Showing 45001 words to 48000 words out of 63481 words

Chapter 16 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt

23 Nov 2024

6680

kuma ɗora hannunsa saman cinyarsa cikin kowacce ƙafa, kallon Abbasa yake tun ɗazo take magana yaƙi cewa komai ko tari kuma bai yi ba, raunukan jikinsa ya kame sai saura, ido biyu za ka yi da shi ba zaka ƙara marmarin kallon nasa ba, babu rahama a fuskarsa nan zaka ɗauka tunda Ammo ta kawo shi duniya bai taɓa yin murmushi ba, ko haɗa hanya da inda fara'a take.


"Kalli nan"


Ya dubi abin da take nuna masa, zanen kamfanin ne da photon jariran sai kuma kalmar A.M.A "Da fari mu fara gano ma'anar kalmar A.M.A, photon jariran kuma mai sauƙi ne ana nuna maka har jarirai da aka haifa yau ana siyar da shi a kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY, abu biyu ne wanda dole za ka yi ko kusan ukun, da fari sato ita wannan yarinyar ta yiwu a samu wani haske tattare da ita, na biyu kasan yadda duk ka yi ka mallake wannan kamfanin cikin sauƙi, na uku....," sai kuma ta yi shiru ta dinga kallon Moh ciki da bai


"Waye Mutallab, waye kai, dole ka faɗa mini asalin waye kai kana ji na?"


"To na haƙura"


Ya miƙe tsaye a hankali a lokacin ras yake sai abubuwan da sukai masa tsaye a zuciya da maƙoshi "Dole na san waye kai, ko ka faɗa mini ko ba ka faɗa ba, abu na uku sai ranar da asalin naka ya zo kunnuwana zan furta maka shi" bai dai yi magana ba, hannunsa zube cikin alijun kayan da Abbasa ta basa ya sauya da ƙyar yafi ƙarfin minti ashirin a tsayen yana harhaɗa kalmomin abin da zai ce mata ransa duk a jagole. "Lalacewar Moh bai kai ya sato yarinya ba"


"Kuma dole a yi hakan fa"


Ya yi waje abinsa yana yana ƙoƙarin ficewa daga cikin bukkar ta ce "Baka da lokaci fa Mutallab, kuma baka da ikon taɓa ta a waje idan ba kana shirin komawa gidan yari bane, kasan yadda za ka yi dai wish you all the Mutallab"


Bai ƙara bi ta kanta ba, ya dinga ɗora ƙafafuwansa a ƙasa kamar mai tsoron taka ƙasa sai haɗe fuska yake yana kwaɓewa duniyar ya ji ta yi maza zafi ta ko'ina, ya rasa ina zai je me kuma zai yi sai ɗaga yatsun ƙafarsa yake wanda suke zara-zara matar nan Abbasa ta fara takura masa ko waye ya ce ta yi masa gyaran farce? Yama a ka yi ta samu mai yin aski ya wani kwashe masa suma? Bakin bishiya ya samu ya zauna ya sunkuyar da kansa ƙasa, zufa ta shiga tsattsafo masa ta tsakiyar goshi ya sa yatsa ɗaya yana gogewa ya shafa jikinsa ba kayan garawa ko ɗaya yana buƙatar fita daga yanayin da yake ciki, baya son tunawa ko da wasa.
_“One day i will leave you, duk son nan da nake maka”_


Ya ji saukar muryarta a kansa ta sauka har ƙasan zuciyarsa a ɗan lumshe idanunsa da ya yi, ya juya zuwa gefe sai yake ganin bidiyon abin da ya faru bayan kammala assembly, at that time yana can baya zaune ya yi shiru yana kallon students bai san da zuwanta ba sai ganinta ya yi ta baya kamar zata shige jikinsa ya fiddo manyan idanunsa waje yana miƙewa tsaye hannunsa ɗaya zube a aljihu ya dinga kallon ta da ƙyar ya furta "And what is this Safiyyerh?"


"Bestie shi ake cewa love mana" ta langwaɓar da kai gefe yana sake kallon yaluwar fuskarta kamar zabiya. "To iskanci za ki mini?"


