Showing 51001 words to 54000 words out of 78289 words

Chapter 18 - SEXXI'ES HOUSE COMPLETE DOCUMENT Book by Maman Teddy .txt

19 Dec 2024

6955

ƙara riƙe masu yarinya da Amana ,idan ya zalunci yar nan to Allah zai saka mata wannan shine .






Jiki a sanyaye Ammmie tace " To Hajiya Ayi haƙuri don Allah . Itako Momyn Aaman juyawa tayi tana ficewa daga Falon a zuciyar ta faɗi take naga Ɗan iskan da zaiyi mawa yaro na dole , Ai a hakan Auren nan da zaiyi na haɗi an cutar dashi ,Baga maganan so ba , a'a shi kan shi yasa Watsatstsiya zai Aura . Cikin da jin zafi ta nufi part Ɗin ta .


Ɓangaren Aaliyah kuwa tana ficewa daga Falon kan ta tsaye farfajiyar gidan ta nufa tare da nufar Gate masu Gadi suna buɗe mata ta fice daga Gidan . Wayar nan naga Nokia ɗin ta ,ta fiddo tana fara kirar numbern Hajiya Munaya. Ringing biyu taji bata ɗaaga ba wannan yasa ta saurin fara barin layin tare da nufar mai adaidaita. Tana shigewa adaidaita Aydaan na fitowa . Ganin sa da tayi a can bayan ta yasa ta ce mawa mai adaidaita yi sauri ka ƙara Gudu . Kamin Aydaaannnnn yazo tuni sun bar layin . Tsayawa yayi yana Kirar sunan ta amma ina Bama ya iya hangen su . Ji yayi an dafa shi tare da sauke ajiyar zuciya . A hankali Aydaaannnnn ya juyo yana kallon Aaman dake tsaye a bayan sa . Aaman Ni zaka cuta? Ni zaka yaudara?. Ina Aaliyah take? Ina ta nufa yanzu ?. Banza Aydaan yayi masa kamin a zafafe yace " Matar ka ko matata? Ka bani Amsan tambaya ta malam.! Shiru Aaman yayi kana yace " Kayi haƙuri Aydaaannnnn , Har Abada babu Aure tsakanin Kai da Jidderh Indai Aaliyah na raye kuma kuna tare da ita . Tausayin nan nata da kake ji shine ya kamani a lokacin da ka faɗa mun cewan Aaliyah da Jidderh yan uwa ne . Sannan kuma kar ka manta Jidderh soyayyar ta yasamu gurbi ne daga yarintar ka ,a lokacin baka san So ba kawai kana faɗan ta ne....a yanzu ne Aydaaannnnn kasan SO domin dai dai da Minti guda ba zaka taba iyaye a rayuwar ka hankali kwance ba tare da kaga Aaliyah ba ko kaji Muryar ta ,wannan shine Son Gaskiya . Bari na faɗa maka wani Abu da baka taba Sani ba , Shine kana Mugun masifar Ƙaunar Aaliyah soyayyar ta wannan a jinin ka yake .


Numfasawa Aydaaannnnn yayi kamin yaji Muryar Aaman Na cewa " Yanzu a tunanin ka ina ne Aaliyah ta nufa? . Kai tsaye Aydaaannnnn ya furta " Gidan Munaya . Okay Bari na fito da Moton ka muje can ,daga can sai ku wuce gida kawai . Juyawa Aaman yayi ba tare da ya jira cewan Aydaaannnnn ba wanda ya tsaya yana faɗawa duniyar tunani ,idan suka matsa mun zan bar Aaliyah dani kaina ƙasar nan sai kowa yayi shi kaɗai .


**


Tun da Aaliyah ta shiga Falon Munaya ta kasa ɗaga koda ɗan yatsar ta saboda tashin hankali da kuma ɓacin rai . Tsayawa tayi a tsakiyar Falon hawaye na cigaba da bin Kuncin ta . A hankali ta fara jin fitowar Munaya cikin wannan takon nata mai dauke hankalin maza da mata baki daya . Wani irin crazy dress up tayi , rigar mai kama jiki kuma roba ,duk ƙiban ta Wando ta saka ta ɗame cikin English wear tana saka ƙatuwar Ɓakar gilashi wanda ya mamaye rabin fuskar ta . Kan nan nata yasha fixing na attachment...Saurin sauke gilashin idanun ta tayi kamin tace " Aaliyah kece yau?. Me ya kawo ki gidana? Mayaudariya azzalumai muguwa ,Ni kika ha'inta , bakiyi mun aiki na ba , kika sa nayi gidan yarin na tsawon ƙwana ki , Aydaaannnnn ya sa aka tura Ni nan . Bayan fitowa na wai labarin Auren ku nake ji , Anya ke mutum ce Aaliyah? Butulu ce ke ,mai manta alƙawari .




