Showing 33001 words to 36000 words out of 63481 words

Chapter 12 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt

23 Nov 2024

6687

zuba ke kina ignoring nawa for God sake"


"Idan ba ƙi auro ba sai ki auri ɗan daban kawai" Kinal ta yi tsaki ta ce "Kuma zan iya, mene a ciki"


"Shi auren ɗan daban?" Fiyya ta buƙaci amsa tana kallon Kinal. Kinal ta ce "Deal, nama yi miki alƙawarin in dai ina da numfashi wallahi wallahi sai na auri ɗaya daga cikin ƴan daban nan, kamar ni mawaƙiya za su yi wa haka? Uhm" Fiyya ta lumshe idanu ta buɗe deep down ƙirjinta na bugawa sai ta ce


"You most like them ma, ƴan daban ai sun iya soyayya"


"Ke ta ya kika san sun iya?" Shoulders kawai Fiyya ta ɗaga ba tare da ta ce komai can ta sauke numfashi tana kallon Kinal ta ce


"Kinal Ashraf ya rasu, mijin da zan aura ya bar ni Kinal ina cikin damuwa ina jin da old Safiyyerh ce ba zan ce ina cikin damuwa ba, gwara ta kashe ni haka nake ji" Kinal ta jinjina kai "Fiyya something is over doesn't mean your life is over, ki yi haƙuri mu ɗauki ƙaddara ki yi wa Ashraf addu'a Please kar ki saka damuwa wani abun ya zo yana damun ki daman ke idan kika birki ce kamar mai ƴar mero a ka, ƙaddararmu zata zama mai kyau muna tare da addu'ar iyaye ai" sun jima tare da Kinal har yamma kana ta tafi gida tana jin dole ta sake komawa wajan ƴan kodin ɗin nan.


Da ƙyar da daddare Fiyya ta sakko ƙasa bayan tayi sallar issha tana sanye da hijabi har ƙasa, fuskarsa looking ok ba yabo ba fallasa sai dai ta faɗa idanunta ya fito akwai damuwa a tattare da ita. Inda ta yangi su J ta nufa ta shiga tsakiyar ƴan mazan ta zauna a nutse ta ce "Sannun ku" Awais ya ɗago ya kalleta ya ce "Yawwa Manager ya ƙarin haƙuri?" Idanunta ya juya ta cije baki ta ce


"Allahamdulilah,thank you" daddy dake kallon ta cike da tausayi ya ce "tashi a nan wajan Safiyyerh"


"Daddy me ya sa?"


"Ki dai tashi na ce ko?"


A sanyaye ta miƙe sai kawai ta yi sama ya bita da idanu a hankali ta ce "Sai yaushe zaka faɗa mata batun auren?" Daddy ya ce "Da sai an kammala Visa ɗin ta, na san wacce take da ita a baya ta yi expired, to Safiyyerh stubborn girl ce da na yi maganar visa zata kalli cikin idanuna ta fara mini turanci wayonta tsoro yake bani, kuma yanzu i feel very comfortable da Aliyu matsayin mijinta duk da basa shiri amma ba zai ɗaga mata ƙafa bana son dai ta yi rayuwa a wajan shi kamar Prisoner, za ta yi shakkar yi masa abu"


"Kana ganin zata amince da auren?" Ya miƙe tsaye yana haurawa sama ya ce "In sha Allah" daman daga sallah ya dawo shine ya zauna. J dai baya uhm baya uhm'uhm abubuwa da yawa ke yawo a ƙasa wanda baya rasa nasaba da tunanin wace Safiyyerh waye Aliyu?


Ummi ta kalli yadda ya shigo ba wanda ya kula kamar bai ga kowa ba ta ce "Aliyu tun safe ina ka je ne?" Ya buɗe ido ya yi shiru ta ce "Kuma ka ci abinci ne? Kodayake ba'a tambayar soja ko ya ci abu da za'a buɗe cikin ka duk ganye ne" kallon Ummi kawai yake kuma ya yi shiru


"Yaushe zaka tafi goben?"


"A'a, night Ummi" ya ce yana shigewa cikin ɗakin shi dake part ɗin mazan.


