Showing 33001 words to 36000 words out of 78289 words

Chapter 12 - SEXXI'ES HOUSE COMPLETE DOCUMENT Book by Maman Teddy .txt

19 Dec 2024

6959

tace " Aydaaannnnn ka gani ko? Wallahi Ni nasan haƙƙin ka ne ke bibiya ta, Aydaan...... Ke Rufe mun baki koma ciki , Baba ya katse Jidderh dake fashewa da kuka . A yau zan sa a kira Salisu ya koma dake gidan sa .bazan yarda da Wannan shashashun yaran ba .!




Idanun Aydaaannnnn ne suka kaɗa ,hannun sa har Rawa yake na ɓacin Rai . Wanda Ganin haka yasa Aaman kama shi yana cewa " Aydaaannnnn mu wuce , ma dawo next time". Ran sa a ɓace baya jin komai sai sautin kukan Jidderh......!






Gn*Don Allah don darajar Allah ki taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi , kema Don Allah kar ki karanta mun Indai baki biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani ba Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya siyan Data na WhatsApp ,to kam tabbas zaki iya cire ₦300 dai ki saya littafin The Sexxies House ƙaramin group kenan , Vip group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .*


Suka nufi Moton yayin da Baba ya banzama yayi na cikin Gida ransa a matuƙar ɓace , Tun daga Zauren Gidan yake Faɗin ,daga Fitowar ki Hauwa shine har kin Sanar masa yazo ku cigaba daga inda kuka tsaya? Dama Ni tuni nake zargin ki Hauwa ,yau kuma gashi zargi na ya tabbata . Banda iskanci yau ko ma Saki uku Salisu yayi miki ai idda kike yi , shine zaki fara Kula wasu maxan . Subhanallah Malam mai kuma ya faru? Umma tayi maganan tana Ɗagowa tare da kallon Baba da ya sauke Wular kansa yana sababi . Ina Hauwan take? Yayi maganan ba tare da yaba Umma amsa ba . Hauwa.! Ya fara ƙwaɗa Kirar Hauwa Ransa a matuƙar ɓace . Saurin fitowa Hauwa tayi jikin ta Ko ina Rawa yake yi na tsoro , Zubewa tayi hawaye na bin Kuncin ta , cikin matsanancin kuka take fadin " Baba Don Allah kayi Hakuri , Wallahi ban san waya faɗa mawa Aydaaannnnn wani Abu ba, Kuma bana tunanin yasan komai dake tsakani na da Salisu . Rufe mun baki Shashancin Banza da Wofi , bai sani ba yazo kofar Gidan nan yau ? Rabon shi da Gidan nan shekara nawa? Eiyee?? Tun lokacin da kikayi Aure tsawon shekaru goma bai kara saka ƙafarsa a kofar gidan nan ba ,sai yau tun da kina shirin zama bazawara . Hauwa ki sani Aydaaannnnn ba zai taba Auren ki ba , saboda yafi ƙarfin ki ,yaudara ce kawai ta ya'yan masu kudi ,ya gama dake ya barki Fanko . Haba Malam haba malam ... wannan Abun naka yawa yake yi Wallh . Me kike nufi to me ƴa? Naga dai bake kika haifi Hauwa ba, Hauwa jini nace don haka kome zanyi akan ta kisa mun ido .




A'a gaskiya saka idon yayi yawa , Gaskiya na gaji , Hauwa fa Allah ne ya bamu it....Wayyo Umma don Allah kuyi hakuri,kuyi Shiru Umma .... Hauwa tayi maganan tana Rushewa da matsanancin kuka tare da cigaba da cewa " Baba zan koma Gidan Salisu ,wallahi zan roƙesa . Kinji maganan gaskiya nan , Baba yayi maganan yana cigaba da muzurai .


