Showing 60001 words to 63000 words out of 78289 words

Chapter 21 - SEXXI'ES HOUSE COMPLETE DOCUMENT Book by Maman Teddy .txt

19 Dec 2024

6953

kama hannun ta tana cewa mu tafi . Da fari Gida Hauwa ta isa ,tana shiga ta nufi Madafi tana Aje itacen da manja kana ta fito tana kama hannun Aaliyah suka bar gidan don A wannan lokacin Umma bata nan .


Kasuwar kanti suka nufa kai tsaye ba tare da Hauwa tasan ina zata kai Ƙanwar nata don taci Abinci ba . A bakin Shagon Mansura mai sayar da abinci ta tsaya . Don Allah Mai Abinci ki taimaka ki ba ƙanwa na yunwa take ji . Hauwa tayi Maganan tana tsayawa a inda Mansura ke irgar kudin ta . Wani Irin kallo Mansura tayi mata ,kana tace " A'a kyauta ne zan baki abincin , idan kina Son ƙanwar ki taci Abinci to ga Ƙwanoni can ki wanke mun su ,idan kin gama sai na biyaki da Abincin . To shi kenan kawo omo . Nuna mata Omon tayi yayin Da Hauwa ta juya tana kallon Aaliyah zauna anan Ƙanwata yanzu zan kammala sai kici Abinci kinji? . Gyada kai Aaliyah tayi tana zaune a can Gyefe tana kallon Hauwa tana wanke tulin wanke -Wanken kaman na gidan biki tana kammalawa ta mike tana goge zufan Goshin ta kana tazo Wurin Mansura tana cewa" Na kammala . To ga Abincin can ki ɗauka a saman teburi . Mun gode Abun da Hauwa tace kenan kamin ta kama hannun Aaliyah tana cewa " Mu je kici Abincin.


Zama suka yi tana tasa mawa Aaliyah abincin ,cikin sauri Aaliyah ta fara ci ,cin abincin take sauri sauri kaman zai gudu ita dai Hauwa sai kallon ta take tana goge Hawaye . Sai da taci Sosai sannan ta juyo cikin sauri tana cewa " Adda Hauwa ke ba zaki ci ba,kema mu ci tare . Jin hakan yasa Hauwa murmushi kana tace " A'a Aaliyah ta kedai kici ki koshi Kinga Ni idan na koma Gida Umma zata bani na dare ,amma ke kuma ba lallai Inna Turai ta baki ba . Hauwa ta kare Maganan tana shafa Saman kan Aaliyah wanda kitson kan ta yake a dankare tun wanda tayi mata zane guda hudu yafi tsawon wata uku a kitse babu wanda ya kara kallon mata . A haka suke gudanar da Rayuwar su cikin kunci sai dai abu ɗaya ne baya Wuce su a rayuwa shine karatun su ,duk da makarantar Gomnati Aaliyah tayi amma kuma dalibace mai matuƙar hazaka kaman Yar Uwar ta Hauwa . Bayan Hauwa ta maida Aaliyah gida ,da ta dawo Gida tasha dukan Baba ,don cewa yayi yawo ta tafi daga Aiken manja . Da kyar Umma ta kwace ta . Nisawa Hauwa tayi tana jin zuciyar ta na mata nauyi tana dawowa daga Tunanin ta duk da Maganan Aaliyah na dawo mata kwanya . Adda Hauwa komai sai dai ki bani ,ke ba kya ci me yasa ?.


Aaaliyah saboda ina son naga Rayuwar ki tayi kyau fiye da tawa rayuwar ,na ce mawa Maman mu zan kula dake sosai tun kamin ta tafi ta barmu ...komai zaki iya bani kenan ?. Murmushi Hauwa tayi kamin tace " Jindadin Rayuwa ta kaf zan baki don naki rayuwar , har ta Rayuwa ta zan iya sadaukar wa domin ki ..... Tari ne ya ƙwace Hauwa nan take tayi saurin tsugunawa daga inda take tsaye . A hankali take furta " Alhamdulillah Allah na gode maka da naga Wannan Rana , Yau Ƙanwata ce ke cikin jin dadi da ƙwanciyar hankali,nasan ko bayan Rai na Aydaan zai kula da Ƙanwata Sosai ,don yasan yanda nake Son ta a zuciya ta da Rayuwa ta . Wani irin tafi ne ya turniƙe ta , zuciyar ta na ƙullewa tare da mata zafi . Taffin Hannun ta tasa tana rufe bakin ta inda taji ruwa na biyo hannun ta . Sai da ta tsagaita da tarin ne sannan ta Bude Hannun nata tana Gani ....Idanun ta ta fiddo a tsorace ganin Gudan Jini da tartsatsin sa a hannun ta......!




