Showing 57001 words to 60000 words out of 63481 words
Chapter 20 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt
ta sake shi ta ce "Fito waje" saƙo Aliyu ya samu cikin gaggawa sunansa ya fito a jerin sojojin da za a yi posting nasu wajan aiki ya dinga kallon saƙon yaushe ma ya dawo da za a sake tura shi wani wajan bayan babu shi a sojojin da aka yi list? Sai kawai ya fita da nufin zuwa kiran da ya samu domin bata uzurin yana da wani muhimmin aiki akan nasa iyalin ya manta da batun a tsarin aikin sojoji babu sauyi idan har a zaɓe ka.
****Mafarki ta yi mai ban tsoro ta farka a gigice tana kiran sunan TAHHB sai haki take yi fitila taga an kunna an hasko ta ya zuba mata idanu a ransa yana ƙara mamakin wannan hasken nata gefensa zabtareriyar addace saboda tsaro ya miƙe a hankali ya kunna hasken parlon sai a lokacin Fiyya ta lura da Goje dake cikin kwance cikin jini haka Mangal ga wuƙaƙe a gefen su sai numfarfashi suke yi. Ya taka ya je gabanta ya tsaya can ya duƙa dab da ita baki ta buɗe za ta yi ihu ya saka yatsarsa a bakinsa "Shhhh" ta yi tsit ya cake addar
"Mene?"
"Ban kira ka ba wallahi" ya zuba mata idanunsa masu kaifi ta janye nata "sunan wa kika kira to?"
"Tahhb"
"Sunanki ne? Ko na Abdu Marafa?" Ta girgiza kai "Mafarki na yi a mafarkin na ji sunan, amma ban sani ba ni na manta komai na mafarkin ma kai na ciwo yake i have a headache"
Ya ɗaga addar ya cake ta tsakanin ƙafafuwanta sai sheƙi take yi ya ce "Ko dai ki faɗa mini waye Tahhb ɗin da kika dame ni da kiran sunansa yanzu ki na ɓula miki cinya"
"Don Allah ka yi haƙuri wallahi ban san shi ba"
"Ke wace?" Moh ya tambaya "Safiyyerh sunana" ya cije bakinsa sosai ya ce "Matar soja ko?" Ta jinjina masa kai
"To ni waye? Kuma ya nake a wajanki?"
"Wallahi ban san ka ba, kai ba kuwa bane a wajane" idanunsa har ruwa yake ya daka mata tsawa a gigice ya ce "Waye ni? Waye ni waye tell me....
❤🔥🔥💃1 page remain ba zan taɓa buɗe komai ba shafi 15 is nothing nothing ku biya you'll never regret sai mun yi nutsu za ku fahimci labarin MUTALLAB bai haɗa hanya da kowanne kalar labari ba, idan za ka yi kuka ka fara tun yanzu 😭😂ba kuma zan taɓa sauya labarina a yadda nake ba, you better shut up...
MUTALLAB.
Book 1, 2 &3
500 Naira
0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385
'Yan Nijar ku turo carte airtel ta 300fcfa saman wannan layin 84506476
[10/27, 4:07 PM] Nanameera: *The story of a thug husband MUTALLAB, as a good parents za ku bada auren yarinyarki ga ɗan daba ɗan ta'adda? Ban ce ku fara kuka tun yanzu ba,ban ce ku ji soyayyar ciki kamar a ƙirjinku ake wanzar da ita ba.* *The story of TIGER and MOH The destiny of CAPTAIN and FIYYA. Finally the eternal love* *between..The love that separate them and back them together❤🔥😭*
*❤🔥 MUTALLAB ❤🔥*
Page 15 last free episode
*Bright pens.. 2nd batch*
For more updates follow Mutallab on Arewabooks in sha Allah ❤🔥🥰
Page 15 shine last free pages na labarin, kar ka yi tunanin ganin wani page ɗin a waje ka yi payment a yi naka into paid group akan 500 kacal, love ɗin da kuke showing yanzu ne zai yi aiki🫠MUTALLAB.
