Showing 15001 words to 18000 words out of 63481 words
Chapter 6 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt
so?" Ya yi shiru yana tunani can ya ce "Zan sanar"
Eng Ali wali ya ɗakko ƙatuwar bana da fastoci ya bawa Goje da yawa ya ce "Kuje ku fara da aikin liƙawa wannan a unguwanni da saƙo da lungu ya zamana babu wanda ake ganin sai Eng Ali wali, bayan wannan akwai wani dattijo da yake zuwa gidan rediyo yana yi sojan baka kuma duk ni yake kushewa yana son jiƙa mini aiki a tabbatar an saka shi yin shiru da baki da kowacce hanya" kuɗi ya ciro daga cikin Aljihu ya miƙawa Goje ya ce "Aje a yi caji a huta" har Moh zai juya sai kuma ya tsaya ya cake waje guda kamar saƙago ya ce "Me ya sa kuke son a kamata?"
"Aiki ne kawai naka wani abu ba sai ka sani ba, mune shuwagabanni ku dai a baku kuɗi da kayan sararawa shine" kai tsaye Moh ya ce "To nemi wani" Eng Ali wali ya ce "Me ya sa? Bayan kai ka cancanta?"
"Ba zan ba"
"Shikenan na gane, Safiyya Abdu Marafa na faɗa maka ƴa ce wajan tsohon leccara, yana kawo mini barazana a sabgar siyasa tare da nuna rashin cancanta a fili. Matasa na jin maganarsa abin da ya zaɓa kuma da shi suke yin aiki a yau ɗin da muke ciki matasa sune siyasa ina so a sa shi yin mubaya'a dole. Kasan da yawan lokaci Malamai suna kawo mana cikas" Mai dawa ya jinjina kansa alamar ya ji sai dai bai yi magana ba a hankali ya duƙa yana buɗe hannu ya ce "Sai godiya"
"Sai godiya" Mangal da Goje suka faɗa suna zagaye shi. Cikin sauri kuma ya fice daga cikin parlon suna mara mishi baya.
Eng Ali wali ya dubi wanda ke zaune sai kuma ya yi dariya sosai ya ce "Amfanin su kenan fa babu wani aiki da ɗan daba zai iya yi maka banda bangar siyasa kashe kashe da sare-sare mu kuma sai mu jefe su da abin da sukewa"
Fiyya na tsaye gaban madubu tana gyara rolling mayafin kanta yau ma suit ce a jikinta ta mata riga da wando blue black ta amshe ta sosai ta kalli kanta a madubin she missed the old Safiyyerh komai nata sabo take jin shi, ta ji kamar ta rasa wani abu mai amfani a tattare da ita amma mene? Shi ne abin da sam ta gaza fahimta ko a cikin bacci. Ta sauke numfashi tare da ɗaukan wayarta da jakarta tana ƙoƙarin buɗe ƙofa ta fita Ummi na shigowa cikin ɗakin Fiyya ta yi baya tana bata hanya kafin ta ce "Good morning Ummi" daga sama har ƙasa Ummi ta kalle ta sai kuma ta je can bakin gado ta zauna tana sake kallon Fiyya "Ina za ki?" "Ummi Company"
"Junaid told me ba ki da lafiya, na yi bacci da wuri" a hankali ta ce "Lafiya lou nake Ummi ga alama kin gani zani aiki"
"Fiyya bana son irin wannan shigar taki, kuma ki haƙura da aikin nan yau za a kawo kayan auren ki" da sauri ta ce "Aure kuma Ummi? Ba sai nan da watanni ba?"