Kallon Munaya Aaliyah tayi kamin taja magina tana sa hannun ta tare da goge Hawayen Fuskar ta . Hajiya Munaya.! Aaliyah ta kira sunan ta cikin wani irin murya kamin ta kalle ta tun daga Sama har ƙasa . Bakya ne ya kamata kimun wannan munanan maganganun naki ba , a'a nice Wacce ya kamata na faɗa miki su . Tsakani na dake ALLAH ya isa ba zan yafe miki ba ,kin haɗani da musifa...tun da na fara miki Aiki hankali na yaƙi Ƙwanciya har iyau . Aaliyah ni kaka zaga? . Na zageki Munaya Kiyi mun duk Abin da zakiyi . Kuma Wallh ba zan bar gidan ba sai munje wurin Aydaan kin faɗa masa cewa ' ke ce kika sani komai bani nasa kaina ba ,don ban taɓa sanin sa a rayuwa ba sai a sanadiyar ki ...... Aaliyah Aydaaannnnn ya san komai ki ƙwantar da Hankalin ki . Suka ji Muryar Aaaman dake shigowa , Aydaaannnnn na biyo bayan sa . Wani irin kallo Aaliyah tayi masu duka kamin tace " To saura ya bani takardan saki na ,ya Auri Munaya itace ta shirya komai ,ita zai dauki fansa da mataki akan ta ba Ni ba .




Keee waya ce ki taho Gidan nan ? Da izinin Wa kika zo gidan nan? . Aydaaannnnn yayi mata maganan cikin arrogant voice Din shi babu alamun wasa . Wani irin kallo ta masa cike da mmkin halin sa kamin Aaliyah tace " kai kuma a wane? Ai yanzu bakin alkalami ya riga da ya bushe , a yau yanzu sai ka sake Ni... Babu rabuwa a tsakanin mu sai dai mutuwa.! wani irin waro ido Aaliyah tayi idanun ta na cigaba da Ambaliyar hawaye. Wallh baka isa ba ,sai ka rabu dani a yau ... Ta ƙare maganan tana fashewa da Kuka . Wani irin sheƙeƙen kallo yayi mata kamin ya tako zuwa inda take . Hannun ta ya kama yana cewa " Oya mu tafi kar kuma na ƙara Ganin ki a cikin gidan nan. Janye jikin ta tayi da hannun ta kamin tace" Me ka ɗauke ne Aydaaannnnn ,kalli yanda kake mun kaman yar cikin ka ? Babu inda zan tafi .........!
#Mmnteddy
#Rmdnkareem🌙*Littafin na kudi ne Regular Group ₦300...Vip group ₦500... SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number nawa 08081202932 idan VTU transfer ne sai a tura ta Wannan number 09061466409 #Mmn teddy*
38-39
#Mmnteddy
Da fari bani ce Wannan masoyiyar taka ba da kake nema , Adda Hauwa ta saka Ni a masifa ,ta fahimci komai amma ta tirsasani Auren ka , na biyu Bani ce na shirya zaluntar ka ba , Ɗaurani Akayi kuma ka sani ,ƙarshe ma ga wacce ta sani , to meye yayi Saura ? Kawai Ka ɗauki mataki akan ta mana ,sai kace akai na ne zaka Ɗauki Fansa? To a yau sai ka sake Ni ka Auri Wanda .....Kamin ta rufe baki ne taji tasssssss Ya ɗauke fuskar ta da Wani irin Mari ,wanda sai da taga Tartatsin Wuta . Baya tayi taga -taga zata faɗi ya finzota da hannu ɗaya ta Faɗo Jikin shi. Jah baya Munaya tayi cikin tsoro tana nufar can Ƙusurwa tana manne kan ta kaman bango Ya tsage ta shige Ganin Aydaan take tamkar Damisa ko Zaki . A zuciyar Munaya cewa take " Tabbas Wannan Yarinyar bata san Waye Aydaaannnnn ba . Ba kuma tasan Irin fusataccen Zuciyar sa ba . Tabbas don So yana Son Aaaliyah da badon hakan ba ,wannan Maganan ma ba zai bari ta tsaya ta rinƙa faɗa masa ba . Aaaman ne ya matso cikin Sauri yana ƙoƙarin takowa zuwa inda Aydaaannnnn ke Riƙe da Aaliyah sai ihu take tana Kirar Sunan Abba amma kuma bashi yasa zuciyar shi yin salama ba . Wani irin kallo ya Watsa masa Aaman tare da ɗaga masa Hannu yana dakatar dashi , Juyawa yayi da Fuskar sa yana kallon na Aaliyah dai dai lokacin A'aman na cewa " A'a Aydaaannnnn Kar kayi mata Wani Abu , Cikin Salo da dubara zaka saye zuciyar ta har ka samu gurbi a ciki ba ta wannan hanyar da ka ɗauka ba . Plsssss Aydaaannnnn Ka saurare Ni .


