Showing 54001 words to 57000 words out of 63481 words

Chapter 19 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt

23 Nov 2024

6685

zata riƙe shi ya yi saurin baya yana ficewa daga gidan Goje yana ta dariya da buga ƙafa


"Kinga aikin Mai jeji gana Scorpion nan"


****Eng Ali wali yana zaune a gidan wutawarsa yana zantawa da wasu manyan mutane masu taimaka masa a harkar kamfel ya dubi P.a ya ce "P.A ina tunanin iya abin da ake buƙata kenan kuma na bada, ka sani ba kuɗi yanzu a ƙasa kamfen ya cinye komai, you can manage ko?"


"Ba damuwa amma muna da raguwar list na local government wajan biyar da bamu je ba yanzu haka, ga ƴan media sun matsa kasan mutane babu amana gwara a fara watsa musu hatsi tun yanzu fa a yi maganin yunwar data addaba musu" Ali wali ya yi murmushi yana juya kai kafin ya ce "Ku je za mu yi magana zuwa dare ina da hira da ƴan zuwa dare we'll talk" P.A ya kalli mutanen ya ce


"Don't make any mistakes idan kun shiga gidan rediyon ku tabbatar kun yi abin da ya dace, kar kuma ku nuna wata alaƙa tsakaninmu da ku yadda na faɗa muku haka zaku faɗa" "In sha Allah, ai harma da abin da baku buƙata ba mu indai za a biya mu ai buƙatar maje hajji sallah zamu farfaɗi ayyukan bogi da ya yi kuma ya yi mana"


"Nice to hear this, you can leave ku je"


Tafiya suka yi suna murnar ƴar dubu biyar biyar ɗin da za a basu akan faɗar abin da ba haka bane. Ali wali na shirin miƙewa ya ji numfashi a bayansa ya juya da sauri, tsaye ya ga Moh fuskarsa rufe sai ƙwayar idanunsa da take a fili ya cake yana muzurai. "ka bani tsoro amma"


"Mara gaskiya ko a ruwa zufa yake"


"Me na yi na rashin gaskiya?" Ya yi masa shiru yana wani irin fito ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗora saman kujera yana zaro kunama ya ajjiye saman kujerar wajan ta fara yawo tana ɗaga ƙari sama ta kumbura sosai. "Yaushe ka shigo? Na ce ni zan dinga nemanka bawai ka dinga biyo ni duk inda nake ba, bana so a san ina mu'amala da kai"


"Saboda annoba ne ni? Tunda ka jawo ni haka zaka shanye duk abin da na dama, na kwalo yarinyar mene next?" Murmushi Ali wali ya yi ya ce "Ai na san kun ɗakko ta, tunda CSP ya yi mini magana akan case ɗin kidnaping sannu namijin duniya"


"Zan kawo ta nan"


"Ina? A'a ka bar ta nan wajanku zan baka key ɗin wani gida sai ku tafi can kwafi sararawa ni bani da gaske koda zaka dinga huta gajiyarka a wajanta kana rage zafi" Moh ya ɗaga kai ya kalli Ali wali da kyau.


"Wacce gajiyar, sanyi ne a jikinta?"


"Kana abu kamar ba wayayye ba, mu bar maganar ka yi mini aiki na farko and i appreciate it. Sai batun Scorpion" daidai nan kunamar dake yawo a wajan ta shige hannun Moh ya matse ta ya yar waje guda Ali wali ya cigaba da cewa "Scorpion ba zai bar mu ba, Hon Maɗatai yake hari a yanzu nasan kuma bayan nan ni ne a list, yana neman zame mana masifa yana kawo mana barazana a akan siyasarmu gwara Hon Maɗatai ya samu dukkan abin da yake nema a mulki ya samu nasa rabon ni yaushe na fara? I will never let that happen ba zan bari ya yi galaba akai na ba"


"Me za ka yi?"


