Showing 27001 words to 30000 words out of 63481 words
Chapter 10 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt
ba, akwai hakƙin iyaye akan yara haka akwai hakƙin yara akan iyaye shin kina buƙatar Ubangiji ya tuhume ki da hakƙin Mutallab? Allah da kan shi cikin hadisi mai girma ya ce; ƴaƴanku amana ce kuma kiwo ne a gare ku, lallai za mu tambaye ku wannan amanar da kiwon idan an ce ki faɗi inda yake a yanzu ba za ki faɗa ba wannan abun da kuke kun bashi dama da lasisin ƙara lalacewa ne idan yaro ya ɗaƙko hanyar kangara jawo shi aje jiki a nuna masa ƙauna da soyayya"
Miƙewa ta yi tsaye tana share idanunta "ya zo mini jikinsa duk sara kamar korarre mara iyaye a duniyar nan har na yi na gama magana bai tanka wani kuskuren iyaye ke haddasa shi"
Tana kaiwa nan ta fice abin ta inda ta shige Inna Binta da Mama Zaituna na kokawa akan wani ƙanzon tuwon da aka baza ya bushe sai ya yi gwanin sha'awa tana ɓantara da kaiwa baki ta ce "eh, kya yi kya gama wannan ƙanzon sai na bawa Mufee ke ni fa akan abinci ba wani kirki gare ni ba, ba zan zauna yunwa ta yi ajalina a gidan nan ba, tunda mai gidan zuciyarsa a mace take bai san fus na hakƙin iyali ba sai auri saki da tare yara kamar ƴaƴan ɓeraye kowanne kana kallonsa yunwa zata fara maka sallama a jikinsa haba me ake da hali na..." Da sauri ta yi shiru ganin malam tsaye ta yi mamaki da bai tanka mata ba ya shige.
Safiyyerh ta sakko daga saman bene tana yi tana duba wayarta ganin saƙon da Ashraf ya tura mata cewa ya ɗan yi tafiya ba ta yi reply ba ta riƙe wayar. Yaya J ta gani zaune ta juya masa manyan idanunta da suka sake fitowa farare tas ta ce
"Office ɗin kenan?"
"Ina ni ina zuwa office banga yadda little sis ta farka daddy's favourite" ta girgiza kai tana ɗan murmushi iya leɓe ta ce "Yaya J kenan, good morning"
"Kin tashi lafiya sai ina?"
"Office, ina da meeting kuma Yaya J ka yi mini addu'a Please da wannan kyakkyawan harshen naka, zan baka labari mai daɗi" ya ware hannunsa ya ce
"To ina jira ko na kai ki office ɗin?" Ta girgiza kai ta juya tana nufar sashin daddy dake ƙasa. Fiyya tuni ta manta abin da ya faru ta manta wani Mutallab fresh take jin kan ta, tana ƴar waƙarta ta turanci tama manta ta shigo parlon daddy dake zaune ya zuba mata idanu ta yi saurin rufe ba ki ta ce
"Ka yi haƙuri daddy i enjoying when i sing a song, don Allah ka yafe wa Maama"
"Sai an yi magana idan kin yi laifi kina buɗe manyan idanunki kinawa jama'a turancin yaran zamani ke ba kowa naki da yake bature"
"To babana babban laccara ne wanda ake alfahari da shi dukkan matasa ke son shi saboda ƙoƙari da iyawar shi" Fiyya ta ce tana zaman ƙasan ƙafafun daddy "Tiger" sak ta yi jin sunan da ya kira ta da shi, lallai an taɓa donganta ta sa wannan sunan na Tiger ta share kana ta gai da daddy.
Ya amsa cikin kulawa duk motsin da take akan idanunsa Fiyya na da mugun wayo dana da wani experience da Qualities bata yin abun da za a iya following footsteps ɗin ta, she is a clever girl faɗanta har tsoro yake bashi ga taurin kai da miskilanci har addu'a yake Allah ya sassauta mata sai gashi Ubangiji ya gyara komai a lokacin da bai zato ba. Ya ɗauke kai yana kallon wani gefen
"Aliyu yaushe ka dawo?" Idanunsa a kan waya yana dannawa, wandon uniform na sojoji ne jikinsa sai fara t.shirt tas wacce ta kama damtsen hannunsa ya saka p.cap ta sojoji fuskarsa kamar ya ce ya shiga uku can ya ce
"Da daddare"
"Dare da yaushe? Aliyu kai kana son shigowar dare kamar mara gaskiya?" Captain ya ɗan kalli daddy ya ce "Tun 12"
"Kuma baka shigo ba me ya sa?"
