Showing 6001 words to 9000 words out of 63481 words

Chapter 3 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt

23 Nov 2024

6668

a zaune a parlon duk dawowar su daga aiki kenan. Wajan tare suka dinga cewa "Sannu Manager" ta shige tsakiyar su tana kwanciya a cinyar Marafa ta ce "Thank you brothers, ku yi mini tausa akwai labari"


"Gulma dai ba labari ba, daka dawowa ko wanka ba ki yi ba kin zaunawa mutane a jiki ƙazamar banza" Shiru ta yi masa don basu fiye shiri ba sosai ta juya idanunta rufe, tana jin yadda Marafa ke ta danna mata farar ƙafarta. Yaya J kallonta kawai yake with different thinking running on his mind. Gabaɗaya suka juya jin tafiya cikin sauri ana sakkowa daga saman bene shiru duk sukai suna binsa da idanu domin basu san ya dawo gidan ba, hannunsa ɗaya zube cikin aljihu farar riga ce a jikinsa ta kakin sojoji a gaban rigar wajan gefe an rubuta A.A MARAFA.


"Kee!" Ya faɗa a tsawace da sauri Fiyya ta buɗe idanunta lokaci ɗaya kanta ta sara sosai tsawar ta ratsa kanta, ta miƙe zaune fuskarsa babu walwala kamar yadda itama ta yi kicin kicin da rai "Tashi a nan, stupid kawai" ta miƙe tsaye tana murguɗa baki ko inda yake bata kalla ba ta nufi saman bene kai tsaye daƙinta ta nufa idanunta cike da bacci ta faɗa saman gado cikin ƙaramin lokaci bacci ya ɗauke ta. Firgigit ta farka jin sautin labaran ɗ da ake faɗa a gidan rediyo wacce take cikin ɗakin nata, ta miƙe tsaye ta ɗauki rediyon ta ƙanƙame a jikinta tare da lumshe idanunta wasu hawaye masu zafi suna shiga bin idanunta. Ta cikin idanunta take hango fuskarsa a lokacin da rigima ta haɗa su da ita sai take ganin kamar yanzu ne komai yake faruwa.


Students ne an cika sosai saboda class partyn da ake yi na kammala exam maza da mata babu teacher ko ɗaya tunda ta shigo hall ɗin makarantar tasu take duban inda zata ganshi. Cikin sa'a ta ganshi yana zaune saman window sanye da gajeren wando fari tas sai armless ɗin riga wacce duk aka yanke hannunta gashin kansa rabi a aske ya zubawa wani tafkeken gidan masu kuɗi idanu ta waje baya ko ƙiftawa kamar an ce ya juya ya ganta tsaye ta zuba masa idanu yaja tsaki kafin ta yi magana an shigo an ce "Mutallab, principal yana nemanka an kai ƙarar ka wai kana son Fiyya"


Ya ware idanu abin da bai taɓa zuwa tunaninsa ba kenan sai kuma ya cije baki "Shi principal ɗin ubana ne Malam Abdullahi kenan?" Ya juya ya kalleta sosai ya ce "Sai godiya, ni? Kuma ke hauka kenan"


"Kai ne mahaukaci" furucin ya fita daga bakin Fiyya "Kuma na yi maka nisa, kasan yadda nake da masoya a makarantar nan amma ni ubana ba soyayya ya kawo ni ba, karatu zan yi ina da buri mai faɗi da zan cimma" Ya miƙe tsaye yana kallonta daga sama har ƙasa a ransa yana ƙissima abu "Shi uban naki can ta matse masa, karatun banza kawai ka zama mai iko shine"
"Ba dai ubana sai dai....." Ya buɗe idanu sai kuma ya fasa abin da ya yi niyya ganin hawaye a idanunta abin da bai taɓa gani ba. Da sauri ta fice daga hall ɗin ta zaga baya ta durƙushe a wajan tana fashewa da wani irin kuka kamar zata haɗiye zuciya "Daddy na shiga uku ina son Mutallab"


Ƙanƙame redion ta yi tana sake fashewa da kuka jikinta har jijiiga yake ta ce "Na shiga uku Daddy, ba zan iya ba I can't do it ina son shi.


