Showing 3001 words to 6000 words out of 63481 words
Chapter 2 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt
bulala a ɗuwawu ta yi saurin dire tukunyar ta ce
"Kan uba wanne mai tsautsayin ne haka?...," shiru ta yi ganin Malam ya ce "Kina sake magana ina ƙara cauɗa muku shasha kawai mara kan gado"
Ya juya wajansu ya ce "Mayu marasa godiyar Ubangiji kawai akan abinci duk maƙota da unguwa sai anjiku" Inna Binta ta ce "Yaushe rabon da muga sisi taka banda masifar tsiya kana bamu za mu yi haka ne?" Kan ta ya yi da bulala ta yi saurin waftar dambun a hannu ta yi ɗaki tana "Ohho dai na ɗiba na mai da mugun miyau"
Haushin karnuka suka ji wanda rabon da su ji shekaru uku kenan gabaɗaya suka juya wani ihu Mama Zaituna ta yi tare da fatali da dambun da ake ta yin masifa akan shi har zaninta na kuncewa zuwa ƙasa ta yi saurin juyawa zata ɗakko ta zame da ɓawan albasa ta faɗi dif a ƙasa Kasancewar ƙatuwa ce sosai ta fasa ƙara da jan ɗuwawu ta shige ɗakinta hankali tashe. Shi kansa Malam sai da zuciyarsa ta motsa saboda tsoro ya dinga kallon karnukan da idanu yadda suke ɗaga jela tare da zaro harshe waje jibga-jibga dasu sai zagaye wanda ya shigo suke yi. Da ƙyar Malam ya ja numfashi ya ce
"Muɗallabi Ɗanmalam nake gani haka? Ya suka sake ka basu kashe ka ba, ni na ɗauka ma tuni ka mutu wallahi, ikon Allah" sosai kansa ke masa ciwo kamar zai rabe ga wani ciwo da jikinsa yake yana jin fatarsa na rawa, ya yi baƙi sosai amma manyan idanunsa na nan kayan jikinsa duk a yage ya zubawa Malam idanu.
"Kai Muɗallabi ba da kai nake magana ba? Yanzu da suka sake ka me suke nufi ka kashe ƴar mutane a banza kenan? Ba zan goyi bayan gaskiya ba dole na je wajan jami'an tsaron yanzu na bi ba'asi"
Cikin sauri Ammo ta fito daga ɗakinta jin sunan wanda aka kira zuciyarta har rawa take tana fitowa suka haɗa idanu dashi ya kafe jikin bango a hankali yaran gidan suka fara fitowa ya dinga bin guntattakin yaran da kallo wasu duk bai san su ba. Ya nufi Ammo ta yi saurin ɗaga masa hannu ta ce. "Ina jin tsoron kiran ka a matsayin ɗana na ji na yi dana sanin haihuwarka wallahi"
Ya buɗe manyan idanunsa sai kawai ya ja ya lumshe yana ƙara yunƙurin zuwa wajanta kenan ya ji ihu a waje kafin ya motsa Goje ya shigo da sauri yana cewa
"Mai dawa ƴan unguwa ne ɗauke da makamai wai za su ɗauki fansar....." Da sauri MOH ya ɗagawa Goje hannu baya son ma a kira sunanta a kusa da shi zuciyarsa buɗewa take sosai. Goje ya sake cewa "Ba ƴan unguwa kaɗai ba har da gajoji da cinnakun layi" kafin Goje ya ƙarasa sun ji ana cewa
"Ba iya Mai dawa ba har Malam da babarsa yau sai sun mutu da duka mutanen gidan sai mun ɗauki fansar yarinyar daka kashe tunda jami'ai sun sake shi a banza" Mutallab ya kalli karnukansa ya musu inkiya Tiger ne ya fara zuwa ƙofar ɗakin Ammo ya tsaya Rainbow ya je ƙofar gidan ya tsaya, Spider kuma ya tsaya yana kewaye Malam. Goje ya ce "Kai ƙarfe baya cinka tsine baya ratsa jikinka su Malam sune matsalar" bai magana ba kai tsaye ya nufi waje gaban Ammo ya faɗi ganin ba makami a hannun Mutallab. Inna Binta ta fito tana zunduma ihu tana jama'a su kawo musu ɗauki tana leƙa ƴar ƙaramar katangar gidan ganin tarin matasan da suke waje ɗauke da makamai ya saka Inna Binta kurma ihu tana faɗin "Ya gafilan zanbi waya kashifal gammi...." Bata gama ba aka raɗa mata gora aka ta faɗo ɗaga saman katangar ta baje wanwar a ƙasa Mufee ta fasa ihu tana yin wajan Inna Binta ganin haka sauran mutanen gidan suka shige ɗaki banda Ammo da Malam.
