Showing 42001 words to 45000 words out of 46466 words

Chapter 15 - DA WATA A KASA BOOK COMPLETE BY BINTA UMAR ABBALE .txt

Writing By
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
~~~~~~~
*🌎Manazarta Writers Asso*
_'Kungiyar Masu Nazari da aiki da Ilimi._
~~~~~~~


*YA SHAFI👏🏻*
*YA KAFI👏🏻*
*YA MU'AFI👏🏻*






*Last Free Pege19_20*
Mommy tace"Asiya abinda Taburni take fad'a gaskiya ne dama abinda kika aikata kenan a garinku kika gudo."Asiya ta shiga girgiza kanta hawaye na zuba a fuskarta ta zube kasan kafet tana cigaba da girgiza kanta hade da wanin irin kuka me ban tausayi. Taburni tace"Haba hajiya ai mara gaskiya ko a ruwa gumi yake yi baki ga yanda ta razana na lokacin da ta ganni wallahi dik abinda na fada dangane da ita gaskiya ne." Jiki a sanyaye Mommy ta nemi guri ta zauna tana kallon Asiyan da mamakin abinda ta aikata. Prof ne ya sakko daga sama yaga Asiya durkushe tana kuka su kuma sun zuba mata ido. Cikin 'bacin rai yace."Me yake faruwa ne? naga Asiyatu na kuka kuna kallonta." Mommy ta kalleshi a nutse tace"Yallabai zo ka zauna kaji aikin da Asiya tayi a garinsu ashe 'kauyan su Taburni take." Prof ya zauna kusa da ita yana kallon Taburni fuskarsa babu yabo babu fallasa shi sam baya son gutsiri tsoma irin na mutane, Yace."Taburni kin san wannan yarinyar ashe, masha Allah dama haka muke so muga wanda yake da ala'ka da ita."Prof ya warware wa Taburni yanda akayi suka tsinci Asiya da yanda suka dinga fama da ita ta sanar dasu daga wane gari take ta'ki. Taburni tace"Alhaji Wannan yarinyar ai ba zata so ta koma cikin garin Fanisau ba saboda tasan mummunan aikin data tafka a garin, kisan kai ne kawai yarinyar nan ba tayi ba amma tayi sanadiyar shiriricewar Alaji Bawa mutumin da ya rufa mata asiri ya aureta a lokacin da kowa ya guje ta.'' Nan Taburni ta warware wa Prof zare da abawa abunda ya faru wanda ya saka Asiyan guduwa domin ta tsira da ranta.
Prof shima abin ya daure masa kai sosai ya jima yana kallon Asiyan kafin ya girgiza kansa ya kalli Taburni a nutse yace."Yanzu ya jikin mutumin da wannan al'amarin ya faru dashi." (Yana nufin Alaji Bawa) Taburni tace" To jiki dai za'a ce da sau'ki Alhaji amma al'amarin na Alaji Bawa kullum 'kara gaba yake yi." Prof Yace."Allah ya bashi lafiya, yanzu tunda mun san inda Asiya take da iyayenta insha Allah zamu shirya zuwa garin tare da ita domin mu sadata da iyayenta da shi mijin nata ta nemi afuwarsu gabakid'aya amma ha'kik'anin gaskiya abinda tayi ba dai-dai bane, sha'anin 'kuruciya ne kawai Allah ya kyauta." Suka amsa da ameen." Asiya da rarrafe tazo ta ri'ke kafafun Prof tana kuka take fad'in Daddy kayi mun rai dan girman Allah kada kace zaka mai dani garinmu wallahi kasheni zasuyi ni bana son Alaji Bawa ni ba mijina bane, Daddy idan kuka mai dani garinmu karatuna fa? kada ka manta kaifa kayi mun al'kawari cewar zaka zama uwa da ubana daddy ka cika al'kawarin daka dauka ni bani da iyaye sai ku."
Prof ya dinga kallonta cike da tausayi yace."Asiya dole ne muje dake garinku mahaifinki shike da iko dake bayan shi ga nauyi aure a kanki tilas muje mu zauna dasu domin mu san abinyi."
Taburni tace"Ai tuntuni ya saketa saki uku." Prof yace."Subahannalahi." Taburni ta cigaba da cewa "Yana fitowa daga asibiti yaje har 'kofar gidan maishanu yay sallama dashi ya mika masa takardar sakinta." Prof yace."To alhmdullhi naji dadi faruwar wannan al'amari yanzu zamuje ta nemi gafarar mahaifinta bisa bujirewa umarninsa da tayi, sannan kuma da kaina zan kaita fadar maigari na sanya a kira shi tsohon mijin nata tabashi hakuri kan abinda ta aikata masa." Taburni tace"To hakan yayi Alhaji Allah ya kiyaye gaba." Asiya gefe ta koma tana goge fuskarta, wani irin haushin Taburni take ji, Cikin 'bacin rai! Mommy ta shiga yi wa Asiya fad'a kan abinda ta aikata Asiya na kuka tace"Mommy bana sonsa ne shiyasa naji ba zan iya amince masa ba, dan a lokacin ma ji nake kamar na caka masa wu'ka! na kasheshi na huta." Prof yace."Subahannallahi! Ya kalli Mommy yana 'kokarin mi'kewa yace."Maganar nan ta isa haka tunda dai anyi abun ya wuce sai a bari! 'kuruciya ce kawai ta d'ebeta a lokacin, dama kuma irin wannan abun ake gudu ga auran dole ga wad'anda basa so, naji dad'i da al'amarin ya tsaya iya haka bata aikata abinda take fad'a ba yanzu." Jiki a sanyaye tace."Shikkenan Allah ya kyauta ya kiyaye gaba." Ya kalli Taburni yace."Ranar asabar zamuje can garin naku sai kiyi mana jagora." Taburni tace"To Alhaji dama ranar zan koma gida sai mu tafi tare daku." Bece komai ba ya fita daga palon.....Mommy ta mi'kawa Taburni kaya cikin manya manyan ledoji guda biyu tace"Kije da wannan insha Allah ranar Asabar idan kinzo zaki tarar da wasu na had'a miki." Taburni ta dinga godiya kamar zatayi sujjada Ladidi yayarta na taya ta......Sallama sukayi wa Mommy suka mi'ke tare Da yake dama Ladadi ba a gidan take kwana ba tana da karamin gidanta da Prof ke biya mata kudin haya can tsallaken layinsu idan tazo tun misalin shida da rabi na safe bata tafiya sai ta gama komai da duk abunda suke bukata.