***


Kai Aaman Kar ka tafi bazan iya barin Ƙofar Gidan nan ba tare da na ji Muryar Ta ba , Ina Son Jidderh , Don Allah ka dakata , zata fito Ni Na sani . Dakatawa Aaman yayi daga Driving din da yayi niyya ,cike da jin matsanancin Tausayin Ƙanin nasa Ya ce" Aydaaannnnn Kana Son Hauwa ,Amma kuma tun farkon Rayuwar ka bata taɓa nuna maka So ba ,sai Wahala....Me ya kawo Aaliyah nan? Muryar Aydaaannnnn ya katse Aaman wanda shima yayi saurin juyawa Yana kallon inda Aaliyah take tsaye tare da mai adaidaita . Sallamar mai adaidaita tayi tana ɗaukar Ghana most go ɗin ta tare da nufar Gidan Su Hauwa . Innalillahi wai'inna ilaihir raji'un me take anan? Me ke shirin faruwa ne? . Abun da Aaman ya furta kenan wanda kamin yayi magana Aydaaannnnn ya fice daga Moton yana nufar inda Aaliyah take cikin Sauri da sassarfa .




Caraf taji an riƙo Hannun ta wanda yasa Aaliyah saurin juyowa tana kallon bayan ta , Waro ido waje tayi tare da masa Kallon nashiga Uku . Aaliyah.! Ya kira sunan ta cikin wani irin sanyi ,wanda tun da take bata taba ganin sa a irin Wannan yanayin ba." Yallaɓai Aydaan me nayi maka? Har nan ma ka biyo NI? Aaliyah Aaliyah Jidderh ta?. Wani irin kallo tayi masa kamin tace " Wacece Jidderh kuma? Don Allah Aydaaannnnn ka rabu dani , Meye ka Ɗauke Ni wai? Ni Bazan Aure ka ba shi yasa na Taho gidan Wan mahaifiya ta , Saboda Nasan shi da halin sa idan ya tsaya akan Gaskiya babu mahalukin dake dakatar dashi duk kudin ka duk girman ka . Tsayawa Aydaaannnnn yayi yana juya maganan Aaliyah a kan sa ....kamin ta fixge hannun ta tana wuce shi da sauri . Keee .! Ya kira ta a gadarance da izza . Ni mijin ki ne kin manta ne ko sani ne baki yi ba? Ai aure an riga anyi shi ,saura tarewa nan da kwana biyu. Naga mai hanani tafiya da matata ....!
#Mmn teddy
#morning Update*Don Allah don darajar Allah ki taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi , kema Don Allah kar ki karanta mun Indai baki biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani ba Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya siyan Data na WhatsApp ,to kam tabbas zaki iya cire ₦300 dai ki saya littafin The Sexxies House ƙaramin group kenan , Vip group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .*




22


Cak ta ja ta tsaya , wani irin murmushi ya saki tare da cigaba da cewa " Sannan magana ta gaba , wannan maganan da kika faɗa mun zaki maimaita mun shi nan da ƙwana biyu sai kin maimaita gani ga ki ....Kallon sa tayi rasa Abun da zata ce masa abun ka ga yarinta kawai sai ta fashe da kuka tana cewa " To kawai yanzu gani Yallaɓai ka kashe Ni ka huta dama haka kake so . Ai tun tuni ka faɗa mun idan muka yi Aure Wahalar dani zaka yi .... Shiii ya zaki rinƙa ihu haka ,a kan hanya kaman ba mata da miji ba? Yayi maganan yana mata wani iri kallo na kin san Sauran ,sai kuma ya cigaba da cewa " matsowa kusa Zaki yi , amma idan ba zaki iya ba ai ba wani Abu bane ,Ni sai na matso kusa da matata ... Yayi maganan yana matsowa daf da ita ,har suna jiyo daukar numfashin juna . Yauwa ko kefa Nur Albi . Ko da mijin ki ya ɓata miki rai har rungume sa zaki iya yi ba wani damuwa ba ne ? . Wani irin kallo tayi masa A hasale don ta lura ya maida ita kaman yarinya yar shekaru tara , wannan yasa ta a zafafe cewa " Kaman ya kenan ?. Kamin ta rufe baki dama neman hanyan da zaiji Sanyi a zuciyar sa yake yi , ita dai ji tayi ya sa hannun sa yana jawo ta jikin shi tare da Rungume ta yana sauke ajiyar zuciya da cewa " Kaman haka mana ,sai Kiyi ta mawa Aydaaannnnn ɗin naki kukan shagwaɓa Ni kummm....jan ye jikin ta tayi da Sauri tana waiwaigawa gyefe² kar yazo Wasu sun gansu masu wucewa . Kallon sa tayi tana buɗe Baki zata yi magana ,sai kuma ta rasa me zata ce masa ,kawai sai ta fashe da Kuka .... Saurin sa hannun sa yayi yana Warewa tare da cewa " Oya Come lemme Hug you...! Da gudu ta juya tana shigewa Gidan ,tana jin Muryar sa yana cewa ' Ki gaida mun da Baba .