*Littafin na kuɗi ne Regular Group₦300...Vip group₦500... Special₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*
#Mmnteddy*🕊️SEXXI'ES HOUSE🕊️*


Forty-Two 42
#Mmnteddy


___________________




*Littafin na kudi ne Regular Group₦300 Vip group₦500 SPC₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 ko ta wannan number 09061466409*




Wani irin harbawa Zuciyar ta keyi tare da buga mata da ƙarfi da ƙarfi idanun ta na fara ɓarin Ƙwallah wanda bata san da zuwan su ba sai dai saukar su . Kusan mintuna Uku tana tsugunne nan inda take tare da nazarin Sanadiyar Zuwan wannan jini wanda bata taɓa Ganin tayi irin hakan A duk lokacin da Tari ya Turniƙe ta ba . Hummm Numfasawa tayi tare da miƙewa duk da jirin dake Ɗabar ta amma a hakan take raɓa jikin bango , Hannun ta tasa a saman igiyar Shanyan Tsakar gidan tana Ɗaukar Mayafin ta tare da Yana jikin ta dashi ....nufar Ɗakin Umma tayi tana leƙawa don ta sanar mata zata leƙa Waje ta dawo ,amma kuma anan ta tadda Umma na Sharar barcin ta wannan yasa Ta juyawa tana nufar Sauron Gidan tare da ficewa izuwa Wani Chemist na Dr Jamilu , Wani matashin Likita dake anan layin nasu . Duhu duhu ke ɗibar ta amma a haka take tsallake Ƙaramin Titin Layin har ta isa Bakin Shagon Jamilu . A'a Sannu da Zuwa Hajiya Hauwa kece da kanki da Wannan yammaci Haka ?. Murmushi ta ƙaƙaro kamin tace " Eh Fa Dr Jamilu , nazo ne a rubuta mun maganin Ciwon Alcer a tunanin ta gyembon ciki ne . Okay to bari na duba na dauko miki. Zauna ga kujera bayan ki . Juyawa Hauwa tayi tana zaunawa a wani Rober Chair ,tana zama Wata Yar budurwar Yarinya na shigowa ƙawar Aaliyah . Adda Hauwa kece anan ? Bakya jin dadi ne ko Umma ce?. Murmushi Hauwa tayi kamin tace " A'a Salmah ba Umma bace wallh Ni ne dai bana jin Dadin jikin nawa , ƙirjina kemun zafi nafi tunanin alcer ne shiyasa nazo sayar magani .




Wayyo Adda Hauwa Sannu , Wallahi ciwon nan baya da Daɗi sam , Allah yakaro Afuwa . Amin Salma . Adda Hauwa tayi Maganan tana juyawa tare da kallon can Wajen Hanya . Zuwan Salma yasa ta tuno da wani lokaci da yarintar su . A duƙe ana ta Wasa tsakanin ita da Aaliyah , Ɗago kan da Salma zata yi sai tace " Aaliyah Tsakanin Maman ki da Abban ki Wanne kika fi so ? , nidai nafi Son mama na kefa?. Shiru Aaliyah tayi tana kallon Salma kamin cike da Yarinta tace " Ni dai Nafi Son Adda Hauwa ta . Adda Hauwa sai Anjima Allah yakara Sauƙi ....Maganan Salma ya katse mata tunanin da ta Faɗa a lokaci daya . Okay ki gaida mutanen Gida . Muryar Jamilu ne ya katse ta yana cewa " Wai Hauwa ba asibiti kika je aka yi miki Gwaji ba ,aka sanar miki da ciwon ki ?. Girgiza Kai Hauwa tayi kamin tace " A'a gaskiya banan naje ba ,Ni ce dai nayi tunanin hakan . Hauwa Maganan gaskiya ba Wannan ciwon na gani a tare dake ba . Don haka ba wannan maganin zan baki ba ,yanzu zaki zauna na duba ki sannan sai na baki maganin . To to Likita babu damuwa Ai .