*****
Madam Semi zuwanta biyu asibiti tana duba Baba Tinde, sosai ta tausaya masa kuma ta shiga data sanin taimakon Asiyan da tayi ganin tana nema ta jawo mata masifa, kuka ta dinga yi tana bashi hakuri Baba Tinde kuwa jinta kawai yake yana kallonta yana so kawai ya samu sau'ki ya kame 'yar iska yasa ayi ta azabtar da ita har sai ta fada masa ina ta 'boye yarinyar dan duk bai yarda da irin maganganun da take masa na cewar bata da ala'ka da Asiyan bayan kuma had'uwarsu ta farko ta tabbatar masa da cewar 'yarta ce, yana ganin cikin maganarta babu shakka akwai lauje cikin nad'i yana ganin ta shirya wannan makircin ne duk domin taci kud'insa.


*****
Hafeez kam duk sanda zai tuna al'amarin dariya yake yi sosai dan sai da ya kasa 'boye maganar ya fadawa su Huzaifa labarin Asiya da yanda suka tsinceta da kuma abinda ta aikata a garinsu wanda ya zama silar guduwarta, To suma mamaki! sukayi sosai da sosai lokaci guda sukaji suna sha'awar ganin yarinyar ido da ido saboda yanda al'amarin ya girgiza su, Hafeez yace kuma kada ku dauka babba ce Farhana ma ta girmeta sai tafi Farhana girman jiki, duka bata fi 15yeras ba, amma wai itake aikata wannan aikin." Yana dariya yake maganar.Ishak Yace."Babu shakka yarinyar nan 'yar daba ce ko a can 'kyauyen nasu ma, amma nan idan tace zata aikata wannan iskancin ubanta za'aci wallahi! Ni sai naji ma ina sha'awarta wallahi so nake inga zata iya aikata wannan d'anyan aikin akaina, wallahi sai naci ubanta sai na yagalgala ta na cinyeta tsaf! sai na d'aukarwa mutumin da tayi wa wannan iskancin fansa.
Huzaifa yace."Kai! ni kuma wallahi tsoranta nakeji haka kawai ina d'an jin d'adina ta kassarani, duk hukuncin da zanyi mata bazan huce ba kaima kayi taka tsantsan."
Cikin rashin damuwa da kulawa Hafeez yace." Guy kana da damar da zaka nuna mata kai d'in namiji ne dan wallahi nima taba ni haushi sosai tsanar da nake mata ta sake ninnkuwa saboda martabarmu data ta'ba.
Ishak yace."Kaine ai zaka had'ani da ita xanje da sigar ina sonta da aure daga nan na shigar da kaina sosai sannan naci ubanta sai na 'kwa'kuleta wallahi kuma na d'aure mata baki! mu har a gaya mana duniya."
Hafeez yace."sai an kwana biyu zamu tsara yanda za'ayi." Da wannan shawarar suka rufe maganar da sukeyi suka shiga wata.