Kai malam don Allah kayi mana shiru kana ji da kunnen ka wannan yarinyar zata na rinƙa faɗa mun Abubuwa son ranta , Just because I love her? Wannan daman kaɗai ta samu take shirin maida Ni yaron ta ?Hannun sa yasa yana ɗago fuskar ta yana kallon idanun ta da suke fidda Ƙwallah masu raɗaɗi " Aaliyah kar Kiyi tunanin barazanar ki ,ko nuna tsana a kaina zai sa na sauya Ra'ayi a kan ki ,No.! Ba zan taɓa daina Son ki ba saboda son ki ba a fatar baki na take ba , daga Zuciya ne , haka yake pumping tare da gauraya da gaba Ɗaya ilahirin jinin jiki na . Tabbas Maganan Ammmie gaskiya ne ,a baya nayi soyayya a makance ne , a kuma yanzu da duka biyun nake , zanyi komai ma wanda yayi yunƙurin raba Ni dake ,koda ke kan ki ne.! Ina Son ki a yau ,gobe kullum kuma a koda yaushe har izuwa numfashi na na ƙarshe . Wuce mu tafi....! Ya ƙare Maganan yana fuzgar hannun ta . Tsorata Tayi sosai da yanayin sa , Dama ta dade tana tunanin Lafiyar ƙwaƙwalwar mutanen Gidan Moddibo's Family , Musamman yanda take ganin Suna lalata da junan su . A yau ne a kuma maganganun Aydaaannnnn ta tabbatar mawa da kanta Cewan Yaran gidan basa da cikakken Ƙwaƙwalwa . Me kake nufi da ko Nine ba zaka bari ba Indai na yi yunƙurin raba mu? To duka-duka yaushe ka Sanni ma? Ka cika mun hannu na , ba zan tafi ba ,ba zan bika ba.... Aaliyah ki bishi Aydaaannnnn yana cikin Wani irin yanayi wanda zai iya aikata komai . Aaaman yayi Maganan yana kallon Aaaliyah . Tsayawa Aaliyah tayi a tsorace tana kallon Aaman tana ji tana Gani ya fice da ita yana saka ta a mota ko tsayawa bi takan A'aman baiyi ba ya Jah Moton yana ficewa daga Gidan cikin Wani irin mahaukacin gudu .