"Kawai daddy" ficewa ya yi yana cilla wayar a aljihu yana jin Fiyya na gaishe shi ko inda take bai kalla ba. "daddy ni ba zan iya ɗaukan wannan halin ba wallahi bai ishe ni kallo ba zan daina ko gaishe shi ina dalili, Safiyyerh Abdu Marafa na da class babu mai ɗaga mini shoulder, duk wannan abun da ya yi aure a waje ne yake soja" Ranta duk a ɓace ta miƙe tana cewa daddy ta tafi ya ce "Allah Ya tsare Manager ya shirya safiyyerh Abdu Marafa". Kasancewar sauri take yi ta saka ta yi driving kamar zata tashi saman bata wasa idan tana kan titi, tana isa ta buɗe office ta shiga fahimtar da sabuwar envelope a table ɗin ya saka ta sa hannu ta ɗauka tare da buɗewa taƙaitaccen rubutu ne mai ɗauke da jan biro wanda ke nuna rayuwarta na cikin matsala. A hankali ta fara duba consent ɗin da takardar ke ɗauke da shi tana ajjiye waya.
“Jarumtarki bai kai ki tsaya bincike akan FS WORLD INVESTMENT COMPANY ba, kina iya ɗaukan rubutun matsayin wasa amma gargaɗi ne da jan kunne ga yara masu rawar kai irin ki. Ki tsaya da binciken da kike you're nothing but a manager”
Ta dinga juya takardar a hannu tana jin confidence nata na ƙara hakan kamar wata dama ce aka haska mata na nuna cewa lallai akwai ƙullalliyya a wannan kamfanin, kuma ta shirya buɗe faifai ko da za su yi zubaibai ƙwarya ne, ko da gaskiyar da take ƙoƙarin bayyanawa zai yi silar barin ta numfashinta daga ƙirjinta. Ta yi Addison na cikin abubuwan da take ƙarawa a binciken za ta yi komai ko hakan na nufin fito na fito da surukinta ne. Zama ta yi ta fara duba files na sabbin kayan da aka kawo can ta saka aka kira mata accouter bayan ya shigo ba tare data kalle shi ba ta ce
"Accouter kana buƙatar wani abu ne?"
"Allah Ya taimaki manager kamarya fa?" Still bata kalle shi ba ta yi baya tana duba maganar da aka turo mata yanzu a waya ta ce "kawai kuɗi idan kana so na buƙatun rayuwa"
"Ina jiran lokacin albashi ya yi ai nasan za a sallame mu da wuri" ta ɗago idanunta masu sanyi ta zuba a kan shi sai ta cillo masa ƙaramin file ta ce "na saka hannu ka yi signature as a accouter ka cire 1m a asusun kamfani na baka" da mamaki ya ce
"Ni kika bawa kuɗin?"
"E, ko baka so?"
