Showing 42001 words to 45000 words out of 63481 words
Chapter 15 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt
ji ya ce wani abu?"
Sp Ghali ya dinga kallon Safiyyerh yana jin wani irin abu a ransa na motsa masa sai ya yi murmushi ya ce "dear kin ce basu nemi komai ba, ba wanda kika gane ba suna amma haka kawai sai su caka miki wuƙa think Safiyyerh" sarai Safiyyerh ta tuna sunan da ta ji ya ambata na Mutallab sai ta yi shiru a hankali kuma ta ce
"Sp kasan matsalar da ƙasar nan take ciki musamman Jiharmu akan ƙwacan waya, wayata zasu ƙwace ni kuma na hana saboda ina da abubuwa a ciki shine sukai mini haka" ya jinjina kai ya ce "Haka ne dear za mu yi bincike zan gano kowaye za mu hukunta shi ƙarƙashin hukuma bisa kundin da aka wanzar, get well soon dear" ya sake faɗa yana murmushi kan ta dai a ƙasa yake. Sallama sukai dasu daddy suka tafi. Captain na zaune ko tari bai yi ba wayarsa kawai yake dannawa can ya miƙe ya fita daddy ya bisa da kallo haka Yaya J ganin ko sannu bai yi Fiyya ba daman bai jima da zuwa ba.
Eng Ali wali ya dinga kaiwa yana kawowa ransa duka a ɓace ya kalli Mai dawa ya ce
"Yanzu daka kashe ta fa? Wai me kake nufi da wannan abin da ka yi ne Mutallab?"
"Ka dai na yi mini ihu kamar Malam Abdullahi" Ali wali ya jinjina kai kawai ya ce "Kasan ka raina ya ɓaci kake cewa haka? Ya zan aike ka ka yi sato yarinya kuma ka caka mata wuƙa salon ka ɓata mini aiki da sanyin safe ake kama fara ba mai dawa"
"To na fasa"
Ali wali ya buɗe idanu ya ce "Meka fasa ɗin? Ba dai ɗakko yarinyar ba kake nufi?" A taƙaice ya ce "Shi"
"Haba uban mafarauta, kai baka san wasa ba kai kamar ɗa kake a wajena fa" sai a lokacin Moh ya buɗe idanu ya kalli Ali wali yanzu dai normal yake ba'a buge ba "baka haifan ba, san da aka haifan baka da labari" ya yi fito yana miƙar da ƙafa ya ce "To ka kira ɗan naka ya yi maka aikin, mu fa kuke sawa a wahala har a yi zaɓe aci a cinye ka hau kujerar ba lallai yaranka suna ƙasar ba, ba'a rainawa Moh hankali ka bar mu matsayin ƴan daban kawai" Ali wali ya ce
"Ya batun yarinyar?"
"Na ji" ya ce yana miƙewa tsaye har zai shige ya dawo ya ɗauki bandir ɗin kuɗi ƴan dubu-dubu ya watsa cikin aljihu. Sautin daya ji kamar gurnani kamar kuka kuma ya sa ya nufi ƙofar da yaje jin hakan ya murɗa handle zai buɗe cikin sauri Eng Ali wali ya riga shi ya ce "Haba Mutallab idan iyalina ne a ciki fa?" Moh ya zubawa Ali wali ido ya kalli ƙofar sai kawai ya fice yabar wajan. "Ɗan wahalar yaro ɗan jaraba Allah Ya nufa na lashe kujerar ganina sai ya yi maka wahala"
Hon Maɗatai yana zaune ya kalli Sp Ghali ya ce "Ka lemo record ɗin nasa?"
"Na samu Hon amma cin dai amana ne irin namu na jami'an tsaro amma fidda record ɗin wani criminal ya saɓawa kudin tsarin ƙasa" Hon Maɗatai ya ce "Waye Mutallab?" Sp Ghali ya ce "Nothing serious about him hon, shekaru uku da suka shige an kama shi da laifin kashe matarsa ranar da aka kai masa ita matsayin amarya, kafin nan yana da record na zama gidan yari na watanni sai kuma taɓa guduwa Legas, a baya kuma kafin hakan shi mafarauci ne ma'abocin shiga jeji ya yi farauta"
"Hon akwai matsala ne? Na ga ka yi shiru?"