Moh na fita suka yi masa ƙawanya kasancewar akwai shafi a hannunsa duk wanda ya daka sai ya baje a wajan, suna da yawa sosai cike da rashin sanin cewa tsarin jikinsa ya karye ya shiga tsakiyar su ɗaya ya ɗauki dutse ya buga masa aka nan take ya fashe, wani ya ɗaga wuƙa ya soka masa a ciki nan take wuƙar ta shige Goje ya zaro idanu ganin sun yi nasara ya saka suka zagaye Moh suna kai masa sarawa, baya faɗa da makami bai san kuma ya ake yi ba, kafin wani lokaci sun kai shi kasa ko'ina na jikinsa jini ke fitarwa daidai lokacin tawagar mafarauta suka ƙarasu wajan tare da zugar karnuka faɗan ya koma tsakanin ƴan unguwa da mafarauta cikin mawuyacin hali Moh ya ja jikinsa a hankali jin wani yana waya da ƴan'sanda ji ya yi dama layya zana na wajansa a yanzu haka? Ya dinga tafiya yana jan jiki har ya bar unguwar ya shiga cikin wani waje mai kama da gonaki kuma jeji-jeji. Tana zaune cikin bukkar hannunta riƙe da ƙwaryar nono ta ji an faɗo cikin bukkar a gigice ta miƙe tsaye...
*To ga dai shi nan ban san ya zaku amshe shi ba, amma tabbas zai zama daidai da ra'ayinku musamman iyayenmu mata da maza 😭da suke wasa akan yaransu. MUTALLAB zai zo da sabon salo in sha Allah za a yi kuka sosai kuma za a yi dariya fatana kar ku yi mini zagin da kukai a MIJIN MALAMA 😭ku amshi labarin da hannu bibbiyu ku tayani isar da saƙon zuwa ga manya ta hanyar yin sharing saboda Allah*
08164069385
WhatsApp only
[10/2, 8:40 PM] Nanameera: *❤🔥 MUTALLAB ❤🔥*
Page 2
Nimcyluv
Bright pens..... Second batch
*🔞 Warning... For criminal issues*
Cikin bukkar ya faɗa jikinsa jina-jina da jini sara ta ko'ina da ƙyar yake iya fidda numfashi, ya zube a gabanta idanuwansa a lumshe har yanzu yana jiyu sautin ihu da kukanta, ya kasa ceton ta, ta sake mutuwa, yaushe zata ci-gaba da rayuwa tana sake macewa akan idanuwansa? Ya cije jajayen laɓɓansa wanda jini ya ɓata sam bai damu da yadda yake shanye jinin yana koma masa ciki ba, a matuƙar fisge ya yi maganar mai sautin gurnani ya ce "Na amince, da gaske na amince Abbasa, zan zama mata maza, ki mayar dani jinsin mace ina tunanin zama macen ya yi daidai da tafiyar ƙaddarata! Zan zama mata maza, bana iya kwanaki ba, bana iya wa'adin sa'a ba, ba kuma iya na tafiyar sakwanni ba, ba kuma iya na gilmawar kwanaki ko shuɗewar watanni da nisan shekaru ba, a'a Abbasa, a'a Abbasa ina son zama mata maza ne na daidai da tafiyar agogo da adadin shekarun da zan yi a duniya"
Yadda furucin ke fitar da kan su, da yadda yake magana idanuwansa na fiddowa waje duka jikinsa rawa yake da ɓari yana wani irin tsuma bakinsa har wani hayaƙi yake yi jijiyoyin kansa tamkar zasu ratsa fata bakwai su keto, ganin halin daya shiga ya saka Abbasa cewa. "Iya zubin tunanin naka kenan? Iya jarumtar kenan? Mayar da suffarka zuwa abi mafi nakasu a rayuwarka? Ka zama mace shin ko ka mace da......"
"Abbasa!"
