Showing 21001 words to 24000 words out of 63481 words
Chapter 8 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt
ta zare idanu waje ta ce "A'a ki fara samun mai kamfanin ku yi magana dashi tunda ke ce Manager" "Sai yanzu na fara tunani, i wonder aka bani Manager a kamfanina bayan akwai maza da yawa sosai da na yi tunanin ko experience ɗina ne yanzu kawai na ji ina zargi"
"Zargin me?"
Ta ɗaga kafaɗa ta ce "I don't know, na fara bincike dole zan gano gaskiya" Kinal ta ce "To ki bi a hankali Please Fiyya we care about you ni ma zani anniversary na makarantarmu FGC dana shigo Kamfanin gobe, har waƙa na yi mana yanzu haka wani Eng Ali wali na yi wa waƙar da aka saka ni" shiru Fiyya ta yi tana nanata sunan FGC a ranta "Na ji kamar na san makarantar nan fa"
"Ke da ba ita kika yi ba ina za ki sami, ni a can na yi secondary school kinga"
"Haka ne bari na je"
"To ki kula Please kar ki saka kan ki cikin matsala don Allah Fiyya" murmushi kawai Fiyya ta yi tana ficewa daga cikin studio ɗin.
*****
Kamar an cillo shi haka yaga Mai dawa ya faɗo masa cikin office ɗin nasa da yake tare da manyan mutane sosai tun kafin ya yi magana ya ce "Kowa zai iya tafiya" duk suka fice ya ɗaga kai ya kalli Mai dawa ya ce
"Ka daina zuwa ina nake ni zan dinga neman ka"
"Ka yi ƙarya"
"Ni nake maka ƙarya Mai dawa?" Ya wani haɗe fuska tamau fuskarsa ɗauke da sabon yankan da aka yi masa jiya har yanzu ba'a gyara ba. "Kai ai ba Malam Abdullahi bane da ba zan ce kana ƙarya ba"
Eng Ali wali ya jinjina kai ya ce "Me ya kawo ka yanzu? Har cikin office nawa"
"Ka saka ni aiki har biyu, da kamo maka ɗawar can da nemo Scorpio" ya shagiɗar da baki gefe ya yi fito wanda ya cika office ɗin sosai "Na je gidan asawanta jiya"
"Kana nufin gidan Abdu Marafa?" Ali wali ya ce yana miƙewa tsaye cike da tsoro Mai dawa ya ɗaga ƙafa ya ɗora a saman table ɗin gaban Ali wali "sharaɗin kawo maka ita barewar shi ne mallaka mini kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY, aikin Scorpio kuma ka saka cinnakunka cire hannu daga sabgar ka bar mini ni zan nemo maka shi, bana haɗa aiki da wasu"
Ali wali ya ce "Mene haɗina da kamfanin nan? Karka saka ni rigimar da tafi ƙarfina da ka san ma'anar abin da FS WORLD INVESTMENT COMPANY yake nufi ba zaka haɗa kan da shi ba, wannan Kamfanin ciwon idanu ne" Mai dawa ya ce "Ni Mutallab Tahhb ɗan babana Abdullahi da inkiya Mai dawa bana harin abu na haƙura, wannan kamfanin shi ne burina" Ali wali ya goge zufa ya ce "baka san kamfanin ba shi ya sa a ba ki yake maka wahalar faɗa ni Ali wali sabgar siyasa na sani na saka gaba, ka bar ni a haka ba zaka saka ni a masifa ba"
"Waye mai kamfanin?"
"Sannin hakan daidai yake da tunuwar asirin manyan mutane da dama, ka bar komai yadda ka sani" jinjina kai Mai dawa ya yi ya ce "Zan maka jahilanci ne, ka riƙe amana ka bi sharuɗan da na ce zan maka komai ni ɗan daba ne kai mai neman iko da muƙa mi ni na sare na kashe mu bauta maka shi ne. Batun kamfanin zan yi bincike da kai na, kar ka zama butu don wallahi sai na yi maka daƙiƙanci"
"In sha Allah, daga nan har bayan zan yi maka komai"
"Dar zan doƙa yanzu sai godiya"
Yana fita Eng Ali wali ya ɗauki waya ya kira Csp ya ce "Waye Mutallab yaron da ya fito daga wajan state cid kwanan nan bayan ya yi shekaru uku a wajan su" ta cikin wayar Csp ya ce "Sunan shi dai Mutallab ya kashe matarsa aka aka kama shi, daga baya kotu ta sake shi a zama na ƙarshe ba wanda ya san dalili" Ali wali ya kashe wayar yana sauke numfashi a fili ya ce "waye MUTALLAB?"