"Zan tabbatar an nemo shi an ɓatar da shi, don ba haka kawai yake yin abin da yake ba akwai abin da ya taka yake taƙama da gadara dashi, ka yi ƙoƙarin nemo mini shi kafin hukumar FID su kama shi zan ruɓanya maka abin da duk na yi niyya"


"To kuna da case da shi?" Ali wali yace "Pardon? Kamarya kenan"


"Basar"


Key ɗin gidan ya basa, hadda na mota Moh yaƙi amsa wai he don't know how to drive ya basa kuɗin abincin Fiyya mai kyau da duk abin da take so.


"Kaƙi faɗa mini waye kai dai ban san komai dangane da kai ba Moh, sunanka kawai na sani Mutallab without surname and middle name, whatever shikenan dai" Moh ya ƙara ɗaga ƙafa zai fita Eng Ali wali yace


"One more think Mutallab"


"Ali wali ka kira ni da ɗan daba ko ɗan ta'adda sai mu yi magana" Ali wali ya yi murmushi ya ce "Sai godiya" ya tsuke fuska Moh.


"Professor Abdu Marafa ya mini mummunan tabo a zuciyar matasan jihar nan,ya ɓata mini suna na ji ina son ɗanɗana masa kwatankwacin abin da ya yi mini ta hanyar ramuwar gayya wacce ake cewa tafi ta gayya daɗi, kamar yadda ya ɓata ni shima haka nake so a ɓata tarihin tarbiyyar gidansa da sunan da yake taƙama da shi, a dinga masa kallo a matsayin wanda ya gaza" Ya yi shiru yana sauke numfashi yana duba wayarsa ganin shugaban jam'iyya na kiran shi ya miƙe tsaye.


"Bayan sato budurwar ƴarsa da kuka yi har gida, ina son ka yi Safiyyerh Abdu Marafa fyaɗe, ina son ka yi wa Safiyyerh Abdu Marafa ciki kaga tana da auren wani, wani kuma daban ya yi mata ciki wanin ma ɗan daba, ɗan daban da basu san waye shi ba, kaga Safiyyerh zata haifi ɗan zina ko"


"Ɗan zina?"


Moh ya maimaita a fili Ali wali ya ce "To ɗan mene? Yayinda da wani wanda ba mijin yarinyar ba ya keɓe da yarinya har ta samu ciki wannan cikin ya sunan shi? Cikin shege ba haka lissafin yake, idan na ce wani zan bawa wani aikin lissafin Eng Ali wali bai gama cika ɗari over ɗari ba, dole kai zaka aikata haka Mutallab dole kai zaka yi wa Safiyyerh ciki domin dauɗar gora ciki kan shata"


"Wanne zunubi ita yarinyar ta aikata, gyatuminta ne kamar batun nan ba zan ba, shi kuma daman cikin yinsa ake yi? Ba kawai girma yake ba?" "Au baka san yin ciki ake ba? Shekarar nawa?"


"Koma mene ba za a yi ba" Ali wali ya yi murmushi ya ce "Dole zaka yi, ka rubuta kuma ka ajjiye sanda za ka yi baka sani ba jeka" bai wani ɗauki maganar Eng Ali wali da muhimmanci ba ya fice daga gidan.


***Safiyyerh ta rufo ƙofar bayan ta gama dubawa ta kalli Goje ta ce "Kawai ku siyo mini kayan abincin na dinga dafawa sai ina san muku?"


"Kin iya wato ne?"


"Mene wato?" Ya ce "Shi girkin nake batu" ta jinjina masa kai ya miƙe tsaye ya ce "Da kin yi dabara daman ba ki da wani amfani. Ita mamaki ta yi ganin kitchen hadda tukunya plates da spoons ga risho da sauran tarkace. Babu jimawa Goje ya dawo hannunsa riƙe da Indomie guda biyar da ƙwai guda goma hadda kayan miya da magi ya bata ya ce


"Ta yi musulmin daɗi kin ji Manager"


Ta samu kanta da yin murmushi a ranta kuwa dabara take yi ta samu hanyar guduwa. Suna tsaye ya faɗo cikin gidan sai ya yi turus yana kallon Goje yaƙi yadda ya kalle ta, ta ƙasan idanu ita kuma take binsa da idanu mamakin yadda jikinsa yake a murɗe take har ƙasan zuciyarta ta ji tana shakkarsa. "Barka da antayowa mai jeji ya ƙarin haƙuri" banza ya yi masa ya shige ciki Safiyyerh ta ce


"Au rashi ma aka yi masa?"


