Showing 36001 words to 39000 words out of 78289 words
Chapter 13 - SEXXI'ES HOUSE COMPLETE DOCUMENT Book by Maman Teddy .txt
ta Inna tayi tare da shafa bayan ta tana rarrashin ta ya isa . Zata daina kinji?.
Saurin riko Hannun Inna Turai tayi tare da cewa " Inna Adda da gaske zata daina fushi dani? . Gyaɗa Mata Kai Inna Turai tayi tare da cewa " Ai kin san bata taɓa fushi dake ba , Yau ma dai ta nuna miki kisan darajar Auren ki ne . Mu tafi ɗaki muje kici Abinci . Miƙewa Aaliyah tayi Abba na Murmushi cike da jin sanyi a zuciyar sa ta fice daga Ɗakin tare da nufar Ɗakin Inna Turai .
**
Basu samu isa Garin Ibadan ba sai Safiyar goben ranan . Koda suka isa Gida Kowa part ɗin shi ya nufa tare da kimtsawa ,kana kusan Awa biyu Aydaaannnnn ya fito yana nufar Ɓangaren Ammiee . Anan ne take ƙara Sanar masa da Isowan Amaryar sa a gobe , Wanda Batasan Tuni Abban Ibadan ya sanar masa ba . Ammiee ne tace dashi yaje ya duba jikin Summy ,don har yanzu jikin nata sai a hankali ,ciwo sosai take yi . Jin hakan yasa shi nufar part ɗin Hajiya Rahina . A Falo ya tadda Momy Rahina don saukowar ta kenan daga Bedroom din Summy . Hannun ta dauke da glass cup da alama ruwa ta bata sannan ta fito . Washe baki yayi cike da jin dadi da faharin ya zama sirikin ta tace " dawowar yaushe ?.. murmushi yayi yana gaishe ta kamin ya haura upstairs don nufar bedroom din Summy .
Da shigan shi Bedroom din ya ga ko ina ta rufe ruguf , a hankali ya taka yana nufar window tare da yaye labulan , Tun shigowar sa taji ƙamshin turaren sa ,wanda a ko'ina taji bazata yi makowar mai shi ba . Wani irin Raɗaɗi take ji tana ɗago idanun ta tare da Ware su daƙyar dai dai yana isowa. Hannun ta ta ɗago masa tana miƙa masa , Wanda a hankali ya miƙa nasa yana haɗawa da nashi ,tare da matsowa kusa da ita yana hayewa saman gadon ,dama sun saba. Matsa hannun nata yayi a hankali yana jin Zafin jikin nata yayi tsanani . Ɗago da Lulun idanun sa yayi yana zuba su a kan fuskar ta , wanda suna haɗa ido tafara zubda Hawayen da suka dade da daskare mata a zuciya . Kuka take sosai har dasu Ajiyar zuciya . Wanda duka yasan dalilin yin masa hakan ,bai wuce kishi da bakin cikin Auren sa da Aaliyah . Kallon ta yayi yana cewa " Meke damunki Summy? Ina ke miki ciwo ? . Ɗago da idanun ta tayi da suka yi Jah kaman zata masa magana sai kuma ta kasa . Please ki faɗa mun ? Me yasa kika ƙi bari a kaiki asibiti?. Aydaaannnnn ina Son ka.! Bazan iya jurar ganin nayi kishi da ko wacce ya ma ce ba ,zan iya komai , bazan iya kishi da Yar Talaka ba kuma abun Haushin ma yar Aiki na.!