Ya kira sunanta a karo na farko a tsawa ce, domin baya son tuna abinda take ƙoƙarin cewa "Shikenan shikenan, zaka zama jinsi biyu, mai halitti biyu" ya girgiza mata kai yana jin amo da sautin muryarta cikin wutar da suka babbaka ta ciki "Kawai ki nakasta ni" "Tabbas zaka nakasa, zaka zama kamar jaririn da aka haifa yau, zaka zama riƙaƙƙe zaka gagara, ubanka zai alfaharin haihuwarka duk da tsinuwarsa na tattare da kai, zaka sake yi rashi, rashi irin wanda baka taɓa yin irinsa ba, zaka samu dukkan wata shahara da ɗaukaka da kake buƙata, amma zaka dauwama a matsayin mata maza"
Ihu ya fasa yana ƙoƙarin miƙewa tsaye da ya yunƙura gefen cikinsa yake sake buɗewa saboda shafcecen saran da aka yi masa, jikinsa bashi da wani gurbin da babu sara.Abbasa ta miƙe ta ɗakko wani farin abu a hannunta tana zuwa kan shi ta danne shi da duka ƙarfin daya zo mata, ta ɗauki garin abun ta fara shaƙa masa a hanci yana shaƙa da ƙyar da sauri ya damƙi hannunta ya kifa fuskarsa da hancinsa gabaɗaya, yana ihu da gurnani jikinsa na rawa ya fara sambatu, Abbasa ta ce "A me ka zo waje na?"
"Taya" ya bata amsa a raunace idanunsa na lumshewa. "Wasu sun biyo ka ne?" Ya girgiza kai can ya ce "Cinnaku, Cinnaku na fi ƙarfin su" ya dinga juyya kansa can ya ce "Akwai Kimini a tattare dani, ya faɗawa ƙashi wani abu, sun nemi asawa da Tsohuwa....!" Ya kasa cewa komai idanuwansa har yanzu na hango yadda gangar jikinta take ci a wuta.
Ita dai Abbasa ta kasa cewa komai ta zuba masa idanu, ta dinga kallon yadda jikinsa je rawa a hankali kuma ya fara saki idanunsa ƙur a saman bukkar cikin fitar hayyaci da yanayi irin na maye yake sambatu tare da kiran sunayen da ita kanta mata sani ba. A hankali ta ce "Mutallab" bai amsa ba sai zuciyarsa kawai dake rawa ta hango hakan ne a yanayin yadda ƙirjinsa ke ɗagawa. Ganin ya zama kamar matacce tsoro ya kama Abbasa ta tuna ashe bai taɓa shaƙar abin da ta bashi ba a yanzu, maganin ƙarfe dana tauri kawai yake sha gashi kuma zaman da ya yi na shekara uku a hannun jami'an tsaro ya sa tsarin ya karye.
Ƙwarya ta ɗakko ta jiƙon wani magani tare da ruwa mai zafi ta fara danna goge masa jinin jikinsa sai a lokacin ta lura da gabaɗaya farcen yatsun ƙafafuwansa dana hannu babu ga jikinsa duk alamar an jona masa shokin akan tilasta masa amsa laifin da babu wanda yake da masaniyar komai akai, sun yi masa haka ne da nufin ya amsa laifin kashe matarsa da ya yi. Ta sauke numfashi tare da kallon bakinsa a hankali ta kara kunnenta a tausashe yake cewa.
"Ina son ta, ina son ta zuciyata zata fito ita ce wajan ta uku me ya sa.... Ina jinta a ƙasan zuciyata" Tunda suke bai taɓa yi mata zance ɗiya mace ba, haka bai taɓa magana mai tsayin da ya yi a yanzu ba, duk abin da ya saka Mutallab magantuwa ba ƙaramin abu bane ba. Miƙewa ta yi ganin kamar ya samu yin bacci ta fita waje zuciyarta cike da saƙe-saƙe.
