Showing 39001 words to 42000 words out of 63481 words

Chapter 14 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt

23 Nov 2024

6686

ranta zai fita wai wanne irin abu ne haka? Ta shiga uku meke faruwa aure fa, auren ma da Captain innalillahi wa'inna ilaihirraji'un addu'a take Allah ya yafe mata komai ta fahimta da ƙyar bacci ya ɗauke ta ko abinci bata ci ba. Cikin dare ta farka ganinta ta yi rufe da bargo ta yi saurin buɗe ido don bata san kwanciya a duhu gashi an kashe mata hasken ɗakin babu mamaki Yaya J ne. Gani ta yi wajan ɗaya da rabi ta miƙe ta ɗauki ɗan makullin mota da wayarta ta saka hijabi har ƙasa, ƙofa ta buɗe ta sauka downstairs ba kowa ta buɗe ƙofa ta fita mota ta shiga mai gadi ya buɗe mata cikin sauri ta nufi kamfani gari shiru sai hasken fitilo na titi ta dinga duban hanya ba wanda ke biye da ita a haka ta isa kamfanin ta ajjiye motar a waje, ciki ta shiga wajan mai gadi sun jima suna magana ya ce "Ana shigo da mata cikin dare ana kuma fita da su, na yi bincike abin da ya saka ke iya ɓangaren abinci kika sani to akwai asibiti a cikin wannan kamfanin" ta ce "Ka ɗauki number motar ko haddacewa?"


"A'a ranki ya daɗe"


"To shikenan na gode Baba, ga wannan" ta ɗauki kuɗi ta bashi a cikin aljihun rigarta. Tana ƙoƙarin buɗe gate ɗin kamfanin ta fita kawai ta ji ƙarar dingowar mutane, ta juya da sauri suka haɗa idanu da Darma da kuma Goje da Mangal wani irin mummunan faduwar gaba ne ya sameta lokacin da idanunta ya shige cikin nasa shi bai kai ga dingowar ba yana zaune saman katangar shima ɗin ita yake kallo babu ƙiftawa...


MUTALLAB PAID BOOK ne a jerin littafan bright pens. We're still on free pages kar ki bari a yi bake.
MUTALLAB.
Book 1, 2 &3
500 Naira
0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385 via WhatsApp only.




DOMIN INGANTA NONO🔥
Assalama alaikum


Hajiya muna da ingantaccen maganin gyaran nono wadda ya amsa sunansa magani


Maganinmu ingantaccen maganine da yake tada jijiyon nonon da suka saki y'ar uwa breast dinki ko yakai silifas saboda kwanciya kikai amfani dashi in sha Allah zakiga amfaninshi acikin 1week maganinmu powder ne yana ciko da breast y gyarasu bashi da illa ajikin mutum munyi amfani da saiwoyi da magunguna gargajiya domin gyaran breast 08063114606 ina garin kano karki sanya y'ar uwa nono yana karawa mace martaba a gurin mai gida maganinmu kowa zai iya sha wadda zatai yaye ko gyara budurwa duk zasu iya sha breast dinki ya ciko yayi bull -bull
[10/18, 9:23 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥*


Page 11
*Bright pens.. 2nd batch*


Ya ƙura mata idanu yana daga zaune saman katangar a hankali yake girgiza ƙafarsa, fuskarsa rufe da baƙin ƙyalle a lokacin duniyar ya ji tana masa daɗi yana jinsa kamar a cikin jirgi ana juyawa dashi, shi ya sa yaƙi sakkowa ƙasa daga katangar, shi kansa bai san wacce irin ƙwaya Mangal ya kawo masa ba. Fiyya ma shi take kallo ganin shi kaɗai ne ya rufe fuskarsa Goje da Darma da Mangal suka zagaye ta, ta juya ta kalli securityn da yake on duty ranar ta nuna masa Goje


"Su kuma waɗannan fa security?" Kai tsaye ya bata amsa da "Ban san su ba, amma Hajiya akwai hatsari bamu san me suka zo nema ba" Goje ya matsa kusa da ita yana kallon ta


"Mai dawa wannan ce ƙuruciyar? A hotun kamar bata kai haka girma ba, ƴar firit da ita kamar benu, nan kuma an ci kuɗin jama'a an sha madara da milo an yi ɓulɓul" sai ƙarewa Fiyya kallo yake ita kuma ta yi tsaye tana jin yadda warin wiwi ke dukan hancinta kamar za ta yi amai amma taƙi matasa saboda taurin kai irin na Safiyyerh Abdu Marafa da rashin tsoro. Tsaki ta yi kawai ƙasan zuciyarta kuma tsoro ne fal ga ƙirjinta dake bugawa kamar zai fito waje sai buɗe manyan idanu waje take yi.


