Showing 48001 words to 51000 words out of 63481 words

Chapter 17 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt

23 Nov 2024

6684

na fansa ta, macace ni fa a gidan mijina kuka je har gabansa kuka sato ni, don Allah ku buɗe mini wallahi wari zai kashe ni babu iska a ɗakin ku tausaya mini" abin da take faɗa tana dukan ƙofar da hannu, amma ko tari ba ta ji sun yi ba, kuma tana da tabbacin suna jinta ta sake ɗaga murya ta ce


"For the sake of Allah, da girman iyayenku ku mayar dani gida gaban iyayena me na yi da za a yi garkuwa dani,ku barni da raina kar ku kashe ni zan muku kwatancen gidanmu ku je wajan daddyna a baku dukkan kuɗin da kuke buƙata, idan ba ku yarda ba ku a cikin kuɗina zan baku wallahi mahaifina ya ji abin da ya same ni mutuwa zai yi, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un me na yi muku ne kukai garkuwa dani na shiga uku ni Safiyyerh Allah ka kawo mini ɗauki" ta sake durƙushewa a bakin ƙofar ta tura kanta cikin cinyoyinta saboda warin sholi daya gama hautsina mata ciki kamar kayan cikinta zai fito haka Safiyyerh ke ji, duk girman idanunta sai da ya yi mitsi-mitsi abin ka da zabiya da ƙyar take buɗe idanun nan, ba sunan wanda bata kira ba hadda Anty Turai akan su kawo mata ɗauki Yaya J ya sha kira. Ta sauke ajjiyar zuciya tana karanta addu'ar neman tsari da kuɓuta daga magauta ta yi zumbur ta miƙe saboda fitsarin dake mintsinin mararta.


A can wajan ɗakin a cikin gidan da su Goje basu san da shi ba, duk suna zaune suna busa kayan shaye-shayensu hayaƙi ya cika wajan, wani na shan sigari wani na shan sholi wani wiwi sun hautsina sai surutai suke yi. Moh na gefe ɗaya ƙwance ƙafarsa ya ɗora akan ɗaya idan yana acting ka ɗauka jinin sarauta ne ko wanda yake da aljanu sarakai a kansa, duk ihun da Fiyya take yi da surutai yana jinta. Goje ya kalle shi ya ce "Wannan yarinyar tafa dame mu wallahi, ka kira ka faɗa masa tunjiya mun ɗakko ta ya san abin yi"


Shiru ya yi yana sake kaɗa ƙafarsa a hankali har lokacin idanunsa a rufe yake. Goje ya kalli ƙofar ɗakin da Fiyya ke ciki ya sake kallon Moh kafin ya miƙe tsaye ya ce "Ina da matsala da jin kuka gaskiya, ko dai a rufe mata bakin ko a ɓara bakin biyu yanzu da askira"


"Mangal"
Da sauri Mangal ya kalli Moh jin ya kira shi domin tunjiya da suka ɗakko Fiyya ko tari bai sake yi ba, bai runtsa ba har gari ya hawaye ba wanda kuma ya kula a cikin su. "Ankar sarki, faɗa taka cikawa tamu akwai wani sagi a ƙasa ne?"


"Bana son hayaƙin nan" lokaci guda suka kalle shi a take suka cillar da sigarin tare da saka ƙafa suka murje "Angama sai mene na gaba?" Bai magana ba ya juya musu baya a hankali ya buɗe idanunsa ya zaro takardar da yake faman ajjiya kamar rai, kusan kullum yana karantawa sama da sau wajan biyar a rana abu ɗaya ne amma sai ya ji baya fahimta,baya kuma ganewa, ya zubawa rubutun idanu Goje shima ya leƙo kai yana kallo ganin ya ninke ya ɓoye ya saka ya yi siririn tsaki "Na ji takaicin rashin makarantar da ban, shi ilimi ko yaya yana da rana"


"Ina zargin wannan takardar bata tsafi bace, kamar ita ce ransa ko iskar dake shaƙa ya manta da komai amma banda ita, watarana sai na sace ta yasin" dariya Goje kawai ya yi ya san Mangal faɗa kawai yake yi. "Mai dawa kasan a yankinmu an sace mutane har biyu, yau da sakaliya anga gawar ɗaya ba idanu" ya juyo a hankali ya zubawa Goje idanu kamar mai tunani sai kawai ya miƙe yana taku ɗaiɗai ya fice daga cikin gidan, suka bisa da idanu ganin yau ya zama wani so silence kamar ba Moh ba.


