Showing 60001 words to 63000 words out of 63481 words

Chapter 21 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt

23 Nov 2024

6682

yi magana ba ya saki ƙofar zai fita Ali wali ya ce "Ka manta kaga wannan, sirrina ne"


Ko magana Mutallab bai yi ba ya kwashi kuɗi ya yi waje abinsa yana rufe fuskarsa. Bayan ya fita Ali wali ya ɗauki waya ya yi kira ana ɗauka ya ce "an samu matsala P.A yau wani yaga ajjiyata, fitar maganar nan daidai yake da zuwana gidan yari" ta cikin wayar P.A ya ce


"Kafin ka je gidan yarin ka fara tura wanda yaga ajjiyar taka can"


"Mutallab ne"


"Tab, matsala kenan ina ruwan ciwon idanu wannan yana matsala kuna samun akasi za kaga ba daidai ba" Ali wali ya yi murmushi ya ce "Ina da tsari P.A idan na tabbatar na ci wannan kujerar zan yi tuggun da za a yi wa Mai dawa ɗaurin rai da rai a gidan yari, ka zo mu yi magana wai kasan har batun ƴa ta Noor ya sani, uhm sai ka zo dai"


Yana gama wayar ya duba interview ɗin da za a yi da dukkan wani ɗan takarar ɗan majalisa daka mabanbanta jam'iyyu wanda BBC ke shiryawa hakan yana nufin za su haɗu waje guda da Hon Maɗatai da Dr Abraham Denial David yana da buƙatar ya zauna ya rubuta dukkan abin da zai faɗa a wajan.


***Yana zaune ya zubawa yaron idanu gabaɗaya ba zai shige shekaru biyu da watanni ba a duniya ya yi wayo gwanin sha'awa duk wanda yaga yaron sai ya burge shi akwai shiga rai da ƙyar yake buɗe idanu saboda farin da yake da shi ya sauke ajjiyar zuciya yaushe zai rabu da damuwar ran shi sai yaushe zai ga Safiyyerh ya nuna mata abin da Ubangiji ya bata, daga samun cikin har haihuwar ba wanda ta sani. A fili ya ce "Come back please Safiyyerh, where are you ina kika shiga haka me ya sa hakan? Jininki fa Safiyyerh haba my innocent Mahmah"


"Ka dinga yin addu'a komai zai daidaita ya zama tarihi Ubangiji yana gani kuma yana kallo ba zai bar addu'ar ta tashi a banza ba, zata dawo ta damu ɗan ta, zata dawo a faɗa mata gaskiya, mu ma muna da namu laifin"


"I missed Safiyyerh dear, ki bar ni na koka" ya ƙarasa ya ɗauki babyn ya rungume a jikinsa hatta farinsa irin na uwarsa ne sak yaushe zai ga Safiyyerh ne? Wayarsa ya ɗauka ya yi kira ana ɗauka ya ce "Har yanzu ba wani information akai ko?" Ya yi shiru can ya ƙara cewa "Ka san komai ba, ka san yadda na samu na tsira da raina bana sha'awar komawa kuma ni da aikin lauya har abada, komai namu a can muka baro bani da picture ɗin Safiyyerh ko guda wallahi zan yi ƙoƙarin neman ƙwararren mai zane na gani ko za a dace thank you"


Kashe kiran ya yi ya ajjiye wayar yana sake rungume yaron da ko ɗomin jikin uwa bai sani ba, balle ya sha nono kamar yadda kowacce uwa ke shayar da nata ɗan.


***Safiyyerh na zaune bayan ta gama musu girki Goje yana ci da sauri yana ƙona harshe ta ce "Kaci a hankali mana akwai zafi" ya yi murmushi ya ce "Allah dai ya ba ki kada Manager"


"Amin"


Suka yi shiru can ta ce "Wai ba ka ce yayar wannan babban naku ce ta mutu ba? Me ya sa yake zaune a nan wai, ina yayenku suke" Goje ya ce "Babata ta mutu ni haka baba, shi kuma iyayensa suna nan cikin Birget Scorpion ai baya son zuwa gida ko unguwarsu baya son zuwa, tun bayan daya dawo daga gidan yari wajan state cid"


"Kai me ya yi haka to? Kwanansa nawa a wajansu"


"Shekara uku"
Safiyyerh ta jinjina kai har ranta ta ji tana son cin labarinsa waye shi a hankali ta ce "Ai daman naga baya ji shikenan da wuƙa a hannu ya sari wani wacce kalar rayuwa ce haka?"