"And what is my business with you? Me kuke nema a wannan kamfanin kun zo sai warin ganye kuke mini" Mutallab ya sake buɗe manyan idanunsa jin sautin muryarta zaƙwai a cikin kansa ya kalli bakinta dake motsawa cike da masifa duhun dare ne amma kamfanin haske tar tar ko'ina. Mangal ya lailayo ashar ya dannawa Safiyyerh "ke dan ƙaniyarki mune muke warin ganyen, su waye sila idan baku ba, ƴar wahalar yarinya idan ban bawa tiger namanki ɗanye ya cinye ba"


Safiyyerh ta juya ta kalli tiger daya hauro ya zauna kusa da Moh, yana zaro harshe waje ta nuna karan da hannu ta ce "abin da ya fi namana ɗanye, banda rainin hankali jikin nawa zaka ɗauka ka bawa shegen karan naku, idan kuɗi kuke buƙata na baku don nasa na yin caji kuke nema, stupid" Goje ya juya ya kalli Mai dawa ya ce "ba zamu rage wa yarinyar nan tsayin harshe ba kuwa? Kauɗinta ya yi over, ka je ka zauna matsalar idan ka sha wannan ƙwayar baka gane komai yanzu babu mamaki jinka kake a saudia"
Moh ya lumshe idanunsa ya sake buɗe su a kan Fiyya duk motsin da take yi a kan idanunsa sai dai ba wani fahimta yake ba muryarsa a cunkushe mai ban tsoro ya shafa kan tiger ya ce "shiit"


Tiger ya diro shima ya diro ya tsaya a kan ƙafafuwansa hannunsa ɗaya yana murza gashin kansa wanda ya zama wani iri ba kyan gani na shegun shahararrun ƴan daba ɗin nan.


"Mai jeji ƙirit ka ankare ba lokaci ka ɗaƙkota a kafaɗa mu fece kafin kwalawa su kawo kai dan akwai kimini a nan wancan mai fararen kayan" ya nuna securityn wajan wanda shi kaɗai ne kawai ya rage. Safiyyerh ta ja baya tana juya idanunta ta ce "ban gane ya saɓo ni kafaɗa ba kamar wata ƴar iska ko mara gata, kai naga alamar kai ne shugabansu ko? To wallahi ba wuƙa ba ko bindiga ce bana tsoro kana taɓa ni sai na raba ai an ce ba wani ƙwari ne daku ba" ta ƙare maganar tana kallon cikin idanun Mutallab wanda tun ɗazo shi take kallo shi kuma yaƙi furta komai.


"Ki iya harshenki ƴar kanzagi ko na fitar miki da jini yanzu na shata miki bille a wannan fuskar kamar gwada" juyawa ta yi ta ce "Baba wai where are the securities? Where are the rest ka kira su yanzu" kafin baban ya motsa Mangal ya saka ƙafa ya kwarfe shi zuwa ƙasa, ya sake saka ƙafa ya danne masa baki. Darma ya zaro wuƙa ya ce "Ke fitsararriya ce ko? Ba wata uwar muke nema ba ke muka zo ɗauka, don ke muka cikin wannan kamfanin ke za mu yi kidnaping yanzu kin fahimta kin gane ko, ki shige salin alin ko na ɗauke ki yanzu na haura dake wallahi"


Fiyya ta buɗe idanu tana kallon wuƙar dashi kansa Darma ɗin ta yi murmushi zuciyarta kuma bugawa tsoro ya shige ta, ƙoƙarin danna recoding take a wayarta hannunta ya shiga rawa ta dake a ƙasan zuciyarta tana kiran sunan Allah da ƙyar ta furta "kidnaping kuma ni, ni Safiyyerh Abdu Marafa za ku sace, ni Safiyyerh matar soja guda kuna hauka ne ko kuna tunanin mijina zai bari hakan ta kasance?"