Safiyyerh ta ji an turo ƙofar da sauri ta miƙe tsaye tare da ja baya, mutum biyu take gani Goje da Mangal shi kuwa tunda ya cillar da ita a ɗakin bata ƙara ganin shi ba. Abincin hannunsa ya cilla mata da ledar ruwa pure water ta kalli takeaway ɗin da ruwan, ta ɗauke kai a hankali tana sake ja baya "Saura ki ƙi ci kamar na ɗazo, idan kuma kika sake yi mana amai a nan sai kin lashe abin ki tas" ta ƙurawa wajan ido ta ce "Ba zan iya cin abinci a nan ba, ni bana shan ruwan leda abincin ma ba irin wannan nake so ba, ko nama babu akai"


"Kuma a ina kike tunanin ganin nama? Don ma kin samu an kawo miki dar yarinya saboda kina Manager kun saba cin mai kyau a sha mai kyau, a saka suttura a shiga mota a kwana cikin a.c ga naru a gida 24/7, a ci shinkafa basmati da ruwan gora dole ki ce haka, ɗiyar ƙaruna"


Girgiza masa kai ta yi muryarta na rawa ta ce "Da gaske nake maka, ni kawai a bani ruwan jakar da lemo ko snacks" Goje ya dinga kallon ta ganin she is serious juyawa ya yi zai bar wajan ta yi saurin cewa "Don Allah ku bani waya na kira daddy na maka alƙawarin yanzu za a kawo kuɗin da kuke buƙata wajan nan akwai sauro headache da fever zai kamani" ta langwaɓar da kai gefe alamar neman alfama.


"Ki jira Mai dawa ya zo, sai ki tambaya bani da ikon haka. Da kike maganar kuɗi kin ji mun ce muna buƙata ne? Ba kidnapped ɗin ki mukai domin a bamu kuɗin fansa ba, mun sato ki saboda a koyawa asawa hankali a rage masa tsayin harshensa da yake da kauɗi kin gane? Daga yanzu ki cire rai da samun ƴanci"


"Daddy?"


Safiyyerh ta faɗa a gigice tana dafe kan ta idanunta ya cika da hawaye, tausayin kanta dana daddy ya cika mata zuciya babu wani wanda take so a duniya sama da daddy da Ummi me za su yi masa rayuwarta suke son kassarawa tabbas idan suka taɓa kimar mahaifinta. "Me daddy ya yi muki, mene alaƙae sato ni da kukai da mahaifina me kuke nema a wajansa na roƙe ka da girman Allah kar ku cutar da mahaifinsa kar ku illata rayuwarsa, shi ne jin daɗi da farincikin zuciyata, ku duka kuna da iyaye na tabbata ba za ku so rasa su a rayuwarku ba ka ji tausayina Please brother"


"Ni ba brother naki bane ni ɗan daba ne sunana Goje kin gane, idan kina buƙatar wani abu kina iya bubbuga ƙofar" kafin Safiyyerh ta yi magana ya yi sauri rufo ƙofar ya fita. Ya je ya samu Moh a wajen gidan zaune ya sake tanƙwashe ƙafafuwansa ya kalle shi sosai kana ya ce


"Scorpion"


"Kana son faɗar sunan, zan manna maka hauka Goje zan ja maka ruwa". "Me ya sa baka son na dinga faɗa ne? Ai dafinka ma ya fi na kunama ni ina son sunan" Moh ya yi shiru yana sake harɗe hannayensa duka biyun ya zubawa samaniyya idanu. "Idan zan nuna maka asalin kalata a Scorpion ba zaka ɗauka ba, za ka daina haɗa idanuwa dani sauƙin sunan na wajan faɗa ne, ka kalle ni a Moh ko Mai dawa ok"


