Showing 51001 words to 54000 words out of 63481 words
Chapter 18 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt
tuba jama'a an cire idanun Hameeda gatan na ammo ta shige jama'ar gida Hameeda ta mutu a kawo mana ɗauki" a gigice Inna Binta ta zari mayafi tana ficewa zuwa maƙota. Mama kuma ta yi shiru idan haka ne ba ƙaramin gigita mutuwar Hameeda ya saka ta ba. Ammo bata ce komai ba a ranta tana nanata kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Ita kawai ta yi mata saura a cikin baki "Ba a tabbatar bata, saboda haka ki taso muje a gani ƙila ki fini ganewa sosai" kafin Ammo ta yi magana Baba uwar mijin Anty Hameeda ta shigo tare da mijin idanunta ya yi ja cikin sauri Mama ta ce
"Yaya lafiya dai Baba?"
"Ina lafiya, Hameeda ce daga fita siyo magani da daddare mun neme ta mun rasa kwana biyu kenan wallahi". "Shikenan ta tabbata an kashe Hameeda" kafin ka ce me cikin gidan ya cika Inna Binta sai rusa ihu take yi tana sun shiga uku an kashe musu yarinya. Koda aka kawo gawar Hameeda ba kowa ya iya gani ba kamar dodo har ta fara wari an cire kyakkyawan idanun nan nata. Ammo ta dinga tuna nasihar Hameeda ta ƙarshe da ta yi musu,daga nan bata sake dawowa gidan ba wani abu ya tokare wuyan Ammo ta kasa magana balle kuka sai kallon gawar take cike da sarewa.
****Kamar kullum yau na Goje ya buɗe ƙofar tana durƙushe duk ta fita daga cikin hayyacinta idanunta ya faɗa ba zaka taɓa cewa Safiyyerh bace. Ya dire mata abincin yau dai pure water ɗin hadda sanyin shi "Kar ki sake buga mana ƙofa domin ba wanda zai buɗe miki"
"Ka ɗauke bana ci"
"Dar kin yi kyan kai ƴar kurciya" ya juya baya ta faki idanunsa ta zare ƙaramar wayar data gani a jikin aljihunsa ta yi saurin ɓoyewa. Goje kuma ya dawo cikin harabar gidan Moh ya gani zaune yana sake karanta takardar sai ya yi murmushi yana dafa kafaɗar Moh ya ce
"Ni dai na fara gajiya da siyo abinci gaskiya" banza Moh ya yi yana ninke takardar tun daren da aka kawo Safiyyerh bai sake ganin kamarta ba sai sautin kukanta da yake ji kullum yanzu ma kukan take tana buga musu ƙofa da ƙarfi a fusace ya miƙe tsaye ya nufi ƙofar ɗakin Goje ya bisa da kallo can ya miƙe ya bi bayansa. Da ƙafa ya daki ƙofar ta buɗe da sauri Safiyyerh ta miƙe cak kukan nata ya tsaya a maƙoshi ta tattare ta haɗiye ta mayar zuwa cikinta, fitsarin dake mintsinin mararta ya saki kansa ya fara zuba a gefen ƙafarta, dukkan wata gaɓa ta jikinta ɓari take yi. Ashe da bata san waye ba, bata san waye ya yi kidnapping nata ba sai yanzu cikakkiyar siffarsa ta bayyana zubi da tsarin da halittar da Ubangiji ya yi masa mai firgitarwa bata san waye mafi muni a cikin ƴan daba amma ta san wannan tantirin ne ko daga tsaiwar da ya yi, cikakken namiji a tsaye majiyin ƙarfi matashi kuma mai jini a jika da cikakkiyar lafiya shine matsayin ɗan daba tsaye a gabanta gefen fuskarsa wani zabcecen yanka wanda akai masa ɗinki har ya zama tabo. Salati take ƙoƙarin yi ta kasa ta gama jiƙa wajan da fitsari ƙiris ne babu numfashinta ya yi ƙaura daga ƙirjinta ta yi saurin ƙasa da idanunta.