Jin furucin Safiyyerh ya saka Moh sake kallonta da sauri yana hana zuciyarsa abin da yake ji, haka kawai ya dinga jin tafasar zuciya ya nufi wajan Safiyyerh jikinsa na rawa idanunsa suka fito waje kamar zasu faɗo da muryar mai ban tsoro mafi muni ba muryar ba ita kanta fuskarsa abar tsoro ce tsaf mutum zai dinga mafarkin ta. Hannunsa riƙe da wuƙa yana kallon cikin idanunta da kyau dab da ita ya ce "Ba mijinki ba ko ubanki Abdu Marafa aka bani umarnin daƙƙowa ko kashewa sai na yi balle ke" ya cije bakinsa ya feshi ya cilla mata ƙatuwar baƙar kunama ta shige ƙirjinta kai tsaye, zufa ta dinga yanko mata saboda tsananin azaba ta kasa ihu ko kuka ga warin da yake yi yana neman kashe ta, idanunta ya juye ya yi ja ta zuba masa idanu tana kallon fuskarsa data yaye,ta miƙa hannu da nufin shafo fuskarsa ta ji ya caka mata wuƙar a gefen cikinta ta yi wata ƙara tana buɗe idanu duk yadda jikinta ke rawa ga jini na zuba mai hanata sake kai hannunta ta shafo fuskarsa ba, daidai nan ya yunƙura zai saɓata a kafaɗa suka ji shigowar motoci na jami'an tsaro, bai niyyar barinta ba yadda Goje ke jan shi da ƙarfi ya saka kawai ya sake ta a wajan yana furta “Mutallab”
Ɗaya bayan ɗaya suka kama katangar suka haure daman kuma kaf kamfanin ita ce ƙaramar katanga wacce babu kwalabe jikinta.


Securities kala biyu ne dana fararen kaya da masu uniform sai shi da yake sanye da wando three qauter da farin takalmi da riga baƙa ko p.cap ɗin kansa babu, ya nufe ta sauran suka nufi wajan baba suka fara ɗaukan statement "Baba kwantar da hankalinka babu abin da zai sameka in sha Allah, bayan waɗannan ƴan daban da suka zo, an bamu tabbacin a daidai yanzu Scorpion ma yana wajan nan ko kuma ya zo" a hankali Aliyu ya juya ya kalli baban jin tambayar da ake masa, sai kuma ya ɗauke kai ya saka hannu ya ɗauki Fiyya zuwa cikin mota bayan ya kwantar da ita ya tsaya yana kallon wanda ke ɗaya motar a tsaye da yake ce masa "Ya akai kuka barta ta fito cikin dare haka? Macace ita fa"


"Sir ƙuruciya, thanks for the call"


"Anything for you Captain Aliyu" suka shiga mota duk suka bar wajan ya rage sai jami'an F.i.d kawai da suke tambayar baba.


Su Goje cikin kwalabati suka shige suka ɓoye suna zare idanu da muzurai a hankali ya ce "Akwai matsala jami'an tsaro ne fal yasin, baka dai bar sheda ba kuma me ya saka ka caka mata wuƙa idan ta mutu fa?" Moh ya yi shiru can ya ce


"Ba zata mutu ba"


"A ciki ka soka mata wuƙar fa? Baka kalli yadda jini ke zuba bane da zaka ce wai ba zata mutu ba?" Kai tsaye Moh ya ce "ba zata mutu ba"


"A buge kake shi ya sa, askira ka caka mata fa na ɗauka tsoratar da ita kawai za ta yi"


A firgice ya kalli Goje idanunsa kamar za su faɗo "Goje, idan ka sake maimaita mini cewa na saka mata wuƙa zan maka jahilci yanzu wallahi zan iya kashe ka"


"Kashe ni mana daman ai daba babu wata amana a ciki dole na faɗa, ɗaƙkota aka ce kawai ka yi ba kashe ta ba" Mutallab ya wani juya cikin zafin nama ya damƙo wuyan Goje cikin sauri Darma ya shiga tsakiya ya ce "Sai godiya kar a yi haka akwai amana, kai Goje ka iya bakinka idan ba farkawa kake so ka yi ka ganka a ƙiyama ba" Moh ya cije bakinsa kansa na wani irin sara masa yana girgiza kansa ya kalli sama "duk sanda na sake ganinta sai na kashe ta don uwarka" duk sukai masa shiru sun daɗe a wajan kafin jami'an tsaron su bar wajan suka fito tare da barin wajan suma kallo ɗaya za ka yi wa Moh ka ɗauke kai saboda yadda yake huci ya fiddo da ƙarin jikinsa neman inda zai sauke kawai yake.


