Showing 15001 words to 18000 words out of 133548 words
Chapter 6 - YAR AIKIN KARUWAI BOOK COMPLETE by Asma Baffa .txt
ni a hanya ganin Kamar ko zararriya ce ni,yace ke...a gabansa na tsaya Ina kalle kalle,gashina na sosa na kasa tsayawa kyam,kana ganinsa kaga kamili yace Ina Zaki je? nace ai Almajira ce ni,kai ya jinjina yace kina zuwa makaranta Kuwa? Murmushi na saki nace tab ai ni Jahila ce bani da ilimin komai yanzu ma littafi da karatu bazai Shiga kaina ba,galala ya kalleni yace kina so ki iya? da sauri nace ae,yace Okay da zaki iya zuwa dakina da na koya Miki dole sai karatu ya shigeki da yatsansa ya nuna kirjina yace idan bai shiga ta kanki ba dole zai shiga ta nan idan bai shiga ta nan ba to Dole zai shiga ta nan ya nuna gabana da yatsa,nace har ta nan karatu Yana shiga kaji karya,to Malam Iskanci aka ce ana yi da wajen,Kai baka sani ba Iskanci fa akeyi da wajen ba ruwana wajen Iskanci ne,na ja tsaki na juya nayi tafiya ta abina Ina masifa ya dauka bani da wayo zai taba min wajen Iskanci na Allah ya kiyaye.
Direct hotel din nan na koma ko zanga mutumin jiya gashi bazan ma ganeshi a Fuska ba sai dai ko idan naji kamshinsa na dade Banga alamar shi ba na bar wajen na tafi barata yau ma iya kudin abinci na tara, Wasa Wasa kullum Ina zuwa Hotel har da dare ban sake Jin me irin kamshinsa ba har na kwashe kwana biyar,shi Kuma Nawwar bai ma duba wallet dinsa bata nan ba,yau da dare na sake komawa nace wallahi daga yau Matukar ban ji me kamshinsa ba bani sake zuwa, ranar Kuma Nawwar ya nemi wallet dinsa ya rasa musamman atm card dinsa sune Suka dame shi, Fitowa yayi ko zai iya gani a cikin motarsa Nan ma ya gama dubawa babu, Fitowa yayi dake da duhu a wajen ko fuskarsa ban gane ba nidai naga hadadde ya wuce,Yana wucewa wani kamshi ya dakeni naji Kamar irin kamshin Wanda ya jefar da wallet dinsa jiya,Ina juyawa Naga ya Dan min nisa da karfi nace Malam....tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba da gudu na fyalla naci wawan birki a gabansa Ina haki na zaro wallet din tare da Mika Masa nace t...taka..ce? Yau sati guda kenan ka jefar da ita na ganta kullum sai nazo ko zan ganka,kasan irin hatsarin da na Shiga a hanya sabo da zan kawo maka abarka ai Saura kadan wani ya taba min wajen Iskancina,wai dan Allah karatu ai baya Shiga ta wajen,Nawwar bai gane me nake nufi ba ko saurarar zancen nawa baiyi ba, farin ciki ya Kama Nawwar cikin muryarsa me dadin saurare yace ta ya Kika ganeni? Nace kamshinka yasa kawai danni ko yanzu in za a kasheni bazan ce ga fuskarka ba sabo da duhu,karbar wallet din yayi Ina kallo ya duba komai nasa Yana ciki inda suke ya fito da dalolin masu yawa ya irga ko wacce dala dari dari ce a ciki ya zaro guda Uku yace gashi na gode
Baki na turo nace Hmmm uhm jam ni me zanci da wannan takardar ai gwara ka bani dari biyar,dariya ta kamashi yace kudine fa idan Kika canja sunfi dubu dari nace wallahi bana so kaji mutum dama can baka yi Niyyar kyautata min ba in hakane ka bani dubu daya mana,Nawwar ya buga buga nace wlh bana so,yace to jirani a nan Ina tsaye a wajen ya koma cikin hotel din sai gashi da kudi Yan dubu dubu ya Mika min Yace gashi dubu talatin Kika samu ba cash a hannuna da yawa,da sauri na karba nace Allah ya shi Albarka za kaga daidai a rayuwarka bukatunka sai sun biya da iznin Allah na juya na take da gudu,yace jita Kamar yarinya da bakar Fuska kamar bayan tukunya Kai wannan da baki take,ni kuwa ko gane fuskarsa banyi ba nasan dai fari ne sosai dan dogo haka ,baki ya tabe ya juya ya koma ciki Yana cewa Kai amma tana da Amana a Zamanin nan.