"Yadda ka ce haka za a yi, ya zamu yi da yarinyar nan yanzu? Kwananta ɗaya da wuni fa, kuma bata cin abinci"
Cikin rashin fahimta Moh ke kallon Goje su yake ya tambaye shi wacce yarinyar bakinsa kuma ya yi masa nauyi ya dinga juya idanunsa akan fuskar Goje, fahimtar hakan ya saka shima Goje cewa


"Manager wacce Ali wali ya saka mu ɗakko yarinyar da muka je gidansu jiya" haɗe fuska sosai Mai dawa ya yi idanunsa ya shige ciki haka kawai ɓacin ransa ya sake ninkuwa ya yi shiru ya datse laɓɓansa kamar zai raba su gida biyu ya yunƙura zai tashi Goje ya ce "Wannan sauyin na yanzu na mene? Na fara jin daɗi a raina kwana biyu baka sha ƙwaya ba, lafiya dai?"


"Mutallab" still ya yi shiru Goje ya sake kiran sunansa yana leƙa fuskarsa ganin babu alamar zai kula shi kawai ya miƙe ya fice ya bar wajan.


***Gabaɗaya suna zaune a cikin parlon banda shi dake tsaye, zuwan nasan ake jira amma tunda ya shigo bai kalli kowa ba balle ya yi magana, fuskar nan a murtuke kamar kodayaushe. Yaya J, Awais Dr Hash, Anty Turai Waheeda sai Ummi dake zan gefe bata cewa komai sai goge hawayen da yaƙi tsaya mata take yi. Daddy baya uhm baya uhm'uhm kansa a ƙasa zuciyarsa ta bugawa da ƙarfi yama kasa yarda da abin da ake faɗa har lokacin gani yake wasa ake yi masa da hankali da kuma wahalar da zuciyarsa da ake saboda anga yana ƙaunar Safiyyerh ƙauna mai tarin yawa an fahimci ita ce rauninsa.


"Captain Aliyu Abdu Marafa shiru ba naka bane, ba muzo nan da a shiru ba a matsalar kidnapping ba a yi mana wasa" cewar Sp Ghali daya ƙara amsar case ɗin Safiyyerh a karo na biyu ya ɗaga kai ya kalli masu gadin asalin gidan da kuma na part ɗin su Captain sai kuma ya ce "Heyy you man, mene sunanka da aikin da kake yi?" Cikin rawar murya ya ce "Sunana Isma'il ni mai gadi ne Yallaɓai"


"Isma'il sanda abin ya faru ƙarfe nawa ne? A daidai lokacin kana ina kuma?" "Ban san ƙarfe nawa bane a lokacin don ban duba a gogo ba, sanda abin ya faru kuma ina bakin gate ne amma kafin nan na miƙe na shiga banɗaki kama ruwa wallahi gaskiya nake faɗa maka Yallaɓai"


"To na ƙaryata ka ne? Kenan Isma'il bashi da sani akan waɗanda suka shigo gidan ko? Da ɗauke Safiyyerh?". "Duk abin da na ce maka na yi ƙarya abu ɗaya na sani fitowar su ɗauke da ita, hannunsu riƙe da makamai ɗaya ya ce na buɗe ko ya ɓola mini ciki na ji tsoro haƙiƙa sai na buɗe ashe sun yi parking mota wata ɓaka mai kyau daga can gefe"


Murmushi kawai Sp Ghali ya yi yana duban ɗaya ma'aikacin ya ce "Kai kuma fa? Mene information?" Shi wannan jikinsa har ɓari yake don tsoro ya ce "Yadda na gansu Allah Ya sa naga Annabin Rahama, misalin biyu da arba'in ne ina zaune na ji ana dirowa ta katanga kafin na yi magana ɗaya ya make ni yana nuna yatsarsa a baki alamun na yi shiru, ni kuwa na yi shirun don wallahi a lokacin na ɗauka mai gida shi sojan kenan daman shi ke kai wa dare a waje saboda yanayin aikin nasa, suka ɗaure ni ina hango sanda suka nufi part ɗin tunda can babu masu gadi daga nan ban san mene ya faru ciki ba sai gani mukai sun fito da ita a kafaɗa kamar ma a sume take yadda ta langwaɓar da kai"


Daddy da Captain suka runtse idanunsu lokaci ɗaya, kowanne tunanin da yake daban a ransa, is he a loser? Captain ke tambayar kansa or he is falled as a husband maybe da yana kwana ɗaki ɗaya da Safii da hakan bai faru ba, idanunsa ya ƙara sauya kala. Daddy ma nasa tunanin dabanne, ko dai ya yi gaggawa ne ba yanzu ya dace ba? Ko mistake ya yi daya aurawa Aliyu Safiyyernsa ne? Is he a loser? Daya kasa tsare rayuwar yarinyarsa mace ɗaya tilo a duniya ko dai da gaske he is falled as a father?