"Iskanci kuma bestie? Me ya sa kake haka ne, son ka kawai nake yi fa why are you doing this to me? Kai ba'a gane maka sam? Ko murmushin masoya ne ka dinga yi mini mana, bafa ni na ɗorawa kai na son ka ba" idanunta ya cika da waye tana jin zuciyarta na yi mata zafi bata ganin komai a idanunta sai fuskar Mutallab.


"A love? Shine za a yi wa mutum fyaɗe a soyayyar??" Ta buɗe idanu tana rufe baki jikinta har rawa yake tana jin kamar ta idda abin da zuriyarta ke umartar ta "To ka yi haƙuri idan dai na mutu ka huta, kuma idan baka zo gidanmu yau ba Allah a wajan Ammo zan kwana" fuskar nan a ɗaure ya ja sirirn tsaki ya shige cikin class kafin ya ƙarasa ya ƙara jiyo ta a bayansa tana sake yunƙurin riƙe shi da sauri ta juya sai kuma ta ɗauki school bag ɗinta ta fice daga makarantar tana kuka.


*** "i missed the hug" ya furta ƙasan zuciyarsa lokacin da bidiyon abin ya ɗauke daga kusa da shi, ya yi shiru yana tunani har yamma ta yi lis bashi da niyyar tashi daga wajan baya son shiga cikin jama'a yana jin nan ɗin shine daidai da ina ya kamata ya ɓoyewa kwalawa. He feels uncomfortable a cikin jama'a haka nan.


Safiyyerh na zaune bayan ta dawo daga kamfani ko ɗaki bata shiga ba idan ta tuna yadda Hon Maɗatai ya sake matsa mata akan hannun jarin da yake son sawa a FS WORLD INVESTMENT COMPANY sai ranta ya sake ɓaci, duk dukiyar da Ubangiji Ya bashi bai gode Allah ba, mutane nawa ne a wannan duniyar da basa ci, idan anci na safe ana fargabar na rana, idan na rana ya samu dare kuma sai dai a yi salatin Annabi a sha ruwa a kwanta, masifar rayuwa ta yi wa talaka dirar mikiya, yunwa na neman illata su ga lalura ga rashin aikin yi? Amma hon Maɗatai shi dukiya yake nema idanu rufe ƴan siyasa da yawa kansu kawai suka sani suke ginawa, mene amfanin talaka ya je ya yi zaɓen? Gabaɗaya sabgogin dimokuraɗiyya ya lalace son zuciya kowa yake bi. Ta yi tsaki tana jin ko zata rasa kujerar Manager ɗin ba zata taɓa bari Hon Maɗatai ya saka hannu a kamfanin ba.


Miƙewa ta yi ta nufi bedroom bata ɗauki wani lokaci ba ta fito sanye da wando da riga,wandon iya cinya kanta ko ɗan kwali babu da mamaki take kallon Captain ganin ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana danna mata system ga wayarta a hannunsa kafin ta ƙarasu ya kashe system ɗin ya ajjiye har wayar. "Yaya me kake nema a system ɗita kuma?" Ya yi mata shiru ta zauna kawai tana buɗewa bata sake kallon shi ba, ta shiga duba dukkan ayyukan da aka fitar yau da sauri ta kira accouter da number da take amfani da shi na kamfanin tana girgiza ƙafa a hankali cikin faɗa ta ce


"Accouter me nake gani a haka? Kuɗi fa kimanin miliyan 500m yanzu sun shigo account na kamfani dana gani a bayanai, bayan tafiyata me aka fitar ne shinkafa ko me?" Faɗa take sosai domin ta iya faɗa ajin ƙarshe ce a fannin.


"Manager nifa kina tunawa accouter ne kawai, bani ke da alhakin saka hannu a fitar kaya ko shigowar su ba, kawai ni ke saka hannu a duk wani kuɗi da zai shigo ya fita, i am nothing but a Accounter"
Miƙewa tsaye ta yi tana riƙe ƙugu ta ce "Rubbish; ka tura mini ducoment na PDF via email na abin da aka siya har miliyan 500m yanzu yanzu accouter"


"Ki yi magana da Md ni kawai kuɗin naga shigowar su babu wani file daya zo officer nawa, trust me manager ba zan ɓoye miki, na san dai bayan tafiyarki Professor Abdu Marafa ya shigo kamfanin" "daddy!"
Ta furta da ƙarfi "E, mahaifinki shi"


"Kamarya to?"