"Ka yi haƙuri kar ka mini komai, don Allah ko nan waje ne ku bar ni na fito kalli skin ɗina zai lalace akwai ants a nan waje" ta tattare hannun rigarta tana nuna masa farar fatarta da ta yi wani irin tabo ritsi-ritsi kamar kwanciyar ji fuskarsa ta kumbura ta yi jaa sai susa take yi saboda ƙaiƙayi. Ta langwaɓar da kai ta ce "Ka gani ko na sake nuna maka har bayana" ta juya bayan tana ƙoƙarin ɗaga rigar ta ji ya daki ƙofar da mahaukacin ƙarfi kafin ta juyo ya bar wajan. Ta sauke ajjiyar zuciya feeling reliver ganin ƙofar a buɗe.
Tana fitowa suka haɗa idanu da shi da sauri ta juya kanta na bugewa da jikin bango, anya tana da hankali da lissafi kuwa? Fitsari fa a wando sai ya tsuke fuska. Suna zaune Mangal ya shigo yana hakki da sauri Goje ya zare wuƙa sama tiger ya yi zumbur ya miƙe tsaye yana gurnani Moh kuma kallon Mangal yake yana jiran ya ji suwaye suka biyo shi don yana da yaƙinin ba wanda ya san gidan da suke.
"Kai ɗan wahala mene su waye suka biyo ka?"
"Daga layin su Mai jeji naje an yi rasuwa kuma a gidansu Moh aka anyata lahira wallahi" duk suka juya suka kalli Moh shima ɗin kallon nasu yake fuskarsa ba wani sauyi kawai ƙarashen maganar yake jiran ji. "Sai aka ce waye ya baza? Iyayen Moh dai akwai sauran rai wannan dar in sha Allah"
"Wai ko Hamida ko Hamda, idanu aka ƙwaƙule mata ashe tana cikin mutanen da aka sace ta" Moh tunani yake yi ina ma ya san mai sunan Hameeda tasa Hameedan ba zata taɓa mutuwa a irin wannan halin ba, sam ba zata mutu ba duk da yanzu ba ruwansa da ita. Bayan wasu shuɗewar daƙiƙo zumbur ya miƙe tsaye kansa na sarawa a dagule ya furta "Amini?"
Da sauri kuma ya yi wani ɗaki suna shiga suka same shi yana cakawa kasan wata sabuwar allura da Ali wali ya basu da maye, bayan ya zuƙe ruwan a jikinsa ya ƙara ɗakko wata ya sake cakawa kansa sirinjin ana ukun Goje ya yi saurin matsawa ya ce "Easy Mutallab,zaka haukata kanka a banza kasan wacce irin allura ce ko dan baka jin turanci muma bama ji, haukatar da mutane take yi fa?"
Sakar masa allurar ya yi ya sake ɗakko wata Goje ya sake riƙe wa ya ce "Wallahi in dai ina nan ba zaka sake yi ba" ya ƙara sakar masa ya ɗakko fenta zai yi Goje ya ƙara riƙe, Moh ya shammaci Goje ya ɗauke shi ya damfara shi da ƙasa ya saka ƙafa ya take hannunsa hannun ya yi ƙara, ganin yana shirin kashe shi ya sa Mangal ya ɗakko abu ya makawa Moh aka, ya ɗauke ƙafarsa ya juya yana kallon Mangal da sauri Mangal ya zare Goje ya fito da shi daga ɗakin da gudu suka fice daga cikin gidan.
**The following days.
Buɗe ƙofa Captain ya yi ya shiga ɗakin a hankali wanda ya yi wa Aliyu mugun sani shi zai lura da ramewar da ya yi. Idanunsa akan Ummimi dake zaune gefen gado hannunta tsakanin cinyoyinta ta sunkuyar da kanta ƙasa ya ƙarasa ya duƙa gabanta ya ɗora hannunsa a cinyarta a hankali kuma ya leƙa kansa ta ƙasa ya kalli fuskarta suka haɗa idanu ta zabga masa harara lallausan murmushi ya yi mata a hankali ya ce "Love"
"Aliyu fita"
Ya girgiza mata kai ya yi shiru sai lokacin ta yi shiru tana ƙare masa kallo "Ciwo ka yi ne Gadanga?"
"A'a love"
"Kuma yaushe ka damu da Maama har haka ka dame?"
"Love, Safii is my wife" ta wani buɗe idanunta na rashin fahimta "Waye Safii?"