Asiya komai takeyi cikin rashin jin dadi takeyin sa duk lokacin data tuna zasuje gida sai gabanta ya fad'i dan har 'buya take taci kukanta ta 'koshi! Mommy da Farhana ma sun fahimci sauyawarta, Prof da yaga tana salo salo ya shiga rarrashinta da fad'in Idan sunje zai nemi alfarma gurun babanta kan ya barta a hannunsa har ta kammala makaranta, wannan maganar ce ta sanya ta sakin jikinta ta shiga walwala da mutane.


****


Ranar Asabar ranar Tafiya babu yanda Prof beyi da Hafeez ba kan ya shirya aje dashi ya 'ke'kashe ido yace ba zai je ba, haka Prof ya hakura ya kyaleshi suka tafi suka bar masa gidan shi kad'ai! Damar da ya samu kenan ya kira Titi a waya yace tazo gida ta sameshi, dan ko ofis beje ba so yake yau ya ra'kashe sosai tunda masu takura masa basa gidan, dama baya son yana neman Titi a ofis saboda rashin sakewa da kuma saka idon mutane....Titi tazo gidan suka haye benansa suka bud'e shafin iskanci kala kala, Yanda suke mu'amula da juna ke kyace masu aure ne.




Tunda suka shiga garin Fanisau! Asiya take kuka a mota, sam bata kaunar ta sake yin tozali da wad'annan mutane guda uku Alaji Bawa Gaje da kuma Dalladi, har ta k'are rayuwarta ta duniya ba zata ta'ba mantawa dasu ba.


Kai tsaye fadar maigari suka nufa Taburni ce keta nunawa Dalha hanya har suka isa fadar, Dalha ya samu wani fili yayi parking din motar, Maigari da mu'karrabansa na can bakin wata 'katuwar bishiya a zazzaune kan tabarma suka ga katuwar mota mai kyau da daukar ido tayi parking, ai sai maigari ya soma washe baki yana adduar Allah yasa wani mai kudin ne ya shigo siyan gonaki da filaye yasan dole ya samu kudi masu yawa.....Prof ne ya soma fitowa sannan suka fito gabakid'ayansu, Asiya sai 'buya take bayan Prof jikinta na rawa. Kai tsaye fadar maigari suka nufa.


Maigari Halilu na ganin Professor na tunkaro in da suke sai kawai ya mike tsaye yana gyara babbar rigarsa sai dashare bakinsa yake, jama'ar fadar suka bishi da kallo cike da mamaki! sun rasa me yasa maigarin garin nasu yake haka duk sanda yaga 'bako ya shigo garin ya fahimci mai kud'i ne sai ya watsar da mulkin nasa a maimakon ya zauna a hakimce a kan kujerarsa azo a gaisheshi tunda garinsa aka zo A'a shine yake mi'kewa da gaggawa yana mi'ka gaisuwarsa, maigari Halilu baya nuna mulkinsa a ko'ina sai a iyakacin cikin garinsa.