Kamar daga sama haka ya faɗo cikin gidan, jikinsa duk liƙe da bandeji jini na ɗiga kaɗan-kaɗan kwana biyu yana jinyar raunin bai san waye ya yi masa ɗinki ba. Idanunsa jajur har lokacin saboda bai gama dawowa daidai ba sai muzurai yake yi ya ja ya tsaya yana kallon murhun da aka sauke abinci akai ya juya ya kalli ɗanwaken dawar da Inna Binta ta yi ta shiga daƙi ɗakko magi ta barbaɗa ko arziƙin yaji bai samu ba, yaja kwanon da hurɗu-hurɗu yake tura ɗanwaken kafin wani lokaci ya kammala cinyewa tas ya zube a wajan ya kwanta ya rufe idanu, wata nutsuwa yake jin daya kwanta a tsakar gidan mahaifin nasa. Ya yi kamar bacci yake yana jin Inna Binta ta lailayo ashar ta ƙunduma ta ce "Wanne ɗan abu takazar ne ya cinye mini abinci Mufee wanne mayunwacin ne mara godiyar Ubangiji" tsit ta yi ganin Moh kwance hannunsa duk manja taja baki ta tsuke ta ɗauke kwanan tana suɗewa a zuciyarta tana jan Allah Ya isa. Har ya shiga ɗakin Ammo ta bankaɗa labule ta ce "Wallahi abincin da ɗan ta'addar ɗanki ya cinye mini Allah Ya isa, kawai kin haifa mana jaraba ko ɗanɗana ɗanwaken ban yi bafa ya cinye" ta dinga zagin Ammo ta uwa ta uba ta shige ɗaki tana sake suɗe kwanon da ƙyar ta samu rancen ɗari biyu ta yi cefane da ledoji ta dafa.


Tana shiga ɗaki ba jimawa ta ji an bankaɗo labule sai ta zuciyarta ta buga ganin shi tsaye hannunsa riƙe da gora ya suke askara a gefen ƙugunsa ga gori a hannunsa, ya juya ya kalli Mufee da hannu ya yi mata alama data fita cikin sauri ta fice tana fita muryarsa a daƙushe kamar dole ya ce "Tiger spider a yi mata aiki" manyan karnukan suka faɗa cikin ɗakin Inna Binta ta fara ihu tana maƙale jikin sif "Nafsi nafsi jama'a na shiga uku ya Allahu Ya Rahmanu, don Allah ka yi haƙuri Muɗallabi zan bawa Ammo haƙuri ka rufa mini asiri kar Mufee ta zama marainiyya" Haushi kawai karnukan suke Tiger na kai mata cafka Inna Binta ta fashe da kuka fitsari na bin ƙafarta ta ce "Hal'àtaka hadisul gashiya ni Binta na shiga uku"


Moh ya ce "Sai godiya" gabaɗaya karnukan suka tsaya cak Inna Binta na haki ta jiƙe gabaɗaya da fitsari har lokacin tana maƙale jikin sif kamar ba zai magana ba ya ce "Bani ƙudin nan" jiki na rawa ta miƙa masa ɗari biyar ɗin hannunta ya amshe ya yi waje ta sake sif ɗin ta fashe da kuka tana faɗin "Tsinannen yaro manta ganin yaron dake son uwarsa kamar mutuwa ba irin shi" Moh na fita ya leƙa ɗakin Ammo ta ɗaga kai tana ganinsa ta ɗauke fuska ya yi ta kallonta ya jima tsage kafin ya sauke labulan ya juya. Yana fita wani babur na tsayawa a gabansa aka cillo masa takarda da gudu aka ja babur ɗin tare da barin wajan. Ya ɗauki takardar ya buɗe rubutu ne bai fi layi biyu ba a hankali ya fara karantawa.


