauri ta dauki tulu ta nufi rafi domin jidon ruwa.
Sai da ta cika ko ina na gidan da ruwa kana ta ajiye tulun ta zuba ruwa zatayi wanka Gaje ta fito daga daki tana harararta tace"Kina dai da sabulu ko."? Cikin tausayawa kanta tace"Bani dashi." Gaje tace"To sai kiyi da ruwa, dan baxan baki sabulana ba ki 'karar mun dashi gurun gurzar wannan annakiyar daudar ta jikinki." Asiya ta dauki karamin bokiti da ruwa ta shiga bandakin ta wawwatsa a jikinta ta fito tana wani mai'ko kaf daudar dake jikinta ta tashi a sakamakon zubawa jikinta ruwa da tayi, ita kanta tasan tana wari! haka dai ta shiga dakinta ta kwance 'kullin kayanta ta d'auki wani kod'addan lesi wanda take kwalliyar juma'a dashi tana shirin sakawa a jikinta, lalurarta ta tashi, zama tayi ta bude kafafunta ta shiga kartar gabanta da hannu bibbiyu tana lumshe idonta, sai da ta sosa iya son ranta sannan ta hakura aikuwa fatar gurin ta d'auka d'au! ta dinga yi mata zafi da rad'adi! Kuka tasa tana wage kafarta ta kasa saka wando saboda axaba. Mai shaniya ya shigo gidan cike da farin ciki yana fad'in "Gaje kina ina ne? ina Asiya maza ga Alhaji mijinta yazo su gana."
Gaje ta fito daga daki tana fadin "Ganinan malam to lale maraba sannunsa da zuwa aikuwa anci sa'a yanzu naga tayi wanka bari na shiga na fada mata ta fito."
Gaje ta nufi dakin Asiya tana fadin"Alhaji Bawa attajirin gari ai mu kakarmu ta yanke sa'ka." Tana d'aga buhun d'akin taga Asiya zaune dirshan babu kaya a jikinta ta bud'e kafafunsa tana kuka.
Gaje ta rafka salati! wanda ya dawo da Asiyar hankalinta a gigice! ta zabura ta mi'ke tana neman zani ta rufe jikinta, Mai shaniya ya shiga dakin da sauri yana fad'in "Lafiya menene."? Gaje tace" Mallam ni naga abinda nagani! O! duniya ina zaki damu? yarinyar nan da kanta take biyawa kanta bu'kata shigowa nayi naga ta bud'e kafafunta tana 'kwa'kular gabanta wannan wace irin jaraba ce."!
Tana kuka wiwi! tace"A'a Baba ba haka bane wallahi gurin ne keyi min zafi shine na bude domin yasha isk......Kafin ta karasa Mai shaniya ya buge mata baki, yana fadin"Karya zatayi miki? ai ni duk abinda akace kinyi bazan musa ba, tunda aure kike so ai shi zanyi miki kada ki jawo min abun kunya."
Gaje tace"Shine yafi alkairi a gareta." Yace"Dan ubanki yi maza ki saka kaya Alhaji Bawa na zaure yana jiranki." Da sauri tasa kayanta tana hawaye, suka fita daga dakin Gaje na fadin "Ai halin uwarta ta tsotsa haka Mariya ma tayi tashen jaraba a gidan nan." Mai shaniya dai waje yayi yaje yana d'ebewa Alhaji Bawa Kewa kafin Asiyan ta fito.






Pls kuyi Sharing👏🏻






*GA MASU BUKATAR BOOK DIN ZASU TURA #300 TA WANNAN ACCOUNT DIN......0542382124........BINTA UMAR GTBANK.........A TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBAR....07084653262.....IDAN KATIN WAYA ZAKI TURA TO KIYI MIN MAGANA TA WSP DA WANNAN NUMBAR....07084653262 ZANYI MIKI BAYANIN YANDA ZAKI BIYA.*




*MUTANAN MU NA NIJAR IDAN KUNA DA BUKATAR KARANTA BOOK DIN TO ZAKU TURA DALA DARI TA WANNAN NUMBARS.........90899076_88137740 KATIN AIRTAL KO ORANGE*