Book 1, 2 &3
500 Naira
0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385 'Yan Nijar tsarin biyan zai kasance ta *Stock na airtel*. Ku yi wa wannan layin 84506476 magana sai ta ba ku lambar da za ku turo mata stock ɗin. Kafin ɗorawa da inda muka tsaya zamu ɗauki hutun zango na sati ɗaya tal😂 maybe har a yi albashi ko masu mining ta fashe musu.
Godiya ga Hajja Aisha Abubakar Khadhfsum data biyawa mutane 8 🥰 ga masu business zaku iya badawa a tallata muku idan kun ɗauki nauyin page in sha Allah.
Ba zan manta da BESTIE ba🥰I so much love her wish you all the best Aunty Nazeefah Sabo Nashe ta ce HADARIN GABAS yana hanya. Ina son ta sosai😮😮
Gaisuwa ga haƙarƙarina😂🥰uwar gidan Viper tunda mun amince Nabila ce amarya Ayushercool masoyiya. My beb Zee kumurya sai tallafe ƙirji muke muna sata a addu'a gashi zata fara yi mana ZAYTOON a watan Nuwamba i love them sosai🥰
Conversation bana ce kuci kanku ba, saboda ina ƙaunarku Sarautar's library Mutallab fans, Nimcy paid group my ArewaBooks people. Mikiya writers Association Mikiya fans AUTAR MANYA❤🔥 Ubangiji Ya bar ƙauna.
Page 15
Last free pages
*What if I tell you, I love you?*
"kar ki ce ba ki sanni ba, kar ki ce haka dole ma tarihin rayuwarki ba zai taɓa cika ba sai da sunana, dole a same ni a cikin rayuwarki sai dai idan za ki cire wani sashi na cikin tarihin" ya furta yana huci da gwame numfashi Safiyyerh was shocked and speechless at the same time ta kasa kallon shi wani irin tsoro shi take ji mai girma ya ratsa zuciyarta. A hankali ta ɗago kanta zuwa gare shi hawaye na taruwa cikinsu yana sauka akan fuskarta
Ta ƙura masa ido da sauri kuma ta girgiza kai ta ce "Wallahi da gaske ban san ka ba, ban taɓa ganin ka ba sai kwanakin nan, i don't even know your name balle kai,me ya sa zan sanka to?" za ta sakar masa kuka ya ɗora yatsarsa a baki ya ce
"Shhhh" ba shiri ta yi shiru tana sauke ajjiyar zuciya shi dai har lokacin fuskarta yake kallo yana murza tsinin wuƙar a ƙasa. "To kai ka sanni ne? Ni ka cire mini wuƙar nan ka ji ɗan baƙi" ta furta tana juya idanu ta langwaɓar da kanta gefe guda.
"Ki daina kiran sunana daga yau"
"Sai na dinga ce maka me to? Ka faɗa mini ban ma san sunan ba ai" ƙoƙarin biye mata yake wajan ganin ya samu abin da yake buƙata amma a duk kalma ɗaya daya furta ko kafin ya furta sai ya fama hautsina kan shi kafin ya san me zai furta mata. Wuƙar ya ɗauke ya cilar gefe guda ya juya ya kalli Goje jira ya ke yi safiya ta yi ya fara tunanin yadda zai samu likita ya ji ta ce
"Kai ne ka yanke su ko? Ba kyau wallahi ka mutu a haka wuta zaka tafi babu fashi kana kallo za mu shige aljanna muna jiyo ihunka a cikin lazza ko saƙara tunda baka da wani aiki a rayuwarka sai daba da bushe-bushe cikinka ba komai sai ƙwaya da hayaƙi, gabaɗaya gudanawa kake daka zaɓi wannan rayuwar ne ɗan baƙi? Bayan rayuwa akwai mutuwa fa karka bari ka mutu cikin wannan halin ba zaka ji da kyau wajan Mala'iku ba"
"Kina da ɗan'uwa mala'ika ne?"