"Yayarsa aka sace sai jiya aka kanta an ƙwaƙwale mata idanu" Safiyyerh ta zare idanu tana dafe ƙirji sai tausayinsa ya kamata a raunace ta ce "Kuma bai je gida ba? Anya yana son yayar tasa kuma kun tabbatar wannan ba mahaukaci bane?" Shi dai tuni Goje ya bar wajan. Ta gama dafa Indomie wacce ta ji azabar Attahiru rabon da ta shiga kitchen a rayuwa ta manta fuskarta ta yi jajir da wani irin roɗi-roɗi idanun sukai micin-micin ta dinga mata ƙaiƙayi fuskar saboda zafin wuta ta nemi kaɗan ta juye musu a faranti.


Moh yana kallon yadda ruga lauma kamar mayunwata sai jan yaji suke yi ya kalli Indomien ya kalle su can ya miƙe ta ce "Kai baza ka ci ba? Ni ina son yin sallah fa" duk suka share ta, suna gama ci suka fice tare da rufo ƙofar ya rage sai ita kaɗai ta haɗe kai da qwwia ta dinga kuka kamar ranta zai fita har bacci ya ɗauke ta a wajan.


Cikin bacci ta ji an cillo mata abu ta miƙe da buɗe idanu tsaye ta ganshi ya juya baya leda ce ya cillo ta buɗe taga duguwar riga guda biyu da hijabi da takalmi ta yi ta mamakin yadda ya san size ɗinta ta miƙe tsaye yana jin zata zo wajansa ya nufi hanyar fita ta sha gabansa ya yi turus ta dinga kallonsa shima yana kallonta


"Wai kai baka yin magana ne, ko ƴar dariya babu kafin na tafi mu ƙulla mu zama abokai" ta miƙo masa hannu ya kalli hannunta mai ɗauke da siririn zobe sai yatsunta zara zara da su "Am Safiyyerh Abdu Marafa You?" Ya sake yin shiru ta langwaɓar da kanta gefe guda ta ce "Ina son zama ƙawarka fa, zan maka labarin daddyna da yadda yake so na, da labarin kamfanin da nake aiki hadda labarin Ashraf wanda zan aura ya mutu aka aura mini captain labarin Ummimi da Kinal ƙawata i will tell you everything, abota Frist?" Ta sake miƙa masa hannun a karo na uku. Gefenta ya bi ya shige yana rufe ƙofar gidan ya bar ta tsaye da hannu a ƙaƙe takaici ya ishe ta shi wannan yana ɗan ta'adda yana jin kansa kamar ɗan gidan ƙaruna saboda faɗin rai ga miskilancin masifa the manager ita Safiyyerh take magana ake sharewa bai san cewa akan dole take yin maganar ba? Ta lumshe idanunta hawaye na cika cikinsu da ƙyar ta yi alwala ta fara jero salloli. Goje ne ya shigo da sauri ya ce


"Ke kina ina fito maza taso" ta miƙe za ta yi masa gaddama kawar Moh ya shigo ya damƙi hannunta ta kalli baƙin hannunsa da ɗan mitsitsin nata farin hannun ya jata sukai waje mota ta gani bai tsaya jiran komai ba ya dannata a gaba Goje ya shiga baya Mangal dake tsaye ya ce


"Waye zai ja motar yanzu? Ni ban iya ba kuma haka?"


Moh dake shirin shiga mazaunin driver ko me ya tuna ya kalli Safiyyerh a karo na farko ta ji muryarsa a sake ya ce "Dawo nan" tsoran shi take ji ta fito ta koma wajan driver ya dawo ita ta tashi, ya cilla mata key ɗin motar "Muje" bisimillah ta yi ta fara driving ta juya ta kalle shi ta ce "Ina?" Ya bata wayar hannunsa wacce yanzu ya shigo da ita ta duba location da ya fara driving cikin sauri har suka bar wajan.