"Alhaji sannunku da zuwa sannu sannu ai tun daga nesa na hango zuwanku nasan babu shakka muhummin a'lamari ne ke tafe daku."
maigari ne yake wannan maganar yana ta faman gyara babbar rigarsa.
Prof ya mika masa hannu suka gaisa yana fadin"Kwarai kuwa muhimin abu ne ke tafe damu shiyasa ma kai tsaye nace mu nufo fada dan ta inda aka hau tanan ake sauka." Maigari yace."Babu shakka maganarka haka take Alhaji ku zauna ga gurin zama nan.." Prof ya nunawa su Mommy gefen doguwar tabarmar da babu kowa akai yace su zauna. duk suka bi layi suka zazzauna Asiya kanta a cikin hijab sai 'boyewa take. Gaishe gaishe aka shigayi kafin gurin yayi tsit! kowa ya zubawa Prof ido yana son yaji karin bayani....Prof yace."To Alhamdullhi ni sunana Prof Aliyu Nasir Adahama mamalakin Adahama motors and spire parts, Ina zaune a wannan jahar wato kano wataranar alhamis da ta wuce nida iyalina mun dawo daga ziyara muka tsinci wannan yarinyar kan titi kwance..........Prof ya shiga warware musu abunda ya faru komai bai rage ba sai da ya fada musu, kana kuma ya sanya Asiya ta bude fuskarta, a take suka zabura ganin Asiyatu 'yar gidan maishanu yarinyar da suke nema ruwa a jallo.
Maigari ya bude bakinsa zai magana Prof ya tareshi ta hanyar daga masa hannu yace."Ranka shi dade ban tari numfashinka ba." Maigari yayi shuru yana muzurai ya had'e da watsawa Asiya harara. Prof yace."Nasan kana so kayi min bayani kan irin abunda ta aikata wanda yayi sanadiyar guduwarta daga garin, to na samu labarin komai daga bakin waccan baiwar Allahn data kasance 'Kanwa ga mai aikin gidana Ladidi, Aranar da taje duba 'Yar uwarta tayi tozali da Asiya a gidan nan take shaida mana duk abunda ya faru a baya, wannan dalilin ne ma ya sanya nace mu sauka a fada domin a warware matsalar yanzu ina so yallabai ya tura a kira mahaifin yarinyar nan da tsohon mijin nata." Maigari ya tashi na kusa dashi yace maza-maza yaje gidan maishanu ya tawo masa dashi, ya kalli wanda yake gefan hagunsa shima yace dashi yayi maza maza yaje gidan Alaji Bawa yace yazo fada zasu tattauna magana..............Mintuna goma wanda aka tura kiran maishanu ya dawo ya zube gaban maigari yace."Allah ya taimake ka na samu labari daga bakin Ma'kotan maishanu cewar yau kwanansa biyu da barin garin nan shida iyalinsa." Maigari ya zabura yana kallon dan aiken yace."Maishanu ne ya bar garina ba tare dana sani ba."?
Maga takarda yace"Ranka ya dade shin ka manta abubuwan dake faruwa kenan, 'Yayan Alaji Bawa sun dauki alkawarin 'kona gidan maishanu har in dai basu dauki fansar abunda 'yarsa tayiwa ubansu ba, ina kyautata zaton wannan dalilin ne ya sanya maishanu yanke wannan hukuncin." maigari yayi shuru yana zullumi! Asiya kuka takeyi sosai tana kaunar babanata tasan wani abu n duk bayin kansa bane Gaje ce ke zugashi. Prof yace."amma abu baiyi dadi ba wallahi naso na samu mahaifin yarinyar nan mun tattauna dash........Kafin ya 'karasa maganarsa suka soma jiyo d'ure-d'uren ashar! d'in Alaji Bawa tun daga nesa suka hango tawowarsu shida d'an aiken yana sanye da babbar riga kawai da gajeran wando a ciki, kafafunsa babu takalmi yana tafiya yana nuni da hannunsa sai zage-zage yake yi......."Haka kawai ina zaune a gida ina hutawa za'ace nazo akwai mahimiyar magana ni akwai wata magana data dameni a yanzu burina kawai naga Asiyatu na rama abinda tayi mun, shegiya tsinnanniyar yarinya sai naci ubanki 'yar butan uwa."!!!! Asiya kanta tasa cikin hijab tana makyarkyata had'e da nanikar jikin Mommy wacce take a tsure! sai zare ido suke ita da Farhana.
Prof ya dinga kallon Alaji Bawa tsoho d'an kimanin shekaru saba'in da wanin abun sabida tsabar zulama da son zuciya shine zai auri yarinya kamar wannan 'yar 15years wani abu sai kyauye.