"Batun Scorpion ba, case ɗin yarinyar nan Manager a ranar ance shima Scorpion ya je wajan" Sp Ghali ya ce "Hon Scorpion da ƴan siyasa irin ku yake da matsala fa, ko mutumin daya kashe last yana da za hujjar kisan mune dai bamu sani ba, waye Scorpion ba wanda ya sani jami'an mu na neman shi haka F.i.d Federal investigation department wallahi suna kama shi wannan kisa ne nan take ko su yi masa allurar hauka" "Al'amarin Scorpion ya yi kama da ɗaukan fansa fa, za mu zuba ido ya kashe mu ne? Ku hanzarta nemo ko waye Sp Ghali"
"In sha Allah Hon"
Aliyu na zaune saman kujera daddy ya ce "Kaji ai ko?" Ya jinjina kai kawai "Zuwa dare sai ka ɗauke ta ku tafi can part ɗin dake gidan daman tuni an zuba komai empty dai yake to ɗazo an kaiwa Safiyyerh kayanta, Aliyu Safiyyerh amana ce idan ka ci amana ba zan yafe maka ba, na yi haƙuri na rabu da kai amma na so kun bar ƙasar gabaɗaya" addu'a daddy ya yi musu sosai duk da Fiyya bata wajan. Aliyu ya tashi ya fita. A daren ranar ƴan jarida suka shigo saboda hirar da za su da daddy. Sosai aka yi hirar inda yake cewa. "har kullum ni Professor Abdu Marafa bana goyan mutumin da bashi da wata nagarta wanda baya duba rayuwar yaranmu matsa wanda kuma zuwa gaba sune zasu gaje mu, duk wanda ya buƙaci ku zaɓe shi ku fara duba nagartar shi waye shi, bane background na rayuwarsa waye shi tun farko? kar a yi amfani da talauci da rashin iliminku a saka ku yi zaɓan tumun dare a wannan lokacin matasa yana da kyau ku yi gangami ku magana da murya ku saka iyaye na gida ƙanne da yan'uwa su zaɓi cancanta, wannan masu gamu taliya gishiri ko masu siyan ƙuri'ar mu basu ne wanda suka dace ba, ƙuri'armu ita ce ƴa'cinmu kana siyarwa baka da damar yin zaɓe ku kalli yadda ake mayar da ƙananan yaran ƴan daba masu bangar siyasa ana basu ƙwaya suna aikata zunubi suna kai kansu inda za'a kashe su, ku faɗa mini ko sau kun taɓa ganin ɗan wani daga cikin ƴan takarkarun nan? no! Sai yaran talakawa wanda basu da ilimi ko basu da sana'a sai a yi amfani da wannan damar a janyo su a kurɓata musu rayuwa a ƙarshe kuma ko gidan yari yaro ya tafi wallahi sai dai iyayensa su yi fafutuka duk da cewa har da laifin wasu iyayen a lalacewar yaran, matasa ku haɗa ƙungiya da za ku dinga taimakon juna kar ku yadda da mulkin kama karya kuna kallon shekaru huɗu da suka shige yadda zaɓe ya kasance"
"Professor Abdu Marafa kenan a yayin da yake bawa matasa shawara akan su miƙe tsaye domin ƙwatuwa jiha ƴan'cinta. Professor mai ya sa duk maganar da zaka yi akan matasa ne? Da batun shaye-shaye ko daba?" Daddy ya rantse idanunsa yana jin zuciyarsa na yi masa zafi can ya ce
"Ɗan jarida kenan baki abin magana, saboda matasa sune yau, sune gobe haka jibi matasa sune cigaban ƙasan idan har aka tsaya musu aka fitar da iri mai kyau, shaye-shaye kuma....," sai kawai ya yi shiru. Yakasai ya ce "Gabaɗaya abin da zamu iya naɗa kenan a wannan satin, zamu cigaba da bibiyar professor Abdu Marafa domin ganin haƙar tasa zata cimma ruwa ko yaya ne? Ni Khalid A Yakasai nake cewa a huta lafiya"
****
Numfashi Mutallab ke fitarwa a hankali jikinsa duk yanka saboda faɗan da suka yi da ƴan cikin gari bai san adadin mutanen daya sara ya fitarwa da jini ba, bashi da tabbacin ko bai yi kisa bama rabin fuskarsa duk yanka ne wani wajan har ya zame masa tabo. Goje shima cikinsa rauni ne da ƙyar yake fidda numfashi a hankali ya ce "Sun kashe Darma fa, ni ban ɗauka haka zuwa kamfel ɗin yake ba, wallahi sun kashe Darma na yi ƙoƙarin kai masa ɗauki amma ta kai nake"
"Goje"
"Na'am, Sarki"
"Nemi maɓoya" ya ce "Idan na ɓoye kai fa? Naga ba zaka iya tashi ba gwara ni ma kai ma da tuni sun kai ka kushewa, gashi wannan ɗan jakar Mangal ban san inda yake ba, balle a jira Ali wali a faɗa masa koda taimakon da zai mana"
"Wai baka jina idan ba ƙiyama kake shirin zuwa ba ka tashi ka face Goje" da sauri Goje ya miƙe ya yi kwana saboda ƙarar motar kwalawa da ya ji, Moh ya saka hannunsa a aljihu ya danna laya tuni ya ɓace a wajan.