Kuma yar Aikin gidan mu .! Wani irin ba dadi yaji , wannan yasa shi yi mata Wani irin kallo kamin yace " Nine nace ina Son ta ai , so ina ke miki ciwo?. A Maimakon ta basa amsa kawai sai ta fashe da kuka ,nasani ai . Aydaan ka tsane Ni me nayi maka? . Ke Summy , Wai ke bakya duban Ni Ƙannin ki ne? Me yasa zaki Soni? .So babu ruwan sa da Wannan , Amma zaka iya kashe Ni ta hanyar yimun Allura yanzu ai kai likita ne ." Kallon ta yayi cike da jin dan tausayin ta . Hannun sa yasa yana Rungume ta jikin sa , wanda nan naga Abun mamaki shigar da kan ta tayi saman ƙirjin sa tana shaƙar ƙamshin jikin sa tare da masa Wani irin kuka can ƙasa² na tada Sha'awar masoya . Sarai tasan waye Aydaaannnnn shi yasa duk wani Abu da zata ja hankalin sa take yi . Hannun sa yasa yana shafa suman kanta har zuwa Bayan ta tare da hura mata iska a Gyefen kunnen ta a hankali ,is Okay my Summy ,ya Isa ina Son ki kema . Sauke Ajiyar zuciya tayi tana saka hannun ta tare da shafa saman ƙirjin sa tana wasa da ƙwantattun gashin ƙirjin shi . Lumshe ido yayi tare da saurin riƙe hannun ta cikin wani irin yanayin murya yace " Stop it". Yayi maganan tare da miƙewa yana cewa " Bari na Dauko first aid box na yi miki allurao . Ga shi nan ai , Ammie tun juya ta shigo dashi .
Juyawa yayi yana kallon inda ta nuna masa , nufar wurin yayi yana dubawa tare da Ɗaukar Wasu alllurai yana haɗawa wuri guda tare da jan shi a ƙaramin sirinji ....Takowa yayi zuwa inda ta miƙe zaune . Tsayawa yayi yana kallon ta , kamin yace ' Bani Hannun ki nayi miki?. Kallon sa tayi a shagwaɓa tace " A'a Ni ba'a mun Allura a hannu kamun a baya kawai . Cike da yagewar ido da yafi nata yace " Okay juya ,kuma kar ki mun raki . Juya masa tayi yana sa hannun sa tare da Sauke Skirt ɗin jikin ta , Wani irin abu ya haɗiye , hannun sa yasa yana shafa tudun Bayan ta , Kusan mintuna biyar yana kasa sa Sirinjin . Ita ko lumshe ido take , tana fara jin tana tsiyaya . Wani irin magana take a harde kaman wanda ake saka mata shocking . Aydaaannnnn Please... Please Aydaaannnnn , Aydaaannnnn ...! Hannun sa yasa yana shafa Gadon bayan ta cikin Wani irin Salo ,yana jin yanda Alƙalamar sa ke harbi kana yace " Mun kusa saura kwana nawa ne ? Just mu kara hakuri kar muyi sabon Allah . No Aydaaannnnn Babu komai fa . Kai ai miji na ne zaka zama . Wani irin kallo yayi mata bai san lokacin da ya zura allurar ba tana gantsarewa tare da sakin yar ƙaramin ƙara . Hannun sa yasa yana lailaya mata kamin yace " zan Aiko miki da magani ki tabbatar kin sha . Yayi maganan a gadarance kun dai san shi da isa da mulki ga uwa uba Miskilancin hummm. Juyawa yayi yana ficewa da ga Bedroom din tare da nufar Farfajiyar gidan .
***
Tsawon dare Aaliyah ta kasa barci ga damuuwar Adda Hauwa ga kuma damuwar daga Yau gobe Ibadan aka kuma yi da ita . Me yasa Adda Hauwa zata Faɗi mun haka ? Me yasa abun da bata taba mun ba ?. saurin miƙewa Aaliyah tayi daga Zaune tana faɗin Wallhi na gane na gane yanzu . Adda Hauwa itace Jidderh n da yake magana , tabbas itace ,saboda yace muna kama ba kaɗan ba .... Dafe kai Aaliyah tayi tana rushewa da kuka mai taɓa zuciya. Shine wanda Adda Hauwa zata yi fushi dani akan sa , Wayyo Ni Aaliyah , Me yasa Zaka shigo mun rayuwa ta . A haka ta wuni tana kuka har aka fara korar sallar subahi .