For more information
08164069385
WhatsApp only.[10/11, 9:21 PM] Nanameera: *❤🔥 MUTALLAB ❤🔥*
Page 7
*Bright pens... 2nd batch🔞*
The door is open... Ga masu buƙatar ayi musu tallah. Na hango wasu ƙwailaye a conversation group da Mikiya writers 😛Maman Sayed ta ce a faɗa muku akwai maganin gargajiya cikin sati guda komai zai kankama haɗaɗɗan maganin da Fiyyar Ashraf ke amfani da su ta ce a baku numberta ba... 08063114606
Washegari da safe Fiyya na ƙoƙarin buɗe ƙofa ta fito da nufin zuwa office ya rigata buɗe ƙofar, kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kan ta zuwa gefe a hankali kuma can ta ce "Ina kwana?" bai amsa ba sai cewa da ya yi "You told Abba za ki wajan wata, amma kin yi ƙarya ina kika je?" Manyan idanunta ta ɗago ta kalle shi ta ce "Ƙarya kuma?" Ya rufe ƙofar ya tsaya "Idan kina yi mini kamar ba ki gane ba, kwaɗa miki mari zan yi maybe it will help you to understand it very well" ita mamakin shi take yi "Ni fa Manager ce business zai iya fitar dani ko'ina" ya buɗe mata manyan idanunsa sosai sai kuma ya ce "ina kika je" ta tura baki gaba sosai ta yi gefensa za ta shige ya saka hannu ya fisgota kafin ta yi motsi ya ɗago fuskarta ya wanka mata mari ƙwayar idanunsa tamkar zata fito waje yana ihu a saman kan ta ya ce "Idan na sake maimaita miki tambayar sai na tabbatar yatsun hannuna sun kwanta fuskarki"
"Sai dai ka kashe ni" ta yi maganar ko gezau gefen fuskarta ya yi jajur dakakkiyar zuciyarta kuma ya saka ta nuna ko a jikin ta, ƙasan zuciyarta kuma wani zafi da raɗaɗi take ji "ni kike cewa na kashe ki?" Hannu ta saka zata ƙwace nata hannu idanunta cikin nasa ba tsoro ta ce "Me kake so na yi maka? Ka shigo kana tambayata abin da ban sani ba, ka saka hannu ka mari fuskar da kullum nake shafa mata mayuka masu tsada, ni ka mara ban maka komai ba, tunda ka tsane ni ka kashe ni kawai" da ƙyar ta iya ƙare maganar saboda muryarta dake rawa Captain ya saka hannu ya sake ɗauke fuskar Fiyya da mari yana huci ya ƙara ɗaga hannu zai mare ta cikin sauri ya tsayar da hannun nasa ganin hancinta na fitar da jini sosai kuma yaƙi tsayawa.
Ta yi masa ƙuri da idanunta da ruwa ya kwanta a ciki, jinin kuma bai fasa zuba ba daidai nan aka buɗe ƙofar tare da shigowa ciki da sauri Fiyya ta nufi wajan Daddy ta riƙe shi tana fashewa da kukan dake cin ran ta jikinta har wani irin rawa yake yi da ɓari jinin dake fita a hancinta kuma ya shiga ɓata masa farar rigar jikinsa. Daddy ya juya ya kalli Captain daya haɗe fuskarsa "Aliyu me ka yi mata?"