Fiyya ta ci kuka a ɗaki kamar rai da sauri ta buɗe system ɗinta taga saƙo a e-mail nata tun sanda sukai last called da Ashraf bayan hakan ta minti ashirin da wajan biyar. Maganar daya tura mata ya saka ta buɗe idanu sosai.


_Safiyyerh daddy ya zo ya fita yanzu, ko ma dai menene ki tabbatar ba ki bawa wani damar mallakar FS WORLD INVESTMENT COMPANY ba Fiyya mutane biyar sune mamallakan wannan kamfanin mutane masu haɗari ko ni ban san su ba, da ina da yadda zan yi a yanzu zan faɗa miki komai domin sauƙaƙa miki, ki fara nemo ma'anar FS shine key ɗin binciken, don't cry when you miss me i love you"_


Safiyyerh was shocked, thinking me ya saka Ashraf ya yi mentioned sunan daddy a lokacin, meke shirin faruwa ne gabaɗaya kan ta ya ɗauki zafi da gaske ta yi rashin Ashraf sai yanzu ne take jin gudun zuciyarta na ruɓanya aikinta a kan Ashraf ɗin. Ta kwanta tana rufe idanunta ƙarar notification na wayarta ta saka ta buɗe idanu tana janyo wayar a hankali, rubutu a taƙaice mai ɗauke da azanci da ɓoye manufar abin da ake so a bayyana.


_“laifi akan laifi again? Kodayake shi laifi tudu ne Safiyyerh ke inuwar wani ce ki yi ƙoƙari kar a saka ki shiga wuta”_


A gigice ta ce "Na shiga uku ni Safiyyerh"


****
Cikin dare ne wajan biyu da arba'in motarsa na gefen titi cikin duhun daren ya saka facemask ya rufe fuskarsa tsoro da fargaba ya gaba gitta masa zuciya a hankali ya zuge glasses ɗin motar babu mai cewa shine a ciki, yana buɗewa ya faɗo cikin motar ya ce "Kira cikin dare? Ban fiya son ina tsaka da wani aikin kuma ana kira na wani ba, ya akai?"


Photo ya fito masa da shi na wani kyakkyawan yaro fari tas da shi idanunsa buɗe ya shagwaɓe fuska tare da miƙa hannu alamar a bashi wani abu, yana sanye cikin wasu ƙananun kaya baƙaƙe. "Na gani photon waye? Wannan yaron fa?"


"Ɗan gidan Safiyyerh ne" ya furta yana lumshe idanu tare da yin baya ya jingina da kujerar zuciyarsa na buɗewa sosai tsoro da fargaba na cika shi "What! Safiyyerh yaronta kuma?"


"E, idan kaga Safiyyerh ka gan shi kamar an yi kaki ban san ko ta san da yaron ba a tabbatar an gano mini inda sa Safiyyerh take"


Kwanakin wajan biyar da rasuwar Ashraf daddy bai faɗawa Fiyya batun auren ba, haka ma Aliyu Fiyya kullum sai ta fita wajan aiki ba kuma ta dawowa da wuri. Yamma wajan magariba take driving a gajiye take sosai fahimtar ana bin bayanta ya saka ta ƙarawa motar giyar da sauri ta ɗakko waya number J ta fara kira amma bai ɗauka ba, ta shiga kiran ta daddy amma a kashe duk wanda take tunanin kiran number shi a gidan ta kira bata samu ba,






ta kalli madubin taga har yanzu motar na biye da ita, tare da wasu babura biyu bata iya hango fuskar mutanen amma kallo guda ta yi musu ta san ƴan daba ne, ko dai masu satar mota ne ko satar waya ta shiga uku. Baburan guda biyu suka cimma ta ɗaya ya saka hannu ya daki glasses motar nata, ta yi gefe tare da ƙarawa motar gudu suma suka take mata baya a lokacin tsoron da ya yi mata yawa ya saka ta fara gani dishi dishi kan motar na neman kwace mata, cikin sauri tana ƙanƙame steering ta shiga lalubar numbersa bata da tabbacin ko tana da ita cikin sa'a ta gani ta danna kiran sai da ta yi kiran biyar bai ɗauka ba, gashi hanya babu mutane a kira na shida ya ɗaga cikin ɗaga murya da fitar hayyaci ta ce


"Yaya na shiga uku Captain wasu ne"


Ya yi mata shiru can ya ce "Who are you?"