"Shine ban sani ba" sai kawai ta kashe wayar ta ajjiye waje guda, ta sauke numfashi da ƙyar ta shiga uku meke shirin faruwa ya ake ƙoƙarin amfani da ita ba tare data sani ba?"


"Yaya" bai amsa ba idanunsa a ƙafarta ta ce "Yaya bacci nake ji" "to ina ruwana"


Sai kawai yaga ta ɗora kanta a cinyarsa maimakon ta juya masa baya sai ta juyo wajan cikinsa ta yi shiru tana kallon ƙirjinsa dake buɗe. Ta yi shiru tana sauke numfashi shi dai bai yi magana ba, bai ɗauka haka take da masifa ba yana jin ƙirjinta na ɗagawa a hankali kuma bacci ya ɗauke ta. Cikin baccin ta ji hucin numfashi ta buɗe idanu kallonsa ta dinga yi yadda ya kifa fuskarsa a tata hannunsa ɗaya tamƙe cikin nata "Captain" da sauri ya buɗe idanun ya ƙurawa cikin idanunta ido sai kuma ya ɗauke fuska yana haɗe rai. Fiyya bata ce komai ba ta miƙe zaune shi kuma ya shige cikin part ɗinsa yana taku da sauri sai shafa kai yake yi.


Notification ta gani kamar wancan lokacin saƙo ne ta dm nata. Ta buɗe ba wani magana mai tsayi bane sai dai maganar dab take da rusa tunaninta ta bi saƙon da kallo inda ake cewa.
_“bai ci a ce kin yi mantuwa mai nisan haka ba, ki tuna akwai hakƙin wani kan ki Allah Yana kallon ki TIGER“_ ta dafe kan ta to hakƙin waye a kanta waye mai wannan saƙon kuma? Tsaki ta yi ta miƙe ta bar parlon. Bata sake ganin Captain ba har dare ta yi kwanciyarta.


****
Cikin sauri take tafiya tana yi tana juyawa sauri take ta isa chemist amsar maganin ga dare ya raba mijin nata ya fita. Kamar daga sama taga mutane sun tsaya gabanta fuska rufe "Su waye ku? Don Allah ku rufa mini asiri magani zan siyo" muryarta na rawa ta yi maganar. Haɗa idanu sukai sai suka ɗaga ta sama tare da danna ta cikin napep ɗin basu tsaya ko'ina ba sai wani kango a nan taga wasu mutanen kwance kamar basu da rai, kuka take tana duk addu'ar data zo bakinta "Don Allah kar ku cutar dani don Allah ku rufa mini asiri da yarana da rayuwarsu"
Tana ji tana gani suka danneta tun tana ihu har ta kasa jini kamar an yanka rago babu imani suka cire ƙwayar idanunta duk biyun tare da watsa su cikin aliju da gudu suka fice daga kangon.


Bayan ta dawo daga wajan aiki ta shige gidan Anty Turai saboda kiran da ta yi mata, a parlo ta samu Anty Turai da yaranta da kuma wasu ƴan mata zaune. "Ina yini Anty?"


"Sannu matar Captain Aliyu Marafa?" Cewar Anty Turai ita dai Safiyyerh idanunta akan waya bata ce komai ba Waheeda ta ce "Mama wai shi Uncle captain ɗin son ta yake yi ne? Ni banga abin so a jikin wannan zabiyar ba sam sam wallahi" Zahiderh ta yi saurin cewa "Ina fa? Captain ne zai ce yana son Fiyya never wallahi, kawai dai auren dole aka yi masa, wannan fari ko na lalura"


Safiyyerh dai jinsu take Anty Turai ta ce "Sannu Safiyyerh, ya kamfanin yanzu ai Aliyun ya bar nan wajan Zahiderh ya zo ki dinga haƙuri da shi ya jaddada mini baya buƙatar ki cikin rayuwarsa bai san me zai yi da zabiya ba" miƙewa Safiyyerh ta yi ta ce "To Anty a ɗaura masa aure da Zahiderh ni bani da wata matsala, zabiya kuma ina jira ku halitto irin kalar idan da sauƙi, so kuma ba abin da ya yi mini zafi da shi zan zauna da mijina haka tunda zaɓin daddy ne, wallahi babu wanda ya kai level ɗin ɗagawa Fiyya hankali" Anty Turai ta miƙe tana nuna Fiyya idanunta ya rufe sam bata kula da shigowar shi ba, balle ankarar da ita da su Waheeda suke ta ɗaga hannu zata mari Fiyya dake tsaye tana juya idanunta ta ji an riƙe hannun.