Alaji Bawa ya zauna yana kallon maigari da fad'in"Bani goro naci tukkuna kafin wata magana ta biyo baya dan na lura da ba'kin fuska dake zaune a gurin." Da sauri maigari ya mika masa wani katon goro ya kar'ba ya rabashi biyu ya soma taunawa yana tsotse ruwan......Prof ya zuba masa ido kawai yana kallonsa, Alaji bawa ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya yana kallon Prof din yace."Alaji kamar nasan wannan fuskar taka shekaru saba'in da suka wuce kamar munyi akin dukan manda'ko da kai."! Prof ya fashe dariya yana kallonsa yace "Anya kuwa ni ne Alaji."?
Alaji bawa yana tauna goro yana murmushi kamar wani mai hanakali yace." Gaskiya kuna kama da wanda na sani." Fada tayi shuru maigari yana ta tunanin ta ina zai fara.....Alaji Bawa ya k'ure Farhana da ido yana kallonta yana lasar busassan lebansa, Farhana gabanta sai faduwa yake. Wata mahaukaciyar dariya ya saki! yace."Yau nayi sabuwar amarya gata can 'yar fara kyakykyawa tamkar ba indiya hahahahahaha! jama'a ku shida an d'aura aurena.'"!!! Ba Farhana kad'ai ce ta shiga rudani ba har da Mommy da take data sanin zuwa, ta tsani ganin abinda zai daga mata hankali.....Gani sukayi Alaji Bawa ya mi'ke yana tattare babbar rigarsa sama yana nufar inda Farhana ke zaune da fad'in "Kyakkyawar amaryata zo muje gida mana." A guje! Taburni ta mike dan bata manta abunda ya faru ba lokacin da sukaje gidasa. Prof ne yayi gaggawar rike masa hannu yana fad'in "Alaji zauna mana mu tattauna abinda ya tara mu." Fuzge hannunsa yayi ya cigaba da tattare babbar rigarsa yana so ya sab'ule gajeran wandon jikinsa......Taburni tace"Gwara fa kuyi wani abu akai dan wallahi yanzu zaiyi zigidir." Da sauri Maigari da Professor suka shiga rirrikeshi yayin da yake kokarin fizgewa daga hannunsu dole sai yaje inda Farhana take......Mommy ta mike da saurin gaske ta kama hannun Farhana suka bar gurin. Asiya ta mike zata bisu Prof ya hanata kusa dashi ya zaunar da ita jikinta sai b'ari! yake......Da kyar! Maigari da wasu daga cikin fadar suka zaunar dashi ya zauna yana muzurai da neman inda Farhana take.


Sai da ya soma dawowa hayyacinsa tukkuna maigari ya shiga warware masa abinda ke faruwa ya zabura da karfi yake fad'in "Ina mutsiyaciyar yarinyar take yau sai na kasheta."!!! Prof yay gaggawar kare Asiya wacce Alaji bawa ya kaima mata wani mugun duka da hannunsa, Prof yace." Hakuri zakayi dan shine abinda ya cancanta wannan yarinya ba ta aikata maka wannan abu dan ta illata ka ba tsautsayi ne."! da fadin wannan magana ta Prof sai kawai Alaji Bawa ya rikice ya hargitse sosai ya shiga sambatu gami da kunzume kunzumen ashar!! Prof ya mike yana kallon maigari yace."Mu zamu koma ranka shi dade babu halin barin yarinyar nan a garin nan tunda iyayenta basa ciki zan dunga aike sa'i da lokaci insha Allah duk ranar da aka samu labarin inda iyayenta suke to sai a sanar damu, saboda haka yanzu ka tura akwai kaya mota akwashe muku saduwar alkairi." Maigari ya mike yana godiya sai washe hakora yake ta'b! shi zuwan yarinyar ma yayi masa amfani ga kudi ga kayan abinci.....Alaji Bawa ya mike a zabure! zai bi bayansu, da sauri maigari yasa mutane suka rirrikeshi! Allah sarki Alaji Bawa laushi yayi abunka da jikin girma sai kawai yayi lakas ya kwanta a gurin bacci ya daukeshi bakinsa yayi dagaje dagaje! da ti'kar goro.




Asiya suna shiga mota ta sauke ajiyar zuciya, hankalinta ya kwanta tunda sun fito daga garin lafiya yansu babban abunda yafi damunta shine sanin ina mahaifinta ya shiga, duk abinda ya faru dashi tasan itace sila tinda ta kasa yi masa biyyaya, hawaye ta share tana jin wani irin kunci a cikin zuciyarta, babu shakka Gaje ta cutar mata da rayuwarta.


Kallonsu Mommy takeyi ita da Farhana suna ta labarin abinda ya faru, Farhana tace"Daddy wallahi naji tsoro sosai kai Allah ya bashi lafiya tsoho dashi abin ya bani tausayi wallahi." Prof yace."Al'amarin akwai abun tausayi dama, amma kuma komai idan kun duba yana tafiya ne da kaddara kada ku dinga zargin ko Asiyatu ce tayi sanadiyar saka masa wannan lalurar, kaddara ce kawai kuma ita da tasan haka zata faru da bata aikata abinda ta aikata masa, da ace ta kasheshi ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login