Showing 90001 words to 93000 words out of 133548 words
Chapter 31 - YAR AIKIN KARUWAI BOOK COMPLETE by Asma Baffa .txt
ciki ya Kama Sabreen tace kudinka nawa ne? Yace dubu dari biyu nan take ta zaro a jaka ta bashi tana godiya Suka tafi,Jamcy tace matsala ta Kare shike nan suna ta murna, Suna tafiya bokan ya turawa Jamcy dubu hamsim ta accnt dama tace ga abinda zai karba idan sunzo sannan zai bata kasonta shine ya bata nata Jason cikin kudin Sabreen.
Sai dare 9pm suka dawo lokacin ma ni nayi bacci a dakina,Nawwar kuwa Yana Shirin kwanciya shima sabo da jirginmu da asuba zai tashi, Da tun 4:30am na tashi tuni nayi wanka da brush na shirya cikin sabuwar Abayata baka me adon silver nayi Rolling kamar wata balarabiya na fito bayan nayi sallar Asuba na fito dauke da yar jakata rataye a kafadata,takalmi da jakar Silver,kayan mu Kuwa da Muka eba kala biyu ne rak yace ma siya can cikin jakarsa na zuba m,Ina Fitowa Palo ya fito shima.
Fresh milk da Lipton na dan tafasa shi Kuma ya shiga sanar da Sabreen,Sabreen sabo da tana Shirin sa Masa magani a abinci ko baccin kirki kasa yi tayi,Yana shigowa tashi daya yace Sabreen ta mike zaune Zumbur shi Kansa yayi mamaki,yace zamu tafi aikin Hajji anjima kadan jirginmu zai tashi,Gaban Sabreen ya Fadi tace amma ya baka fada min ba tuntuni sai da zaku tafi ni dai Kawai ka daukeni banza wofi a wajenka Allah ya Isa cutata da kake Yi a gidan nan ta fashe da kuka sabo da kayi Amarya shine kake wulakantani,Tsaki ya ja ya juya zai fice ta rike rigarsa tamau wallahi baka Isa ba na gaji da wulakancin da kake min a gidan nan,rigarsa ya fisge ta sake fisga ta rike Yana juyowa ya dauketa da Mari Wanda ba shiri ta sake shi ya juya ya fita abinsa Yana masifa,a zaune ya ganni Ina Shan tea dina na fresh milk da bread da ragowar naman jiya, Ina jinsu suna fada da Sabreen ban nuna naji bama nace zaka Sha? Wanda nake Sha ya dauke tare da shanyewa yace ashe da dadi,ragowar na tsiyayo na ciko Masa cup na hada Masa da sugar nima na sake hada ragowar da ya rage Muka zauna Muka ci Muka koshi tare da kuskure bakinmu,na dakko chewgum Orbit na bashi biyu Nima na tauna biyu na maida sauran jaka yace muje Saura 15mt a fara screening, driver ne ya kaimu airport har an kusa gama screening muka bi layi aka mana sai jirgi, sit dinmu daya Ina gefensa sai Selfie nake Mana da videos,Kaina na shiga dauka Ina video nace Alhmdllh.. Alhmdllh... Alhmdllh Allah ya sauke mu lafiya Allah yasa muyi hajji mabruk,dariya yayi yace ba saban ba duk kin dame mu, pics da videos na zaba masu kyau na maka a WhatsApp nayi status harda sauran social media dina na saka,Wise suna can su tuni kullum Ina ganin nasu a Madina Kamar mutanen kirki,ai suna ganin Status dina Suka ce mayyar aure gata ga mijinta tare Suka taho babu shanawa kullum ya manne Mata Kai masifa,Sera tace ai Rabi tana ganin ta kanta da aure,tana Shan wahalar auren nan.