**


Ɓangaren Dangin Aaliyah kuwa an samu gutsiri tsoma a cewan su ,tun da suke basu taɓa Ganin Aure irin na Aaliyah ba , Dangin Ango mutane ƙalilan ga cin mutunci , sam suka ce babu Wanda zai zauna dasu sai Amarya . Hasali ma babu Wanda yakai Amarya ɗakin ta a matsayin su na dangin Amarya . Duk dai Ƙananun Maganan da Dangin Aaliyah keyi Inna Turai ta toshe kunnen ta , a zuciyar ta ita dai babu Abun da take yi sai fatan Allah ya basu zaman lafiya . Duk da itama hankalin ta ya tashi Ganin su Hajiya Rahina da Momyn Hibba . Gafara Dai ,sannun ku sannun ku.". Juyowa Inna Turai tayi cike da mamakin Ganin Hajiya mai riga wanda take Yaya a gurin Abba ,Indai iya masifa ne ita kankat ne ,tsoran ta kowa keji . Cikin Rawar murya Inna Turai tace " Hajiya Barka da Hantsi ?. Barkan mu dai Turai ,ashe kuma haka Abun ya kasance? Kun ɗauki Marainniyar Yarinya kun ba ahalin da bamu san nagartarsu ba ?. Duka me yasa haka? Eiyee ko don Saboda Mahaifiyar wannan Yarinya bata a raye ne akayi mata haka?. Shiru Inna Turai tayi tabbas maganganun Hajiya mai Riga ya dafata sosai , A yanzu tana ganin Aaliyah babu bambanci da itace wacce ta haife ta . Kuma wannan Abu tabbas in ba don ta ga Yaro na Son Aaliyahn ba itama ba zata bari hakan ya faru ba . Muryar Hajiya Mai Riga taji a sama tana cewa " Ko da yake bake ya kamata nayi magana dake ba , Shi Uban yarinyar da suka amshi Auren ya kamata na samu . Juyawa Hajiya Mai Riga tayi fakan fakan da silifa ɗin ta tana gyara mayafi ta fice daga Gidan . Kasa sukuni Inna Turai tayi wannan yasa ta aje Shinkafar da take tsinta tana ba Sha'awanatu tare da cewa " Sha'awanatu ku cigaba da tsintar Ni Bara naje na Dawo . Yaya Turai Don Allah kar Wannan magann ta ɗaga miki Hankali. ko kaɗan Sha'awanatu babu Abun da ya ɗaga mun Hankali . Zan tafi Gidan Umman Hauwa ne , ina So nayi magana da Hauwa . Tana faɗin haka bata jira jin cewar na Sauran mutanen ba ta nufi Ɗakin ta tare da Ɗaukar mayafi tana fitowa tare da masu sai ta Dawo .!


**


Kuka Summy keyi tun bayan Barin su Part Ɗin Hajiya Barmani , A haka Hajiya Rahina ta shigo ta same ta . Bin ta da Kallo Momy Rahina tayi kamin ta nufi Window tana janye labulen da suka ƙara mawa Bedroom ɗin Duhuwa . Nisawa Tayi tana juyowa tare da kallon inda Summy take Maƙale da Teddy bear 🐻, idanun ta a lumshe suke amma hawaye ki fita daga Cikin su . Babu fuskar da take gani take kuma jin tamkar ta kashe Rayuwar ta kaman na Aaliyah . I hate her mum , i hate that Stupid Girl . Ƙaramar Yarinya ta addabi rayuwata , Ta saka a halin mu cikin ruɗani da tashin hankali?. Mum She's not up to 18 Amma duka ta galleze mu ,mun rasa yaya zamuyi da ita . Idan na kama yarinyar nan kashe ta zanyi na kashe banza . Duk na ƙosa na ga An ɗaura Aure na da Aydaaannnnn mun zauna Gida Ɗaya da Wannan shaiɗaniyar Yarinyar . Sai tayi na dama marar Amfani . Duk Maganan Da Sumayya keyi Mom Rahina bata ce komai ba ,don ita kan ta a yanzu bata ƙi a ce Yau Aaliyah ta mace ba . Bin jikin Sumayya tayi da take sanye da Ƙananun kaya , Marasa nauyi bomb Short ne a jikin ta sai Wani yar ficiciyar Riga mai kaman vest . I'm very sorry Darling Daughter , the First time Dana kasa shawo matsalar ki a Rayuwa . Ki shiga Gidan Dole za mu san yanda zata fice . Yanzu ki tashi ki watsa Ruwa kiji sanyi a zuciyar ki , Aydaaannnnn ne kuma zai zama naki nan ba da jimawa ba, Daga nan kuma sai yanda muka juya taswirar Rayuwar sa ,Maganan Wata ba ke ba , a bar shi ma kawai . Nasan kin gane me nake nufi ?. Karo na Farko da Sumayya ta saki murmushi mai sauti don ta fahimci inda zancen Mom ɗin nata ya nufa . Gyaɗa mata kau tayi tana dariya . Oya to maza tashi ki Wanka ki wanke fuskar ki da ta kacame da Hawaye duka akan yar matsiyatan can . Momy ai yau tafi mun ko wacce Rana jin Dadi . Allah ko?. Eh mana Momy Bara dai na shiga Privacy na fito . Ki sanar ma cook's ina buƙatar Jalop yaji kayan Lambu , Pepe meat Su haɗa mun Salad🥗 yaji Bama Sosai. Hummm amma kin san na hanaki cikin kayan maiƙo sosai ko?. Mum kawai saboda ina cikin farin ciki ne ,amma ai kin san na rage . Okay Ni BAMA cream ɗin ne bana so kina cin shi ,yana advantage da kuma disadvantage a You know?. Yeah Mum . Sumayya tayi Maganan tare da shigewa Privacy tana furta " I'm sorry Momy ....! Murmushi Momy Rahina tayi tare da kwakkwayon Muryar ta tana cewa " You're Wlcm Baby 🥰.