Abbasa ta dinga kallon Mutallab kamar baya numfashi ta girgiza kawai ta kalli mai yi masa treatment ɗin bayan ya gama ya miƙe ta ce "Sannu da ƙoƙari" ya jinjina mata kai ya fice kawai. Ta yi shiru tana sake kallon Ɗan'malam.
Kamar yadda daddy ya buƙata Safiyyerh ta tare cikin part guda da yake gidan daga can baya, ita dai da to kawai take binsa sai kuma idanu ta yarda ba zai zaɓa mata abin da bai dace da rayuwarta ba, ta amince zata zauna da Captain Aliyu zata koyi son shi. Cikin sauri yake gudanar da komai kamar mai tsoran wani abu. A harabar gidan Aliyu na tsaye yana kallon Awais da yake cewa "Yaya ban gane tambayar da kake mini ba"
"Ya sunanka ma?"
Da mamaki Awais ya ce "Ikon Allah Yaya ni fa ƙaninka ne tsayin shekaru baka san sunana ba?" Aliyu ya haɗe fuska ba wasa ya ce "Kuma dole akai na haddace, seriously bana iya tunawa"
"To kai ne Baba captain Aliyu sai Junaid sai Dr Hash sai ni Awais sai Maama" "Ok, shi likitan wanne allura ya ke yi mata ban damu na san ba a baya yanzu ina so"
"Wai Dr Hash da ya kewa Fiyya? Ban sani ba gaskiya Yaya why not ka tambaye shi?" Wata tsawa ya dakawa Awais yana cewa "Get lost mumu" fita ya yi daga cikin gidan gabaɗaya.
Har ɗaya saura Safiyyerh na kwance a bedroom ta yi shiru tana jin ciwon na yi mata zafi ta yi kuka sosai na rashin sanin dalili har bacci ya ɗauke ta. Cikin bacci ta ji an buɗe ƙofar an shigo ta yi saurin rufe idanu yana sanye da kayan bacci farare ya ƙarasu ya duba magungunan yaga ko ɗaya bata sha ba, ya ƙarasa bakin gadon ya zauna shi gabadaya ya manta cikakken sunanta na gaskiya rashin sanin ne zai ce kawai ya saka hannu ya janyo ƙafafuwanta zuwa ƙasa ta matso dab da shi da sauri ta buɗe idanu, suna haɗa idanu ta tura baki tana juya fuska
"Zan saka bindiga na harbe ki a iska kina juyawa" ta kalle shi ta ce "To yaya ciwona ka fama mini" kallon da yake mata ya saka ta miƙe zaune "kin accepting auren?" Ta jinjina kai ta ce "Na yi kamar yadda ka yi na san daddy yana da nasa dalilin damuwata ɗaya na rashin sanin gaskiyar ni ce ƴar daddy ko kai, amma aure tun kafin na zo duniya Allah Ya rubuta wanda zai zamo miji gare ni ina da sani daidai gwargwado zan zauna ƙarƙashinka duk da baka so na, ko kana so na?" Ya girgiza mata kai alamar
"A'a"
"Ni ma,sai mu koyi son juna" ya kalleta kawai sai ya ce "Muga ciwon" "Yaya a wajan ƙirjina ciwon yake fa" da rashin fahimta ya kalli ƙirjin ya kalleta kuma ya nisa ya ce "Kuma mene a ƙirjin?" Ya faɗa yana yaye rigar.