The following days.
I. Qasim ya ce "Tunda ta bar I.c.u ai Allahamdulilah, she will soon recovering"


"Dr Qasim ba dai abin ku kuke mana na likitoci ba, ya jikin Maama don Allah ita ce kawai last hope ɗina" Dr Qasim ya yi murmushi ya ce "Safiyyerh zata ji sauƙi in sha Allah, ba'a caka mata wuƙar inda za ta yi mata illa ba ta zubar da jini sosai ne sai kuma zuriyarta data ninka gudun da take yi, ka yi mata addu'a"


"Shikenan Allah Ya bawa Maama lafiya,zan iya shiga ai kwana biyu ba'a barin mu shiga sai na ji kamar har yanzu bata dawo hayyacinta ba" I. Qasim ya girgiza kai ya ce "Daddy kana son Safiyyerh da yawa, shiga ka ganta" har bakin room ɗin da take ciki ya shiga ya shiga sanye da kayan daya dace a shiga aga mara lafiya. I. Qasim ya juya ya fita daddy ya zubawa Safiyyerh idanu tana ƙwace ta sake yin fari a barka da farar mace ta ɗan faɗa an ja mata rigar marasa lafiya zuwa saman ƙirjinta duk da baya kaya a jikin sai iya rigar an buɗe wajan ciwon da akai mata aiki a wajan ya zuba mata idanu ya matsa a hankali yana kama hannunta addu'a ya shiga yi mata sosai ta samu sauƙi zuciyarsa duk babu daɗi idan ya rasa Maama bai san yaya zai yi ba kuma.


"Allah Ya baki lafiya Maama, don Allah ki rage wa kan ki fitina da zaƙewa cikin wasu al'amuran kalli yadda za ki saka rayuwarki ta lalace, Safiyyerh ban shirya ba ban shirya ba Safiyyerh" ya damƙe hannunta yaga bakinta na motsawa amma sam baya jin me take cewa. Ta shi ya yi ya fita yana sake yi mata addu'a a ransa na samun sauƙi da rangwame.


Bayan ya fito waya ya saka ya kira Aliyu yana ɗagawa ya ce "Aliyu kana ina ne, an fito ita daga i.c.u amma babu kai a wajan bana son haka fa, da baya da yanzu ba ɗaya bane matsayin Safiyyerh ya jima da sauyawa"


"Allah Ya sauwaƙe"


Kawai Aliyu ya furta ta cikin wayar daga nan ya yi shiru ran daddy ya sake ɓaci yana jin kamar ya yi kuskure na aurawa Aliyu Safiyyerh na damƙa masa dukkan ragamar rayuwarta da tunanin zai kula da lamarin Safiyyerh amma ba lallai hakan ta kasance ba, sosai abubuwa da yawa ke damun zuciyarsa yana hana shi sukuni tare da rashin isasshen bacci, idan Safiyyerh ta tare a gidan mijinta dole ne ya amshi responsibility da Ubangiji ya ɗora masa na mijinta.


Ummi na kallon daddy da jajayen idanunta ta ce "Ina ta zuba idanu rayuwar yarinyarta na neman lalacewa, ka yi abubuwa da yawa Professor na ja baki na yi shiru da tunanin duk abin da ka yi daidai ne, zuciyata ba zata ɗauka ba Safiyyerh gabaɗaya nawa take ni kawai ta haƙura da aikin wannan Companyn da bana gane masa ai shekarunta bai kai ya kawo ba, ban shirya rasata ba" daddy ya yi shiru yana kallon yadda Ummi ke kuka.


"Ki tashi muje dare na yi" da sauri ta kalle shi tana share hawaye ta ce


"Kuma ban gane muje ba zuwa ina?"