"Safiyyerh, your Maama" da sauri ta miƙe tsaye tana girgiza kai "Yaushe aka yi haka? Tunanin waye hakan decision ɗin waye wannan professor ko?" Gani take sauri take yi amma sai ta cire ƙafa ɗaya take mayar da ɗaya ta fice daga ɗakin a parlo taga duka mutanen gidan hadda police da team na musamman da suka fara bincike akan sace Safiyyerh Abdu Marafa. "Ashe daman baka yarda ba professor za ka iya mini haka? Bana baƙin ciki da auren da ka yi musu amma ina da hakƙi na sanin ka haɗa Safiyyerh da Aliyu aure, Professor burinka ya cika ƙudirinka ya tabbata ka aurawa Safiyyerh Aliyu" masifa Zahiyerh take yi tai Hausa tai turanci ta koma larabci ba wanda ya tanka ta, kan Abba a ƙasa. Da ƙyar Aliyu ya janye ta a ransa ya gode Allah da bata ce a raba auren ba tsaf zata iya. Ta nemi kujira ta zauna sai nishi take yi na rashin lafiya.
"Zo Aliyu" ya ƙarasa wajanta ta nuna masa kusa da ita ya zauna, sai kawai ta rufe idanu ta kwanta ta yi shiru a hankali ya fara danna mata kanta Dr Hash shima ya ɗauki ƙafarta data kumbura ya fara danna mata sai a lokacin Daddy ya buɗe idanu ya kalleta ya girgiza kai fatansa kafin ta farka Safiyyerh ta dawo gida.
"Sp har yanzu ba wani kira da muka samu akan batun sace Safiyyerh, ina zargin anya issues na kidnapping ne?". "Za su kira ai sun sauya salo ina mai tabbatar maka cewa za a kira Safiyyerh zata dawo gida" daddy ya jinjina kai ya yi shiru.
Wayar Aliyu ce ta fara ƙara yana dubawa yaga kamar private number har sai share sai ya yi tunanin ko masu sace Safiyyerh ne? Da sauri ya amsa kiran was the first abin da ya ji daya nemi buɗe masa zuciya sautin kukan Safiyyerh ƙasa ƙasa ya runtse idanu can ya ji ya ce "Yaya Please help ants za su cinye mini fata Yaya za su kashe ni"
"Safiyyerh listen"
Karo na farko daya kira sunanta "Take a heart peanut, ke matar soja zama jaruma". "Yaya am scared wuƙaƙe" ya buɗe idanu ya ga duk kallonsa suke yi hadda daddy Sp Ghali ya yi masa alama ya saka speaker. "Kina ji na?" Kamar tana gabansa ta ɗaga kai "Be strong Maama, daddy is here for you, Ummi kowa ma hadda ni am here for you ƴan mata, hadda Ummimi" da wani irin sauri ta ce "Ummimi? Ummimita Yaya?"
"Sure, ki nutsu wanne waje suka kai ki, za ki iya tuna suna ko wanne abu da zai bamu haske?"
"Yaya sun rufe mini idanu ban san komai ba, don Allah ka taimaka mini daddy help me please" idanun daddy ya yi jajur already anyi connecting na wayar an fara bincke da ƙoƙarin tracking daga ina wayar ke zuwa. Shima kuma daga can haɗaɗɗan ɗakinsa da suke zube da kayan na'ura kamar hauka ya saka abu a kunne ya ɗora ƙafa yana girgiza kai a hankali yana jin conversation ɗin Safiyyerh da Aliyu yana yi yana duba time da cije leɓe.
Abin da Aliyu bai taɓa yi ba kenan ƙoƙarin jan Safiyyerh da hira da ya ji Ummimi zata motsa zai yi saurin girgiza ƙafarsa "In sha Allah i will save you Safii, ki yi ƙoƙarin gane wani abu ki yi addu'a" tana ƙoƙarin sake magana suka ji ihunta da ƙarar buga wayar da ƙasa "Safiyyerh kina nan kina kan kayi baby?" Aliyu ya jere tambayar. Kafin sun an kare daddy ya sulale a wajan babu numfashi.