Goje ya ce "Manager kenan, ai yanayi ne ke sanyawa a zama haka babu wanda ke son zama mutumin banza fa, ki gane hakan". "Son zuciya dai, Ubangiji daya halicci bayinsa an ce baya ɗora musu abin da ba za su iya ba, a tsaftace halicci kowa tun daga cikin uwa mahaifiya, a nan son zuciya ne da rashin wadataccen imani a zuciya da kuma yana da ilimi ai ba zai yi hakan ba" Goje ya ce
"Ko? Kin san shi ne kin san waye shi? To ki maye masa gurbin abin da ya rasa sai kiga ya dawo daidai idan an yi sa'a"


"Me ya rasa shi ɗin?"


"Soyayya, ta uwa, ta mahaifi, ta mata"


"Ok nan wai a haka yana da mata?"


"Ta rasu" Goje ya ce a taƙaice ta yi shiru "Ki gwada cewa kina son kiga ki ce za ki aure shi" da sauri Safiyyerh ta kalli Goje ta ce "Kasan me kake cewa ne? Ina da aure fa ai zunubi ne haka"


"Zance kenan, ba ki da wani aure yarinya haka kalar masu auren take kenan?" Safiyyerh ta yi shiru ita dai ko bata aure shi ba kawai za ta yi using opportunityn ɗin nan ya bata labarinsa, ko a lissafin ƙaddarorinta babu batun zama da ɗan daba balle soyayya har ace aure amma idan har zai bata labarinsa lallai za ta yi wani abu. Ta yi murmushi ta ce


"Kana da gaskiya ka gano ni, ai kaf ƙawayena ni ce bani da aure to bana son gori shine fa nake cewa ina da aure shi Captain ɗin ai yayana ne don ka ji, amma kana ganin zai so ni? He is such a arrogant, boring person yana da matsala"


"Ki gwada mana"


"Zan ƙoƙarta, ya sunan shi ok ka ce Scorpion ko?"


"Mutallab sunan shi, mantawa na yi"


"Wow a nice name, sunan shi ya fi shi kyau shine kuje ce masa mai jeji? Kai ya sunanka?" Ya yi mata shiru kawai sai ta miƙe ta shige ɗaki.


***A karo na biyu Aliyu ya kalli Commander ya ce "Sir ka yi replacing nawa da wani mana"


"Aliyu me ya sa kake yin haka, na lura kamar aikin soja ya fara fita daga ranka ko? Ka je ka yi tunanin tun farko wahalar daka sha kafin zama abin da ka zama, ƙiriƙiri an ƙara maka muƙami amma ka nuna baka son ana kiranka da sunan muƙamin sai Captain? Why?"


"Sir to a ɗan bani sati guda ok?"


"Ba zai yiwu ba, ka je ka fara shiri cikin daren nan da kwana biyu za a poster ku" rai ɓace Aliyu ya miƙe ya fita bai taɓa Jin takaici da kuma dana sanin zama soja ba a rayuwarsa sai wannan lokacin, shekarunsa nawa a duniya sai yaushe zai cigaba da jurewa yaushe zai ta yin haƙuri baya son shiga cikin ko barrack ne balle a nisanta shi da garin, ya samu sauƙi daga matsalar mata ga kuma wannan matsalar he need his wife, seriously he need his Safii yana buƙatar Safiyyerh a gefensa.


Daddy ya dinga kallon Aliyu kafin ya ce "Aliyu mene plan ɗinka akan case ɗin nan wai? Sp Ghali yana neman information ka ja baki ka yi shiru na ce ka cire hannunka a wannan matsalar ko, ka san me hakan yake nufi?"