"To Daddynku ya ce cikin satin nan"
"Shikenan zan je aiki"
"A'a ki haƙura yau" marairai ce fuska ta yi sosai kamar za ta yi kuka ta ce "Ummi akwai buƙatar na je, ina da meeting da ma'aikata ba zan jima ba" Ummi bata san damuwar Fiyya dole a hankali ta ce "Allah Ya tsare ki dinga kula ke dai macace ba namiji ba, kina lura da abubuwa da kike yi" Fiyya ta yi dariya tana yin waje ta ce "Kuma ki saka tsoron Allah a ran ki Fiyya ban da wulaƙanta jama'a, al'umma ta Annabi ce" Ummi ta girgiza kai kawai ta ce "Wato kin haddace kenan"
"Dole na Ummi"
Cak ta tsaya tana riƙe kan ta Ummi ta ce "Subuhanallahi Fiyya kina lafiya? Ba za ki haƙura da zuwa aikin nan ba?" Ta ɗan ya tsuna fuska da nuna alamar ba komai ta ce "Kawai na ji kaina kamar an saka mini shocking" gaban Ummi ya faɗi sosai sai bata nuna ba ta kama hannun Fiyya suka sakko ƙasa.
Dr Hash ne ya fito shima sanye da farar riga ta likitoci Fiyya na kallonta ta ce "Likita bokan ture, kuma fiɗe ku ɗinke"
"Kamar wasu mahauta" ta yi murmushinta mai kyau tana lumshe idanu "Barka da safiya Dr" ya yi mata murmushi "The whole Manager in the world" Ta buɗe ido shima ya buɗe kafin su ce komai J ya fito shima yana cewa "In the world mana, wannan kamfanin nan ku ina ne basu da reshe ni dai watarana zan zauna ki bani labarin kamfanin sosai na ji ai na yin wanda yake da shi" "Kai Yaya J nima ban san ko na waye" ya buɗe ido ya ce "Ban gane ba?"
"Da gaske nake Yaya ban san asalin me shi ba, kawai dai na san ni Manager ce"
"Ji nake Ashraf's father is the owner of the company"
Ta tura baki gama tana harar shi "Kuma ka sani kake tambayata" ya ɗaga mata gira ya ce "Zan zo ki nema mini alfarma wajan surukin naki nima ya bani ko messenger ne" bata kula shi ba. Ɗago kai ta yi suka haɗa idanu da shi yana zaune ya watsa mata harara yana ɗauke kan shi gefe "Aliyu ba yau zaka tafi bane" ya yi shiru a hankali kuma ba tare daya ɗago kai ba ya ce "A'a"
"Ok na ɗauka yau ne, ni wallahi duk firgitar dani kake mutum ba walwala kamar a filin yaƙi nan fa gida ne, amma kodayaushe kamar an yi maka dariya ko yaya ne ka dinga murmushi"
"Ban iya ba Ummi"
"Murmushin ne baka iya ba Aliyu? Ka gwada zaka iya" ya miƙe tsaye yana yin waje "Ban san yadda zan ba" "Ina kwana Captain?" Fiyya ta faɗa tana haɗe fuska ko inda take bai kalla ba ya yi waje abin shi. Shi dai J murmushi kawai yake yi halin Captain na bashi malam sosai suka jera shi da Fiyya suka fita. Mota ta shiga yana ɗaga mata hannu shima ya shiga tasa motar kowa ya kama hanyar wajan aikin shi. Fiyya na driving a nutse ta hangi wata mota na bin duk inda ta yi sai ta taɓe fuska ko a jikinta a fili ta ce "Ɗan wahala ko waye"
Daddy dake zaune bayan shigowar Ummi cikin parlon sama ya kalleta ya ce "Me kike cewa Ummi?" Ta damuwa ta ce "Kwana biyu ba a amshi maganin Fiyya ba, kuma kamar ciwon zai tashi" ya ajjiye littafin hannunsu yana saka glasses ya ce "Wani abin ya faru?" Ta numfasa yana faɗin "Irin abin da ya faru kwana ki tana jin kamar ana mata shocking a kanta, ni wallahi bana son ma ta dawo daidai bana fatan ubangiji ya ƙara gwada mini tashin hankali dana gani shekarun baya" Daddy ya jinjina kai "Nima addu'ar da nake a raina shi ya sa ma na matsu kawai a yi ai maganar auren nan, wallahi bana son Maama ta dawo old Safiyyerh"
"In sha Allah hakan ba zai kasance ba"
