Showing 36001 words to 39000 words out of 63481 words
Chapter 13 - MUTALLAB BOOK COMPLETE DOCUMENT By Nimcyluv.txt
mu"
"Ɗan daba irin ka dai, shi Malam Abdullahi ne balle ya yi mini baki, ko Malam Abdullahi can ta matse masa" Modara ya buɗe baki da nufin sake magana "Kana kira mini sunansa sai na yi maka sabuwar kaciya" ba shiri ya tsuke bakinsa suka ja Lauje tare da barin wajan cike da takaici.
Safiyyerh na kwance tana bacci tun bayan sallar asuba da ta yi, Dr Hash ya sake ɗaura mata ruwa a hankali kuma ya ji tana surutai ƙasa-ƙasa ya kasa kunne da kyau ko zai ji mene take cewa "Ashraf ka taimaka ka dawo ka faɗa mini ma'anar FS, ka faɗa mini suwaye mutane biyar ɗin da kake magana akai, Ashraf the company is belong to your father,ko a mafarki ne ka faɗa mini ko a fatalwa ne ka zo mini bazan ji tsoro ba, Ashraf i really really need your help, don ka dawo" Dr Hash ya juya ya kalli daddy da ya yi ƙasa da kan shi
"Daddy akwai damuwa fa, meke faruwa da Fiyya ne? Me take buƙata wajan matacce ne Ashraf zai fito daga kabarinsa kuma ya yi mata, daddy Ashraf ya rasu fa ranar da za a ɗaura musu aure da Fiyya me ya sa ba za ta yi tawakakkali ba, me ya sa wai?"
"She loves him so much, tana son Ashraf ne shi ne dalili" cewar daddy yana sake matsawa tare da zama a bakin gadon ya kama hannun Fiyya ya riƙe cikin nasa da kyau "wannan zafin hannun fa? Her temperature is too high, bana son zazzaɓi a jikin Maama ka yi wani abu Dr Hashim" Dr Hash ya ce "Ciwon kanta da bugawar ne ya saka mata zazzaɓi, na yi mata allura zuwa anjima zai sauka ai"
Maimakon Fiyya ta yi shiru sai ta cigaba da surutan sosai tana furta "Ni ba Tiger ba ce Tahhb, why are you decided to call me Tiger?" Kamar a gaske kamar kuma yanzu ne ta ji saukar muryarsa a tsakiyar kanta, sautin ya sauka a ƙirjinta "Saboda ke matar Moh ce Tiger, zama matar Moh is not easy we most fight together halinki irin na tiger ne, matar Moh" tar da buɗe idanunta a gigice a kuma sauti na ruɗani ta ce "Motar Moh"
Daddy da Dr Hash suka kalli juna jin abin da ta furta kafin su yi magana Safiyyerh ta juyo ta kalli daddy sai ta yi murmushi mai kyau wanda suka jima basu gani a saman fuskarta ba, ainahin murmushi da kyawun Safiyyerh daya shuɗe ya dawo fil ta riƙe hannun daddy a nutse ta ce "His voice daddy, muryarsa ce"
"Shi wa?"