"Daddy Safiyyerh fa matata ce hakƙin kare ta yana wajena so allow me to do daddy ka rabu dani"


"Allow me to do daddy" daddy ya maimaita ya juya ya kalli Ummimi dake zaune tana kallon Aliyu ya ce "Kin gani ko Zahiyerh idan Aliyu ya saka na rasa Maama zai yi mamakina" murmushi kawai ta yi ta ce "Matarsa ce fa, ta ya ya zai yi wasa da ranta bayan yana buƙatar ta cikin tasa rayuwar, bana son wani magana mai tsayi da bayane babu mai yi wa Safiyyerh kutse a rayuwarta ka sani, su yi nasu binciken shima ya yi"


"Aliyu bar wajan nan"


Fita ya yi rama rasa wanne kalar tunani zai yi, daddy ya lumshe idanunsa a fili ake ganin bugawar zuciyarsa bai shirya ba sam, baya jin kuma akwai abin da zai iya kawo masa cikas bai yi maganinsa ba.


Daddy ya gargaɗi kowa akan kar a fitar da maganar sace Safiyyerh kwatsam zance ya fita a shafin daddyn wanda shi kansa bai san yaya aka yi ba, wayarsa kullum na hannunsa balle ya ce wani ya ɗauka ya yi posting cikin yaran, ya tabbatar kuma ba hacking wayar aka yi ba, aka fara kiran wayarsa domin tabbatar da gaskiyar al'amarin ya rasa ya ya zai yi kawai ya ɗauki wayar ya kashe.


***Mutallab na zaune yana sauraren Goje Safiyyerh ta fito ta saka hijabi har ƙasa bai kalle ta sai haɗe fuska da ya yi ta ce


"Abokina Goje barka ya jiki naga an yi maka treatment, ku siyo ka yayyenki na dinga yi muku tunda dai dabar ya zama dole na iya ai" murmushi ya yi


"Na ɗauka lissafin kuɗi kawai kike ai? Ashe likita ce"


Ta yi murmushi ta ce "Ina yini?" Ta faɗa tana kallon Moh ya yi kicin-kicin da fuska bai amsa ba.
"Wallahi kyau kake mini idan kana haɗa fuskar nan, na ji ina son ka kuma zan iya aurenka wallahi" ya juya ya kalleta da sauri ta kashe masa idanu ɗaya ta ce


"What if I tell you, I love you?" Ta sake cewa


"Idan fa ka amince zan so ka har numfashina na ƙarshe a duniya, kawai dai kar ka wulaƙanta ni"


"Ke bar nan"


Ya furta a kausashe kamar ya ce ya shiga uku "Na san saboda na ce maka ina da aure ne, wasa nake yi don kar ku yi mini wani abun ne na faɗa fa, trust me i love you kuma na ji zan iya aurenka a yadda kake, zan baka farinciki walwala da jin daɗi ka amince mini ka ji dear" Moh ya dinga kallon ta wani irin kallo wanda bai ma san yana yi ba,sai dai ba'a tantance kallon na mene yanayin fuskarsa bai bada damar hakan ba, kaifin idanunsa ya saka Safiyyerh ƙasa da nata idanun, duk da shaye-shayen da ya ke yi da ɗaukar wuƙa matsayin abokiyar rayuwa da tarin raunukan da suke fuskar bai hana wani irin tsoro da shakkarsa ta gitta a zuciyar Safiyyerh Abdu Marafa ba, wani kwarjinin take hango wa na musamman a fuskar Mutallab Tahhb haibarsa da kwarjininsa mai ban tsoro ga namiji balle ɗiya mace sai yanzu take ji ta yi tsaurin idanu wajan tunkarar shi da wannan maganar mai kama da tatsuniya a gare shi, gare shi kallon kin raina mini wayo ya kewa Safiyyerh da tunanin ko ta samu matsala da nata tunanin tunanin ne? Idan ba matsala ta samu na gushewar tunani ba abu mamaki ne gare shi da jin furucinta ya yunƙura zai tashi ta riga shi miƙewa kanta a ƙasa hawaye na zuba a idanunta.