Aaman dake can Jikin Moton su yana kallon duk Wani Abu da ya faru tsakanin su , Dariya yake yi sosai kaman zai kifa a sarari yana furta " Aydaaannnnn you're d arrogant boss , Wallahi kana damun ƙanwata da Yawa fa?. Murmushi Aydaan yayi yana jin Sanyi a zuciyar sa , duk damuwar nasa ya nema ya rasa . Sau da yawa yana mamakin kan sa ,a kowani irin hali yake ciki ,yana ganin ta ko jin Muryar ta yayi sai ya nemi ɓacin Ran nasa ya rasa. Ƙwazin mu Wuce mu koma gida ." Gida kuma? Ai na dauka yanzu Gidan su Amaryar mu muka nufa? . Murmushi yayi yana sa hannun sa tare da shafa Sajen fuskar sa tare da cewa " it's remain 2 days a kawo mun ita gida na , naga Ƙarshen Tsiwan nan nata . Dariya Aaman yasa kamin yace " To don Allah Abi ta a hankali, I know you very well, Nasan yanda kake gurzar mata , kake masu caka² ,amma wai duka su Momy fa har yanzu Ganin na Allah suke maka . Kallon sa Aydaaannnnn yayi yana sakin Murmushi tare da lumshe Lulun idanun sa yana buɗe su a hankali , babu Abun da yake Hangowa sai a ranan da aka kawo masa Aaliyah gidan sa . Bazan manta da Wannan Ranan ba.! Yayi maganan yana kallon Aaman da suna haɗa ido su sun san Yaren nasu , Kecewa Da wani irin Dariya suka yi ,wanda tun da nake ban taɓa Ganin sun yi irin ta ba .


Mu tafi Yanzu Please , naga Kirar Ammiee yanzu. Okay so you can call her back so that muji dalilin Kirar nata ko?. Kirar Numbern Ammiee Aydaaannnnn yayi inda buga daya biyu ta ɗauka cikin Muryar dan tashin hankali ,wanda daga Ji yasan babu lafiya yaji tana cewa " Aydaaannnnn kana ina ne? Kazo Gida yanzu yanzu don Allah.! Cikin Sauri ya furta " Ammiee lafiya? Meke Faruwa?. Humm numfasawa Ammiee tayi kamin tace " Lafiya ba lafiya ba , Sumayya ce babu lafiya ,kasan ciwon ta ,kuma taki yarda kowa ya duba ta sai kai wai zaka Duba ta. Wannan wacce irin yarinya ce mai masifar taurin kai ? Taurin kan nata har a lafiyar ta ma sai tayi shi?. Akul Aydaaannnnn Sumayya fa nace maka ba Hibba ba? . Sumayya yayar kace kake kira da yarinya? . Kallon sa Aaman yayi da duk yaji mai ke faruwa shi da yake Gyefe . Alama yayi masa da ido akan yace gasu nan isowa yanzu . Wanda hakan Aka yi , I'm sorry Ammiee , yanzu zamu taso . Datse Kirar Ammiee tayi yayin da Aydaaannnnn ya kalli Aaman dake kallon sa shima .