**
Kaman yanda Aaliyah idanun ta suka gagara rintswa haka ɓangaren Aydaaannnnn ,duk dashi na farin ciki ne ,duk ya kosa safiya tayi a taho masa da Matar sa ,wanda yake ganin Abun tamkar a mafarki . Sai bayan ya dawo sallar subahi sannan ya rintsa , inda a barci mai dadi ya dauke sa . A cikin barcin sa ne yayi mafarkin Aaliyah ta haifa masa cute bby girl , Wanda sukayi kama sak har daƙwa²n idanun . A haka ya tashi cikin matsanancin Farin ciki , Privacy ya nufa don lokacin ƙarfe Goma na safiya . Bayan ya kamala karin kumallo sa ne , ya mike tare da nufar Ɓangaren Ammiee Anan yake jin tun Safe An tura Jirgin yawo Heliƙwafta na malam bahaushe don dauko Amarya . Hajiya Barmani tace bata buƙatar Ganin dangin Aaliyah ko mutum daya ,wannan ne yasa Momy Rahina Da Momyn Aaman su kadai tafiya don ɗauko Amarya , jirgi suka bi don zuwa Garin Yobe.... To ko ya abun xaya kaya.....!
#Mmn teddy*Don Allah don darajar Allah ki taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi , kema Don Allah kar ki karanta mun Indai baki biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani ba Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya siyan Data na WhatsApp ,to kam tabbas zaki iya cire ₦300 dai ki saya littafin The Sexxies House ƙaramin group kenan , Vip group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .*
24
Nufar Ɓangaren Hajiya Barmani Aydaan yayi don Abba ne ya kira sa yana Sanar masa da Abun da bai san dashi ba sai a Wannan lokacin ...Wai Hajiya Barmani ta ce " Ba za'a kai Aaliyah Sabon Estate din su ba , Anan Gidan Zata zauna a ɓangaren sa. Wannan yasa Shi nufar Ɓangaren Hajiya Barmani , inda da Shigar sa ya tadda Summy Hibba , da Sauran ƴammatan Gidan . A'a Aydaaannnnn Ango na . Kallon Hajiya Barmani yayi kamin yace " Waye Angon naki? . Murmushi Hajiya Barmani tayi kamin tace " To ƙwarai ni kuwa , Don babu Abun da zaka nuna mun ƙuruciyar ma na Fika. Ran sa ba Dadi ya shigo Falon nata ,amma jin Wannan maganan nata yasa shi Darawa tare da cewa " Humm To Ni Angon Aaliyah ce. Saurin kallon sa Sumayya tayi yayin da Hajiya Barmani tace " Akul kar Wannan ya ƙara fitowa daga Bakin ka na haneka Kul". Kai Angon mata biyu ne , Yau dai za'a Fara kawo wacce kake kallon ta a mata , don Ni nasan Waye Talakawa da mugun abu ,babu Mamaki an gama da kai ne ,an kai sunan ka an tsaface ka Allon Ƙarfe . Ɗago da Lulun idanun sa yayi yana sakin mawa Hajiya Murmushi bawai don bai ji zafin maganan nata ba a'a . Sumayya itace Ƴar gata kuma Ƴar dangi ƴar uwar ka ta jini ba Wancen abun ba da ba zata taɓa nuna .... Hajiya Don Allah ki bar wannan maganan .! Ni bashi ya kawo Ni wurin ki ba ". Ƙwazin.! Hibba ta kira Sunan Aydaan cikin Sanyin murya tana Ɗago da idanun ta tare da kallon Aydaaannnnn . Ina jinki ,yayi maganan yana Bin fuskar ta da kallo .