"To na ga ban yi wani aikin da na cancanci 1m ba kin sa na fara jin tsoro ba zan iya cin abin da ba haƙƙina ba" ta ɗan yi murmushi ta janyo files ɗin ta yaga ta ce "meye cikakken sunanka ma?" Rainin hankalin Manager mamaki yake bashi sai kawai ya ce Wazeer" da hannu ta ce ya je yana fita ta saka aka kira mata MD abin da ta yi wa Accouter shi ta yi wa Md cikin sauri ya ce
"Yanzu kika ɗakko hanya manager da za ki haƙa ramin da za ki iya binne kan ki ciki ai duk sai na raina wayonki wallahi da ajin nan naki ko mene a ƙasa ba ruwanki mind your own business rayuwar nan kana kallon wasu abubuwan kake yi kamar baka sani ba, to a haka cibiya ta rai ne mu kuma yanzu hankalin jama'a da yawa na kan siyasa, matasa na neman hanyar karatu, wasu na can suna bautawa ƴan siyasa, wasu sojan baka wasu rayuwar social media wasu bangar siyasa wasu kasuwanci. Safiyyerh da yawa ana yin abin da ya samu ne ko yazo hannu ba wanda kake ganin cancnatar shi ba, ba a duba capacity na abu ko a siyasa kana ji kana ganin wanda ya dace amma kake rufe idanu ka ɗauki baragurbi saboda yana watsa maka hatsi mu ɗin kamar ka ji suka ɗauke mu, think big Fiyya ke macace babu mai ce miki don me, akwai kuɗin da shi kan shi Alhaji Baihaƙi bai sani"
"Kana son siyasa"
Md ya yi murmushi ya ce "Safiyyerh siyasa yanzu ai kusan a jinin kowanne matashi take, kinga muna da jam'iyyu uku ɗaya ce mai ƙarfi saboda ita ke riƙe da muƙami ma'ana ƙasar a nan Hon Maɗatai yake neman takarar kujera, sai jam'iyyar su Eng Ali wali sai last jam'iyya wacce mutumin cikin ta ya fi kowanne nagarta kuɗi masu dame shi ba, da ƙyar aka taushi zuciyarsa yake muƙamin kusan matashi ne matasa na son shi amma kasancewar yana cikin jam'iyya ƙarama kusan sabuwa ya sa ba a yin maganar shi ma kuma da ba musulmi bane" Safiyyerh ta jinjina masa kai ta ce "Ka bawa accouter ya yi signature a baka 2m, enjoy yourself MD, but sunan wanda kake bani bayani yanzu?"
Ya washe bakinsa ba ƙaramin jin daɗi ya yi ba ya ce "Abraham Denial David, shine ɗan takarar"
"Yana da hannun jari a nan ne?"
"A'a, i don't think zai saka hannun jari a nan gaskiya" a hankali ta ce "Me ya sa?"
"Kar ki zurfafa a bar maganar, za mu yi aiki tare" sallamar shi ta yi tana jin zata yi amfani da Md da accouter Md zai taimaka wajan sanyawa ta san sirrin kamfanin cikin sauƙi accouter zai taimaka wajan bayyana komai. A gefe guda tana jin kamar ta shiga batun siyasar Abraham ɗin kawai ta ji ya yi mata she just want to help him.
****
Su da kan su sun kwana biyu basu saka shi a idanunsu ba, ba kuma su samu labarin inda yake ba sai yanzu da suka ganshi kamar walƙiya kwance a ƙasa idanunsa buɗe yana kallon sama Darma ya ce "Sai godiya wanda ya ce zai bi sawunka ya wahala, ɗan malam yaƙi halin malam dafinka ƙarinka masifa ne idan ka taɓa mutum da shi"
"Darma"
"Ka dake Mai dawa ka jima ka yi lastin irin na dabino, wa kake so a taka a kashe ko a yi masa fiɗa" Darma ya ce yana buɗe hannu sama tare da karkatar da baki hannunsa riƙe da ledar pure water ya nannaɗe a hannu yana kaiwa baki tare da zuƙa. Mutallab ya sake buɗe idanu a sama ya kasa cewa komai tunaninsa ya tafi wani wajan. Goje ya ce "Sai godiya matsalar goge ce ko wato ka kayan lantarki"
"Zaman gidan yari ba daɗi,amma na ji daɗi"
"Ka ce ka tuna na jakuna nan cinnaku tsakaninmu da su sai ƙarfe ba ma'ana ka tuna na jakin da suka haɗa maka kenan"
"Ina jin zafi a ƙirjina farcuna na da suka cire mini sun ƙi fitowa, zan ɗauki fansa Goje"
Kafin su yi magana an yi sallama an ƙarasu cikin sauri Mutallab ya rufe idanunsa jin muryar zabuwa. Goje ya dinga kallon wacce take tsaye "Bayin Allah sallama nake muku fa" Mangal ne ya kalleta sosai ya ce "Yi batu" ta ɗan rausayar da kai gefe ta ce "Amma dai ku musulmai ne amsa sallama wajibi ce"
"To alaiki, mene sagin aiki kike so a yi miki?"