"Yaya Safiyyerh ce wasu ƴan daba suka biyo ni gashi titi babu kowa, Captain suna da yawa wasu a babur wasu a mota na kira number kowa a gida basu ɗauka ba gashi ciwon kaina kamar zai tashi bana ganin hanya sosai kan motar ƙwace mini yake" ta cikin wayar Captain ya yin siririn tsaki can ya ce


"Ina ruwana?"


"Captain kashe ni fa za su yi innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!"


"Allah Ya ji ƙan ki"




littafin MUTALLAB
Na kuɗi ne we're still on free pages. Ka biya a yi adding naka a paid book before mu yi cutting free pages ɗin. MUTALLAB.
Book 1, 2 &3
500 Naira
0116886423 Union Bank Na'ima Sulaiman S. A tura shaidar biya ta nan 08164069385[10/17, 8:12 PM] Nanameera: *❤‍🔥 MUTALLAB ❤‍🔥*


Page 10
*Bright pens..2nd batch*




"Kamarya Allah Ya ji ƙai na, Captain ina faɗa maka biyo ni ake yi za'a kashe ni, kana cewa Allah Ya ji ƙai na, i called you saboda na rasa wanda zan kira Please help me" ta cikin wayar Captain ya yi tsaki ya ce


"Kee, ina ruwana idan sun kashe ki who cares about your life, zan kira daddy a ɗauki gawarki ok" kashe wayar ya yi. Safiyyerh wani irin zafi ta ji a zuciyarta da raɗaɗi bata san ma wanne gurbi zata saka Aliyu ciki ba idanunta ya kawo hawaye baƙin cikin kiran da ta yi masa tana zargin kanta da laifinta ne. Ta cikin madubin motar take sake kallon motar dake bib bayanta da kuma sauran baburan ta runtse idanunta a fili ta ce "Ya Allahu Ya Rahmanu ka dubi Safiyyerh ka kawo mata ɗauki..Daddy!"
Ta kira sunan daddy a gigice tana sakin steering motar bata sake sanin abin da ya faru bayan nan ba.


Yana tsaye fitowar shi daga motar kenan ya dubi yadda ta yi flat kwance a ƙasa gefen kanta da jini ya kalli sauran jami'an tsaron da suke wajan "Is she ok? Tana numfashi?"


"She is, buguwa ne kuma Allah Ya rufa asiri motar ta tsaya da kanta, ba'a yi nasarar kama ko mutum ɗaya ba, yarinyar ce dai bamu san wace ita ba za mu duba id card nata sai a kira iyayenta a shaida musu ko asibiti ne a tafi da ita" ya yi maganar cikin girmama kan shi a ƙasa, wanda ke tambayar ko Fiyya na raye ya yi baya rungume da hannunsa can ya duba a gogo sai bai ce komai ba "Sir meeting ɗin naka? Ina tunanin ka je kawai za mu kula da komai tunda shugaban jam'iyya da secretary na jam'iyya na jiran zuwan naka" kafin ya yi magana cikin sauri wata mota ta ƙarasu wajan kamar zata tashi sama ko gama daidaita tsaiwar motar bai yi ba ya fito idanunsa a kan Safiyyerh, mutumin ya dubi fuskarta shima a hankali kuma ya ce.


"Easy Captain, ka kira ni sanda muke kan titin da take ta kuɓuta Allahamdulilah" jinjina kai Aliyu ya yi cikin girmamawa ya ce "thank you"


"Anything for you Aliyu, amma ku kula tana da harshe zuciyar nan tata irin take ce, Allah Ya bata lafiya" Aliyu dai na tsaye idanunsa akan fuskarta ya kasa magana har mutumin ya shiga motarsa driver ya ja, jami'an tsaron suma suka shiga motar suka marasa masa baya cikin tafiyar sirri. Ya jima yana kallon ta hannunsa riƙe da wayarsa tunanin yadda zai yi da ita, ƴar mitsitsiyar yarinya ta fito da shi, banda darajar daddy da babu abin da ya yi masa zafi sanin cewa idan Fiyya ta mutu hakan na nufin tsayawar numfashi daddy ya saka ya lallashi zuciyarsa. Cak ya ɗauke ta ya saka ta a gaban mota yana yin baya da kujerar a ransa ya ji ba zai zama drivernta ba, ya ɗauki wayarta ya rufe motar yana shiga ya tare da zama ya sake juyawa ya kalle ta da kyau sosai jinin ke fita a goshin nata ya taɓe bakinsa kawai a hankali kuma yana ɗora mata tissue ya furta