**


Bayan Ta fito Privacyn ne ta tsaya a Bedroom din tana kallon kayan da ya fiddo mata , Ƙananun kaya ne English wear , Riga da Wando ...Ɗaga kayan Aaliyah tayi da hannun ta tana bin su da kallo , kamin ta yi magana a sarari da cewa " da ba irin wannan bane masu yalwa wallahi da ba zan saka ba , Dadin ta daya bana Son kaya masu nauyi shiyasa ma zan saka . Nufar Mirror tayi tana Kimtsa kanta kamin daga bisani ta saka Kayan ...Wow tayi kyau ƙwarai duk da Wandon bai kamata ba mai ɗan yalwa ne , wannan yasa Hips Ɗin ta ke Ya bayyana Sosai kasantuwar Wandon kaman cotton rober ne . Shi kuma Rigar mai kaman T.shirt .Juyawa Tayi tana bin Bedroom din da kallo ,ganin har a wannan lokacin bai shigo ba , Wannan yasa ta juyawa tana nufar Ƙofa tare da ficewa don yunwa take ji sosai . A Falon ma nan taga baya anan wannan yasa ta tsayawa tana tunanin to ina kuma ya je ne?. Juyawa tayi tana nufar restroom ɗin shi ,Wanda anan ne nan ma taga Wayam . To ina yake ne? Tambayar da tayi mawa kan ta kenan .


Juyawa Aaliyah tayi tare da nufar Wannan saman benen inda yace mata Dodon Sa na ciki , murmushi tayo tunano da Ruɗa ta da ya dinga yi , wannan yasa ta karambanin Hawa ba tare da ta san Hanya ba . Bin ko ina take da kallo komai a tsare gunun burgewa ....A haka ta kutsa kan ta izuwa Wani ƙayataccen Falo. Cak ta tsaya tana kallon sa ,wanda shi bai san ma da shigowar ta ba , gaba Ɗaya hankalin sa da kallon sa ya tattara kan Hoton dake maƙale a bangon Falo , yana kuma tsaye hannun sa Ɗaya na akan Saman Hoton . A hankali Aaliyah ta fara takawa tare da isowa inda yake tsaye . Har a lokacin bai farga da zuwan ta ba idanun sa na akan Hoton Adda Hauwa , Wanda take Sanye cikin Uniform alamun Hoton tunna Secondary school ɗin su ne . Gyefe kuma ɗaya ga Hoton shi tare da ita , fuskokin su duka cikin matsanancin Fara'a , ko ba'a Faɗa maka ba a wannan lokacin kasan suna cikin jin Daɗin rayuwar ta su duka . Suna kuma jin Dadin kasancewa da juna .! Shiru Aaliyah tayi jikin ta yayi sanyi Sosai , Kallon Hoton da yake wanda ko ba'a faɗa maka ba kasan yana faɗa mata sirrin zuciyar sa ne . Tausayin shi ne taji ya kamata , bangare guda kuma tana tausaya mawa Zuciyar ta itama , Me yasa zuciya ta ta fara Son maso Wani?.