Kinal ta fito da littafi da biro ta ce "Sunana Kinal ni mawaƙiya ce, har zan shige na hango ku na ji ina son tambayarku na ji ina son na yi waƙa akan ku kasan mu da mu da marubuta kusan aikin mu ɗaya muna da son bin ƙwaƙƙwafi" Goje ya ce "To ina ruwan mu? Fece kafin na yi miki lahani"
"Ku ba ƴan shaye-shaye bane? To akan shaye-shayen zan muku tambaya ina yin waƙar zan kawo muku ku ji, idan kun yi shaye-shayen me kuke ji mene dalilin daya saka kuka fara shaye-shaye kuma kuke harkar daba"
Moh na jin su ya juya musu baya zaka ɗauka bacci yake, ransa duk a ɓace saboda jin muryar mace da ya ji ya san daya juyo zai iya kashe ta tsaf don bashi da wani business da mata. Darma ya ce
"Yanzu yadda muke ji za mu faɗa miki kenan?" Kinal ta yi saurin cewa "E, wallahi na iya waƙa ina da murya sosai babu mamaki idan na yi waƙar na saka a YouTube ta je viral na saka a tiktok ta yi trending" Darma ya ce "To ni dai tun daga sanda a gida na yi...,"Da sauri Goje ya tsayar da shi yana cewa "Kai amma ɗan tsinanniya ne kai, ba haka ake bayani ba"
Miƙewa ya yi ya ce "bari na faɗa miki" wuƙa ya zaro a ƙugunsa Kinal ta zare idanu tana yin baya cikin sauri Mangal ya tare bayan jikinta na rawa ta fasa ihu jin yadda Goje ya yanke ta da wuƙa a fuska,ya danna mata ledan wiwin a baki ta fara zare ido tana ihu. Sai a lokacin Moh ya juyo yana kallon yarinyar ya cije bakinsa tare da juyawa exactly irin ihun da Safiyya ta yi lokacin zata mutu.
"Gani ya kore ji, idan kin rero waƙar muna dakon ki a nan sata ƴar munafuka"
Darma ya dinga tuntsira dariya sosai yana riƙe ciki "Amma Goje baka da imani kamar fa fitsari ta yi a wando gaskiyar kurciyar nan akwai jan ido ga bayani nan kin gani ganin idanunki ai" ya juya ya kalli Moh ya leƙa ga wata cukurkuɗaɗdiyya takarda yake karantawa shi ba wani karatu ya yi ba "Wai wannan takardar mece kamar ta asiri kodayaushe tana wajanka, kamar numfashin shaƙa ka faɗa mana ta mece" cikin sauri ya ɓoye yana damƙe ta a hannu Goje ya ce
"Nima sai fakon farar nake na mata karatun makarantar allo, na rasa wacce tsiyar ce a ciki"
"Goje"
"Sai godiya"
"Zan saka maka tsini idan ka taɓa takardar nan ko na saka su tiger cinye ka ɗanye, wallahi zan iya kashe ka akan takardar nan"
Kafin su yi magana an zo da babur an cillo wata takarda da sauri mai babur ɗin ya juya, Mangal ya miƙe tsaye ya ɗakko ya buɗe cikin sauri ya kalli Mai dawa dai kuma ya miƙa masa amsa ya yi ya duba, photo na gudu biyu ne ɗaya zanen fuskar wata kamar dai mahaukaciya sai kuma photo jira-jirai, photo me mai magana ga wanda yake da cikakken lissafi a gefe an rubuta FS WORLD INVESTMENT COMPANY.
****
Kwana biyu Safiyyerh ta yi busy duk wani family sun zo saboda gobe ne ake ɗaura auren, kamar auren munafurci ba wata gayya ko shagali ɗaurin aure ne kawai ana yi kuma Ashraf zai ɗauki matarsa su tafi. A daren ranar Safiyyerh ta riga data gama accepting auren Ashraf ta yarda bata da wani miji sai shi zata sawa zuciyarta yadda zata zauna da shi tunda tana son shi ko ba can ba. Waya suka yi da Ashraf ya dinga tsokanarta "Har na hango idanun Maama a ɗakin miji, mijin na kuma Ashraf ta yi nasarar samun kyakkyawan saurayi" ta murguɗa masa baki ta ce "Zan fasa" ya yi saurin cewa "Idan ki kaga ba ki auri Ashraf to mutuwa na yi ko ke kika mutu, da gaske Fiyya ina son ki Allah shine shaida duk da ina dalilin auren ki ko saka ni akai na yi hakan amma na yi you're my life partner har janna in sha Allah"
"Kamarya? Mene dalilin auren?"