Mintuna kaɗan da barin su motoci suka tsaya a ƙofar gidan Captain ya fito jikinsa danye da uniform na sojoji da suka amshe shi sosai ga ƙatuwar bindiga sauran yaransa suka fito a hankali ya dinga bin wajan da kallo har ya shiga cikin gidan abin da ya fara cin karo da shi ya sanya zuciyarsa bugawa ganin rigar baccin Fiyya yashe a ƙasa ya ɗuka ya ɗauki rigar idanunsa ya sauka akan wani busasshen jini ya dinga kallon gidan a nan ya kalli ƙwayoyi kala-kala da wuƙaƙe da gorori ya lumshe idanunsa "Where are you Wife? Ina suka kai mini mata?"


"Captain kuma ka tabbatar tracking ɗin nan ya nuna?" Ya jinjina kai don baya jin zai iya magana. "Sun gudu, amma ya akai sukai san an yi tracking location nasu har suka gudu da wuri haka?"
Captain ya girgiza kai irin bai sani ba "Ka kwantar da hankalinka matarka zata kuɓuta ko kana tunanin sun yi mata wani abu ne?" Captain ya nuna masa rigar baccin Safiyyerh da jinin dake wajan mutumin ya dafe kai ya ce
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, in sha Allah ba abin da muke zato bane muje" fita sukai Captain ya ji a ransa ba zai bar abin haka nan ba.


Mutallab wani gida ya kai su madaidaici mai kyau da tsari da yake can bayan gari duk suna zaune Safiyyerh kanta na ƙasa tana mamakin yawan shiriun bawan Allan nan, idan ya yi shiru shi kaɗai sai ya saki ajjiyar zuciya ko ya ƙurawa waje guda ido.


***Wajan sati guda babu labari akan batun sace Safiyyerh ba kiran waya babu komai Daddy ya hana a faɗi maganar ko a social media ko a gidan rediyo ya ce a bar ta tsakaninsu. Yana ƙwace hannunsa maƙale da ruwa muryarsa a hankali ya ce "Aliyu waye ya saka?"


"She is my wife daddy"


"And? Ɗan sanda ne kai ko soja?"


"Zan iya amfani da uniform ɗina ko babu haka ai she is my responsibilities yanzu na kula da haƙƙina zan ji na zama lusari idan ban nemo Safii ba, kar ka dakatar dani daddy police su yi nasu aikin ni na yi nawa"


"Ka cire hannunka a ciki Aliyu"


"Ok zan jire akan wanne dalili?"


"Aliyu yanzu baka tunanin dalilin hakan su yi mata wani abu ne? Baka san su waye mutanen nan ba, duk abin da zaka ji a bayan nawa dana Zahiyerh yake kar ka yi kuskuren da za su salwantar da rayuwar Maama na roƙe ka, mutanen ba mutunci ne da su ba kamar komai hannun Sp Ghali" Aliyu ya miƙe ya nufi ƙofa "I am sorry daddy idan kaga na tsaya to na mutu ne, idan da numfashi a ƙirjina ba zan gusa ba sai na dawo da Safiyyerh cikin rayuwata i am sorry" yana cewa haka ya bar ɗakin.










Daddy ya rufe idanunsa daya cika da ƙwalla ya wani irin ramewa ko abinci baya ci Ummi ta ce "Ka san halin Aliyu da baka fito masa ta haka ba, gwara ka saka Ummimi yi masa magana" daddy yaƙi cewa komai. Wayarsa ta fara ƙara number ya gani sai ya yi sauri ya ɗaga yana kaiwa kunne aka ce.


"Barka, ina magana da Professor Abdu Marafa na sani ko baka amsa, zan fara da yi maka ya jiki don ina da yaƙinin kana nan zuciyarka na ciwo bari na ɗora maka da wata maganar ban sani ba ko zaka iya jure jin abin da zan faɗa. Yarinyar da kake ji da ita ni na saka a sato mini ita Safiyyerh kenan ina son ka lashe aman da ka yi da kanka. Professor ni ɗan siyasa ne lissafin ɗan siyasa daban yake dana Malami, bana barin kota kwana daman mun saba saka jama'a a uku, wallahi ka shiga komata yanzu nine da wasan ka fara lissafa ranakun mutuwar yarinyarka daga yanzu" da sauri Daddy ya ce


"Waye kai?"