"Ai kin san majinyata basa kwana a wannan hospital ɗin, patient ne kawai yake da alhakin kwana" tun kafin ya kammala magana take girgiza masa kai "i don't think zan iya barin wannan asibitin da Safiyyerh ita kaɗai, ni bana ma ganewa irin haka ka yi musu magana ko a nan zan iya kwana I'll manage" Daddy ya yi gaba yana furta "Kar na sake maimaita miki" dole ta miƙe bayan ta sake leƙa Fiyya ta yi waje.


Kafin a rufe shigowar masu ziyara Yaya J ya daɗe zaune gaban Fiyya yana kallon fuskarta, da kwanakin baya ne zai riƙe hannunta cikin nasa yana ta mata sannu da addu'a yanzu kallon ta kawai ya kasa koda yin addu'ar ma, can ya miƙe ya fice haka Awais da Dr Hash duk suka shigo basu da tabbacin bacci take ko farkowa ne ba ta yi ba. Wajajen 2 na dare ya buɗe ƙofar ya shigo bayan I. Qasim ya bashi damar hakan daman aikin kwana zai yi idanunsa a kanta har ya shigo ya rufe ƙofar a hankali ya tsaya gabanta hannunsa biyun zube cikin aljihu ya ɗauki minti a ƙalla ashirin kafin ya ƙarasa ya zauna bakin gadon har yanzu bacci take ya dubi hannun da ruwa yake shiga ya dubi ɗaya hannun da jini ke shiga a hankali ya kama hannun drip ɗin da yake ɗan mitsi-mitsi ya riƙe cikin nasa a hankali yake murza yatsunta can ya ji ta riƙe hannunsa ya ɗaga kai yaga tana jujjuya kanta sai a lokacin ya lura da sauyin ƙarar da na'urar ke yi.


Safiyyerh tana buɗe idanu ta rufe saboda wani fau ɗin haske daya shige mata ciki sai kuma hawaye ya fara bin idanunta ya ɗan sunkuya yana kallon fuskarta. Ta sake buɗe ido ta kalle shi ta dudduba taga ba kowa ta rufe idon still ta buɗe har lokacin jujjuya kanta take yi "Yaya" ya yi mata shiru ya sake cewa


"Me na yi musu?" Still shiru ya yi mata ta buɗe idanu ta kalle sai ta fashe da kuka sosai ƙirjinta na ɗagawa ya damƙe hannunta


"Yaya"
"Safii..." Ya kira sunanta a hankali ta ce "Kai na zai cire ƙirjina ciwo cikina ciwo yaya mutuwa zan yi"


"Allah Ya yi miki Rahma" sai kuma ya matsa dab da kan nata ta saka hannu ta riƙe nashi ta yi shiru a hankali ta sake cewa "Captain"


"Manager"


"Na ce musu mijina soja ne, wai ko sojan zasu kashe balle ni" ta yi shiru ta sake cewa "Ka riƙe mini kai na ciwo yake mini sosai na shiga uku daddy wayyo" maimakon ya riƙe kan nata sai ya ɗora goshinsa saman nata, ta buɗe idanu ta kalli fuskar Captain kamar zau haɗe da data a nutse ya ce "sun kashe kin?" Ta girgiza kai


"Me ya sa?"


"Ban sani ba" ya ɗan murza mata goshinsa yana kallon cikin idanunta ya ce


"Saboda ke matar soja ce" ta yi shiru kawai tana kallon shi can ya matsa yana sauka ya zauna saman kujera.
Washegari da sassafe ƴan sanda suka shigo room ɗin lokacin tana zaune ta ɗan jingina da jikin gado, statement na abin da ya faru suke tambaya. Sp Ghali ya kalli Safiyyerh data sunkuyar da kanta ƙasa ya ce "Da suka zo sun faɗa miki abin da suke buƙata?" Ta girgiza musu kai.


"Za ki iya gane wani daga cikin su? Suna ko kammani?" Ta ɗago ta kalli Sp Ghali dake tsaye ta ce "Idan na gane kamannin sai me za'a yi to?" "Zamu kira a zana mana fuskar wanda kika gane ne"


"To ban gane ba"


Duk suka tsora mata idanu musamman daddy ta buɗe idanunta itama ta ce "Kamarya? To na gane ne?" Daddy ya ce "Maama wa kija

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login