Amma fa kai dan rainin Wayo ne 🙄 Summy ce Yarinya , saboda zaka Aure ta ko? Allah mun gode maka da baka fito a babban mu ba , da wannan mulki naka da Son girma mun shiga uku . Murmushi Aydaaannnnn yayi kamin yace " Ƙwazin yi sauri kasan bata da lafiya tun ba yau ba . Fara barin layin suka yi kamin Aaman yayi duba ga Aydaaannnnn yana cewa " Amma me ya kawo Aaliyah gidan su Jidderh?. Dan taɓe baki Aydaaannnnn yayi kamin yace " Ban sani ba ,Amma zan sani nan gaba inshallah .


**


Aaliyah..! Aaliyah Abba ya fito daga Ɗaki yana Kirar sunan Aaliyah ,wanda Inna Turai tayi tsimi ta rasa bakin magana don ta lura Aaliyah bata cikin gidan nan ,kuma tasan a halin da ake ciki babu inda zata je da Ya wuce gidan Umman Hauwa . Ina Aaliyah take ne? Abba yayi maganan yana kallon Inna Turai , kamin tayi masa magana ne ƙaramar Wayar sa ta fara ruri , duk da yayi mamakin ganin sunan mai Kirar ,amma a haka ya daga cikin faraa tare da cewa " A'a Malam Barka da Rana . Barkan ku dai . Kamin Abba yayi magana Baba ne yace " Aaliyah tana nan Wuri na ,babu mai mata Auren dole . Ƴa tace ". Murmushi Abba yayi tare da cewa " To to Malam , Yanzu bani Aaliyah muyi magana . Cikin zafi Baba yace ita kadai nake Gani na tuna da Mahaifiyar ta ,don haka ba zaku kashe ta ba itama . Jinjina kai Abba yayi yana dannewa tare da cewa ' Haka ne Malam kaba Aaliyah muyi magana . Aaliyah Ƙarana kika kai ? , To ki dawo Gida . Shine Abun da Abba yace tare da katse Kirar . Tsayawa Inna Turai tayi tare da cewa " Malam Aaliyah zata dawo dai ko? . Shiru Abba yayi kamin yace " Inshallah .


**




Ɓangaren Aaliyah kuwa bayan rabuwar ta da Aydaaannnnn , Da gudu ta shiga Gidan Baba tana Cin karo da shi yana sababi , Hauwa tsugunne , Umma itama na sharce Gumi . Nufar Hauwa tayi da Gudu tana faɗawa Jikin ta tare da cewa " Adda Hauwa ,Adda Hauwa nayi..... Kasa ƙarike maganan tayi ganin Baba a tsakar gidan . Hauwa ne ta Ɗago Aaliyah cikin Sauri tana shafa fuskar ta tare da cewa " Aaliyah ta meke Faruwa? Kukan me kike yi?. Kamin Aaliyah tayi magana ne Baba yace " Kema idan kishiyar Uwar taki ta dame ki tattaro kayan ki ,Kiyi zaman ki anan . A'a Malam ba'a yi haka ba? Ba fa muji meke damun ta ba ? Kuma yanzu Turai ta sauya ,tana Son Aaliyah da duk jinin Abba a yanzu . Umma tayi maganan cikin Sanyi , Aaliyah me ya faru? Ta tambayi Aaliyah cikin nuna kulawa . Umma Auren dole Su Baba Salihu suka Ɗaura mun da Wani .... Aure.??? Baba yayi maganan cikin ɗaga Murya , ina wannan bazata saɓu ba.!
#Mmn teddy*Don Allah don darajar Allah ki taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi , kema Don Allah kar ki karanta mun Indai baki biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani ba Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya siyan Data na WhatsApp ,to kam tabbas zaki iya cire ₦300 dai ki saya littafin The Sexxies House ƙaramin group kenan , Vip group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .*