_Mai dawa baka gajiya? Sau dubu zaka kula mace sau dubu zamu kashe ta. Karo na uku kenan ga misali akan matarka nan_ da jan biro akai rubutun ya juya da sauri amma tuni babur ɗin ya ɓace ɓat waye wannan? Su duka shi ne silar mutuwar su kenan? Waya ya amsa hannun wani Almajiri ya kira wata number ana ɗaga aka ce "Sai godiya" Ya numfasha


"Duk inda ƴan daba suke ka haɗa mini su" ta cikin wayar aka ce "Mene haɗinka da daba ko dai ka fara shaye-shaye a state cid ɗin?" Moh ya cije baki ya ce "Zan fitini mutane, na ji daɗin zama can"


"To me za su yi maka?" Wannan yaran da suka sare ni iyayensu za su ɗauki sabbin ciki yau, ƴan cikin gari ne a yi mini kan me uwa jawabi" yana faɗin hakan ya kashe kiran ya goge number tas ya lumshe idanunsa ya buɗe sai kuma ya cije leɓe zuciyarsa zafi take sosai ji yake dama ya yi kuka, amma ba a haife shi don ya zubar da hawaye ba ya ɗaga idanu sama ya ce "Da gaske ni na kashe ta amma ba zaku taɓa sani ba" daidai lokacin mafarauta suka kawo kai suna busa ƙaho da buga gangaga suka zagaye Moh ana "Sai Mai dawa ina uban wasu ga namu wuya a ina wuya a daji, kai ne mai Tiger kai ne mai gadon tawada" Jikinsa ya hau ɓari da karkarwa tsumin shi ya motsa idanunsa na ƙaƙƙafewa ya yi kururuwa tare da ɗaga gora sama ya ja ya ƙame sai jikinsa dake rawa ya fara "La'ilahaillahu, sai ni ɗan babana Malam Abdullahi ɗan malam ɗan gatan Ammo ƙanin Sa'adah ƙanin Bafullatana waye ce bani ba Muɗallabi sarki Mai dawa da jeji" gabaɗaya suka zagaye shi suna sake zuga shi daidai lokacin kuma suka ganta kamar daga sama.....




*In sha Allah za ku ji abin da baku taɓa ji ba 😘*




08164069385
WhatsApp only
[10/4, 9:17 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥*






Page 3
Nimcyluv


Bright pens....Second batch




Da sauri ya nufe ta kamar zai kai mata cafka, ta yi saurin ja baya idanunta cikin nasa. Yana tangaɗi ya ja ya tsaya a gabanta tare da ƙura mata idanunsa da suke lumshewa, har yanzu jikinsa ɓari yake domin basu daina buga ganga da ƙahon da suke busawa ba kamar masu yin gangi.


Hannunsa ya ɗaga musu cikin sauri suka daina abin da suke, cikin izza da gadara ya basu umarnin tafiya har lokacin idanunsa yana kanta ganin yadda take kallon shi kamar ya ta saba ganin halittarsa. "Ban yi zaton a haka zan ganka ba, autan Ammo me ya sa?" Ya ɗauke kansa yana haɗe fuska sosai ba wargi banda cewa ita ce ba zai taɓa tsayawa ba. Cikin raunin murya kamar za ta yi kuka ta ce "Me za ka yi da wuƙa haka?" Ya buɗe ido sosai sai bai magana ba, a hankali ma ya bi gefen ta zai huce ta yi saurin riƙe masa hannunsa tana faɗin "Ni ɗin ma? Yau za a ji kan mu da kai, kar ka faɗa mini sauyin da ka yi ya zagayo har kai na?"


Ya ɗago kai ya kalle ta ya kalli hannun data riƙe shi da shi, hannunta fari tas saɓanin nasa da yake mai kauri kuma baƙi irin na majiya ƙarfin nan wanda suke tashe akan shekarunsu. "Don Allah ka tsaya mu yi magana, ni ko gidan ba zan shiga ba wajanka na zo" ya cije bakinsa ya mai da kai gefe cikin muryar mai kauri ya ce "Kin ci darajar Ɗan Amina, mene sakin?" Ta girgiza kai kawai tana duban gefe dakalin dake wajan ta gani ta je ta zauna akai, ta yi masa alama ya zauna amma ko motsi bai yi ba, ta san cewa yana jinta amma hankalinsa na kan hanya sai waige-waige "Mutallab ka kalle ni bafa wani zai kawo maka farmaki ba" ta nisa idanunta cike da ƙwalla ta ce "Don Allah kai ne ka kashe ta? Ba zargin ka nake ba Autan Ammo ni me iya rufa maka asiri ce idan ya zama kana da laifi ka faɗa mini gaskiya na maka alƙawarin ko Ammo ba zan faɗawa ba, ka kashe matarka ko ba kai bane?"