Meeting hall ɗin ya yi shiru sai muryarta dake tashi cikin faɗa tana ɗan buɗe hannayenta tare da yin baya ta ce "Wanne irin rainin wayo da hankali ne, file ɗin dana ajjiye shi a office ɗina ina jiran a kawo mini proof hujjar abin da aka fitar aka samu shigowar kuɗi zuwa asusun kamfani kamar yadda Accounter ya faɗa mini shine za a ce wai na yi signature a file aljana ce ni da zan taso da gida na zo kamfani na saka hannu, idan zan saka me ya sa ban yi ba tun da file ɗin ya zo table ɗina?" Ta miƙe tsaye tana kallon su gabaɗaya duka maza ne ita kaɗai ce mace ta koma ta zauna tana juyi a kan kujerar "I need to find out the truth, meke faruwa a wannan kanfanin. Md da kai da secretary za ku kai ni na duba ko'ina a wannan kamfanin yau ɗin nan, kai kuma Director ka kawo mini record ɗin komai daga watan daya shige zuwa yau ɗin nan, ina buƙatar statement yanzu a office nawa" ta sauke numfashi fuska a haɗe sosai "An gama" secretary ne ya kalleta kamar a tsora ce yake ya ce "Manager akwai baƙi da suke jiran ki"
File ta ɗauka ta miƙe tare da ficewa daga cikin meeting hall ɗin. Bata nufi office ɗin ta ba inda suke ganawa da baƙi ta nufa ta tura office ɗin a hankali a hankali ta yi sallama ta shiga. Manyan mutane ta gani su biyu zaune a kan kujera kana ganin su ba sai an yi magana ba ta zauna kan kujera mai cin mutum biyu a ladabce ta ce "Ina kwanan ku? Welcome to FS WORLD INVESTMENT COMPANY i am Safiyya A. Marafa how can i help you?" Wani rushehen mutum ne daya Hakim ce a kan kujera ya dinga kallon ta kamar zai haɗiye ta idanunta dai na kan system tana ta dannawa da aikin tura saƙo can ta ɗago kai suka haɗa idanu ta sake kame fuska ta ce "How can I you? Ta ya ya zan iya taimaka muku"
"Ba ki gane ni ba"
Sarai ta gane ko waye ta ce "Yau na taɓa ganinka"
"To ma sha Allah. Sunana Hon Maɗatai zan saka hannun jari ne a cikin wannan Company"
"Ok, me kake buƙata?"
Ya gyara zama sosai ya ce "Za a dinga bani shinkafa, suger, wake a kan farashin yadda Company yake siyarwa ni kuma zan ɗora kaso 50 domin cin riba amma daga lokacin Company ba zai sake siyarwa da kowa kaya ba sai ni" Fiyya ta dinga kallon shi sosai a ranta tana mamakin son zuciyar wasu ya suke so talakawa su yi da ran su ne? Burin shuwagabanni talaka ya faɗi ya mutu saboda yunwa? Ta yi jim sai kuma ta ce
"Da wata ce matsayin Manager ba Safiyya A. Marafa ba do wataƙila ka samu wannan damar a yanzu ina maka murna da cewar we're not interesting anymore, da wannan zai fi kyau ka buɗe naka masana'antar ka nemi matasa marasa aikin yi wanda suke lalacewa ka basu abin yi" ya dinga kallon ta can ya ce "Kin san waye ni? Ƴan'mata ki bi a hankali fa"
"Ai ba a yi wa Fiyya maimaici Hon Maɗatai ba zamu baka hannun jari ba You can leave" ya miƙe tsaye yana jin ba'a taɓa yi masa wulaƙancin da yarinyar ta yi masa ba "Safiyyerh ko? Ki bi a hankali haɗuwar farko ce wannan, zan tafi amma zan dawo"
Ficewa ya yi rai ɓace zuciyarsa na zafi. Fiyya ta ɗauki kayanta ta nufi office. A hankali take bin bayan Md da Secretary ɓangaren kayan abinci aka kaita kana da mai daga can baya wajan shara inda ake ajjiye bukar kamfanin ta dinga jiyo wari da sauri ta nufi wajan Md ya ce "Manager sharar kamfani ce nan" bata kula shi ta nufi wajan sharar tana rufe hanci da f facemask kamar an ce ta juya idanunta ya sauka akan yatsun hannu guda huɗu da suke a leda ƙuda na bin su.