Ni Kuwa cike da murna na kwana da sassafe Ina idar da Sallar Asuba wanka nayi da ragowar sabulun wankina na wanke fuskata tas duk da na dan canja sabo da yawon bara a rana,kayana dana jiya na wanke su tas jakata na dauka Yar wayata na Kira Saratu kawata tana shiga Kiran duniya ba a daga ba,nace ya zanyi haka Zan tafi Kawai,sai dana jira 8am tayi na samu na karya sannan na tambayi wani me Napep inda ake shiga motar su Anambra ya kaini Kuwa har can irin inda ake shiga mota haka Ina zuwa aka saka ni a motar Onitcha direct duk haka Ina ta Kiran Wayar Saratu amma taki dagawa Kuma tasan number ta haka mota ta ja Muka tafi,mun biya kudin mota tuni harda Yar ragowar kudina na adana abina cikin aljihun doguwar rigata domin sanye nake cikin doguwar rigar wani material orange rigar harda aljihu shine a kayana me Dan dama dama Yana min kyau,na yafa dan karamin mayafina,tunda muke kwarara tafiya nake uban bacci na farka na koma cike nake da nishadi Kamar ba gobe, sai tsakar dare Muka Isa Wanda mafi yawa a tasha muka kwana,in Banda turanci da Kuma pidgen English sai yaren Igbo shi Kawai ke tashi,gaba daya a tsorace nake,na matsu na ga Saratu nace yanzu Saratu dan masifa ta iya Zama a garin nan ko tsoro bata ji Kar fadan arna da musulmi ya barke a halakasu, gashi bana Jin turanci,Fitowa nayi daga tashar ba Wanda ya saurareni kowa Harkar gabansa yake yi, Napep na gani na tare iya sunan street din na iya fada masa yace you be Hausa? Yana cewa Hausa na washe baki na daga Kai sama kamar naga Dan uwana bahaushe,shiga nayi ya Fara tafiya Naga haduwar birni gidaje na gani na fada Muna tafiya Ina ta farin ciki,a fili nace yanzu nasan nazo birni, Birni na shigo,Yan Kudu gani sunana Rabi ae Rabi me zamani dariya na saki hahahaha kamar sabon kamu,nace wuhuhu kuturun dosan uwa ana bala'i a kudu, na nuna wasu Yan Mata da yatsa nace kalli cinyoyi Kai cinya a waje haka da Dan wando gajere wasu da mini sun Sha takalma masu tsini,na saki ihu nace yehoho ana tsiya nayi tafi da hannayena nace naga waje.
Munzo wucewa ta wata GRA nace wuhuhu Kai Saratu lallai kinci gaba haka Zan zauna a katon gidanki,bani ba Arewa dole sai nayi kudi inzo inyi ta aikina in tara kudi ba inda zanje naga waje,Kai Rabi kin dace Ina magana da karfi Ina dariya Ina zazzare Ido Ina nunawa da yatsa Ina ta kallo,Me Napep bai San me nake cewa ba, tafiya mukeyi kamar zamu bar gari tafiya taki karewa tun Ina nishadi har na gaji nace Allah dai yasa yasan unguwar da nace,tafiya akeyi na gaji ma tun Ina magana har na gaji nayi shuru ga yunwa na cina,cikin birnin naga mun bari munzo wasu unguwanni Ghetto area unguwar talakawa da Yan jagwal badan ginin bulo bane da yawa sai nace kauyenmu yafi nan komai da komai.