“Fitinanniyya... Safiii”


Farar safiya ce gari ya yi shiru amma shi idanunsa biyu, yadda ya ga dare haka ya ga rana idanunsa tarwai a sararin subuhana yana kallon sama da abubuwan da Ubangiji ya wanzar a cikinta, a hankali ya juya ya kalli Darma da Goje sai kuma Mangal dake can gefe guda ya sha ta gaya masa babu daɗi sai lilo yake da ƙafarsa a sama. Mangal ne ya buɗe idanunsa da sauri ya miƙe zaune yana murza idanunsa alamar bai gama wastsakewa ba.


"Jeji naka dawa taka ka huta mai dawa, ba dai gaba da gaba ko ta baya ƙaryar mutum dan uwatar ya aka yi ba ka yi kasa bane ka raya daren da gadin mu?" Moh ya yi shiru ƙirjinsa sai ɗagawa yake. "Ina tsoron shirun nan naka don ba zai haifar da ɗa mai ido ba, ka tara dafi a cikinka jira kake ka samu inda zaka sauke ƙarin dake damun jikinka ka sarara a kaiwa mai duka lillahi kukan kawai" sai a lokacin ya juyo da gajiyayyun idanunsa da suka shige ciki duk girman da suke da shi, sun yi wani bala'in ja ya zubawa Mangal ido


"Talk da turanci kenan da hausa na goga maka yi magana sarkin jeji"


"Mangal"


"Yes inji masu jajayen kunnuwa bi ma'ana na'am" muryar Moh bata fita sosai a lokacin duk wanda ya nutsu zai hango wani irin sanyin murya da yake da shi da sauti maraya hayaniya. "Wacce cuta aka taɓa yi maka a rayuwa wacce ba zaka iya yafewa ba?"


"Kan uban nan, ni ai ka sani a kusurwa kaina ya kulle wanda sukai mini kuma tuni sun girbe abin da suka shuka bana yafiya bana cuta bana bari a cutan" cije baki kawai Moh ya yi yana lumshe idanunsa da sauri ya buɗe su tar saboda yadda yake jin kakari da numfashin fitar ranta yana yi masa amo a kunne, ya mirgina kaɗan ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗora akan ɗaya yana girgiza wa ya zubawa zara-zaran yatsun ƙafarsa idanu tare da rungume hannayensa a ƙirji.


"Wai what happened Mai dawa?"


"Ka dai na yi mini turanci don uwarka"


"Ɗan tsinanniya ba, ba uban da ya iya kuma ya san ai duk bama ji shima a Legas ya koya" cewar Goje yana farkawa tare da zama dukkan su babu wanda yake da niyyar miƙewa domin yin sallah. Goje ya kalli Mutallab ya ce "Yaushe za a kwalo berewar nan ne? Ka yi shiru karfa ka jiƙa masa aiki"


Da sauri Mutallab ya kalli Goje jin sunan daya kira na barewa ya lumshe idanu ya buɗe zuciyarsa na bugawa sosai sai bai ce komai ba can dai ya miƙe zaune a hankali kuma ya tashi tsaye ya zaga bayan katanga ya daɗe kafin ya dawo wajan Darma ya kalli hannun Mai dawa ya buɗe idanu ya ce "Bura... Wannan ƙwayar ka shanye to kwarankwasa ka shirya zama mahaukaci, ƙwayar doki ce fa? Wai kashe kanka za ka yi akan wasu ƴanƴan jakuna ka fito musu gaba da gaba mana, a yi komai duk abin da zai faru ya jima bai faru ba, ƙarshe dai gidan ɗan kande ne kuma mu ba wai baƙin ta bane"


Mutallab ya tsaya cak a tsakiyar wajan naman jikinsa na motsawa musamman kakkauran ƙirjinsa mai faɗi sai kawai ya shagiɗe bakinsa gefe kamar zai yi murmushi da sauri ya tsuke fuska zuciyarsa na tuna masa shekarun da suka shige a fusge ya furta "Sai godiya" gabaɗaya suka miƙe tsaye suna maimaita


"Sai godiya"


Basu fargaba sai ganin tarin wasu ƴan daba suka gani suna fitowa daga wasu lunguna a ƙalla sun fi su ashirin ɗauke da gorori wasu wuƙaƙe. "Dara ta ci gida lallai an raina mu, mu wasu daƙiƙai zasu kawowa farmaki har lukanmu?" Cewar Darma Mangal ya kalle su ya ce "Kuma suwaye ku yara?"