23




Baba ne ya kalli Aaliyah yana cewa " Tayaya zasu yi miki Auren Dole , idan suna taƙama su iyayen ki ne ,nima matsayin Uba nake a wurin ki koda bani na kawo ki Duniya ba . Malam ka bar wannan zancen don Allah , Aaliyah faɗa mana ke kin san yaron ne ? . Kallon Umma Aaliyah tayi kamin tace " Eh na san shi ,aikatau nayi a cikin Gidan su ,har part ɗin shi ma ... Nan Aaliyah ta fara basu labarin Aydaan , Wanda tun da tace Gidan Moddibo Hauwa ta fahimci Wane ne . Shiru tayi tana jin Wani irin yanayi tsikar jikin ta na tashi . Sai da Aaliyah ta gama maganan ne Baba ya dafe kai yana cewa " Wannan tabbataccen Yaron Suka Wanke ki suka miƙa masa? Tabbas zaki dawo ba'a hayyacin ki ba Aaliyah , kuma Indai ina da Rai ba tare da amincewar ki ba bazan taba yarda a miƙa ki gidan Aydaan Moddibo ba . Tsayawa Aaliyah tayi tana Son tambayar Baba dama yasan Aydaan ne ? Sai kuma tayi shiru tana nazarin kalaman sa. Ita dai a wannan lokaci taji yana mawa Abba Sababi ne ta Wayar sa , wanda kamin tayi Aune taga ya mika mata Waya suna magana da Abba . Jiki a sanyaye ta mike tana cewa ' Baba Bari na koma.! A'a Aaliyah ki taho dakin Umma ko ruwa ki sha kamin ki tafi . Wani irin kallo Baba ya watsa mawa Hauwa , Wanda tayi Saurin kasa da kan ta . Kama Hannun Aaliyah tayi tana shigewa Ɗakin Umma da ita .


Aaliyah ne da shigar su ta fara neman wurin zama ,wanda kamin ta zauna Hauwa tace " Ke dakata.! Bana kirawo ki bane don ki zauna ... Aaliyah kalli idona ki faɗa mun matsayina A wurin ki . Cike da mmkin sauyawan Hauwa Aaliyah idon ta na cikowa da Ƙwallah tace " Ke Adda ta ce , Yaya na Uwa ɗaya uba ....ya isa ban tambaye ki wannan ba . Kin san da hakan ? Hauwa tayi maganan tana kallon Aaliyah wanda tayi saurin gyada Mata Kai . Motsa Baki Hauwa tayi tare da fara cewa " ke da Bakin ki a kwanakin baya kika taho kika same ni da cewa " Na faɗa miki duk wani Abu da zai ɓata mun rai game dake ,domin ki kiyaye ,nace miki babu komai, To Aaliyah yanzu Akwai . Na'am Adda Hauwa me nayi miki? Aaliyah tayi maganan tana narke mata ,domin tana Gab da fashewa da kuka . A'a bance kimun kuka ba , Aydaan .! Ki sani idan kika kuskura ko sau Ɗaya kika ɓata ma Aydaan tamkar Ni Hauwa kika yi mawa , Haka idan kika guje shi kusani tamkar Nine kika guje mawa." Aaliyah idan kika azabtar da Aydaan Wallh bazan yafe miki ,ki fita ki bani Wuri Kiyi duk Abin da kikayi niyya .




Fashewa da Kuka Aaliyah tayi kamin ta juya da Gudu tana ficewa daga Ɗakin ko sallama ba tayi mawa su Umma ba ta fita tana kuka . A hanya sam kan ta ya kulle ,me Adda Hauwa take nufi? Shin tasan Aydaan ne? a'a Babu ta yanda Za'ayi Tasan shi . A haka ta isa gida ,tana shiga Ta nufi Ɗakin Abba . Zubewa tayi har ƙasa tana basa Haƙuri tare da cewa " Na tuba Abba , na amince Wallh zan masa biyayya zan zauna da Aydaan ,amma kuce Adda Hauwa ta daina fushi dani Don Allah. Inna Turai ne ta riƙo ta tana cewa " Ita Hauwan ke fushi dake ? Gyada Mata Kai tayi tana fashewa da Sabon kuka . Dafa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login