Sai da muka zo daidai wani lalataccen gida yayi parking Yana min alama da na fito,Ina mamaki na fito dauke da jakata a Hannu nace ya za ayi ka kawoni kauye ni da nace birni dan mugunta sai da ka wuce duk wurare masu kyau sanna ka kawo ni lalataccen wuri ni nasan wacce nazo wajenta baza ta zauna a nan ba Yar gayu ce me kudi tace Mansion ta gina a birni wata ce ta karaso wajen tana Jin hausa da alama ma bahaushiya ce itace ta tambaye shi da turanci meke faruwa? Yace shi bai San me nake cewa ba,tace ke meke faruwa? Ina masifa nace Odimgbe Street nace ya kawoni shine ya kawoni kauye Kuma wajen kawata nazo Saratu Amma kamar ana kiranta da Seraline,nan take matar ta sheke da dariya tace nan ne Abeg dauki jaka ki Shiga ciki kice a nuna Miki dakinta ki jirata, Ni dai nace Yar gayu ce fa me kudi ce kawata matar ta sake shekewa da dariya tace bawa me Napep kudi dalla malama kinzo mansion din Sera,Ina mamaki duk na hada zufa na biya me Napep kudi na Shiga ciki,matar ta rakani wani dan daudu ya shigo Yana karairaya yace wannan fa daga Ina haka? key zaka bata na dakin Sera zata jira ta bakuwarta ce,shewa Dan daudun yayi tare da furta ahayye daga Kauye amma wannan za'a kwashi gara,nidai mamaki nakeyi Dan yanda Naga Saratu ta hadu bazan taba yarda a irin wannan gidan take ba, gidane baida Fadi sai tsayi zururu daki daki sunfi ashirin ko wacce kofa na facing wata kofar dakin,tsakar gidan siminti duk gidan Kuma bandaki guda daya ne tal dakunan Kuma harda Yan daudu mutum uku a gidan,duka layin unguwar Haka gidajen suke unguwa ce ta karuwai arna da musulmai da duk wani yare a kwai a unguwar, kidane iri iri ke tashi Mata ta ko Ina gasu Nan da kyawawa da munana duk da shigar banza wasu sabo da kyau sai kace mene ma ya fito dasu amma haka aka bude min dakinta na shiga.
Dakin nake karewa kallo da tiles dinsa sai katuwar katifarta da fanka irin ta kasa sai akwatunan kayanta a gefe,can barin Kuma Gas ce karama da duk wani kayan girki na bukata akwai shi,Babu wutar nepa Sanda na shiga sai zafi kamar zai kashe ni na jike da zufa haka na zauna na buga tagumi Ina kallon hoton wani katon gida me kyau manne a bangon dakinta,Daya barin Kuma katuwar poster ce ta batsa Namiji ya rungume mace babu Kaya a jikinsu ni dai kunyar hoton ya kamani na daina kalla na sadda kaina kasa,gajiya nayi da Zama na fito waje na samu a tsakar gidan wasu suna shan giya,wasu sunyi group kayan maye suke sha,wasu suna ta busa wiwi,wasu Kuma suna ta buga chacha sai bina suke da kallo suna kus kus gasu duk matane sai Yan daudu a cikinsu da wasu tambadaddun mazan,Ina juyawa wani yace Kai ji Duwawu dan Allah bakuwar Sera ce,wata inyamura ta kalleni tace Ohh Jesus see her back nidai fita nayi daga gidan da ko kofa babu bare a rufe a jikin wata bishiya na tsaya Ina kallo yanda karuwai ke hada hada wasu suna rawa kamshin girki sai tashi yake,inda nake tsaye Me POS ne wani tattirin dan duniya hancinsa ya saka barima har waje uku,kitso ne a kansa kana ganinsa kasan ya gogu da bariki,yace ke ya sunanka? Yana Jin hausa amma ba sosai ba dake Wai ya zauna a Jos,na kalle shi nace sunana Rabi,ahaa yace yaci gaba da harkarsa,Ina tsaye wata karuwa tazo ta bada dubu dari ya tura Mata a accnt, yace oh lallai Lili jiya an daki harka har dubu dari ko da Alhaji Kika hadu? Tsaki Lili ta ja tace Munafuki Abeg send my money,aikin banza tana tauna chewgum, sai Suka Fara fada,me POS yace see your head mango head,with your toothpick hand idiot,suna ta cece kuce Ina tsaye Ina jinsu sai ga wata mota hadaddiya tayi parking Saratu ce ta fito daga motar taci uwar kananan kaya wani bumshort ne a jikinta sai yar riga bingila komai nata a waje ga takalmi me shegen tsini da jaka ta rataya komai da ta saka blue and white ne sun Mata masifar kyau.