Muna sauka a Jeddah madina Muka nufa Muka,kwanan mu biyu na nemi su Sera nace mu hadu a masallacin Muka hadu bayan mun fito daga Raudah, Muka rungume juna Nawwar Manniru yana gefe na,Star tace kunzo lafiya ya akaji da sanyin tiles dariya ta kwacewa Nawwar Kamar bamu San tiles ba,nace wlh ana Haka ruwan Saudiya yake dama malam kana wanka Yana darewa a jikinka,Laaaa ai haka Nima na gani ruwa baya Zama a jikin mutum in kina wanka kina zubawa Yana darewa malam, Wise tace, fatan kina cika cikinki ki da zam zam,wa zaiyi Wasa da zam zam ma samu ya wanke Mana zunubi, Kalli yanda fuskar mu tayi hasken musulunci to Sallah kullum ba fashi munzo garin Manzo,Star harda rera Mana wakar kasida ta yabon manzo baiti Daya tace a Kano na iya ta,Muna ta nishadi,Nawwar Yana ta dariya yace na gaji fa a gurguje Muka dinga zuba hotuna da videos muna posting Nawwar yana kallonmu ya tafi hotel dinmu yace sai na taho gida,daga nan siyayya muka wuce muka dinga jibgar Kaya na ubansu banda,sai dare kowa ya wuce masaukinsa,Ina komawa yaga uban siyayya yace kina cinye guzurunki bazan Kara Miki kudi ba,wanka na Shiga na fito nayi Shirin bacci Yana kallona,dama bed dinmu daya gashi karami baya kulani nima bana rike ko hannunsa sai da mu farka mu ganmu manne da juna,saman bed na haura nima gefe,yace wannan kawaye sai kace Yan uwanki ko Yan uwanki baza ki so su haka ba,nace kafata ciwo takeyi wash Allah Ina shagwaba,ba dole tayi ciwo ba Kuna ta uban yawo
Mikewa yayi zaune a saman bed din yace muga kafafun ya jawo kafafun tare da dorasu a jikinsa Yana daga zaune,sun birge shi farare masu kyau luwai luwai dan matsa min su yake a hankali Ina Jin wani dadi har wani lumshe Ido nake yi,yana min massage sai da na Fara bacci sannan ya kyale kafar ya kwanta bacci,juyawa nayi tare da rungume shi sosai,da kyar ya samu bacci ya kwashe shi sabo da abinda yake ji a kaina shi Kuma sabo da yanda yake jina a ransa baya so ya kusance ni yajini ba virgin ba zai ji haushina ya rasa sukuni shi yasa yake tsoro.
Haka sosai yake karanta min adduar da zanyiwa kaina da ma wasu har da shi Kansa kuma Ina Yi din akan halin da nake ciki,haka har Muka sauke Aikin hajji Muna makkah Muka gama iya kwanakin da Muka samu sannan Muka yo gida abinmu.
Sabreen kuwa tana gida in Banda shaye shaye ba abinda take yi sabo da ta samu kudinta na aikin Hajji,ta hakura da kashe kudinta wajen boka daga gwadawa sau Daya yanzu tace da tuggu zata fidda ni,tare da neman shawarar Jamcy,Ni Kuwa satina Daya da dawowa naje na yini a wajen Mami.
Sai Yamma likis na fito da ma da motar Nawwar na zo Ina Fitowa na hadu da Baffa tare da Amaryarsa,dake makira ce ita sai tace Wai ba Amaryar Nawwar bace? na juyo nace ae, shine baza ki je ki gaishe ni ba ku fa yaran zamani haka kuke baku da tunani,a gaban Baffa nayi mata wani kallon banza sannan na furta ai baki Kai aje a gaida ki bane ke din banza ke Ina tunanin naki yake har kina da tunani duk abinda kayiwa wani sai an Miki Kuma wlh dan kin San ya juyawa Mami baya a banza mu mun San kafin ai daram akai kwandi a Sannu Allah zai tona miki asiri,Baffa yayi mukus Yana so ya taka min birki Yana tsoro na da kunya sabo da yasan me ya aikata, Ummin Haidar tace Baby kana jinta fa wannan bai kamata a bar Nawwar ya zauna da ita ba,Tsaki na ja sabo da nasan tun zuwana Naga Baffa Kuma na gaida shi gaisuwa ta mutuntawa Kamar komai bai faru ba shi yasa na shige mota abina, Su Iyamami basu San ma Ina zuwa gidan ba tunda na Mata tatas ko ta ganni bata fitowa
Baffa bayan na tafi muzurai ya Fara tare da furta Zan dauki mataki a kanta Kamar yanda Kika Sanni to tunda ta taboki ta jawa kanta,Ummin Haidar tayi Murmushi tare da rike hannun Baffa suke shiga mota driver ya ja Suka fice.