"Don darajar da Allah Ya yiwa Manzon Sallallahu alaihi Wasallama ka saurare ni, ba zan taɓa juya maka baya ko da nasani b a kasancewa ta da kai, kai musulmi ne nima musulma ce babu haramci idan mace ta ƙaunaci namijin daya kwanta a ƙasan zuciyarta, a kullum na ganka sai na ji zuciyata na kiran Safiyyerh wannan shine ƙaddararki zaɓin da kike jira irin namijin da kike fata, idan zuciyata ta kusanci zuciyarka sai na ji tawa zuciyar ta sake buɗewa da tarin tausayinka, kullum mutuwa nake da farfaɗuwa da soyayyarka ta yan kwanakin nan data rutsa da zuciyar Safiyyerh Abdu Marafa, kullum mutuwa nake da son ka, wallahi...," kasa cigaba ta yi saboda kukan daya ƙwace mata da gaske, da ace ita ƴar wasan kwaikwayo ce irin fina finai da ake haskawa sai ta ce a yanzu acting take, duk abin da take faɗa she doesn't mean it, iya laɓɓanta ne kawai ta yi hakanne saboda ta yi kutse cikin rayuwarsa ta san waye shi me ya sa ya zama abin da ya zama, tana son jin labarai mai kama da hikaya ko almara ko na soyayya.


"Will you love me?" Ta ce tana marairace masa fuska tare da ɗan turo masa jajayen cute lips ɗinta, ya bi lips ɗin da kallo ta haɗe hannaye waje guda ta langwaɓar da kai


"Please, Safiyyerh loves you a nan a cikin nan ɗina"


Ta nuna masa saitin ƙirjinta wajan zuciya da yatsarta manuniyya sai ƙifta idanu take. Har lokacin bai ce mata komai ba kamar yadda ta lura yawan magana ba ɗabi'arsa bane yana wanzuwa da shiru da tunanin ya fi masa. A duk maganarta ɗaya ƙare haɗe fuska yake yi ya zaro sigari ya kunna ya saka a baki da ƙarfi ya zuƙi hayaƙin yana jin saukar hayaƙin ƙasan ƙirjinsa ya hura kumatu ya matsa dab ya fesa mata a fuska ya yi gaba abin shi yana taku ɗaiɗai irin he don't care. Safiyyerh ta bisa da idanu ta yi shiru ta ji ta damu sosai a ranta tana Astagafirulla data tuna da gaske ita matar aure ce matar Aliyu Abdu Marafa ce ita halaliyyarsa ta jingina da jikin bango tana lumshe idanunta.


Moh bai ƙara dawowa cikin gidan ba, har dare ya nutsa bama shi ɗaya ba kusan dukkan su basa nan ta dinga sallah tana addu'a har girki ta yi musu ta ajjiye amma ya yi sanyi. Tana haka ta ji an buɗe gidan da sauri an shigo ta buɗe ƙofa ba tsoro ta fito Mangal sai nishi yake yana kallon ta, da gudu Goje shima ya shigo yana shigowa kuma ya rufe ƙofar ya zube a ƙasa ta kalle su cikin sigar damuwa ta ce "Ka rufe ƙofar shi kuma fa?"


"Bai shigo ba?" Ta jinjina masa kai ya miƙe tsaye ya ce "Jagwal kenan, ai kuwa bama tare"


"Innalillahi kamarya like how bakwa tare?"


"Ke bafa wani abu saɓe kawai ki je ki yi kasa ko". "A'a don Allah ka je ka nemo shi ka ji ɗan'uwanka ne fa idan wani abu ya same shi ai ba za ka ji daɗi ba, shi ma ba zai bari komai ya same ku ba" ya yi murmushi ta lura yana da fara'a ba kamar sauran ba "Ubangiji nada kyakkyawan tanadi a rayuwar Mai dawa, ba yanzu zai mutu ba kin ji ko?"


"Na kawo muku abinci?"


"Dar daidai kenan kin taimaki ƴan hanjina jagwalo shi nan a ɓatar da shi a rufawa ciki asiri" abincin ta ɗakko ta kawo musu duk yadda taso su wanke hannu ƙi sukai Kodayake haka ogan nasu shima yake. Har bacci ya ɗauke ta bata saka shi a idanunta ba. Sai da asuba ta fito dafa ruwan wanka kamar jiya haka ta ganshi ya yi shiru yana kallon sama, tunanin maganganun da Abbasa ta yi masa yake da abin da Ali wali ya dinga nanata masa akan Safiyyerh.