Unguwar ta yi shiru saboda zuwan ƴan'sanda wanda da ƙyar suka raba tsakanin mafarauta da jama'ar da suka zo ɗaukar fansan wacce aka kashe zai ya zama kamar an saka kafiyo ne kasancewar babu wanda bai san labarin kisan rashin mutuncin da aka yi wa yarinyar ba. Tiger, spider, rainbow sune suke ta kai kawo a ƙofar gidan Malam saboda basu tsaro kamar yadda Moh ya saba musu ya raine su tamkar mutane hatta mara gaskiya suna ganewa. Da sauri suke tafiya hankali tashe gabaɗaya basa cikin nutsuwa ɗaya sai ɗaga hannu sama take ba'a jin maganarta sai sautin murya. "Ki yi haƙuri"
Sa'adah ta ce tana shafa hannunta a ƙirji alamar ban haƙuri da yaran kuramen da zata gane ta girgiza kai tare da sunkuyawa tana buga ƙasa ta ɗaga yatsa sama alamar rantsuwa. "Allah Ya kyauta, da kin bari mun ƙarasa gani ai ya kori ji Bafullatana" daidai nan suka ƙarasu ƙofar gidan ba kowa a rumfar Almajiran sai allonansu da rubar tadawa da ƴan rubobi na bara. Tiger ya ƙare musu kallo yana shinshina su sai kuma ya ja da baya yana ɗaga ƙafa ya basu hanya suka shige cikin gidan.
Da Inna Binta dake yashe a ƙasa suka fara cin karo jini na zuba a gefen goshinta ɗan tofinta a bankaɗe Allah Ya sa ba yara a wajan cikin hanzari Sa'adah ta nufeta tana girgizata ta juya ta yi wa Bafullatana alama data bata ruwa bata fahimci komai sai kawai ta kinkimo ruwa bokici guda ta kwarawa Inna Binta ajjiyar zuwa ta sauke a firgice ta miƙe zaune tana furta "Dambun Mufee, a kawo ɗauki jama'a dambun Mufee ƴan ta'adda za su kashe ni" ta ƙanƙame hannunta jikinta ya jiƙe jagab amma har yanzu dambun na hannunta ta miƙe ganin Sa'adah da Bafullatana sai kuma ta ja tsaki "Irin bala'i wallahi Ammo ta haifawa unguwar Birget masifa ɗai-ɗai da ɗai-ɗai zai dinga kashe mu yana zuƙe jininmu ku duba wannan yarinyar ma ya kashe ta kari na uku"
Idanun Sa'adah ya cika da hawaye amma ta ɗauke kai ba tare data tanka Inna Binta ba. Inna Binta ta watsawa Bafullatana harara wacce ke ta ihu tana taɓo Sa'adah ta ja tsaki "Kurman banza da wofi gayya masifar, daga haihuwar kurma sai ta ɗan jagaliya" tana kaiwa nan ta shige daƙinta ta samu Mufee tana bacci ta yi maza ta tashe ta, tura mata ɗan guntun dambun ta yi a baki bayan ta cinye ta ce "to sha ruwa kiji abin da kika samu sai kuma gobe, ki yi addu'a ki goge Allah ki gode Muhammadur Rasulullah. Banda ina buɗe ido a gidan nan kema mutuwa za ki yi saboda yunwa kamar taki ƴar'uwar" sai kuma saka dariya sosai "Inna mene?"
"Tukunyar dambu ta kife dan ubanki da tuni ba ki lasa ba kema" Mufee dai ta buɗe manyan idanunta irin na Mutallab tana kallon Inna Binta.
Ammo ta dinga bin Sa'adah da idanu ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita, Bafullatana kuma ta haɗe rai sai girgiza kai take "Ammo don Allah ina Mutallab yake? Da gaske ya dawo an sake shi? Sun wanke shi daga zargin da ake masa, yana ina?" Ammo ta ɗauke idanunta zuwa can gefe tana kallon wani waje daban a ɗakin nata can ta ce "Ki daina kira mini sunansa sallamamman yaron nan a kunnena Sa'adah, ki yi hankali watarana zai iya kashe ki"
"Ba zai taɓa kashe ni ba, duk lalacewar shi jinina ne ɗan'uwana ne a wannan halin da yake ciki na ɗauka za ki yi murna Ammo? Za ki ja yaronki jikinki ki nuna masa kulawa gudun kar ya sake lalacewa, kar ki ce za ki yi abin da kikai a baya duk lalacewar Mutallab kece wacce kika haife shi, tun yana ƙaramin kin san zuciyarsa yadda yake da zafin nama taurin kai. Kin san yadda yake da ƙulafucin uwa kodayaushe yana manne dake, me ya sa za ki yi haka?" Miƙewa Ammo ta yi ta nunawa Sa'adah hanya ta ce "Tashi ki tafi gidan mijinki, banga dalilin zuwanku ba ni bani da wani ɗa Mutallab kuma na sani kuskurena ya saka na haifeshi. Wallahi kika sake yi mini maganar tsinannen yaron nan sai na daina amsa gaisuwar ki har abada" tana kaiwa nan ta fice ta bar musu ɗakin, fuuu Bafullatana ta fice daga ɗakin zuciyarta na yi mata zafi Sa'adah ta yi shiru ita dai tana mugun son ƙannin nata ai da ba haka yake ba, ya kamata su amshi hakan matsayin ƙaddara!