Tunda ya nufu layin su tiger na biye masa baya hannunsa riƙe da gora yara suke watsewa sai waje ake bashi hatta almajirin Malam sai da wasu suka bar wajan banda Ɗanyaro dake zaune yana danna sabuwar wayar daya siya sosai Malam yake ji da shi yanzu lokaci zuwa lokaci yake yi malam alheri na kuɗi ga nama da yake kawo masa, sai dai cikin dare Ɗanyaro zai lallaɓa ya gudu ba zai dawo ba sai safiya. Moh na ƙoƙarin shiga gidan Malam ya tare ƙofar ya ce "Na haifi yaro sunan shi Muɗallabi amma yanzu bani da wannan yaron na bar wa ƴan iska shi da ƴaƴan banza tunda ya zama shaiɗani ba zaka ja mini masifar da zan mutu a gidan ɗan kande ba" Moh zuciyarsa ta fara tafasa har wani hayaƙi ke fita ta cikin bakinsa ya dinga kallon asawan nasa ya kasa cewa komai ya leƙa surar gidan ko zai ga Ammo amma sai Inna Binta dake suɗe tukunya tana faɗin "Matsalata ɗaya a duniyar nan abinci idan na ci na ƙoshi Mufee ta ci ni fa ko a jikina" Juyawa Moh ya yi kamar zai yafi sai kuma ya nufi saman katanga ya kama ya dire ta cikin gidan Inna Binta ta zabura tana faɗin "ƙulna naru ƙulni bar dan wasalamun Allah Ibrahim, auzubillahi" jikinta sai rawa yake masifar tsoron Mai dawa take kamar ran ta sauran jama'ar gidan duk suka shige ɗaki banda Mufee da ta yi tsaye tana kallon shi sosai idanunsu yake iri shi bai san wace ita a gidan ba, bai damu daya sani ba yara ne kamar yaƙi wasu iyayensu basa cikin gidan.
Labulan ɗakin Ammo ya ɗaga ya ganta zaune tana ninke kaya ya fi minti goma tsaye kamar zai juya sai kuma ya shiga cikin ɗakin idanunsa akan kwanon abinci sosai yake jin yunwa idanunsa na rufewa ya miƙa hannu zai ɗauki abincin Malam ya ce "Kana ci zan maka Allah Ya isa ka tashi ka bar mini gida tsinannen yaro" da sauri Ammo ta kalli Malam sai kuma ta ɗauke kai.
Jikin Moh ya fara rawa jijiyoyin kansa na mimmiƙewa jin uban daya kawo shi duniya na yi masa Allah Ya isa ya yi ƙasa da kansa idanunsa kamar za su fito waje ya ji babu abin da yake buƙata sai ƙwayar da Mangal ya bashi ya sha, ita kawai zata sauke masa abin da yake ji ya manta da komai, yaushe ne zai zama daidai kamar kowanne mai rai an ci zalin shi an lalata masa rayuwa. Ya miƙe da sauri yana banko ƙofar ya yi waje "Sallamammen yaro Allah dai ya rabani da ƙaddara na huta"
Kai tsaye Moh dabarsu ya nufa yana zuwa suka mimmiƙe Darma na faɗin "sai godiya Mai dawa sarki mai jeji, wani ya ce ba kai ba yanzu mu fito mu yi farfesun hanjinsa"
Yanayin fuskar Mai dawa a bar tsoro ce ya takure waje guda yana jin kamar zuciyata zata fito waje don baƙin ciki. "A sama yake ku bashi sha fara kaga aljan" cewar Darma Mangal ya girgiza kai ya ce "Ba za ta yi masa ba, kawai a yi masa allurar fenta"