Ƙwazin Wannan Abun da kake is not Good , Bai dace ba , Anty Summy tana Son ka ,me yasa kake kokarin fifita Soyayyar Ƴar aikin mu akan na jinin ka? Mun taso tare , Tun muna yara muke So da ƙaunar junan mu , but Why now zaka ce baka Son jinin ka ko nace kana fifita wacce Da ita da Dabbobin gidan nan basu da mara ba . Don dabbobin mu sun fi mana ita amfani , su ko ba komai zamu yanka muci Namar su tayi mana Dadi. Ita kuwa fa? Sai dai ƙarin Ɗawainiya da Jidali iyaye.....Keeeee..! Ya Wani daka mata gigitaccen Tsawa wanda tun da take dashi bai taba masu irin wannan Tsawan ba ,don ko ina na Wurin sai da ya amsa . ina Wasa dake ne?? Ni sa'an Wasan ki ne? , Saurin girgiza Kai Hibba tayi tana kokarin sa kuka , Kamin yayi magana ne Summy da ta gama tunzura tace " Saboda An kawo aibun ta shine kake Wannan maganan ? Ai maganan Hibba gaskiya ne , Nima kamin Tsawa amma sai dai ta tsaya iya nan don babu duka ". Saboda me kika ce haka? Yayi maganan yana maida kallon sa ga Summy dake farfar da ido na musifa . Saboda Ni Yayar kace ,bakai ne ka riƙe mun hannu ba a yarinta, nice Wacce na kama hannun ka kana yaro mu tafi makaranta , Aydaaannnnn baya na ya goya ka ba sau Ɗaya ba Sau biyu ba... Soyayyar ka jarabta ta ne a gare Ni ...a kullum bani da burin da ya wuce na ganni tare da kai , amma kai da yake butulu ne mai manta alheri , kasha faɗa mun baka SO na sau nawa ? . Me yasa me yasa Aydaaannnnn duk matan duniya ka rasa wacce zaka hada Ni kishi sai Aaliyah?? .
Saboda Ina Son ta , kuma ba zan daina Son Aaliyah ba har ranan da zan ban doraar duniya , saboda ina jin ta tamkar jini na dake gudana cikin jiki na.' Hajiya Aaliyah zasu sauka a yau a cikin gidan nan ,amma ban yi Alƙawarin zan barta takai gobe ba ,ba tare da na Kaita Gidana . Yana Gama Faɗin haka kamin Hajiya Barmani tayi magana ya juya fuuuu yana barin Falon .... Zuciyar sa na masa Wani irin Zafi ...zaki maimaita ke yayata ce ,tabbas sai kin maimaita wannan kalmar , Kuma zaki sha mmkin Waye Ni Aydaaannnnn , baki Sanni ba har yanzu.
Bayan fitan sa ne Hibba ta kalli Summy tana cewa " Anti Summy you make a mistakes , Maganan ki yayi kaushi da yawa ,kin san Fa Waye Ƙwazin? Baya da kirki ,baki masa ba ma yayi miki bare kin masa . Na tausaya miki kar ki manta yau saura kwana nawa ne ? . Ni nafi So Aydaaannnnn ya kashe Ni na bar duniyar na Huta . Jin Haka yasa Hajiya Barmani cewa " A'a fa , sam duk bata kai ga Hakan ba Sumayya , Ni dai kawai abu daya zaki mun yana miki abu ki rabu dashi , idan kin zo ki faɗa mun ,zanyi maganin tijarar Wannan yaron , Rashin kirkin Aydaaannnnn yayi yawa , daɗi na dashi Daya shine yawan Sadakan shi da Tausayin marasa Ƙarfi . haɗa ido duka suka yi sai kuma suka yi shiru a zuciyoyin su kowa na fadin " Baki san Waye Shi Ɗin bane , Ai dole ya rinƙa Wanke zunuban sa da Sadaka ."