Ya juya da wani irin sauri yana kallon fuskarta da take kallon shi cike da damuwa, idanunsa ya yi jajur naman jikinsa na motsawa ya kasa furta komai. Miƙewa Anty Hameeda ta yi tana girgiza kai kuka na cin ƙarfinta "Ko minti ashirin ba mu yi da kai maka matarka ba, sai labarin mutuwar ta muka ji da kisan wulaƙancin da aka yi mata. Mutallab kai ne fa muka gani tsaye akan gawarta, kai ne fa riƙe da wuƙar da aka kashe ta da ita jikinka duk jinin matarka innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na kasa yadda ka kashe ta, daman soyayyar da ka nuna mata na iya fatar baki ne?" Wani irin ihu Anty Hameeda ta yi tana kaiwa jikin bango ganin ya ɗaga hannunsa ya yo kanta sai kuma ya tsaya cak, a hankali da baya da baya ya dinga ja yana ƙare mata kallo sai kuma ya taune bakinsa idanunsa kamar zasu zazzago don girma kallo ɗaya idan ya yi dasu sai an razana da ƙyar ya iya ware laɓɓansa biyu da sukai masa nauyi sosai ƙasan zuciyarsa na ta fasa banda cewa Anty Hameeda ce tabbas da sai ya karya ta gida huɗu.


"Ni na kashe ta, ta cancanci haka ne" ya juya da sauri Tiger da spider da rainbow suka bi bayansa kamar zai tashi sama haka ya sha kwana. Zubewa Anty Hameeda ta yi a wajan tana rushewa da kukan baƙin ciki, su waye suke da saka hannu wajan lalacewar Mutallab? Ba komai ta sani ba ita ba ma'abociyar zaman garin bace ita da mijinta ta dinga kuka da ƙyar ta rarrashi kan ta, ta miƙe tsaye kamar zata shiga gidan nasu sai kuma ta fasa tana ƙoƙarin barin wajan ta ji Malam ya ce "Hameedatu me kike anan ina mijin da yaran naki?" Kanta a ƙasa ta ce "Suna gida, ina yini Malam?" Ya jujjuya yana kallon hannunta ganin babu komai ya ce "Ba za ki shiga bane?" Ta girgiza masa "Zan juya wajan Mutallab na zo" ya jinjina kai domin ba wannan ne a gabansa ba.


"Ba wata mutalla da zan iya samu a wajanki na siyo wainar rogo?" Ta buɗe jakarta ta zaro kuɗi tana irgawa ya yi maza ya fisge ya ce "Mene na lissafi? Maza jeki wajan yaranki kuma na ja kunnenki babu ke babu yaron nan idan ba su kike watarana ya ja miki masifar da za ki ƙare rayuwarki a gidan ɗan kande ba" bata ce komai ba sai data juya zata tafi ta ce "Duk lalacewar Mutallab kai ne ka haife shi, jininka na wanzuwa a nasa" tana kaiwa nan ta yi gaba abinta saboda ɓacin rai da damuwa ko gabanta bata gani sosai.

Moh na kwance a saman wani dutse idanunsa a rufe tun bayan barin shi wajan Anty Hameeda ya zo wajan ya kwanta, zuciyarsa a cunkushe take babu gurbin samun sauƙi a cikinta duk yadda ya ke son tuna waye shi me ya sa ya zama haka sai ƙwaƙwalwarsa ta yi hooking, ya ɗauki zafi sosai ta yi ta processing ya ji Ammo ɗinsa kawai yake son kasancewa da ita yanzu. Ya motsa kaɗan zazzaɓi ne sosai a jikinsa saboda saran da aka yi masa bai gama warkewa ba, baya kuma shan magani wacce zata iya kula da shi baya jin zai iya zuwa wajanta. Ya ƙanƙame jikinsa sosai abubuwa da yawa baya son tunawa sai ya cimma muradin zuciyarsa sai ya ɗauki fansa na abin da aka aika, sai ya bayyana abubuwa da dama tunda har suka bari ya shiga cikin gidan yari ya kuma yi shekaru uku a Cid ya rayuwa cikin masu aikata manyan laifuka. A sama ya ji an kira sunansa