Kafin kowa ya yi magana ta shigo cikin gidan a gigice duk da nutsuwar da take da ita, da sauri kuma Daddy ya miƙe tsaye cike da tsoro da mamaki hatta Captain sai da ya ji wani abu mai kama da faɗuwar gaba, who told her? Tun kafin ta yi magana daddy ya yi saurin matsawa kusa da ita ganin yadda take ta zare idanu fararen idanunta fuskar nan nata ya ɗakko rana kamar ta yage don fari "Zahiyerh"


Girgizawa daddy kai ta yi a daburce ta ce "Ina Maama?" Ya yi shiru yana ƙoƙarin riƙe hannunta ta ƙwace ta yi baya da ƙarfi kuma ta ce


"Ina Maama? Ka bani ita na tafi da ita where is Safiyyerh"


"Safiyyerh has been kidnapped"


"Kidnapped?" Ta maimaita tana juyawa ta kalli Sp Ghali anya ya san wacece ita da yake furta mata maganar anyi garkuwa da Safiyyerh kai tsaye bai tauna harshe ko ya lissafa maganar ba, Safiyyerh fa? Sp Ghali zai yi magana daddy ya girgiza masa kai yana sake kallon Zahiyerh wacce zuciyarsa ke buɗewa a duk sanda ya kalle ta. "Ummimi please ki kwantar da hankali ki samu nutsuwa tafiyar nesa kikai jirgi kika hau"


"To na ji, ka faɗa mini meke faruwa da Safiyyerh?" Daddy ya sauke numfashi a hankali kuma ya nuna Sp Ghali ya ce "As he said, he told you already Safiyyerh has been kidnapped"


"Uhm"


"Komai zai daidaita Ummimi" ita dai bata sake magana ba can ta ɗaga kai ta kalli Aliyu da sauri ya zame idanunsa ƙasa ta harɗe hannayenta a ƙirji ta tsaya jikin hawa steps ɗin bene. "Afuwa Sp muje ko?"


"Next question ɗin mu akan Captain ne"


"Ok ka yi mana" in ji Anty Turai.


"Aliyu kafa yi haƙuri kalar aikin ku na sojoji daban, namu daban kowa da nasa iyawa da ƙwarewar a nasa ɓangaren ok. Aliyu kai ne zaka faɗa mana abin da ya faru a cikin gidan su waye suka sace maka mata har cikin gidanka a matsayinka na soja wanda kodayaushe zaka iya samun ƙarin matsayi na aiki, ya akai haka ta faru? Su waye?"


"Ban sani ba"


Kai tsaye Captain ya bada amsa "Baka sani ba? Har kuma suka ji maka ciwo kada ka saka na fara zarginka na yi tunanin sace Safiyyerh set up ne kuma ne ka yi plans ɗin hakan, ka sace matarka?"


Aliyu ya dinga kallon Sp Ghali a hankali kuma ya ce "E". "kana nufin ka sace matarka Safiyyerh?"


"E" ya sake cewa
"Aliyu!!" Daddy ya kira Aliyu da ƙarfi ya miƙe ya ce "Da gaske ka sace Safiyyerh?" Kamar idanun Captain za su faɗo ƙasa saboda yadda suka fito waje sai kawai ya lumshe ido ya buɗe ya ce "E, na sace ta daddy" yana cewa ya fita daga parlon yana banko ƙofar da ƙarfi kamar ya cire ta. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Muryar Ummi ta karaɗe parlon ƴan mazan dai sukai shiru.