Tun zuwan shi ta ji ƙamshin turaren nasa, ya tsaya a bayanta Anty Turai ta kalli Aliyu ta kasa cewa komai ya saki hannunta yana matsawa bayan Fiyya ya zagaye hannunsa a ƙugunta ya jata jikinsa daga baya yana sake kallon Anty Turai "Shekararki nawa Anty yaushe na zo gidan naki kuma? And who told you bana son ta?" Duk a dagule yake maganar yana sake haɗe Fiyya da ƙirjinsa kasancewarta duguwa sosai so ma sha Allah. "Aliyu ni zaka shigo gida ka faɗawa haka?"


Bai kalleta ba sai Fiyya daya kalla wacce take shirin juyawa idanunta cike da hawaye ya yi saurin riƙo hannunta yana "Wait" sai kawai ta kifa kanta a ƙirjinsa tana shassheƙar kukan da bata shirya saboda ganin idanunsa "Anty karki sake mini haka"
"Idan na sake me za ka yi Aliyu na ce me za ka yi?" Ya girgiza kai ya rungume Fiyya tsam a jikinsa ya ce "Ban san me zan iya yi ba, kawai dai na faɗa miki, kuma i love my wife" Fiyya ta yi saurin ɗago kai ta kalle shi ya ɗage mata gira "Yes, I Iove You Safii" yana cewa haka ya kama hannunta suka fice.


***
Suna zaune a dabarsu ya yi sauri ya miƙe tsaye Goje ya ce


"Sai godiya, ina aka nufa don shirwa kake baka jewar banza, ɓauna mai tafiyar ɗaukan rai jeji naka dabbobi naka, a lafiya mai dawa" jikinsa ya ji ya fara kakkarwa tsohon tsuminsa na neman tashi ya yi ƙasa da kansa yana ƙoƙarin hana kansa yin kirari da amsar saƙon Goje, ya bar wannan layin tuni. Da ƙyar yana girgiza kai ya ce


"Goje"


"Sai godiya, wuya a ina wuya a daji kai ne mai dawa da jeji na Malam Abdu shalelen Ammo, ƙanin Sa'adah da Bafullatana a lafiya aminin Hamida, ɓauna taka mesa taka ba wani bayanka jan biro maganin daƙiƙin yaro Allah Ya ja da ran mai dawa" gabaɗaya jikin Mai dawa ɓari yake yana damƙe hannunsa wajan ganin mai ɗaga su sama ba har can cikin kansa yake jin kirarin. Kawai ya juya ya bar wajan "Wai ina zaka ne kasan yanayin da ake ciki fa akwai cinnaku"


"Baka haifan ba balle ka tambayan karka biyo ni" yana cewa haka ya bar wajan ya jima yana tafiya kafin ya ƙarasu gidan sai ya saka maƙulli ya buɗe ya shiga.


A ɓangaren su Safiyyerh tunda suka bar gidan Anty Turai suka shiga mota basu ce komai ba ya kuma haɗe fuska itama bata ce komai ba, daidai wani gida a bakin titi taga ya tsaya ya kalle ta "Kar ki fito jira ni nan" ta jinjina masa kai. Fita ya yi ta jingina tana ɗaukan waya, abin da ta fara cin karo da shi a X picture ɗin wani kyakkyawan yaro yana murmushi ya rufe idanunsa saboda hasken da ya yi masa yawa kamar ka taɓa shi jini ya fito, ta dinga kallon picture ɗin sai kawai ta yi skipping zuwa next tweet.