"Ni kuma?" Ya tambayi daddy irin bai ma san me ya faru ba "To ita da waye haka ji bi yadda take kuka hancinta na jini kuma kai na gani a ɗakin, dole kasan mene ya faru" cikin damuwa daddy ya yi maganar wacce sai da ta bayyana saman fuskarsa ya ɗago Fiyya yana duban ta sosai ya ƙara kallon Captain
"Maama wannan jinin fa? Daman kina yin haɓo ne wani abun Aliyu ya yi miki?" Ita dai Fiyya taƙi cewa komai sai shassheƙar kuka take yi numfashinta na yin sama, Daddy duk ya rikice baya wasa da al'amarin daya shafi Maama ko kaɗan a ƙasan zuciyarsa yake jin soyayyarta ya kuma tabbatar ita ce rauninsa Fiyya kawai za a taɓa a iya nakasta rayuwarsa. "Ya isa daina kukan haka nan, Allah Ya nuna mini sati mai kamawa ki tafi gidan mijinki ni ma zan fi samun nutsuwa da hakan zan fi samu nutsuwa idan kikai auren nan Safiyyerh"
"I love you daddy" Fiyya ta ce a hankali tana rungume daddy ya shafa kan ta cike da soyayya "daddy love Safiyyerh" tuni Captain ya fice daga cikin parlon. Anty Turai da zuwan ta gidan kenan ta ce "Ikon Allah. Yaya kai ne kake ɗaurewar yarinyar nan gindi wallahi ka lalata da soyayya take yin abin data ga dama, ko Aliyu baka tambaya abin da ta yi masa ba ta wannan figaggiyar yarinyar kake"
"Fita daga ɗakin nan Turai" rai ɓace Anty Turai ta fice tana zabgawa Fiyya harara ranta duk a ɓace. Daddy ya kalli Fiyya sosai kamar zai yi magana sai kuma ya ce "jeki wanke fuskarki I'll drop you"
"Daddy daman i missed your drive wallahi" murmushi ya yi mata a duk santa zai kalli Fiyya sai gabansa ya faɗi ya juya a hankali ya dubi picture ɗinta dake gaban madubi sanye da kayan graduation ta yi wani kyakkyawan murmushi ta rungume hannunta tana kallon gefe guda. Ya ƙarasa ya ɗauki photon ya shafa a hankali "Maama na ni kamar na yi ba daidai ba, bani da wani zaɓi ne i am sorry Safiyyerh Abdu Marafa" ya lumshe idanu ya buɗe a kan photon "kina tunanin kin yi girman da za ki iya kula da kan ki, ki kuma yankewa kan ki hukunci? Maama ba kin san komai ba a rayuwa you're nothing but a stubborn girl"
Ya ajjiya photon ya ɗauki wayarta babu wani password a kai dudduba abu ya fara a nutse yana yi yana kallon ƙofar banɗaki can ya sauke ajjiyar zuciya ya ajjiyar wayar daidai nan ta fito. Ya yi waje yana "Ki same ni a ƙasa"
Suna tafe a hanya daddy na driving a nutse ta ce "Daddy" bai kalleta ba yana dai sauraren ta domin program ɗin da ake yi da Eng Ali wali a redio shi ne ya ɗauke masa hankali. "Zan raka Kinal FGC"
Wani burki ya ja a kusan tsakiyar titin Fiyya ta dafe kai tana "Subuhanallahi"
"Mene haɗin ki da FGC Maama?"
"Daddy Kinal zan raka suna yin taro na makarantar zan bita idan na tashi aiki" zufa har fitowa daddy take a saman goshi sunan FGC ba ƙaramin gigita masa lissafi ya yi ba. "ba za ki ba" shagwaɓe fuska ta yi "don Allah daddy wallahi na ji ina son zuwa"
"Wallahi mistakenly kika je shegiyar makarantar nan sai ranki ya ɓaci kuma sai kin daina fita hatta aikin sai kin ajjiye. Wallahi Safiyyerh Abdu Marafa idan kika je za ki san waye Abdu sai na zane miki jiki da carbi ko bulala" ta yi ƙasa da kanta zuciyarta duk babu daɗi idanunta na cika da hawaye tun tana ƙarama take yin biyaya a komai akan abin da ya yi crossing da buƙatar daddy.