"Mai dawa, sarki mai jeji" bai buɗe idanunsa ba, bai kuma ɗauki murya ba haka baya buƙatar sanin waye don hakan babu abin da zai ƙare shi da shi. Ya nemi waje ya zauna yana furta "Ka saɓe Mai dawa ka basar, fansa kake buƙata ba raunin zuciya ba, ka ajjiye tunanin baya ka fuskanci burinka ka zama abin da kake muradi kafin aga bayanka" har lokacin bai buɗe idanu ba, ko inuwarsa bata motsa ba. Mangal ya ɗaga kai yana busawa samaniya hayaƙin sigari "Idan kana son yin bacci cikin nutsuwa ka manta komai ya kamata ka sha wannan" ya zaro abu a aljihu yana kalle-kalle sai a lokacin Mai dawa ya buɗe rinannun idanunsa ya juya ya kalli mai maganar irin kallon waye kai? Mangal ya ce "Ka dake musulmi akul musulmu, zuwa na yi na taimaka maka"


"Riƙe wannan tiramol ce, ko doki ya sha sai ya gane barno gabas take kana afawa za ka ji zam-zam komai ya zama labari" Mai dawa zubawa ƙwayar idanu shi bai taɓa shan ta ba, bai taɓa shaye-shaye ba ya juya ya kalli Mangal "Da gaske zan yi bacci?" "Darr ne ai aikin wannan kamar yankan wuƙa ne, mai ƙirin ce da ƙyar aka bani ita ina karɓa na doƙu nan" jikin Mai dawa na rawa ya amshi ƙwayar guda ɗaya ya cilla cikin bakinsa, yana runtse idanu ya yi shiru. Mangal ya zubawa Moh idanu a ransa yana jin wani daɗi da kuma farinciki bai taɓa yin aikin da za a bashi kuɗi masu yawan da aka ce ba irin na yau, gashi ya yi nasara Moh ya sha ƙwayar. Jikin Moh ya ɗauki rawar zafin zazzaɓi duk da irin dariyar da yake da ita, gashi duk inda ya motsa ciwon shi jini yake babu wani wanda zai iya duba lamarinsa sannu a hankali ya fara dafe kan shi da wani irin gurnani yaga sama na jujjuya masa ya ɗaga hannu da niyyar ya tare sama ya faɗo daga saman dutsen sai saka hannu yake yana tare sama a hankali kuma jikinsa ya fara saki yana jin wani shuu a tsakiyar kansa yana game jikinsa gabaɗaya zuciyarsa da tunaninsa suka dinga kissima masa kawai ya kashe kansa ko ya cinnawa gidansu huta gabaɗaya kowa ya mutu har shi.


Ganin laɓɓansa na motsawa alamar yana magana ba'a ji sosai ya saka Mangal matsawa tare da kafa kunnensa a bakin Mai dawa cikin mawuyacin hali yake furta "Safiyyerh... Safiyyerh...Safiyyerh" Mangal ya maimaita sunan a fili “Safiyya?” wace haka? Ko ita ce wacce ta mutun wacce aka kashe? Ya miƙe tsaye ya ɗauki wayarsa wata number daya haddace ya saka ya kira ana ɗagawa Mangal ya ce
"Sakin nan ya kammalu, yanzu zan zo a taya na amshi fararen" shiru ya yi yana sauraren mai maganar kafin ya ce "Jira jira jira nifa cikin uwata aka haifan ba ɗan zina ba, na maka al'ƙawarin dole zan bawa Mai dawa ƙwayar kuma da sannu zai zama namu. Sai dai na ji yana kiran sunan wata ɗawa wai Safinu ko Safiya?" Ya ƙara yin shiru ya numfasa ya kalli Moh dake kwance a wajan ya ce "A'a Oga ni bana sabga da masu ɗan kwalin nan. Da ƙirin ka oga kanka baya kullewa a fice kake sai na doƙu yanzu" Kashe wayar Mangal ya yi kuma ya goge kiran cikin sauri kuma ya bar wajan.


Baya tantance halin da yake ciki, sai dai yanayin na yi masa daɗi sosai shi ba'a sama ba shi ba'a ƙasa yana fatan ya dauwama har ƙarshen rayuwarsa. Duk da a cikin giyar maye yake bai hana shi gano fararen kyawawan idanunta masu matuƙar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login