WE'LL SOON END OF THE FREE PAGES. Ku hanzarta biyan 500 domin karanta Mutallab posting za mu babu ɓata lokacin ba lallai ku fahimta a yanzu wanda suka shiga paid group sune da batu ko rabin book 1 babu shiga ba. Tsakiyar labarin akwai muke, mene ya faru a farko me zai faru tsakiya ba zaku taɓa sani ba ko a sashe.
MUTALLAB.
Book 1, 2 &3
500 Naira
0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385
[10/21, 2:10 PM] Nanameera: *❤🔥 MUTALLAB ❤🔥*
Page 12
*Bright pens..2nd batch*
Hannunsa ta cire da sauri ta ce "ciwon fa a wajan ƙirjin yake yaya" da mamaki Captain ya kalleta ya kalli ƙirjin, da gaske bai san mene matsalarta da hakan ba. Ya ɗauki lokaci kafin ya ce "kuma mene special a ƙirjin?"
"Baka sani ba?" Fiyya ta buƙaci jin amsa ganin har lokacin kallon ta yake da alama processing ƙwaƙwalwarsa take yi shi dai ya san wajan da aka caka mata wuƙar kawai zai gani. Bai sake cewa komai ya miƙe tsaye ya nufi fita, Fiyya ta bisa da idanu tana jinjina rainin wayon Captain yana abu kamar baya fahimta. Ta yi shiru bayan fitar tasa, ta ɗan jingina da jikin gadon thinking me ya sa abubuwa suke juyawa tare da faruwa ne? Ba wani tsanar Captain ne a zuciyarta sosai ba, kawai yadda yake abubuwansa ke ƙular da ita amma kaf yayyanta tana matuƙar so da ƙaunar su. Damuwar bai shige dalilin daddy na aura mata Captain ba, bayan shi blood brother ɗinta ne. Yanzu ita ce ba jinin daddy ba ko Aliyu? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!
Da sauri ta riƙe ƙirjinta jin zuciyarta na harbawa, duk yadda take ƙoƙarin ko a cikin bacci ta sake ganin gilmar reflection ɗin shi ta gagara, ko sautin muryar tasa ma ta mata sai kuma tunanin mahaukacin daya caka mata wuƙa ya faɗo cikin ranta wai shi Mutallab? Who is he?
"Who is he?"
Muryarta ta sauka a tsakar kanta tana nanata mata tambayar da zuciyarta ta yi mata a fili. "To ya ɗauke ni ya yi mini me? Safiyyerh Abdu Marafa ai ba sa'ar yara bace, bata zama teddy ba, the whole manager anya ya san me yake ce mini? Ba sai ya sake ganin ko inuwar fiyya ba balle ya aiwatar da abin da ya yi niyya a kaina, aikin banza aikin wofi don ma dai ban san ya zaro wuƙar bane zuwa gaba Captain zan lallaɓa ya ara mini bindigarsa problem solved"
Ita kaɗai take ta yin mita ta zubawa madubi idanu bayan ta miƙe tsaye. Wanka ta yi tare da alwala bayan ta idar da sallah ta ɗauki skin products mai kyau dake sa fatarta laushi ta yi ta ƙyalli, tana son amfani da kayan Aisha s bayero skin care nd herbal medice, ta ɗauki riga mara nauyi saboda ciwon jikin nata. Kasa bacci ta yi ta ɗauki system ɗinta ta fara dannawa hannunta riƙe da ruwan zafi ta jima suna tattaunawa da Md da Secretary ta email kafin ta rufe system ta yi addu'ar bacci ta kwanta sai dai ciwon ya dameta da zafi har zazzaɓi ya saka ta.
Washegari da ƙyar ta yi sallar asuba don bata yarda ta shige ta, ta rufe jikinta da duvet ta girgiza kai da ƙyar baccin ya sake ɗauke ta. Har 12 bata fito ba, sanin abin da ya faru da ita ya saka ba'a nemi ba'asin rashin zuwan nata kamfani ba.