Hannun ta takai tana kama hannun shi tare da cewa " Ya Aydaan.! Saurin juyowa yayi yana kallon ta ,a lokaci guda ya sakar mata Sanyayyar Murmushi kamin yace " Wow You look so cute 🥰 uhmmm💋 ya ƙare maganan cikin kawar da abun dake zuciyar sa yana manna ma laɓɓan ta ht kisss . A hankali ta janye jikin ta tana yin baya kana tace " Yah Aydaan Kana Son Adda Hauwa ko? . Saurin Kallon ta yaya yanayin fuskar sa na sauyawa daga yanda yake . Kasan mene ne ? Ka sake Ni ,idan kayi hakan zaka iya Auren Adda Hauwa ,Nima ina Son.... Yi mun shiru...!! Yayi Maganan cikin Tsawa wanda yasa taji Ƙirjin ta ya buga Dammm ... Baya tayi cikin Sauri tayi idanun ta na ciko da ƙwallah wanda a lokaci guda suka fara Saukowa zuwa ƙwancinta . Bana Son ƙara jin irin Wannan Maganan daga bakin ki kina jina? Idan na rabu dake ,ke kuma da Wane zaki rayuwa ? Soyayya na dake zuciyar ki fa? Ko baki san Zuciyar ki ta kamu da Mahaukacin SOYAYYA ta ba? . Humm ke yarinya ce Aaliyah ba zaki san hakan ba . Hawaye ne ya cigaba da bin Kuncin ta a hankali ta motsa laɓɓan tana cewa " Naji ina Son ka ,Amma nima na sadaukar Da Soyayyar ga Adda Hauwa, tun ina yarinya take saka Ni jin dadi take kuma sadaukar mun da dukkan Wani Abu nata ,komun soyayyar da take mawa wannan Abin zata bani shi halak har abada . Nima .....shiiiii it's Okay .yayi Maganan yana rufe Bakin ta da hannun sa . Saurin janye jikin ta tayi da Sauri da kuma gudu tana barin Falon . Kan sa ne yaji yana mugun masa ciwo , idanun sa na sauyawa daga Fari zuwa Jah . Saurin juyawa yayi tare da bin bayan Aaliyah Hankalin sa ya kasu gida biyu....!


**


Hauwa Hauwa....² Baba ya shigo gidan yana ƙwaɗa Kirar Sunan Hauwa cikin Wani irin murya wanda yasa Hauwa Saurin Afa Ƙwayar da Dr Jamilu ya bata tana korawa da Ruwa , Cikin Sauri ta fito tana amsa Kirar Baba dai dai Umma na fitowa daga ɗaki tana kallon Baba tare da cewa " Malam Lafiya ? Me yake faruwa ne?. Kai-kai-kai Wannan yaro wannan yaro ya cuce Ni ya cutar da Rayuwar Ki Hauwa , Kuma Wallh sai nayi Shari'a dashi . Cikin Sauri Umma tace " Malam Wake nan? Wane ban da Wannan mugun shashashan Yaron Salisu . Yanzu Malam Bala yake sanar mun da baƙar Wahalar da ya ba wannan Yarinyar ,wai shine daga ƙarshe har da tuƙucin Saki......?




#Mmnteddy*🕊️SEXXI'ES HOUSE🕊️*


#Mmnteddy
Forty-three
43
*Littafin na kudi ne Regular Group₦300 vip group₦500 SPC₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932/09061466409 ....*
___________________


Cike da mmkin maganan nasa Umma tace " Malam yau kai da bakin ka kake faɗin Hauwa ta sha baƙar Wahala a hannun Salisu? Yau kai da kan ka kake nuna tausayin ka akan baƙar izayan da Tasha a hannun Salisu? Kai Alhmdlh Allah na gode maka , dama komai ya farko zaiyo ƙarshe , Abun da na dade ina addu'ar Allah ya fahimtar da kai akan zaluncin Salisu da yake mawa Hauwa yau gashi Ka fahimta hakan daga bakin mutane mabanbanta . Amma don Allah Malam kar ka kaishi ko ina ,muna nan Zaka gani Wallh sai Allah ya saka mawa Hauwa ko da Rayuwar mu ko bayan Ran mu . Aaaa Umma don Allah kuyi hakuri , Babu komai ....Hauwa tayi Maganan cikin sanyin Muryar ta wanda hakan ya zama mata jiki . Hauwa duk wannan bakar uƙuban da kika sha kice Na rabu dashi ? Baba yayi Maganan cike da mmkin kalaman Hauwa . Baba ku rabu dashi komai yayi mun yasan bai mun Adalci ba kuma bai mun dai-dai ba , Amma na bar shi da Mahaliccin mu,kuma ku bar shi kawai . Numfawa Baba yayi cike da gamsuwa da Maganan nata kamin yace " Ƙwarai haka ne , Allah zai saka muki Hauwa'u , Maganan ki kin yi gaskiya kin kuma yi dai-dai . Ta shi ki tafi Allah yayi miki Albarka ". Murmushi Hauwa tayi irin na majinyata Wanda basa da Wadataccen Lafiya kamin tace " Amin Baba . Umma bari na shiga daga ciki . To Hauwa .