****Tunda su Goje suka fita yake abu ɗaya kamar wanda za'a zarewa rai, sai buge buge yake yana fasa komai na gidan kumfa na fita a bakinsa ihun da ya yi da gurnani shi ya saka Safiyyerh sakin ihu tana yin cilli da wayar a gigice ta miƙe har lokacin kayan bacci ne a jikinta, tana fita ta ganshi a tsakar gidan ya yi tumu-tumu wani irin mahaukacin tausayinsa ya ratsa zuciyarta ta duba babu kowa a gidan sai ta yi tunanin wannan opportunity ne da zata bar gidan hankali kwance, bata damu da kayan jikinta ba sai kawai ta nufi ƙofa da gudu tana ƙoƙarin fita ta ji muryarsa cikin mawuyacin hali kamar ana fisgar ransa abin da ta ji ya saka ta tsaya ta yi jim itama kanta na sarawa tana gani bibbiyu ta sake yunƙurin buɗe ƙofar ta ji ya ce "Safiyyerh....!" Ya faɗa da ƙarfi a gigice ta juya taga ita yake kallo yana ƙoƙarin tashi ya kasa yana miƙo mata hannu...
*MUTALLAB IS NOT FREE*
We'll soon end the free pages. ka yi payment a yi naka a paid group.
MUTALLAB.
Book 1, 2 &3
500 Naira
0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385
Ƴan Niger kuma ya gadda tsarin yake.
'Yan Nijar ku turo carte airtel ta 300fcfa saman wannan layin 84506476
[10/25, 11:14 AM] Nanameera: *This is not a love story,but a love that builds a story, and a love that destroys the story.*
*❤🔥 MUTALLAB ❤🔥*
Page 14
*Bright pens...2nd batch*
*Author's books*
Munafukin miji
Moon
Mijin malama
Tsintacciya
Idan ba ke
Sirrinmu
E.t.c
Follow on Arewabooks
Follow on telegram
Remain 1 free page
Jikinta rawa yake ganin ya kafe ta da idanunsa har lokacin kuma kakkarwa nasa jikin yake yana fesar da numfashi. Ina ya san sunanta? Take tambayar kanta. A hankali Moh ya lumshe idanunsa bayan ya janye su daga gare ta yana ɗan ciccije bakinsa.
Safiyyerh ta kasa fita, idan ta bar shi ya mutu alhalin zata iya taimaka masa Ubangiji zai kamata da laifin rashin tausayi da imani, ta salwantar da rai ta hanyar ganganci da son zuciyarta.
"Safiyyerh taki rayuwar fa? Kashe ki za su suma fa, ya kamata ki bar wajan nan tunda kin samu dama, shi kinga kamar mahaukaci ne maybe" zuciyarta ta bata shawara cike da gamsuwa ta jinjina kai tare da kama handle ɗin zata fice.
Haɗa idanu suka sake sanda ta juyo ya dinga kallon ta rinannun idanunsa sai ta saki hannun ƙofar tana ɗaga ƙafa zata nufe shi.
"Run Safiyyerh, run away run Safiyyerh"
Ta sautin muryar zuciyarta a cikin kunnenta ta sauka har tsakiyar kanta ƙirjinta ya dinga ɗagawa tana son tafiya bata kuma san meke janta zuwa gare shi ba. Ta girgiza kai
"Save him frist" ta furta a iya harshenta. Yana ganin ta nufo inda yake ya rufe idanu kafin ta ƙaraso ya juya baya yadda ba zata ga fuskarsa ba. Jikinta a sanyaye ta durƙusa cike da tsoro ta kasa magana can ta yi ƙarfin halin furta
"Ina ke maka ciwo?"
Ya mata shiru ba bacci yake ba, domin tana hango yadda ƙirjinsa ke ɗagawa sosai yana ƙoƙarin ganin ya hana kansa yin abin da ƙwaƙwalwarsa ke umarta shi. "To faɗa mini inda maganin yake na ɗakko maka"
Jin shirun ya yi yawa ta matsa tana leƙa fuskarsa suka haɗa ido ya zaro mata manyan jajeyen ƙwayar idanun ta yi saurin ɗauke nata idon "Tab kalli idanunka fa, ko asibiti zaka je?" Ta yi maganar tana ƙoƙarin kai hannu zata taɓa shi ya mirgina gefe yana haɗe fuska kamar ya ce ya shiga uku, da zata gane to tabbas ita ɗin ce baya son gani ko jin muryarta ta kura masa hakan
yake yi sosai ya tsuke fuska yana rufe idanu Safiyyerh ta miƙe gabaɗaya hopefully ya buɗe ido ko ya bata amsa ba sarewa ta sake miƙa hannu dukan da ta ji ya kaiwa jikin bango ne ya saka ta yi baya tana zaman ƴan bori,shima ya tashi zaune yana zazzaro idanu daidai lokacin su Goje suka shigo ya kalli Safiyyerh da take yarfe hannu saboda bugewar da ta yi ya dubi Moh daya miƙe tsaye yana tangaɗi ya shige ɗaki yana rufo kansa a ciki. "Ke me kikai masa?"