Washegari Malam na zaune a rumfa yana sauraren karatun wani sabon almajirin shi. Ɗanyaro ne zauna gefe kusa da Malam yana lissafa sabbin kuɗin hannunsa ƴan dubu-dubu sai sheƙi yake ya duba yaga dubu biyar cif ya mayar aljihu ya zaro baƙar leda mai cike da gurasa da nama ya ya fara ci yana ajjiye lemo fanta a gefe. Ajjiye bulalar Malam ya yi ya ce "Ɗanyaro ina ka samu kuɗi da nama haka?"
"Bani aka yi Malam" kafin Malam ya sake magana Ɗanyaro ya miƙawa Malam baƙar leda guda mai ɗauke da gurasa a ciki da nama ya haɗa masa da dubu biyu ya ce "A yiwa su Mufee girki Malam"
Jiki na rawa ya amsa yana buɗe bakinsa "Da kyau yaron arziƙi, ina ka samu kuɗi fal haka sana'ar me ka fara?" Ɗanyaro ya girgiza kai kawai can kuma ya kalli Malam ya ce "Bana yin sana'a, kyauta ake bani kullum, bani kaɗai ba har Muhajeed da Iro" Malam ya yi sak tunani fal ransa ya sake kallon Ɗanyaro shekarunsa goma rak a duniya a hankali ya miƙe ya yi cikin gida.
****
A kusan tare manyan motoci biyun suka tunkaro babban gate ɗin ganin ya rigata kai hancin motarsa ya saka ta rage ta fiya, hannunta ɗaya a saman sitiyarin motar ɗayan kuma ta ɗan riƙe fuskarta a hankali ta lumshe idanunta gajiya ce a jikinta sosai da ƙyar take buɗe tuƙa motar don dai bata san wahalar driver ne.
"Fiyya" Ya kira sunanta a hankali cikin muryarsa mai cike da nutsuwa ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi ta kalli wayarta ta manta video call suke yi ma suna haɗa idanu da shi ta ɗauke kan ta gefe tana ya motsa fuska "Fiyya na miki wani laifi ne? Kin sauya"
"I am sorry ina driving we'll make a call later" ya zuba mata idanu cike da so da ƙauna yana jin ina ma a janyo ranar aurensu da Fiyya a ce gobe ne? Ya sauke numfashi zuciyarsa na buɗe a hankali ya ce “I adore you Fiyya" ta buɗe idanu ta kalli cikin idanunsa sai kuma ta murguɗa masa baki ya buɗe idanu sosai sai ya girgiza kai yana dariya ya matso da fuskarsa dab da camerar "Na ji kamar ina shaƙar numfashinki...."
Ya yi shiru jin ana knocking ƙofar motar da take ciki, itama ta juya ganin wanda yake tsaye ya saka ta ɗan yi murmushi baya ganinta saboda duhun gilas ɗin motar amma murmushi mai kyau ne a fuskarsa. Ta cikin wayar ya ce "Waye?" Tana ɗaukar jakarta a taƙaice ta ce "Yaya Junaid ne"
"Ok" ya yi sai kuma ya ce "Fiyya" ta ɗago idanunta da sukai laushi ta kalle shi dasu can ƙasan maƙoshi ya ce “I love you Fiyya" da sauri ta kashe call ɗin tana haɗe fuska ta ɗauki wayar ta fita daga motar.
"Yaya J" yana murmushi ya ce "Manager" ta ɗan yi murmushi kawai ya amshi jakar hannunta "Me kika zo da shi"
"Ba kyau bincike J" ya jinjina kai suka nufi shiga gate J ya kalli driver ya ce "Ka shigo mata da motar, she left the key inside the car" Fiyya ta marairai ce fuska tana mannewa jikin J ta ce "Yaya J na gaji sosai"
"Sannu Manager, ko goyaki zan yi?" Ta buɗe idanu sannu yake ta yi mata har suka shiga babban parlon gidan ƴan samari wajan biyar