**
Hannun ta Tasa tana kama hannun Aaman Kamin ta numfasa tana cewa " Aaaman .! A hankali ya ware idanun sa tare da maido da duban sa ga Momyn nasa wacce gaba ɗaya hankalin ta yake ba Ƙwance ba,ta kasa gane gaskiyar inda lamarin Aaaman ya nufa ,shin son Jidderh yake da gaske a jinin jikin sa ,ko kuwa tausayi ne ?. Momy tunanin me kike yi?. Ya katse ta yana kallon fuskar Momy wanda ta sakin masa murmushi kana ta shafa suman kansa tana cewa " Aaaman yanzu fa , Nasan ka fahimta ba Son Hauwa Jidderh kake yi ba, kawai dai Zuciyar ka....Momy Da gaske Ni ina Son ta.! Kuma dai dai da sakani ɗaya ban ji soyayyar ta ya ragu a zuciya ta ba sai dai ƙaruwa ma da yake . Momy ko wani lokaci a duk sa'ilin da zuciyata ta buga ,bugawa yake da Soyayyar ta a haɗe . Ina nufin soyayyar Hauwa ƙaruwa ma yayi daga Wanda kika sani a baya . Shiru yayi yana kauda kan sa don baya tsammanin Momy zata so jin Hakan daga bakin sa . Sauke Ajiyar zuciya Momy tayi kamin ta ƙara murmushi tana cewa " Ina bayan ɗa na ,akan Abun da yake SO ɗari bisa Ɗari . Kuma na sanarwa Abban ka shima ya bani goyon baya akan ka ,kai mijin mace hudu ne ,idan zaka iya adalci tsakanin su , Bama Jidderh ba ko wa kake da buƙatar aure Indai iyayen ta zasu baka ,bani da matsala da Wannan ,sai dai nace Allah ya tabbatar da Alheri . Ohhh Mom...!!thnkyou very much momy. Aaaman yayi Maganan cikin nuna matsanancin Farin cikin sa tare da kama hannun momy yana rikewa ƙaaamm . Ina son Abin da kake so ne Aaaman , Kasan ina Son ka Ni Mahaifiyar ka ce ,zan soka fiye da kowa . Murmushi su duka suka yi kamin ya miƙe yana cewa " Momy ina tunanin a yau zan tafi Yobe Na duba Jidderh acan . Kaiiii Saurin mene kake yi haka? Kasan aƙwai Aiki a gaban ka ko? Dole sai ka rarrashi Ƙanin ka Aydaan don ya amince ,saboda kasan Wacece Jidderh a wurin sa ,Sannan Bikin ku fa yau ya rage saura Ƙwana uku Ɗaurin Auren ku , dole Ku kasance tare da Amaren don ku ji abubuwan da suke buƙata, Sannan kuma kar ka manta tun yanzu fa Abokan ku sun fara cika gida , Zaka tafi ka bar su ne . Hajiya Kaka ta faɗi cewa " Ba zaka Auri Jidderh ba sai An kammala komai na Auren ku anyi an watse sai daga baya . Shiru Aaman yayi jikin sa ya ɗan yi sanyi . Momy yanzu haka zan Zauna har tsawon ƙwana ki Uku ban gan ta ba ,ban kuma faɗa mata Abun dake zuciya ta ba . Ƙwana ki biyar dai ,ba daga Auren bane washe gari zaka tafi . You have to think about ok?. Gyaɗa ma Mommy Kai yayi alamun ya fahimta kamin ya juya yana barin Falourn Momyn zuciyar sa cike da jin dadi .


**


Ruwa take yayyafa ma ƙasan Tsakar gidan tare da cigaba da share tsakar Gidan . Salisu ne ya shigo gidan tare da faɗin " Inna An aje mun Ragowar Tuwon ko?. Aje tsintsiyar Innan Salisu tayi kamin tace " Eh yana nan na Rufe maka , Ya Maganan neman Auren naka da yar gidan malam iro ?. Ai Inna Komai lafiya yanzu ma haka sun bani izinin na tura iyaye . Yauwa mashaallh , Ai yanzu ne zaka san kayi Aure Salisu , da wahala kake yi ba Auren jin dadi ba .....ina zan iya , ai gwara da kuka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login