"Ƙato da shi me zan masa?"
"Abu a duhu na san matan yanzu ba kunya ce da su ba, idanu rufe suke afkawa maza" da mamaki Safiyyerh take kallon Goje zuciyarta babu daɗi ga takaicin rashin guduwa gana wancan da ko inda take bai kalla ba duk maganar da ta yi masa, ta matsa tana takure jikinta waje guda sai yanzu ma take jin kunyar shigar jikinta sosai, ita Safiyyerh yau ita ce take rayuwa a wajan ƴan daba mashaya kuma ƴan ta'adda hawaye ya cika idanunta sosai mutanen da sam basu suwaye su ba, basu san kansu ba basu da wani amfani a wajan al'umma.
"Ke kina ji ko?"
"Safiyyerh sunana"
"Mene ya daman kuma warning zan miki kar ki kuskure ki sake zuwa wajan shi idan kina son tsira da ranki ba, ba kema ko Abdu Marafa bane a nan wallahi zai iya ganin bayansa, ki yi abin da ya shafe ki kawai ki tsaya iya matsayin ki na wacce akai garkuwa da ita kuma ɓarayin gwamnati". "Shi wa?"
Ya nuna mata ƙofa "kin gane ai"
"A'a" wuƙa ya zaro yana gwalo idanu waje ya ce "Idan na cire miki yatsa ɗaya za ki gane ai"
"Ni mu yi magana ta fahimta daku, me kuke buƙata zan baku koma mene amma ku rabu dani don Allah ina kyakkyawan fata da muradan da nake son cimma a rayuwa naga ku babu inda kuka saka gaba rayukan ku ma sam baku damu dasu, wallahi ina buƙatar rayuwa mai tsayi da zan bar baya mai kyau ba zaku ɓata mini rayuwata ba, kuma warin sigarin nan juya mini kai yake da ƙyar nake shaƙar numfashi, ni macace mai hankali da ilimi wacce iyayena suka bawa tarbiyya daidai gwargwado in da ilimin addini saɓanin ku da ba lallai ko ummul kitahhb kun iya ba, ƴan daba ne ko masu laifi rayuwarku a gurɓace take ba a yi muku tarbiyya ba" hatta Moh dake cikin ɗaki idanunsa a sama yana kallon rufin kwano sai da ya waro ido yana sauraren maganganun da take cewa, Mangal ya yi mata ƙuri da nasa idanun haka Goje
"Wuyanki ya isa yanka ba laifinki bane za mu yi maganinki"
"To me na ce na ba daidai ba, don Allah ku ba ƴan daba bane ƴan ta'adda kuma ga tantirin can shine shugaban naku da alama asalin daƙiƙi ne ajin ƙarshe sai wari dauɗa dana rana ga na shaye-shaye wallahi...," saurin haɗiye maganar ta yi ganin shi tsaye a kanta yana huci ta miƙe tsaye hannu ya ɗaga kamar zai kwaɗa mata mari ta kurma ihu tana ƙanƙame jikinta "Don Allah ka yi haƙuri ƙarya nake yi wayyo daddy wayyo captain" sai idanunsa suka sake jirkicewa ta buɗe idanu taga ya zuba mata nasa idanun fuskarsa dab da nata sai juya ƙwayar idonsa yake a saman fuskarta kamar mai son tantancewa wani abu.
Ta tura baki cike da tsiwa ta ce "Kana kwaɗa mini mari zan rama tunaninka rabuwa zan yi dakai ka ci bulus? Bayan an ce duk wani ɗan shaye-shaye bashi da wani ƙarfi hayaƙi ya cinye shi" Goje ya ce
"Wannan yarinyar ƴar wasa ce bayan kuɗi data iya sarrafawa har rashin kunya ta iya Allah kar ka rabu da ita" Shi dai Moh na tsaye yana kallon ta ita kuma ta kasa jure ganin ƙwayar idanunsa ta yi ƙasa da kanta tana murguɗa masa baki, bata ankara ba ta ji ya cilla mata baƙar kunawa cikin riga ta zumduma ihu a gigice ta yi kansa