*IDAN KIN SAN BA SIYAN BOOK DIN NAN ZAKIYI BA KADA KI DAUKI NUMBARTA KIYI MIN WATA MAGANA*






*GA MAI BUKATAR SHIGA VIP GRUOP SAI YAYI MIN MAGANA TA WSP DA WANNAN NUMBAR*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*DA WATA A 'KASA!!*
Writing By
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~
*🌎Manazarta Writers Asso*
_'Kungiyar Masu Nazari da aiki da Ilimi._
~~~~~~~


*PAID BOOK!*


*Free Pege7*
Jikinta a sanyaye ta fito tana 'boye hannayenta cikin wani mayafi data yafe tattararre sai kace abun tatar koko dik ya lalace ya yamutse wasu guraran na jikinsa ma ya yage, Gaje ta bita da wani irin kallo tana murmushi Allah Allah takeyi ayi auran nan tasan matan Alhaji Bawa basu da Imani ga manyan 'yayansa maza duk marasa kunya ne tasan tilas tasha wuya dasu, a hankali take tafiya har ta isa soron kanta a 'kasa, Mai shaniya na ganinta ya washe baki yana fad'in Alaji ai gatanan ta fito." Alaji Bawa ya wani 'kure ta da ido yana washe shegun hakoransa wando suka rine, yace."To to! ai sai ka bamu guri ko." Mai shaniya yayi saurin ficewa daga gidan yana fad'in "Alaji a sauka lafiya." Alaji Bawa bai samu damar amsa masa ba kaf hankalinsa na kan Asiya dake tsaye kanta a 'kasa.
Ya matso kusa da ita a hankali yana dariya wacce tayi masifar 'kara masa muni yace."Asiya 'yan matana ina fatan kinji abinda ke faruwa tsakanina dake ko? yau kwanaki biyu kenan mahaifinki ya kar'bi sadakin auranki a hannuna yanzu ke a matsayin matata kike sosai naji dad'in wannan al'amari dama na dade ina sonki dan duk wasu alamu na nuna kuma na tabbata kema kin fahimta." Yakarasa maganarshi yana sake nani'karta, da sauri ta matsa gefe guda tana 'bata rai! Yace."Tauraruwar zuciyata banji kince komai kiyi magana kinji ko ina so naji ta bankin ki." Ta dago kanta a fusace! tana watsa masa manyan fararan idonta tace"Ni bana sonka."! Alaji bawa yayi wani murmushi na takaici yace."Asiya yanzu ai duk maganar so ta kare tunda na bada sadaki saura kwana uku daurin aure ki soni ko kada ki soni be dameni ba, nan gaba kadan nasan zaki soni ki saki jikinki dani na nuna miki zahirin kauna."
Kallonsa takeyi tana jin zuciyarta kamar ta fashe! ba ita ba ma tana jin ya haifi babarta 'karewa ma tsofai tsofai dashi yazo yana maganar yara ko kunya baiji ba, dik wani girma da mutuncinsa ya zube a idonta wani irin mugun haushinsa takeji, Tace."Yanzu bakaji kunya ba zaka ce zaka aureni nifa a matsayin jika nake gurinka."
Alaji bawa ya shafa gemunsa wanda ke cike da furfura yace"Yaro dai yaro ne Asiya wanene ya fad'a miki ana jin kunya gurin neman aure? ni banji wani kunya ba tunda sinnar ma'aiki nake so na raya, na kuma taimakeki a lokacin da kowa ke gudunki." Tace"Alaji kada kasa na zageka wallahi na tsaneka me zanyi da kai! bana son taimakon ni da na aureka gwara nayi ta zama babu aure kuma wallahi ka sake ka aureni nice ajalinka." Alaji Bawa ya bude bakinsa yana kallonta cike da mamaki yace."Lallai Asiya kuruciya na damunki, ban dauka za'a samu matsala da ta bangaranki ba, to ki bude kunnanki da kyau kiji ni Alaji Bawa sai na aureki wallahi koda kuwa zaki zama ajalina."
Asiya ta fashe da kuka tana ji kamar taje ta sha'ke masa wuya Alaji Bawa maye ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login