"Bai kamata gwarzona ya wanzu yana tunanin da zai iya illata masa rayuwarsa da zuciyarsa ba, haba mafaraucina" ya juya ya kalle ta, ta kashe masa idanu ta ce "Yes, ba farautar dabbobi kawai ka iya ba ka yi dacen farautar zuciyar ƴar Professor Abdu Marafa" kamar a buge yake haka ta lura da shi musamman yanayin zaman da ya yi, sai a lokacin ta lura da yankan dake damtsen hannunsa ta ƙarasa ta duƙa ta ce "Subuhanallahi faɗa ka je ka yi haba mai sunan manya, Muhammad Mutallab fa masu sunanku salihan banyi ne"


Ya duƙar da kan shi ƙasa ta je ta ɗakko kayan da Goje ya kawo ta zauna dab da shi, ta kamo hannun nasa sarai ya jita amma bai kula ta ba, tunani ne ya addaba masa. Ya shiga hura masa iskar bakinsa ganin yankan na kumfa data saka magani ta gama yi masa treatment ta kalle shi taga ya rufe idanu miƙewa ta yi zata fita kamar daga sama ta ji ya ce


"Cikakken sunanki"


"Safiyyerh Abdu Marafa"


"Cikakke" ya sake maimaitawa "Haka sunan yake fa Jarumi"


"Shi Abdu?"


"E, sunan daddy kenan Abdu" ya buɗe jajayen idanunsa ya watsa mata su ta yi saurin yin ƙasa da nata idanun ta fidda ran zai yi magana har zata juya ya ce "Ƙarya, idan na tuna miki na kwaɗa miki mari ko?". "Allah ni dai haka na sani babana ne fa"


"Uhmm" ganin kamar da magana a bakinsa kuma a buge yake ta matsa ta zauna ta ce "Jarumi, do you want to say something? Say it. Ka ce wani abu Jarumi"


"Faɗi mana Jarumi"


"Tiger" ya ce a hankali ta ce "Me ka ce? Ban ji ba"


"Ammm, hmm kika ce ba ki da aure?" Ta ce "E, bani da shi like a told you" ya buɗe ido ya zura mata idanu yana ta kallon ta da ƙyar ya iya cewa "za ki so ni?"


"Zan aure ka na rayu da kai idan ka faɗa mini labarinka waye kai?" Ya sake yi mata shiru "Ina ji"


"Zana ba ki labarina idan za ki aure ni"


"Ni Safiyyerh na yi maka wannan alƙawarin zan rayu da kai a duk yadda rayuwa ta yi da kai Jarumi" ya miƙa mata tafin hannunsa a hankali kamar mai jin tsoro ta kalli hannun cike da rashin fahimta, jiran ba'asi take shi kuma ya yi shiru sun ɗauki minti biyar da wasu daƙiƙo a hankali ya sake furta "Promise" ta dinga kallon hannun kafin ta yi Astagafirulla da tunanin Ubangiji ya yafe mata saboda igiyar auren wani ce a kanta ta ɗora ɗan ƙaramin hannunta cikin nasa, tana sawa ya damƙe kamar abin da yake jira kenan ya yi shiru ya lumshe idanunsa muryarta na rawa ta ce "I Promise you Jarumi" yana riƙe da hannun bai cika ba bai kuma yi magana ba can ya sake ta, ta fara masa magana sai dai ko tari bai kuma yi ba tunaninta bacci yake yi ta dinga kallon shi tana son hango kyau ko ko muninsa.


A daren ranar su Goje basa nan sai shi ɗaya yana busa hayaƙi a sama yake jinsa sosai ya ji an buɗe ƙofa an shigo, maza ne har su huɗu sun rufe fuskokinsu ya damƙi wuƙarsa kafin ya miƙe ɗaya ya cafki wajan yankan da Safiyyerh ta gyara masa ya janyo hadda naman wajan suka fara kokawa yana buga su da ƙasa, cikin sauri Safiyyerh dake bacci ta farka zata fito daga cikin ɗakin ya yi baya da ƙarfi ya tura ta ciki ya rufe ƙofar ta taga ta leƙo tana kiran shi, taga ya ɗaga wuƙa ya sokawa ɗaya a gefen wuya ya ƙara soka masa a ciki ya watsar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login