"Sarai ka ɗauki ne muryarta professor, kana magana da Eng Ali wali mai neman takarar ɗan majalisa, ka hanani bacci yanzu lokaci ne da zaka ji abin da nake ji". "Ali wali me kake buƙata me Safiyyerh ta yi maka karka cutar mini da yarinyar don girman Allah kar ka taɓa ta"


"E, ba zan taɓa ta ba muddin ka yi abin da nake so"


"Me kake so?"


"Ka dawo jam'iyyata kuma tsagina ka lashe aman da ka yi ka kuma gyara ɓarnar da ka mini na rusa mini dukkan shirina, yadda ka ɓata sunana a wajan matasa da al'umma a gidan rediyo da kai da ɗan jaridar da yake mara maka baya ku sake sabon lale wajan wanke ni inma kana buƙatar kuɗi zan bayar hakan ba laifi bane ba"


"Uhm Ali wali kenan tun yanzu har ya yi sauri haka? Ni kake cewa idan ina buƙatar kuɗi kaga na yi maka kala da mabuƙaci? Kamar dai ka manta waye Professor kana buƙatar tuni na, laaa la la dama sauran lokaci ai. And da kake batun Safiyyerh tunaninka ita ce raunina ko?" Daddy ya tsige ruwan hannunsa da ake ƙara masa ya sakko daga saman gadonsa daman tuni ya nunawa Ummi ƙofar fita tun kafin ma ya ɗaga kiran.


"Ka yi kuskure sosai, Safiyyerh is nothing to me kuma she never be my headache idan ka so ka saka wuƙa ka yankata a yanzu is doesn't matter for me, idan akan Safiyyerh ka kira ka mini warning ka makara Ali wali tunda Safiyyerh ta bar gidan nan ko da dai da rana ban taɓa tunaninta ba siyasa ce kai kuma yaro ne mu zuba mu gani"


A ɓangaren Ali wali dariya shima ya yi ya ce "Lallai prof ka cika ɗan siyasa, to wallahi ka shirya ganin gawar Safiyyerh a wannan daren ku tara ƴan jana'izarta". "Idan ka haifo kuma kai cikakken ɗan iska ne idan har ba zina akai ka haifeka ba na roƙeƙa Ali wali don Allah ka kashe Safiyyerh nima fa wani aikin ka rage mini..," ƙit Ali wali ya kashe wayar daddy ya saki dariya yana wani irin murmushi wata number ya kira ana ɗagawa ya shige toilet yana saka key, ya jima ciki kafin ya fito ya zauna saman gado Dr Hash ya shigo da Yaya J ganin daddy zaune ya saka dr cewa "Daddy ya jikin naka?" Hawaye ya cika idanun daddy ya ce "ba abin da zai tafi daidai babu Safiyyerh zuciyata zafi take my innocent Fiyya, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ina tsoran halin da Ummimi zata shiga" ganin hawaye a idon mahaifin nasu ya saka Junaid ficewa dr ya zauna ya dinga lallaɓa daddy da bashi bakin za a ga Safiyyerh in sha Allah.


Aliyu yana zaune a ɗakinsa aka buɗe ƙofa tare da shigowa ya ɗaga kai ya kalleta ya miƙe da sauri duk da babu fara'a a fuskarsa amma sai da ya saki ajjiyar zuciya. Ta juya idanunta "Nan ka ɓoye?" Ya girgiza mata kai


"Ka cigaba da binciken inda Safiyyerh take Aliyu kar ka saurari mahaifinka ka ji ko?" "in sha Allah Ummimi" ta zuba masa ido sai ta juya ya ce "Tafiya za ki yi?"


"Me zan maka?"


"Love, ganin ki nake son yi" ta haɗe rai tana cewa "To ɗakko zani na goyaka" ya buɗe idanunsa ya yi wajanta yana rungume ta ya saki ajjiyar zuciya "I love you Ummimi, and I love Safii too"


Kan shi ta shafa ta ce "Kawai ka zaɓa ni ko ita" ya lumshe idanunsa ya yi mata shiru, rungume shi ta yi a jikinta ta yi shiru tunani daban daban a ranta sai kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login