**
Ɓangaren Aaliyah Kuwa Tamkar ba Amarya ba ,babu ado babu gayun nan na Amare , Kuka take tun da Suka taho har suka Sauka . A ganin ta wannan ba Aure aka yi mata ba sayar da ita kawai akayi ma Aydaan . Haushin Ahalin yanzu da kuma tausayin kan ta take yi , Don bata san wani irin tsana suka yi ma Talaka ba sai a yau , Sun ɗauke ta tamkar baiwa haka suka ce Babu wanda zai biyo ta a dangin ta wai daga baya mai bukatar ganin ta ya zo . Tuno da nasiha n Abba da kuma na Inna ,Umma ya sata cigaba da rera kukan ta a hankali , Gyefe guda na zuciyar ta tana faɗin Na shiga Uku na . Don tun da take kukan Su Hajiya Rahina Momy Muhibba Babu Wanda Ya tankata har suka sauka a farfajiyar Gidan .... Umman Mubarak ne da Ammie suke a farfajiyar Estate din don anan Heliƙwafta Nasu ta sauka da misalin 7pm . Sunan garin yayi duhu ne amma kuma ko ina na harabar gidan tamkar Rana yake haske ya haskaka ko ina . Cikin Sauri Umman Mubarak ta ƙariko tare da kama Aaliyah , Eyyya Come on Baby shiiiii..... It's Okay Dirling . Ta ƙare maganan tare da rungumo Aaliyah jikin ta tana rarrashin ta tare da shafa bayan ta . Tun yaushe take kukan ne ? Umman Mubarak tayi maganan tana kallon su Hajiya Rahina ,wanda ta tabe baki ,Momyn Hibba ne a takaice tace " A haka muka same ta ,muka kuma dauko ta . Oh ...! Ya isa kewan Gida ne ,kin san Abun ka ga Yaro . Umman Mubarak tayi maganan cike da Gogewa Don duk matan gidan ta fisu Gogewa da sanin duniya . Ita da yake ƴar siyasa ce don shekara daya kenan da saukar ta a kujerar sanate , don haka ta saba haba² da Al'umma talaka ko mai kuɗi . Murmushi Ammie tayi tare da cewa " To ko a kira Aydaaannnnn ne ? . Cikin Sauri Umman Mubarak ta amshe ta da Cewa " Of course yess, Saboda tafi sanin sa ƙila shi ya rarrashe ta tayi shiru .
Haushi ne ya kama Momyn Hibba nan take tace " Don Allah ku bar yaro ya huta ,kar ku manta yanzu fa suna can suna kujiba² na Auren su saura ƙwana shida ne , So ai ita ba ƙaramar Yarinya bace sai kace Hibba ,ko Hibba zan kai Ɗakin Aaman ba zata yi ya kukan nan ba haba Don Allah.! Caraf Hajiya Rahina ta amshe da cewa " Tare mun da hanya yar Gari haba . Ammie ne ta kalle su kamin tayi magana Umman Mubarak tace " Hibba tafi shekara ashirin da biyar , Wannan fa ko Ashirin bata hada ba She's not up to 18yrs yarinya ce ƙarama ƙarama kuwa . Don Allah dai kawai ku bar wannan maganan , yanzu mu zamu wuce da ita Apartment din Aydaaannnnn , ku da kuka Hajiya Rahina kwa sanar mawa da Hajiya Barmani Amaryar ta iso . Ammie tayi maganan tana kama Hannun Aaliyah tare da barin Su Hajiya Rahina nan a tsaye . Duk Abin da Aaliyah ke ji nasu bai ɓata mata rai ba don itama ba Auren take So ba . Kawai don yafi ƙarfin ta ne yayi mata fin karfi a cewan ta . Tunanin Adda Hauwa ke sata kuka don ko sallama bata so sunyi ba tun wannan maganan da ta faɗa mata . Ina Son ki Adda , kuma zanyi biyayya a kalaman ki inshallah.....!
#Mmnteddy*🕊️SEXXI'ES HOUSE🕊️*
(Love and romantic story)
*Don Allah don darajar Allah ki taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi , kema Don Allah kar ki karanta mun Indai baki biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani ba Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya siyan Data na WhatsApp ,to kam tabbas zaki iya cire ₦300 dai ki saya littafin The Sexxies House ƙaramin group kenan , Vip group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .*
25
Ɓangaren