Hannunta riƙe da jakarta ɗaya hannun wayarta data kara a kunne suna magana da Kinal, duguwa ce hakan yasa bata fiya saka takalmi mai tsayi ba suit ce jikinta as always fara tas mai riga da wando ta yi rolling da black ɗin mayafi idanunta sanye cikin wani shade glasses mai kyau a hankali take tafiya tana ɗan jinjinawa mutanen kamfanin kai with so much respect tana da girmama mutane kawai rainin hankali ne bata ɗauka "Kinal ki je kawai idan na koma gida za mu yi magana, daddy ya hana" yadda ta yi furucin ya bayyana ainihin abin da take jin a zuciyarta.
"To shikenan nima na zo studio ne zan yi waƙa idan na koma gida zan shirya za mu yi video call na nuna miki cikin FGC ɗin" Fiyya ta ɗan taɓe baki daidai lokacin da take isa bakin ƙofar office nata security ya matsa ta buɗe ta shiga ta buɗe idanu ganin Ashraf zaune a office ɗin "Kinal mu yi magana anjima" ta cire wayar tana kallon Ashraf daya miƙe tsaye yana mata murmushi
"Kuma da permission ɗin wa ka shigo?"
"Wake neman permission idan ana batun ganin mata, na zo ganin matata ne" ta ajjiye jakar hannunta tana zama saman duguwar kujera "Sannu mai mata" ya miƙe ya dawo kan kujerar yana leƙa fuskarta
"Miji ɗaya gare ki a duniya kuma nine" cikin wasa ta ce "Ai kowa ba zan aure ka don ka ji"
"Funny Fiyya" a yanayinta na rashin damuwa da soyayyar ta ce "How are you?" Yana kallonta yana ji wani abu sosai game da ita "Fiyya na yi kuskure wallahi bana sanin ina shige limit ɗina sai na yi wani abu. Ni na san ba wani sona kike ba amma idan kika yi haƙuri watarana za ki ji son nan ko yaya ne kullum kina ƙara nesanta kan ki dani yayinta zuciyata ke ƙara kusanto kanta gare ki. Komai da lokacin shi idan mukai aure muka rayuwa inuwa guda I'll definitely be honest to you, ina jin kishin ki a ƙirjina ne a nan nake ji kina mini motsi Fiyya" ya nuna ƙirjinsa saitin zuciyarsa sai ya ɗan juya gwanin tausayi
"Amma bakya so na"
"Who told you that?"
Ashraf ya buɗe idanunsa "When are you gonna tell me you love me?" Tana kallon shi tana murmushi ita tana son shi sosai kawai bata san ya zata nuna bane sometimes rigimarsa ke sawa ta bijire itama ta miƙe tsaye tana danna kiran number messenger bayan ya ɗaga ta ce "Call Md for me, ka kira mini Md da Secretary hadda accouter" ta ajjiye ta ce ta haɗa shayi a cup guda biyu ta saka cokali tana miƙawa Ashraf ɗaya idanunta cikin nasa ta ce "San da aka kai ni gidanka matsayin mata" ya lumshe idanu ya buɗe
"I'll wait as far as you're with me. Abin da kawai nake buƙata shine ki so ni. Ki so ni ko da kaɗan cikin yadda nake sonki ne"
*****
Anty Hameeda na sunkuye a madaidaicin parlon gidanta tana duba jarkokin lemon ginger ɗin da take siyarwa ta ji hucin mutum da sauri ta miƙe sai kuma ta yi baya a razane ganinsa tsaye a gabanta yana waige-waige kamar wanda aka biyo ga wani irin yanka a ƙarƙashin wuyansa da alama yanzu akai masa jini ja zuba, ya yi zuru-zuru sai huci yake yi naman jikinsa musamman na ƙirjinsa na motsawa "Ɗan autan Ammo wannan hucin fa kamar an biyoka wani abun ka yi? Wane ya yanke ka haka me ka yi masa?" Bai kula ta ba ya juya ta bi bayan shi kitchen taga ya nufa ba jimawa ya fito da kwanon abinci daidai nan wata mata ta fito tana ganin Mai dawa ta yi saurin sakin butar hannunta ta ce