"Tahhb" daddy ya yi murmushi yana shafa sumar kanta ya ce "ai kuwa na ji nima, ki yi bacci Maama za ki samu sauƙi in sha Allah" ta jinjina masa kai tana riƙe da hannunsa har lokacin ta ce "In sha Allah daddy, in sha Allah daddy" jikinta ya saki ta koma bacci daddy ya sauke numfashi ko samun sukunin karyawa bai yi ba, ya dubi Dr Hash ya sake duban Fiyya ya ce "Ka yi mata allura kafin ta farka"
"Daddy ka duba Maama tana cikin damuwa ba, baka jin allurar zai saka ta dawo da ɗabi'unta na baya daddy yin allurar ba mafita ba musamman ga lafiyarta, tsayin shekaru na daddy har yaushe ne ka duba Safiyyerh don Allah" miƙewa tsaye daddy ya yi ya ce "Ka yi hakan Dr Hashim Abdu Marafa, completely tsayin rayuwa haka nake son ganin Safiyyerh" jinjina kai Dr Hash ya yi sai ya haɗa allurar har guda biyu ya juya bayanta ya caka mata cikin sauri ta ƙanƙame jikinta wani irin azaba da raɗaɗi take ji a duk sanda aka yi mata allurar. Yana yi mata ya fice ba tare daya sake kallon daddy ba. Ya zubawa photonta idanu yana juya mata baya a hankali ya ce
"Ki yafe mini Safiyyerh ki fahimce ni ki fahimci mahaifinki, i am sorry Safiyyerh" fita ya yi ya rufo ƙofar ya nufi parlonsa a zaune ya tarar da Ummi tana kallon shi ta ce
"Ya jikin nata? Ta farka ne?" Ya zauna yana numfasawa "Ta sake yin bacci, ina Aliyu?" "Kasan sai ya yi niyya yake shigowa" daddy ya ɗauki wayarsa ya kira number Aliyu yana ɗagawa ya ce Aliyu zo mana ya ajjiye ya kalli Ummi cikin kulawa ya ce
"Ina jin kamar haɗa auren Aliyu da Safiyyerh na yi kuskure ina jin kuma hakan shine mafita, ina jin tsoron tambayar da dukkan su za su yi mini wacce bani da amsar su, da gaske bani da wannan amsar tasu Ummi, ba komai Safiyyerh take ganewa tana jin ta isa ta yankewa kanta hukunci ita ba kowa face yarinya mai wayon gaske da tunani Safiyyerh bata san komai ba ita kawai yarinya ce"
"Ka san dole zaka jira amsar wannan tambayar da kake tsoro, amma sanar dasu auren shine zai fi maka a raina ina jin Maama ba zata yi maka gardama ba" kafin ya ce wani abu Aliyu ya buɗe ƙofar ya shigo da izinin daddy kamar kodayaushe wandon sojoji ne a jijinsa da farar riga tas ya ɗora hula p.cap a kan shi ya zauna kansa a ƙasa yana furta "barkan ku da safiya"
"Aliyu ya aiki, baka san Maama ba lafiya bane naga baka shigo ba?"
"Na sani" ya ce kawai a taƙaice yana danna wayarsa "Ka sani kuma? Shine ba ka yi mata sannu ba me ya sa kake haka ne Gadanga, me ya sa kai zuciyarka bata motsawa sai akan Maama meke damun tunaninka baka ɗaukan responsibility ɗinka as a brother"
"Idan bai ɗauki responsibility nasa matsayin yaya ba, yanzu zan ɗauki responsibility Safiyyerh a matsayin mijinta" da wani irin yanayi Aliyu ya juya ya kalli daddy yana son sake tabbatar da abin da ya faɗa masa a zuciyarsa wani irin fargaba ne ya wanzu ciki a fili kuma ko gezau ya dai zubawa daddy idanu can ya ce "kamarya?"
"Da kai da Safiyyerh baku da wata kalma da za ku replying mutum ko responding maganarsa sai kamarya? To kamarya dai yadda ka ji ai aikin da ka yi na soja bai saka ka daina jin Hausa ba, har gwara Safiyyerh ma" daddy ya gyara zama Aliyu dai kallon mahaifin nasa kawai yake da wani irin yanayi mai ɗauke da zallar mamaki.
"Aliyu ni ban isa na saka dole ba, ban kuma isa na tilasta rayuwarka yin abin da ka yi niyya ko baka so ba, Aliyu ni dai mahaifinka ne ka saka hakan a zuciyarka. Bani da wanda zai mini wannan rufin asirin kaf family, ka manta da batun Junaid da Awais da kuma Dr, kar ka tambayi mai ya saka na zaɓe ka na ji a raina zaka kula da Safiyyerh ko bayan bana numfashi ko bayan ƙasa ta rufe mini idanu na zaɓi aura maka ita saboda dalili mai ƙarfi, na yarda da ingancinka" Ya yi shiru Ummi kuma Aliyun take kallo shi kuma yana kallon daddy da duk nutsuwarsa. "Ranar da Ashraf ya rasu a ranar aka ɗaura maka aure da Safiyyerh, don Allah don girman Allah karka tambayan tsakaninka da Safiyyerh waye ba jinina ba, wannan tambayar shine abu mafi girman laifi a gare ni, ka taimaka ka yi mini alfarma ka riƙe Maama ka amshe ta matsayin matarka"
Captain ya kasa motsi balle magana bai ma san mene zai ce ba. Daddy ya matsa hannunsa "Don Allah Aliyu"
"Ita ta sani?"