"Subuhanallahi, kai ko wa'azin baka so kamar jinin fir'auna ni tausayinka kawai nake ji tunda baka gani shikenan" ta haɗe fuska irin ta ji haushin nan har ƙasan zuciyarta ita ƙyamar shi take yi rayuwarsa a gurɓace take babu wani abu na birgewa ko ban sha'awa a ciki deep down kuma tausayin rayuwar tasu take ji tana jin da tana da iko tabbas ba zata taɓa gazawa ba wajan ganin ta taimaka musu. Ya rufe idanunsa yana daga zaunen saman kujera ya ɗauki ƙafa ɗaya ya ɗora akan ɗaya ya fara yin fito wanda ya cika ɗakin a hankali kuma ya zaro sigari zai kunna ta yi saurin cewa.
"Matsalar daƙiƙi kenan a rayuwa, shi da kansa bature ya ce tana lalata lafiya dake babu arabi ba boko ba'a gane komai ai shikenan, goodness Safiyyerh what exactly wrong with you, that's not your business" ta faɗa lokaci guda kuma tana miƙewa tsaye sai dai bata kai ga zuwa inda ta yi niyya ba ta gan shi tsaye a gabanta hannunsa riƙe da sigarin yana zuƙa da fesarwa, ta saka zata rufe hancinta ya sa hannu ya tukare jikin bango ya sata a tsakiya sigarin a bakinsa yana binta da jajayen idanu bakinta na rawa ta girgiza kai ta ce "Mene haka wai?" Ya yi shiru yana duƙawa fuskarsa dab da nata har lokacin ita ɗin da yake kallo
"Iskanci ne wannan matar aure ce ni fa, saboda ƙwaƙwalwarka bata faɗa maka daidai ko? Idan ka sato ni a gidan mijina shine yake nufin me? Zan barka ka yi yadda ka so ko ƙazamin jikinka ya taɓa fatar Safiyyerh ba zan taɓa yafewa kai na ba, da babbar murya ina faɗa maka ni Safiyyerh matar aure ce ka ji ko? Kana jin Hausa ai?"
Ya zare sigari hayaƙin daya zuƙa ta cikin bakinsa ya dinga fesa mata a fuska ta fara tari tana ɗauke kai, ya ƙara zuƙar sigarin a baki ya matsa dab da fuskar tata ya sake fesa mata lokacin ta buɗe baki za ta yi magana gabaɗaya ta haɗiye hayaƙin, a gigice ta fara tari tare da kakarin amai ganin da gaske aman za ta yi,ya matsa a wajan tare da shigewa wani ɗakin. Safiyyerh ta durƙusa tana riƙe ciki saboda wani irin ciwo da yake yi mata ga amai dake ƙara hautsina mata kayan ciki ta rasa yadda za ta yi ta kwanta tana riƙe cikin da dinga rusa kuka. Duk abin da ya fara Goje na jinsu kawai yana cikin wani hali ne tsautsayi ya saka su fita a daren sukai karo da ƴan daban cikin gari sun shigo ɗaukar fansar wani faɗa da aka yi can kwanaki shine suka rufar musu, a cikin ƴan daban cikin garin wanda yake jagorantar su me suna Bakin wuta shine ya sare su shi kuma Moh sai da ya sari wajan mutum goma a yaran Bakin wuta wanda kuma shine faɗan su na farko a rayuwa ba wanda ya san wani, a cikin yaran ba sai da aka buɗewa wani ciki kuma duka aikin Moh ne yana da tabbacin kuma Bakin wuta ba zai bari haka nan a ci bulus akan shi ba.
Goje ya juya kaɗan ya kalli Safiyyerh dake kuka sosai kamar ranta zai fita itama yarinyar naci gare ta ga bakin tsiwa da Moh na taɓa mace da tuni Safiyyerh bata duniya ya san ba zai iya kashe ta ba amma zuwa gaba zata gane bata da wayo idan ta cigaba da kai shi bango. Tana kukan a haka bacci ya ɗauke ta bata ji kiran sallah ba amma tunda ta motsa bakinta ɗauke da addu'a ta san asuba ta yi ta miƙe da ƙyar ta nufi banɗaki ta yi alwala ta jima tana azkar kafin ta yi raka'atul fijr kana ta yi sallar asuba. A hankali ta dinga leƙa shi abin da ya bata mamaki bai shige ganinsa durƙushe a kan qwiwinsa ba yana kallon gabas ba kuma sallah ya yi ba, kan shi a ƙasa ya yi shiru kamar zata shiga sai kuma ta fasa ta tsaya cak ta samu kanta da yi masa addu'a samun sauƙi da mafita a rayuwarsa da shiriya idan yana da rabo.