A hankali ya buɗe ƙofar ya shiga idanunsa zube a saman tafkeken screen ɗin computer dake jikin bango, gabaɗaya wajan nau'in kayan computer ne kala-kala. Ya ɗan dafa kafaɗar wanda yake zaune akan kujera yana juyawa a hankali, kallo ɗaya zaka yi masa kasan mayen computer ne masanin hakin da duk wani surƙulle. Captain ya ce "Where are you hiding?" Ya ɗaga idanunsa a hankali ya kalli Captain bai ce komai ba kuma ya cigaba da danna wayar, Captain ya saka hannu ya dungure masa kai ya nemi waje ya zauna yana taɓa computer shima. Da sauri ya miƙe kuma jin sautin muryarta da yadda take ƙoƙarin buɗe ƙofar ya yi saurin miƙewa ya nufi ƙofar daidai nan Fiyya ta shigo "Yaya gaskiya yunwa nake ji akwai hadari sosai a gari ina tsoron ruwa"


"Muje"


Ya yi saurin faɗa yana kama hannunta tare da rufe ta da jikinsa leƙawa take son yi ya saka hannu ya juyar da fuskarta ya jata waje, shima ɗin dake zaune ya juyo a nutse ganin sun fita ya saka ya cigaba da abin da yake yi.


Cikin dare Fiyya na bacci ta ji ana buga ƙofar parlon kamar za a cire ta, ta miƙe da sauri riga da wando ne jikinta na bacci wandon iya cinya ta saka slipper ta fito, tana mamakin mai ya sa Captain ya kai dare har haka? Ta buɗe ƙofar "Yaya ka tashe ni daga musulmin bacci da nake..." Shiru ta yi tana yin baya ganin shi tsaye a bakin ƙofa su Goje da Mangal a bayansa "Kai ne me ka zo yi mini har gidan mijina, matar aure ce ni fa" banko ƙofar Moh ya yi ya shiga yana ƙarewa parlon kallo


"Mai dawa ɗauke ta mu shige kar a yi ta kwanaki" ta gudu Fiyya ta juya zuwa part ɗin Captain tana kirin sunansa a tsora ce kafin ta ƙarasa Moh ya saka ƙafa ya falleta ta faɗi ƙasan tayal idanunsa ya yi jajur domin ba haka ya zo da su ba, jin ana shirin buɗe ƙofar ɗakin Captain Moh ya kalli Goje da sauri Goje ya laɓe a baya kafin Captain ya fito, cikin sauri ya rufe fuskarsa da ƙyalle.


"Safii are you ok? Peanut ihun nan fa wife?" Yana fitowa Goje ya saka gora ya maka masa a ka kasancewar Captain bai shirya ba ya faɗi a wajan da sauri kuma Moh ya ce Goje ya ɗauki Fiyya ko me ya tuna sai ya saka hannu ɗaya ya sunkuceta a kafaɗa yana ɗaga wuƙa sama suka fice daga gidan...




MUTALLAB.
Book 1, 2 &3
500 Naira
0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S a tura shaidar biya ta nan 08164069385


Zan yi cutting free a shafi na 15 in sha Allah. Wannan shafin 🥰🥰🔥🔥🔥🔥ku hanzarta yin payment kafin wannan lokacin yanzu kuma na labarin a rufe yake zuwa gaba za ku ce kun shiga uku ashe haka abin yake😂😂ina ƙara tuna muku ba fa farkon labarin muke a tsakiya muke waya san mene ya faru a farkon? Me kuma zai faru a gaba? Just pay 500 naira only.[10/23, 5:43 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥*


Page 13
*Bright pens..2nd batch*


Safiyyerh na durƙushe a ɗan ƙaramin ɗakin da suka ajjiye ta ciki, warin sigari ya cika ɗakin sai yunƙurin amai take yi ta kasa, ta shiga tashin hankali da tunanin suwaye waɗannan da suka je har gidan mijinta suka dake shi tare da yin kidnapped ɗinta? Me suke buƙata a wajanta waya saka su yin hakan? Da alama ba kuɗi suke nema ba wani muradi ne a ran su da suke son cikawa manufar da bata san ta mece ce ba. Ta ɗago kanta da ƙyar tana buɗe kumburarrun idanunta saboda kukan da ta yi da hanzari ta fara buga ƙofar da hannunta tana girgizawa tare da faɗin.


"Wai baku da imani ne me na yi muku idan kuɗi kuke buƙata ku bani waya na kira daddyna zai biya duk abin da kuka buƙata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login