Wajejen ƙarfe biyu ta buɗe idanunta dalilin ƙamshin da ta ji da kuma goshinta da ake murzawa a hankali, ta juya ta kalle shi taga waya ya ke yi muryarsa ƙasa tana jin yadda yake magana one by one jin ana kallon shi cikin sauri ya ce "i will call you later"
Ya juya suka haɗa ido a hankali ta ce "Ina yini?" Ya yi mata shiru yana kallon kanta da sauri itama ta kalla sai yanzu ta lura kan nata yana cinyarsa ne shi kuma hannunsa na gefen fuskarta "ɗaga ni"
"Yaya bani lafiya fa" ya harareta kawai ya yi shiru shima ya ji zazzaɓin ta juya masa baya tana sauke kanta idanunta rufe zafin zazzaɓin na ƙaruwa ji tayi ya ɗago ta zaune kamar wacce zai zaunar a cinyarsa ya faki idanunta ya damƙe gefen cikinta ta yi ƙara tana riƙe shi "Ki dai na yi mini sauti haka, za ki je zaman barrack lazy" ta haɗe fuska tana ji yana taɓa cikinta yaga wajan ciwon na jini ya saka hannu ya shafi ciwon ya taɓo jinin da hannu can ya miƙe yana juyawa.
"Captain jini wajan yake yi ka fama mini na shiga uku" idan ba kuskuren ji ta yi ba, muryarsa ta ji ya furta "Allah Ya ƙara"
Cikin dare ne yana tsaye ya fito daga cikin motarsa sanye da manyan kaya na alfarma da fuskarsa rufe da facemask ya dubi yaran da suke gabansa ya ce "Ina buƙatar aiki cikin gaggawa bana son wani mistake idan aka samu akasi ina cikin taraddi, kuna kallo abu ya taho lokacin na neman cimmana" Ya buɗe idanu yana sake dudduba inda yake tsaye gani yake kamar ana ganinsa za kuma a iya gane wanene shi.
"Mai gida wanne kalar aiki ne ya fito da kai cikin duhuwar nan, faɗa taka cikawa tamu sai da kai iya wuya ba wani shege a baya wallahi" ya ɗan yi murmushin jin daɗi yana kallon mai maganar da kana ganin shi zaka san a buge yake cikin maye kamar kullum
"Idanun mutane nake so, maza uku mata uku" ya ce yana kallon wanda yake faɗawa maganar ganin yadda ya yi shiru kamar dai ban fahimta ba. "Aiki ja idanun bama na mutum ɗaya ba? Akwai kuskure fa"
"Yanzu akwai wani aiki da zan iya sakawa ka yi mini da zai fi ƙarfinka? Kai ɗin amintacce nane na kuma yarda da ƙwarewarka ina jin daɗin business da kai wallahi" ya zaro kuɗi masu yawan gaske ya miƙa masa, ya sake zaro wata ƙwaya kala daban-daban masu kyan gaske da tsada kana gani kasan manya ne ke shan irin ta. "Ka fara riƙe wannan kuɗin nasan kana buƙatar caji a kanka kafi yin aiki yadda ya kamata, idan ka kammala ka sanar mini zan faɗa maka inda zaka ajjiye ko?". "Ka yi ƙarko irin na dabino sai da kai wallahi yau zam dani, ko kan mutum ka ce na kawo maka a yadda ƙwayar nan ke buɗe mini tunani kawowa zan, ba ƙaramin ilimi ne dani ba da tuni fa ni zan yi ministan kuɗi nace na fasa, kaf ƙasar waye bai sanni ba don uwar mutum" sambatu kawai yake na maye ya bugu ƙarshen buguwa, shi mutumin dariya kawai yake basa hakan kuma na yi masa daɗi ainun. Mota ya shiga ya bar wajan shi kuma ya gangara ya shiga lungun titin da suke. Tunda ya tafi ya zauna cikin yan'uwansa mashaya yake tunanin ta ina zai fara? Ina zai samu mutane har ya ƙwaƙwule idanunsu hankali kwance? Ya yi shiru yana kallon sama yana ta furzar da iska mai ɗauke da warin sholi dana bakin gabaɗaya.
*****
Mutallab ya tanƙwashe ƙafafuwansa kamar wani sarki ya