"Allah Ya shiryarka idan kana da rabo"
Ya ɗago kan shi ya juya kaɗan suka haɗa ido, ba ƙaramin gigita ta yi da ganin idanunsa a haka ba, ya ƙura mata ido a ransa girman nacinta yake ƙara jinjinawa duk da bai yi mamaki bai kuma zama sabon abu ba, bai fiya son takura ba wani lokacin. Safiyyerh ta harɗe hannayenta a ƙirji ta ce "Ko yunwa kake ji na daba maka abinci? Ko shayi?"
"To na zo na yi maka shira? Ko waƙa?"
"Get out..."
Ya ce a hankali muryarsa ƙasa ta buɗe ido jin ya yi turanci ta ce "Wow ashe a ɗan san wani abu, nifa ba zan fita ba bakina ciwo yake na rashin magana gaskiya" kafin ya yi magana ta shiga cikin ɗakin ya yi saurin tashi da ƙyar ya nufi kujera ya kwanta ƙafarsa ɗaya a armchair ɗaya a can saman kujera hannayensa ya harɗe a ƙirji idanunsa rufe. Safiyyerh ta zauna a ƙasa ita kanta bata san me ya sa take son yin magana da shi ba, ta ji kuma tana barin wajansu zata haɗa Kinal da shi ita take son auren ɗan daba a hankali muryarta a nutse ta ce "Sunana Safiyyerh Abdu Marafa, ni ce auta a gidanmu..." Ta ɗan yi shiru bata ga alamar yana ma jinta ba kamar bacci yake yi haka yanayinsa ya nuna bata karaya ba ta sake matsawa ta ɗora da faɗin.
"Mahaifina professor ne ya koyar a jami'o'i da yawa a wannan ƙasar cikakken lakcara ne matasa na son shi sosai saboda yana taimaka musu da shawarwari. Ina da yayyi huɗu babban yayenmu sunansa Aliyu muna ce masa Captain shi soja ne, bashi da kirki gabaɗaya baya dariya kamar kai ɗin nan amma shi ba baƙi bane fari tas, yana da ilimi he is educated, sai mai bi masa Dr Hash likita shi a ɓangaren kwakwalwa Neurologist, shi rayuwarsa ba sawa ba hanawa sai my favourite Yaya J sunansa Junaid shi aiki biyu yake yi aikin banki da business, ina son shi sosai kamar yadda yake so na, rayuwarsa abar sha'awa ce wallahi. The last one Awais Shi kuma ɓangaren siyasa yake so amma daddy baya so yanzu dai ya ce yana son zama shahararren ɗan kasuwa ne, sai kuma ni Safiyyerh nima na yi karatu ina aiki yanzu matsayin Manager a FS WORLD INVESTMENT COMPANY, ina da saurayina da nake so kuma yake so na Ashraf sunansa ɗan mai kamfanin da nake aiki ne, akwai wasu abubuwa da bana ganewa a kamfanin..." Shiru ta yi da sauri kuma ta kalle shi taga har yanzu idanunsa rufe yake bai motsa ba
"Kodayake shikenan, saura kwana ɗaya auren mu da Ashraf ya rasu, Ashraf died ya mutu ya bar ni cikin tsoro da fargaba, a ranar daya rasu a ranar ne aka aura mini yayana Aliyu, da dai bana jituwa da shi sam amma ƙaddara ta haɗa kuma Ubangiji kaɗai ya san dalilin hakan, wannan shine labarin Safiyyerh Abdu Marafa"
Ta leƙa fuskarsa taga idonsa still a rufe ta tura bakinta gaba "Nima sai ka bani labarinka ai muna zaune waje guda bai kamata bamu san juna ba" miƙewa taga ya yi ya nufi ƙofa kafin ta bi bayansa har ya fice daga cikin gidan.
****Eng Ali wali ya dinga kallon Moh da yake tsaye kafin ya ce "Ina wayar daka amsa wajena? Mene amfaninta ina kira baka ɗauka wai?"
"Ba gani gabanka ba?" Moh ya ce yana kame fuskarsa kamar kodayaushe.