"A'a ta yi masa girma yaushe ya faɗo sabgar kar ka luda masa ya yi mana na jakuna yanzu" zaro sirinjin ya yi Moh ya ƙurawa siririn idanu ganin yadda Mangal ke zuƙo ruwan ciki ya fara girgiza kai da ƙyar ya ce "Kar ka yi mini Ka bar ni da tunanin bana son mantawa" kokawa suka fara yi da shi ya ɗauki Darma ya buga da ƙasa Mangal ya faki idanunsa ya caka masa allurar a gadon baya. Jinjiga ya fara sosai cikin ƙaramin lokaci ya yi shiru yana jin shi kamar a samaniya yana yawo yanayin ya yi masa daɗi sosai ya ji zuciyarsa wasai a wannan yanayin bacci ya ɗauke shi. Can cikin dare ya farka kam shi ya yi masa nauyi har yanzu bai dawo daidai ba, babu komai a cikinsa ya miƙe tsaye yana layi kamar zai faɗi Mangal ya ce "Mai dawa"
Ya yi masa shiru yana ɗaukar wuƙa ya soke ya ɗauki fitila ya riƙe "Dare ya yi ba, kana fita waɗancan ɗankokin za su iya kama ka gashi babu da goge a hannu ka zauna, kasan kuma ƴan cikin gari sun shigo sun samu labarin mun yage musu poster bama wannan ba ɗazo an ga gawar wani to ana tunanin mu ne kuma yaron ɗan cikin garin ne fansa suka zo ɗauka,na bibiyi abun shi yaron ƙwacan abar magana ya yi jama'a kuma sun fara ɗaukan doka a hannunsu suka rufe yaron da duka har ya mutu. Su Cokali kuma ba za su haƙura ba kar muna zaune su ci mu da yaƙi"
"Sai godiya"
Ya furta da ƙyar daga nan sake yin shiru yana shirin barin wajan kamar zai kifa "Ina zaka ne? Ka dawo ka kwanta"
"Kai fa ba Malam zan haɗaka da Rainbow"
"Shikenan ina zaka yanzu" ya cije leɓe zuciyarsa na ayyana masa abin da zai yi shi ne daidai allurar sai gaibu take faɗa masa a hankali ya ce "Zan kashe Malam ya baza lahira"
For more information
08164069385
WhatsApp only
[10/9, 5:16 PM] Nanameera: *❤🔥 MUTALLAB ❤🔥*
Page 6
*Bright pens... 2nd batch*
*🔞for the adults and criminal side please 🔥 just take it as a lessons*
Goje daya farka daga bacci ya yi saurin miƙewa yana furta "Malam ɗin zaka kashe mahaifin naka?" Ya yi shiru bai yi magana ba, yana sake riƙe wuƙar a hannunsa da kyau duk jikinsa rawa yake, ga wani irin ciwo da kansa yake yi masa sosai, idan ya tuna abubuwan da aka aikata masa sai ya ji zuciyarsa ta bushe ta kuma ƙeƙashewa. Ya saka ƙafa ya banga je Mangal dake tsaye zai shige Goje ya yi saurin shan gabansa yana ɗaure fuska sosai ya ce "Saboda kana jin kanka a sama ta bakwai kake jin komai za ka iya yi? Me ya sa ba zaka yarda sarki sammai ke yin komai ba, mu fa ba haihuwar ta zubar bane ko yaya ne mun san abin da ya dace kashe mahaifinka ba shi ne mafita ba Mai dawa" ya ɗaga jajayen idanunsa kamar zai ci babu yadda ƙwaƙwalwarsa take faɗa masa ba daidai haka komai na duniyar yake yi masa babu daɗi maƙoshinsa na yi masa zafi da raɗaɗi wani abu ya tsaya masa da ƙyar ya iya buɗe bakinsa ya ce
"Ya zan yi?"
Kai tsaye Goje ya ce "haƙuri, ka bi komai a sannu mai dawa ita gaggawa aikin ƴan annaru ce. Kashe Malam a yanzu ba zai rage maka kashi goma a cikin ɗari na damuwar da kake ciki ba, iya wuya iyaye ne su"
"Ba iyaye na bane, ka bari ko ɓalli-ɓalli na yi masa" ganin da gaske shirin tafiya ya ke yi ya ce "Idan kaga ka bar wajan nan sai dai ni za ka fara kashewa" Ya ƙuri da idanu yana kallon Goje har wani hayaƙi ke fita ta cikin bakinsa ya wani cije gefen baki yana karkatar da kai gefe. Kamar wasa Goje ya ga Moh ya nufe