Tana ganina ta saki Murmushi naje da gudu Ina murna na rungume ta tace kawata kece nace ai tun dazu nazo Ina jiranki dariya tayi tace Ina can wajen aiki muje ciki muka tafi cikin dakinta sai kallonmu akeyi anyi sabuwar bakuwa, muna shiga na hau Saratu da fada nace Saratu Wai Ina hadadden gidan naki ne Dan Allah mu bar nan gidan na tsane shi mu koma can,Saratu Tsaki ta ja tace karki sa min ciwon Kai idan zaki zauna ki zauna nan ne gidana gidan da nake fada Miki ban gama gina shi ba,ihu na saki tare da dafe kirji nace Saratu la'ilahaillahu ashe haka kika iya karya kalli gidan da kike a waje marar kyau kalli dakinki sai zafi yanzu a nan kike rayuwa wlh gidan Dagaci yafi wannan sau dubu ke kauyenmu yafi nan layin naku kyau,gidanku ma yafi nan tsari haba Saratu ashe duk karya Kika je Kika yi Mana a kauye na gama ganowa yanzu dama karya ce motar ma naki da ita Kika je Mana data aro,Kinga Rabi idan Zaki zauna ki zauna idan baza ki zauna ba ki koma kauye,badan wlh ke bace baki Isa ki tsaya a gabana ki dinga fada min magana ba,Hannu na shiga tafawa Ina karewa Saratu Kallo nace kalli cinyoyinki kalli duwawukan ki cibi a waje ashe a nan tsirara kike yawo Saratu,tsaki Saratu ta ja tace wai Kinga me ma ya kawoki ne kike fada min magana haka? haka nayi shuru,zama mukayi na bawa Saratu labarin komai na gidan Dagaci,Saratu ta tausaya min tace Yar uwa nasan wasu wahalar da Kika Sha tun Muna yara me yasa baki kai Kara hukuma ba tunda sai da aka cike Miki takardu da komai sannan aka damkawa Dagaci ke tunda yace Yana so ai hukuma bata bashi Kawai dan ya zalunceki ba,nace da a baya Ina karama kin San hukumar gidan raino suna zuwa duba ni Dagaci ya dinga tsarasu ya fada musu karya Kuma suna ganina shar shi yasa ma tunda na girma Suka daina zuwa,idan na Kai Kara ya fini power ta ya za a kwato min hakkina a kasar nan tamu da zukatan mu sun gurbace,sannan ki duba fa Allah ne ya kwace ni Saura kadan ya fasa ni ya lalata min rayuwa Allah ne ya tsare,Saratu tace yanzu uba mahaifi ma neman yarsa yake a Zamanin nan bare ke Yar tsintuwa Allah ya kyauta yanzu kafin nayi girki kinsha wahala bari na bayar a siyo mana abinci me zaki ci? nace ah Ina kudu ai a kawo min Sakwara da miyar Agushi ,Saratu tana yanga ita a dole wayayya ta bawa wani dandaudu kudi ya tafi siyo Mana abinci Muka ci Muka koshi daga nan hirar Kauye ta barke muna ta labari,tace ya labarin saurayinki Kutama? nace Allah sarki Alhaji Kutama ,baki Saratu ta tabe tace ke dalla manta da shi ki fara sabuwar rayuwa,rayuwar yanci rayuwa me dadi ki samu aikinyi Wanda Zaki dogara da kanki,Farin ciki ya kamani nace yawwa Saratu dan Allah ki samamin aikin Yi kinji,karki damu Zaki samu aiki amma sai kin canja suna,Ido na zaro nace na canja suna Wanda aka yanka min rago aka rada min Rabiatu sai na canja suna,Kinga kamar ni Seraline ake ce min ki samu sweet name na Yan gayu irin su cutie,princess,sweet pussy etc,Ido na zaro nace ah Saratu bazan iya ba Ina laifin ma a kirani da Miracle din Kawai, Okay Miracle din ma yayi ai cewar Saratu,duk tunanina wani aiki ne babba.