**


A farfajiyar Gidan Aydaaannnnn ya fito daga Moton tare da nufar Ɓangaren Da Aaliyah take ciki , Buɗe mata yayi yana Sa hannun sa tare da kama nata tamkar Babu abun da ya haɗa su . Wani irin bin sa da kallo Aaliyah keyi cikin mamaki kamin tayi wani magana ne taga Ya sakin mata Murmushi wanda sai da Hushiryar sa na sama suka bayya na . We're back Home now". Hannun ta ta ƙwace daga Riƙon da yayi mata tana fitowa tare da Wuce shi fuuuuu tana nufar Ƙofar da zai sada ta da Falo . Duk gaisuwar da Ma'aikatan ke yi mata Bama tasan suna yi ba . Hankalin ta da zuciyar ta duka babu daɗi . Cakkk taja tsaya a tsakiyar Falon tana tsayawa tare da yin Ware ware . Ina ne nan kuma? Tambayar da tayi mawa kan ta kenan ,ganin ta a wani Sabon Falo wanda sam bai kama da Wancen ba . Dafe kan ta tayi tana lumshe ido tare da buɗe su . A zuciyar ta tana cewa " Makowa nayi ,na ɓace Hanya , mutum Wannan wani irin gida ne?. Tsayawa tayi tana bin tsakiyar falourn da Kallo . Kujeruna ne dogaye sun haura 3str sai dai muce 4str . Guda uku a ƙaton Falon . The same Design Amma colour ɗin ko wanne da banbanci . Ɗaya Arsh ɗaya Black sai na tsakiyar da yake Red . Bangajejen Centre Carpet Ɗin Shima Red ne dukan shi sai Gyefe baki . Cotoons Ɗin Falon suma Red ne Da Arsh . Kamin ta tsaya Ƙare mawa Falon kallo ne ta fara shaƙar ƙamshin sa , wanda hakan ya alamta mata da shigowar sa kamin daga bisani taji motsin sa a daga Bayan ta . Hannun sa yasa yana tallabo Ƙugunta tare da zagayewa yana Rungume ta ta bayan ta . Baby me kika zo yi nan ? Part Ɗin Sumayya ne , ko kina Son nan ?. Juyawa tayi tare da ɓanɓare kan ta daga Garesa tana shirin ficewa daga Falon ne ya yi saurin riƙo Hannun ta . Idanun ta ya tsira ma kallon sa , yana karantar Abubuwan zuciyar ta . Hushhhhhh ya sauke Numfashi mai ɗan ƙarfi kamin yace" ki Zauna anan to ,yanzu nan ne Part Ɗin ki can sai ya zamana nata ai hakan kike So ko?. Did I told you that? Ban faɗa maka hakan ba zaka yanke mun hukunci? To kai ne bana So,ba kuma na Son zama da kai ...! Sakin Hannun ta yayi tana ganin haka ta juya cikin Sauri tana nufar ƙofar da ta shigo ,amma kuma tana isa Taga garammmm ya ja ya rufe . Saurin juyowa tayi tana kallon Inda Aydaaannnnn ke tsaye . Mamaki ne ya kamata Tayaya ƙofar ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login