Wani daga cikin su ya fito ya tsaya a gaba ya ce "Sanin sunana ko waye ni bashi da wata fa'ida a gare ka, da zaka tambayi wanne kalar kisa zan maka zai fi maka, amma saboda gudun tilawa ko tafiya ƙiyama da tunanin wanda ya kashe ka lallai zan goga maka sunan nawa". Ya zaro wuƙa daga cikin ƙugunsa idanunsa akan Moh da bai ma kalle su ba sama kawai yake kallo yana jin yanayin na yi masa daɗi ya ɗora da "Uban ƴan daba nake maganin ƙananun yara masu ɓoyewa a saƙo, to cut you short sunana Lauje, ban duƙo dan na saka muku makami ba, na zo na tafi da uban gidan naku salin alin akasin hakan wajan bijire mini zai saka an samu kwacewar lissafi dar kenan" wanda ke kusa da Lauje mai suna Modara ya ce


"Ka saɓo shi a wuya mana sai ka tsaya ɓata yawun da Ubangiji ya halitta a bakinka Oga?"


"Ban zo don rigima ba, bisa umarnin Hon na zo wannan shine"


Darma ya matsa gefe yana nuna musu Mai dawa Moh kenan ya ce "Bisimillah gashi nan kuje da shi kuna da hannu na san" Moh ya sake juya musu baya maganganunsu da gaske ciwon kai da zafin zuciya suke ƙara masa hannunsa kawai yake dunƙulewa yana hura iska sama ko yaushe ya zama sa'annin yara irin su Lauje?


"Ji mana"


Mutallab ya juyo yana gyara tsaiwa idanunsa a birkice Lauje ya dinga kallon Mai dawa, shi bai ya yi tunanin haka yake ba yaji ana Mai dawa da Mutallab sai ya ji sunan Mutallab kamar na ƙananun yaran ganin Mutallab cikakken namiji a tsaye mai kakkauran hannu da buɗaɗɗan ƙirji gabaɗaya jikinsa a murɗe yake musamman damtsen hannun ya basar ya ce "Shige muje"


Da hannu Mutallab ya yi masa alama da ya zo ya tafi dashi, Lauje ya nufi wajan Mutallab ba tare da sanin cewa akwai shafin hannu a jikinsa ba ganin ba wani makamani hannunsa ya saka ya nufe shi. Yana miƙa hannu da sunan kama shi Mutallab ya yi masa wani naushi a gefen ƙirji, nan take Lauje ya fara fari da idanu ƙashin gefen ƙirjinsa ya yi ƙara ya sulale a wajan ba numfashi. Ganin hakan ya saka su Modara ja baya a tsora ce ya ce
"Kut ya bazar dashi ba, wannan mahaukaci ne"


"Bai mutu ba tafiyar zango ƙalilan ya yi kawai ya samu karaya a ƙirji, kar dai ku manta da Mai dawa kuke magana masu jeji da namomin jejin da kansu matsalar gajanci kenan kun tari mutumin dake da shafi a hannunsa duka ɗaya ka sume gwara ya saka maka kaifi daya saka hannu, ya zame muku hadda. Yi batu waye ya aiko ku?"


"Hon Maɗatai"


"Wani abu ne haka? Me za a yi masa?"


Modara ya ce "Bamu sani ba, ya ce yana buƙatar ganinsa shi kaɗai kuma a sirrince"


"To ba zan zo ba"


Cewar Moh yana cije bakinsa hannunsa har yanzu rawa yake baya son yin kisa, idan ya riƙe wuƙa bai san me zai iya yi ba kuma sam. Da mamaki Modara ya ce "Kasan waye hon Maɗatai kowa? Wallahi taimako zai baka shine kawai yake jin tausayin ƴan daba irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login