"Wannan tantirin ƙanin naki uban ne ya zo yi mana a gida? Yaushe ma aka sake shi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un mugun ji da mugun gani Ubangiji ya kare Allah wadaran ƴan daba ya tsine musu albarka ya saka su fita a cikin ajalin su" matar ta faɗa hawaye ya cika idanun Anty Hameeda ta ce "Baba ina laifin ki ce Allah ya shirya ɗa fa na kowa ne bawa kuma sai me shi, ciki ne mai haife-haife baka san me Ubangiji ya ɓoye ba suma fa ƙaddara ce ba wanda ya zaɓi yadda rayuwarsa zata kasance"
"Ai duk wani ɗan daba ƙarshe wulaƙantacciyar mutuwa ce ko idan sun sha ta faɗa musu babu daɗi su kashe kan su, ko kuma su haukace garin shaye-shaye ko garin faɗan daban su a kashe su. Allah wadai" Moh dai bai yi magana ba abinci kawai yake ci hannunsa ko wankewa bai ba duk jini Anty Hameeda ta shige ɗaki bayan ta share hawayen idanunta lemo ta ɗakko masa da ruwa ta ajjiye tana kallon yadda kusan rabin fuskarsa ya yi tabo da yanka yaro ba ya kalle shi ihu zai yi ba annuri a fuskar nan. Duk yawan abincin ya cinye ta sha ruwa ya shanye lemon tas "Na Ammo yanzu kana jin abin da ka zaɓawa rayuwarka shine daidai ka ji tausayin mu don girman Allah. Wallahi daka kasance cikin wannan rayuwar gwara ka dinga aikata abubuwan da kake a baya, jibi yadda ka yi muni ka zama ƙazami sai warin dauɗa kake yi. Na je gida sun ce sun fi sati uku ko gilmawar ka basa gani wai malam aure zai ƙara kuma da ƙyar idan ba Ammo zai saka ba, na rasa wake bashi kuɗi ya fi son ya yi ta auri saki ana haifa masa yara yana kasa kulawa da tarbiyyar su"
Tamkar bada shi take ba haka ya yi ko gezau can ya miƙe tsaye ta ciro kuɗi dubu ɗaya ta bashi ya kalle ta ya kalli kuɗin idanun nasa a rine kamar gauta yaƙi amsar kuɗi ganin inda ya nufa hannunsa riƙe da wuƙa ya saka Anty Hameeda ihu ta ce
"Me za ka yi ka rufa mini asiri kar ka kashe mini aure na shiga uku" ko kallon ta bai yi ba, ya ɗaga labulan ɗakin Baba tana sujjada ya same ta. Tsartuwa ya yi ya fito da kunama ya cilla mata a cikin hijabi kafin ta ankare ta ɗago jin abu na bin bayanta kamar kunamar tsafi ta shige mata riga ya zaro askira ya daidaici ɗuwawunta ya lafta mana wani uban yanka, baba ta saki ihu tana ta shiga uku ya yi saurin fita askirar na zubar da jini da.
Yana fita su spider suka rufa masa baya. A cikin wani kango ya kwanta ya yi shiru cikinsa zafi saboda faɗan da sukai da ƴan cikin gari akan fita wajan kamfel da sukai kilashin. Ya rufe idanu zuciyarsa na buɗewa wani irin ɗaci yake ji a cikin maƙoshinsa wani a ya tokare masa kamar yanzu komai ke faruwa haka yaga magic ɗin idanunsa ke hasko masa bidiyon komai ta ciki inda take tsaye.
Yana zaune a gida a lokacin yana jin yadda karatun Almajirai ya cika masa kunne ya yi kicin-kicin da fuska. Ammo ta kalle shi ta ce "Yau kuma waya taɓa jarumin Ammo?" Ya yi mata shiru don bai fiya cewa komai ba idan ran shi ya ɓaci kafin ta sake magana wani yaro ya yi sallama ya ce "Wai bestie ya zo in ji bestie"
"Waye bestie? Injiwa jeka tambayo"
Mutallab a lokacin bai motsa ba ya hakimce kamar sarki kansa a ƙasa yaron ya dawo ya ce "Wai in ji Safiyyerh matar Mutallab bestie"
Baki buɗe Ammo ke kallon Mutallab ta ce "Na Ammo yaushe ka yi aure bani da labari