"Karya yake yi" Ummimi ta ce har yanzu taƙi zama lokaci zuwa lokaci kuma tana duba wayarta kawai sai tabi bayan Aliyu. Daddy har jiri yake gani baya so a fitar da maganar ya fiso a yi komai secretly har Safiyyerh ta dawo gare su amma sai yaushe ne?. Only God knows.


****Ammo na zaune ta yi shiru a ɗakinta kamar kodayaushe ta yi nisa a tunaninta bata ma san Malam ya shigo ba sai muryar Inna Binta da ta ji a sama wajan ƙofar ɗakin tana faɗin "Yanzu don Allah Ammo da rana ma ba za ki daina kwantar miji kina satar kwana ba, wacce irin jaraba da masifa ce haka ni Bintalo jaraba kala-kala Malam ɗin duk da basir ya cinye shi da rana ma ba za a bar mana miji mu dinga ganinsa duk da ba wata tsiyar yake yi mana ba" Ammo ta cira kai ta kalli Inna Binta ta juya ta kalli gefe har yanzu ba taga Malam ba cikin rashin fahimta ta ce


"Kamarya?"


"Ohho shafa ki ji mace an girma amma sai shegen munafurci da kissa wato kafin ki gama sallama ɗan naki wa duniya kafin ya gama zama ɗan ta'adda ya miki aikin mallake malam ko? Shi ya sa kaf gidan nan kin fi kowa yawan yara" Ammo ta kasa cewa komai da ƙyar ta buɗe baki ta ce


"To ina Malam ɗin yake yaushe ya shigo mini?" Ta banka mata harara ta nuna mata malam dake zaune ya yi shiru a hankali ta furta "Ikon Allah ki yi haƙuri ban san ya shigo ba" Malam ya yi gyaran murya ko kallon Inna Binta bai yi ba cikin damuwa ya ce "Ammo ki nutsu ki ji me zan ce miki babu tabbacin abin dai har yanzu, ki yi haƙuri idan har hakan ya kasance gaskiya"


Jin haka ya saka Inna Binta neman waje ta zauna a bakin dakalin ɗakin Ammo ita dai wacce ake maganar domin ta shiru ta yi tana bin Malam da kallo gabanta na faɗuwa ba wai yanzu ta saba da faɗuwar gaba ba, ta ji wannan ta musamman ce. "Gawa aka tsinta....," "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na Ammo?" Malam ya ƙura mata idanu bai taɓa zaton tunanin wancan gantalallan yaron mara amfani a duniya zai zo ranta bq, ya girgiza kai kana ya yi shiru caraf Inna Binta ta ce "Idan shine ai gwara ka faɗa ko kuwa? Kai aka cire masa ko wuƙa ce harsashi ne ko rayata ko babbake shi aka yi kasan haka ake yi wa ƴan daba, wallahi wani da aka rutsa shi ƴan unguwar jahilin duka sukai masa, ashe shima dai irin tsinannen yaron naka ne wuƙa bata huda shi, suka dinga rutsa masa dutse aka ina sai da kan ya ya yi dugu-dugu a nan cikin gari akai abin, da iyayen nasa suka je wajan ƴan sanda cewa sukai su yi haƙuri gawar ba zata ɗakko ba ta yi muni yaron nan dai da yake bashi da rabon rahama ko sallah ba a yi masa ba, yana can za a yi gwaje-gwaje da gawar ƴan makaranta daman ƙarshen duk wani ɗan daba kenan"


Malam ya yi shiru bai yi zaton haka Inna Binta take ba, Ammo rasa kalmar da za ta yi amfani da ita ta yi wajan yi wa Inna Binta, ta yi shiru tana sunkuyar da kai.
"Malam ka faɗa mata kawai sai ta ɗauki don gana"


"Wallahi tallahi ko"


Mama ta yi caraf ta faɗa ashe itama tana laɓe a jikin taga daga waje. Ya girgiza kai kawai cike da takaici kana ya ce "Gawa aka tsinta ta mace an cire mata idanu biyu kuma an cillar da ita bakin hanya, aka kira ana tunanin kamar gawar" haka kawai ya ji yana jin tsoron kalmar da abin da zai biyo baya Ammo ta ƙura masa idanu a sanyaye ta ce "Sa'adah ce ko Bafullatana ko Hameeda?"


"Hameeda"


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Astagafirulla Allah mun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login