"Ke ba ki da wani favourite words ne sai kamarya, zan faɗa miki komai a daren ranar da kika zama halaliyyar Ashraf zan faɗa miki, zan sauƙaƙa miki binciken da kike akan Company" a ruɗe ta ce "Ta ya ya kasan ina bincike akan Company"
"Safiyyerh kenan, that's is the difference between man and woman, ina da baƙi sai goben idan na zo ganin matata a wannan lokacin dole na rungume ki halal runguma zan miki Safiyyerh" hankalinta duk a tashe waye Ashraf ne me ya sa daddy ya amince da auren shi? Ta kasa magana har ya kashe kiran sai ya ƙara kiranta video call ƙura mata idanu ya yi taga yana shiri cikin sauri ta ce "Kuma sai ina?" "Inda kika aike ni" ta buɗe idanu
"Kamarya?"
"I miss you Fiyya shine abin da na manta na ce miki, a nan nake jin motsin ki" ya nuna mata saitin ƙirjinsa, daga nan ya kashe wayar. Daga ƙarshe ta yi zamanta cikin bedroom Awais har bedroom ya shigo ya dinga mata shira "Yaya Aiwas ka ɗan yanke mini farce" "to ban taɓa ganin amarya irin ba tunda nake a duniya" ya jawo ƙafar ya fara yanke mata farce ta rufe idanu.
Washegari da sassafe Fiyya na bacci daddy da kan shi ya tashe ta, ta farka da ƙyar saboda kan ta dake ciwo mamaki ta yi ganin kusan family a ɗakin ya kalleta ya ce "Kin dai yi sallah ko?" Ta ɗaga masa kai "Daddy lafiya?" Ya yi shiru ya ce "Junaid je ku fara yin gaba, Captain an kira shi yanzu daga can headquarter, Ummi ɗakko mini hijabin Maama" Hijab ya karɓa ya saka mata ya riƙe hannunta Anty Turai ta yi gaba tana zabgawa Fiyya harara har harabar gidan suka je, abin mamaki gidan shiru ta rasa meke faruwa a motar daddy suka shiga yana baya riƙe da ita Awais na jan motar da Ummi. Motar Fiyya kuma da ita Captain ya yi using wajan fita saboda shi bai Fiyya ɗaukan tashi ba. Fiyya ta yi shiru kan ta a ƙasa,har suka ƙarasu cikin babban gidan mai tarin jama'a daidai lokacin aka fito da shi daddy na riƙe da hannunta ya ce "Mamana je ki masa addu'a"
"Addu'a? Daddy waye?" Ta furta muryarta na rawa ta juya ta kalli makarar da aka ajjiye gabanta ɗauke da gawa, ya sake riƙe hannunta da kyau ya jata zuwa gaban makarar ya duƙa tare da yin namijin ƙoƙarin buɗewa. Fiyya numfashinta ta ji ya ɗauke lokacin da idanunta ya yi arba da gawar Ashraf dake kwance cikin makara, jira ya fara ɗaukar gangar jikinta da gaske Ashraf ne kwance ba yau aka ce za a ɗaura musu aure ba shine zai mutu anya gawar Ashraf ce numfashinta ya tsaya cak tana daga tsayen suka ji ta yi wani irin ajjiyar zuciya tare da yin baya cikin sauri a tare daddy da J suka tare ta, ta ƙarasa suma a jikinsu.
Bayan sallatar gawar Ashraf da binne shi duk ana zaune ana addu'a daddy ya ce yana neman alfarma don Allah suka ce tame "Kar a tambayan hujja ko dalili a yanzu ina son a ɗaura auren Safiyyerh da