Ban fahimci inda aikin nasu ya nufa ba sai da dare yayi naga kowacce har mazan suna ta faman daukan wanka ko wacce ta sa Kaya matsiyata Wanda tsirara Kawai suke,naga wasu matan Wanda zasu kwana da wani me kudin sun shirya anzo an dauke su a manyan motoci wasu Kuma sun shiga Napep sun tafi,Wanda Basu da wani Kuma suna shiri zasu fita gefen kwalta me son kwana da karuwa ya dauka ya biya,na kalli Saratu nace Saratu badai wannan sana'ar itace aikin da Kika ce kina yi ba? Ba kunya tace shine Ashawo work aikin siyar da Pussy kasuwancinmu kenan ka biya ka ci,baki na bude a tsorace nace Saratu kiji tsoron Allah kin cuci iyayenki tunaninsu Kuna tare da Yar uwarku aikin restaurant,ba kyau Saratu ke a karuwancin ma mafi Muni kike yi na kwalta haba Saratu karki biyewa arna akan abin duniya ki tuna addinin mu,tsawa Saratu ta buga min tana duba mudubi sanye take cikin Yar ficikar gown bata fi rabin cinya ba Blueblack ta sa hular gashi me tsada,tace karki dameni idan baza kiyi ba ki kyaleni bana son wa'azi aikin banza local girl,dan bakina na turo gaba nace ni dai bazan yi ba,Ina kallo Saratu ta Sha takalmi me tsini ta fice,sai da safe Suka dinga dawowa,a Haka na kwashe sati biyu har na Saba da kowa da mutanen layin kowa ya sanni Muna mutunci har idona ya fara budewa nima na fara dan zama tsagera sabo da Zama da madaukin kanwa shike kawo farin kai,Ina daki a zaune bani da ko sisi Saratu tace
Rabi ki bude kunnenki kiji zaman da kikeyi a karkashina ya Kare zan hakura mu zauna daki Daya dake amma fa ba kyauta ba dole ki dinga kawo kudin haya rabi Nima na kawo rabi mu hada mu biya,sannan daga yau na gama ciyar dake da kudina sai kema ki fara neman kudi ki dauki nauyin kanki da kanki sabo da haka na baki nan da wata guda ki kawo kudi dubu hamsim nima na kawo mu biya kudin haya,sai abinci ki nemawa kanki daga yau,na rasa me zance ma gashi bani da wajen zuwa,nace to a nan gidan Kinga ni dai bazan iya siyar da gabana ba bazan yi karuwanci ba idan akwai masu daukana aiki zan dinga musu shara da wanke wanke,Saratu tace akwai 'yarzabil kaf layin nan tafi kowa kudi,akwai wise itama tana da kudi ta Dade tana Neman Yar aiki a gidan nan, ga Star itama duk nasan zasu yarda ki musu girki,wanke wanke da shara da mopping,idan duty na wanke bandaki yayi na kowacce ke Zaki wanke musu haka sharar compound kaf gidan nan kullum da duty kowa so Zan musu magana,nace to ai suna da kirki ma ki fada musu Kinga na samu aiki idan na samu miji me sona nayi aure na,Saratu baki ta bude tace aure lallai Zaki kashe kanki yarinya tab, amma rayuwarki ce.
Nace Saratu karki dameni da iyayi na sanki kin sanni me zaki boye min,yawwa idan na samu Miji aure zanyi yawwa ehe yanzu