"A'a, kai na fara sanarwa Safiyyerh bata da wata matsala ga umarni na" Aliyu ya sake yin shiru idanunsa a ƙasa har ya juya baya ya sake juyawa ya kalli daddy a hankali ya ce "tell her first, ko bana son ta zan yi ƙoƙarin ganin na fara son Safii in sha Allah"
"Ba zan tambaye ka ni ne ba ɗanka ba ko ita, zan bar tambayar a raina har sanda ka shirya faɗa mana gaskiya ni da ita, zan rayuwa da fargabar sanin amsa, da gaske daddy zan so Safii iya tsayin numfashi tunda kai ka zaɓa mini ita"
Daga Ummi har daddy kallon Aliyu suke musamman daddy bai yi tunanin jin wannan amsar ba ya dinga kallon Aliyu ba ko ƙiftawa "da gaske zaka so Safiyyerh? Ka san Safiyyan da nake nufi Aliyu?" Aliyu ya buɗe idanunsa wanda hula ta ɗan rufe masa su
"Safiyyerh Abdu Marafa ko ba ita ba?"
"Ita, zaka so ta ka ce?" Daddy ya sake faɗa da mamaki
"Bata da Qualities ɗin da za a sota ne?"
"Haka ne tana da shi, na shirya tafiyar ku za ku bar ƙasar nan nan da kwana biyu bana buƙatar ku gabaɗaya a yanzu domin nutsuwar zuciya" Aliyu ya sake duban daddy ya ce
"Kuma? Ka bar tafiyar nan daddy" sai kuma ya juya gabaɗaya ya kalli Ummi da daddy
"Aliyu soja ne, so i will be with her always"
Yana cewa haka ya fita da ƙyar ya yi jarumtar kai kansa ɗaki ya cire p.cap ɗin kansa ya shiru ba auran ke damun shi ba, tunani ya fara wa daddy ya haifa tsakanin shi da Safii?
Da yamma Safiyyerh ta ɗakko ƙasa bayan tafiyar Kinal daga ita sai duguwar rigar bacci kanta ba hula sosai ƙuruciyar nan tata ya bayyana, ta zauna saman kujera ta lumshe idanunta ta zama wata ira tun bayan tashin ta daga bacci jikinta ba ƙwari. I dake kallonta ya ce "Sannu Manager, ya jikin yanzu?"
"Bayana ke mini ciwo Yaya J, ina jin Dr Hash ya mini allura, bana son allurar nan Yaya J bana jin daɗin ta watarana zata kashe ni don Allah ka cewa daddy ya daina sawa Dr ya yi mini" idanunta ya shiga kawo ruwa ta yi lamo da kanta saman hannun kujera. Daman yana bakin ƙofa jin abin da take cewa sai kawai ya juya shi kuma Yaya J ya ce "Ki yi haƙuri Maama za a daina miki in sha Allah" ta yi shiru kawai.
Dr Hash na zaune a lambun gidan yana waya kasancewar baya da wani aiki a asibiti hutawa yake kashe wayar ya yi ganin Captain tsaye a kan shi. "Babban yaya barka da fitowa" kamar ba zai zauna ba sai kuma ya nemi waje ya zauna fuskarsa kamar kodayaushe babu walwala ya jima a haka kana ya ɗaga kai ya kalli Dr Hash "Akwai wani abu da kake son faɗa ne Captain?"
"Ka daina yi mata allurar da kake mata"
"Me ya sa?"
"Haka dai na ce, idan kuma ka yi zaka sha mamaki" Dr Hash ya ce "Wannan kam ai daddy zaka faɗawa shine ke bada umarni"
"Wa kake da suna, ka da ka sake ka kuma yi mata idan ba haka ba kuma wallahi zaka kwana ɗakin duhu" yana cewa haka ya miƙe tare da barin wajan.
*****
Hon Maɗatai na zaune gabansa zube da fastocinsa yana magana da wani yaronsa wajan keɓantacce ne kamar lambu haka yake bai san da zuwan mutum ba sai huci da ya ji ta bayansa ya juya da sauri sau kuma ya buɗe idanu waje kafin ya ce
"Ya zaka faɗo mini kamar ɓarawo?"