"Yarinyar nan tana wajanka ko Mutallab?" Moh ya yi tsaki a fili da ƙarfi kuma ya ce "Ni a tarihina sau ɗaya ake faɗa mini magana na haddace ka yi batu kawai" ya ƙarasa maganar yana jawo flask ɗin shayi ya tsiyayi ruwan zafi ya saka madara da su milo ya nemi waje ya zauna ya janyo biredi da plate ɗin ƙwai ya fara ci duk zafinsa da taurin kan shi a nutse yake cin abinci sai dai baya laumar wasa
"Daman kai aka kawowa abincin karin Mutallab? Ai shikenan magana nake so mu yi very important akan yarinyar nan daka ɗakko" ya yi shiru can ya ce "magana nake maka fa ka yi shiru"
"Kunne ke ji"
"Professor ya raina mini hankali wai ko kashe yarinyar nan zan yi ko a jikinsa yana nufin bai damu da ita bane ko mene? To wallahi ni Ali wali zan bashi mamaki, yarinyar nan kafin ya ganta sai ikon Allah don haka ka yi yadda na ce a kanta, ka yi mata fyaɗe ka yi yadda ka so da ita har ta samu ciki yadda zamu watsa labaran yarinyar professor Abdu Marafa ta yi cikin shege ya kore ta daga gida ni kuma na ɗauke ta na kula da ita har zuwa haihuwa,kaga daga nan hankalin jama'a zai yi kan Professor Abdu a bar batuna ni kuma na yi amfani da wannan opportunity wajan cin nasara a zaɓen da yake gabatuwa, don this time ba zan taɓa barin Hon Maɗatai ya yi nasara a zaɓe ba zan yi duk abin da zai tabbatar dani ne na ci zaɓe ko a can hukumar zaɓan inec na shirya tsaf ba gudu ba jada baya siyasa sai ɗan siyasa, harkar siyasa da zama wani a harkar ƙasar nan sai ka nuna ba wani shege ka cire tausayi da imani, ba ri ka ji Mutallab duk wani ɗan siyasa kan shi kawai ya sani" ya numfasa yana ɗaukar ruwa ya sha.
Moh dai har lokacin shayin yake sha hankali kwance abin shi. Ali wali ya duƙa ya ce "Dole ka yi wa Safiyyerh fyaɗe dole ne ka yi wa yarinyar nan ciki, samun cikinta shine plan ɗina na farko da zai kai ni matakin hawa kujerar ɗan majalisa"
"To ya ake cikin?"
"Baka san yadda ake yin ciki ba, ciki na haihu fa?"
"E, ban sani ba"
"Mutallab, da ake cewa ka yi aure a ranar an kashe maka matarka da me za ka yi da auren da ka yi"
"Bayan a yi wa mutum girki ya ci ya yi bacci akwai wani abu ne? To ni ban iya yin ciki ba, sara da soka kawai na sani a rayuwa da shiga jeji, ka bar batun hakan bani ba ko waye ba za a yi mata wani abu ba"
"Moh"
"Ali wali" Mutallab ya ce yana yin kyatsa yana miƙewa tsaye kuma. "Mutallab yadda aka fara aikin nan da kai, to da kai za a ɗora kuma a ƙarashe dole zaka yi wa Safiyyerh fyaɗe i am telling you this, za ka ce na faɗa maka"
"To ka fara bani matarka na yi mata ai kana da ita, sai kace Professor ɗinne ya yi mata" Ali wali ya dinga kallon Moh ganin how serious he is da maganar kuma da gaske yake. "Ni zan shige zan na ji kira idan ka shirya bani matar taka tunda yarinyarka Noor bata ƙasar"
"Ina kasan ina da yarinyar Noor?"
"Ali wali kenan"
Hanyar fita ya yi kamar wancan karan ya ƙara jin sauti mai kama da ihu ya dinga kallon ƙofar kafin Ali wali ya ƙarasu har Moh ya buɗe ƙofar ya shiga cak ya tsaya ganin wata mahaukaciya zaune sai ihu take ita kaɗai gashinta ya rufe mata fuska ya juya ya kalli Ali wali ya ƙara kallon matar bai