"Da ɗan siyasa da ɓarawo uwa ɗaya ta haife su, waye kai?"
"Baka san waye ni ba a garin kake nufi?"
"Ba'a haife ni da na sanka ba, ka aika akawo ni ina fatan saƙona ya iske ka?"
Hon Maɗatai ya kalli mutumin gabansa da wani ya ce "Waƙa ta yi, da ita za'a fara fita yawon kamfel a biya a dinga sawa a gidajen rediyo" ya ciro kuɗi miliyan biyu ya bawa mawaƙin ya ce "Ga sadakin ka, ina fatan waƙar gaba tafi wannan akwai wata zabiya wai ita Kinal A Awaya" cikin jin daɗi mawaƙin ya amshi kuɗin ya ce "Na san Kinal ai ta iya waƙa, ba dai ta shahara sosai bane"
"To sai mu saka ta shahara na ji ta yi Ali wali waƙa, ta yi sosai ta zuba kalamai na fikira harshen nata akwai zaƙi dani kuma kawai ya dace a nemo mini ita" "zan kawo ta in sha Allah hon, ka yi ka gama ka karya kujerar dambu mai hawa uku Allah Ya kare ka ɗan Majilisa kai ne da nasara Hon" "zaka iya tafiya sai na jika"
"Akwai taliya da atamfa da su Omo suger, a tabbata duk local government ɗin da aka je kamfel an basu, a kuma ɗauki photo da bidiyo za a bawa ƴan social media su baza shi ko'ina. Sai sauran magana na siyan ƙuri'u za ku yi da p.a you can leave Musbah" Musbah ya miƙe tsaye ya fice sai a lokacin ya juya ya kalli Moh dake tsaye fuskarsa duk rauni
"Nan ai ba jeji bane, ni kuma ba naman jeji bane ba have a seat"
"Bana zama"
"Saboda me?"
"Tsaro, yi magana"
"Shi wanda kakewa aikin baya kula da lafiyarka ne dubi fuskarka Mutallab"
"Ka kira ni da Moh ko Mai dawa sai mu yi magana" Hon Maɗatai ya jinjina kai ya ce "Ina son sanar maka na haɗa hannu da Dr Abraham, ta yiyuwa ya janye muƙamin da yake nema ƙarƙashin jam'iyyarsa idan haka ta gaske zamu kai Ali wali ƙasa ne, ka haɗa hannu dani lallai za ka ji daɗi"
"Me ka shirya yi wa matasa idan kaci zaɓen?" Hon Maɗatai ya ɗaga kai ya kalli Moh sai kuma ya yi murmushi ya ce
"Inganta ilimin su, rage musu kuɗin makaranta samar musu da ayyukan yi cusa musu ra'ayin noma da muhimmanci yinta"
"Su kuma ƴan daba fa? Wanda kuke anfani da su wajan cimma burikan ku, bayan yaran ku na keɓe kuna tattalin tarbiyar su ba ruwansu da sabgar siyasa sai mu ƴaƴan talakawa ƴan wahala kuma ƴan daba mashaya mune ƴan bangar siyasar ku a yau, a gobe a manta damu jibi kuma a neme mu shine ko?" Hon Maɗatai ya yi murmushi ya ce "Mutallab kenan, duk wata nasara da muka samu ai daku zamu rabata ni mulki da siyasa tamkar don su ne aka haifan, ina da kyakkyawan tanadi akan ku ba za a bar rayuwarku haka ba"
"Me kake buƙata"
"An saka ka kamo Manager ta kamfanin FS WORLD INVESTMENT COMPANY ko?"
"Wanne kiminin ya faɗa maka?" Hon Maɗatai ya miƙe tsaye yana zagayawa ya ɗauki fasta ɗinsa ya dinga kallon kansa ta ciki can ya ce "kai yin aikin ne a gabanka, mu ƴan siyasa da idanu ɗaya muke bacci mun raba kunnuwanmu ko'ina, ka dai sani a siyasa babu masoyi na dindin haka ma maƙiyi, iya ruwa je fidda kai kowa ya iya allonsa ya ce wanke kuma ni da Ali wali ai sahun qiwa ne ya take na raƙumi kowa da abin da yake buƙata, idan ka yi kidnaping yarinyar ka tilasata maka ta saka mini hannu domin na saka hannun jari a wannan kamfanin shine abin da nake buƙata" Jin Mutallab ya yi shiru ya saka ya ce "Ko baka ji ba?"
"Na ji"
"Mene alaƙar ka da makarantar FGC?"
"Ban sani ba, maganar kuɗin aikinka sai na yi aikin zai sanar. Sai godiya" yana cewa haka ya bar wajan.
Kasancewar Monday ce Safiyyerh ta shirya da wuri zuwa office har yanzu jikinta bai warware ba dole amma ya zama sai taje. Ba jimawa Md ya shigo bayan sun gaisa fuskarta dai a kame ya shafa kai ya ce "Manager gari ya ci wuta fa" idanunta akan wani ducoment tana juya kujera a hankali kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce "Nawa kake buƙata Md?"
"Ko dubu ɗari biyar ne zan yi maleji"
"Zan saka accouter ya baka miliyan ɗaya" ya dinga mata godiya sosai ta yi murmushi kawai ta ce "Mene ma'anar FS ni kam Md?" Tsam ya yi da ransa sai kuma ya ce "Ba zan iya ba ki wannan amsar ba Safiyyerh, zan dai faɗa miki abin da ba ki sani ba" ta sake juya kujerar hannunta a haɓarta tana murmushi mai kyau "Ina ji Md"
"Yatsun da kika gani kwanaki gaskiya ne, ana siyar da ƙodar mutane a wannan kanfanin tare da jarirai, ana kuma dillacin ƙwayoyi, sauran abun ki yi bincike da kan ki za ki iya dacewa" yana cewa haka ya fita. Kasa motsi Safiyyerh ta yi numfashinta ya tsaya cak da ƙyar ta miƙe ta ɗauki ruwa ta sha ta dawo saman duguwar kujera ta zauna zufa ta dinga yanko mata a hankali ta ware rolling na kanta ta rufe idanu tana kiran sunan Allah. Knocking aka yi da ƙyar ta ce "In"
Ta buɗe idanu da mamakin ganin wanda ya shigo, ya ƙarasu cikin office ɗin "Ba dole ki buɗe idanu ba Safiyyerh, idanunki kenan?" Ta yi murmushi tana gyara zamanta
"I. Qasim kai ne"
"Ni ne Safiyyerh"
Ya nemi waje ya gaisa ta ce "Yaushe gari kuma?" Ya yi murmushi ya ce "Zama likita a garin nan is not easy Fiyya, ya batun ciwon kan ki kowa?" Ta ce
"Yana nan"
"Ayya sorry, akwai maganganu da zan ba ki in sha Allah da allura, gudun kar ki dinga sha ba daidai ba zan dinga zuwa dasu kina sha a gabana na yi miki allurar, za ki samu sauƙi in sha Allah"
"Thank you I. Qasim na gode sosai" wayarsa aka kira ya kalleta sai kuma ya miƙe tsaye tare da yi mata alama da yana zuwa. Ta bishi da idanu har ya fita.
*****
Safiyyerh ta dinga kallon daddy kamar mahaukaciya saboda rashin fahimta ta ce "Daddy, aure da Yaya Aliyu ka ce dani kuma Safiyyerh, mu duka ƴaƴanka ne fa" hawaye ya fara suntiri a saman fuskarta ta saka hannunta ta toshe kunnuwata tana girgiza kanta gabaɗaya ta jiƙa hijabin da ta yi sallah da shi da hawaye "ruɗanin da kake sani a kullum yana shirin haukatar dani daddy, ba auren ne ban yi na'am da shi ba na kasa fahimta ne dani da Captain waye wanda ka haifa waye ba ɗanka ba"
"Ku duka yarana ne Maama, idan har kin yarda ni uba ne a gare ki kuma kina so na da ƙaunar farincikina ki amince da auren Maama, ba zan taɓa cutar dake ba ni ubana ne, uban ƙwarai kuma yana zaɓawa yaransa abun ƙwarai ne ki yi mini biyayya Safiyyerh, kin ji ko?"
"Na amince daddy zan amince da abin da ya fi wannan ma, Allah Ya sa shine mafi alheri a gare ni" ta faɗa tana rushewa da kuka da sauri kuma ta yi waje ta nufi ɗakinta ta faɗa saman gado ta dinga wani irin kunjin kukan kamar