Sai da na koma gida washe gari na gama gyara gidan nayi girki,wanka na sheka naci gayu cikin kana nan kaya,Ina Palo Ina kallo naji motar Nawwar driver ya dawo da shi,mikewa nayi Yana shigowa na furta oyoyo tare da fadawa jikinsa tare da furta Sannu da zuwa,Sabreen ce ta fito sabo da ranar girkinta ne,ranta ne ya baci tace ke malama mayyar maza yau ba kwananki bane,juyowa nayi nace ohh kiyi hakuri na manta na saba ne,Tsaki taja tare da zuwa ta bangaje ni na kusa kaiwa kasa na rike kujera,fuskewa nayi kallona yayi Muka hada Ido ya kashe min ido Daya tare da furta min sorry,Sabreen kuka ta saki tace baka da hurumin Mata kallon so ranar girkina wlh bazan yafe ba ai kallo na ne ya zu ni zaka yiwa kallon tunda nice da girki,yanzu ni zaka yiwa wannan kallon ba ita ba,Nawwar yayi dariya yace kallon ma ni da idona kina da ilimi Kuwa haka akace kallo ma baza ka yiwa wata ba,ai Ina gani kallon kallon soyayya kake mata wato kayi missing dinta muje ta rike hannunsa Suka juya zasu tafi,juyowa yayi Yana daga min hannu,Ido na kashe Masa Ina Masa fari,Muna Murmushi Muna ta magana da Ido,abincin da na dafa na tarra na kwashe komai na kaiwa masu aiki maza na ebi nawa naci na koma dakina,Sabreen kuwa bata Yi girkin komai ba ganin nayi abinci shine tace suje suci abinci sabo da kullum Nike abinci ko ranar girkinta ne sabo da Nawwar nakeyi idan banyi ba to bazai ci abinci ba Kuwa shi yasa yace nayi hakuri na dinga Yi Kawai yau Kuwa bazan iya hakurin bashi ba,shi yasa na bayar da abincin na wanke kwanikan na ajiye,gajiya nayi da Zama a daki na fito Ina kallon film,sai kuwa ga Sabreen ta fito,daga baya Nawwar ya fito ta duba dining Babu abinci ta duba kitchen taga komai a wanke das alamar ba komai.
Dawowa tayi tace Dani Ina abincin? Mikewa tsaye nayi nace kanwar uwarki ce ni ko ta ubanki,ke na gaji da abinda kike min,In zauna kullum na dafa muku abinci Kuma ranar girkinki baiwar uwarki ce ni, ko siyena kika yi banza Jahila kidahuma wacce bata San me take ba duk haushi nake ji Nawwar Yana tare da ita kishi ya rufe min ido,harzukowa tayi da masifa Nawwar ya daka Mata tsawa yace ke bana son hauka idan kina son Miji me ya hanaki kiyi girki ko yaushe ita ke abinci bata taba gajiyawa ba sai yanzu ke har kina da bakin magana,wayata ce tayi Kara Wanda tana kusa da Nawwar kallon screen din yayi yaga an rubuta My love,Ido ya zaro na Mika Hannu Zan dauki Wayar ya rigani dauka tare da dagawa ya Kara a kunne,Muryar Namiji yaji yace Hello Babyna ya Kika je gida jiya? Kinje lafiya,ya gajiyar jiya,kiyi hakuri jiya na gajiyar dake da yawa kece kina da dadi,Allah Miki baiwa Sweety gaki da ruwa.....datse Wayar yayi nan take Muka ga idonsa ya canja,jikinsa na rawa ransa ya baci,kallonsa nayi nace lafiya wace ta kirani ko su Sera ne na Kai hannu Zan karbi Wayar a hannunsa ya mike a wani hasale ya zai haura sama,na mike tsaye, Sabreen nan take ta washe baki ta gyara Zama,idona ne ya cika da hawaye nace wai mene akace ne na sai Mika Hannu Zan fisgi wayar Mari ya sake kwasheni da shi,Raina yayi mugun baci yanzu abu kadan ya dinga dukana wlh bazai yuwu ba Dole na dauki mataki na kwaci yanci na,yana huci yace baki da hankali mahaukaciyar Ina ce ke ashe baki San me kike ba,waye wannan dama jiya ba gidan Mami Kika je ba iskancinki Kika tafi da aurena ki dinga Neman maza,Kuka na fashe da shi tare da durkusawa har kasa nace wallahi ban San komai ba gidan Mami Kawai naje na rantse da Allah,lier ya furta ya mike zai bar wajen na rike Masa kafafu Ina kuka Ina furta wallahi banje ko Ina ba babu abinda na aikita,juyowa yayi yace waye zai je ya Miki saving number din kato da My love waye zaiyi haka,kin bani mamaki ya juya ya haura samansa, Sabreen shewa ta saki tace neman maza har a gidan miji ana da aure tsiyar karuwa kenan shi yasa ake son ka auro Yar asali Yar dangi ba Yar kwashe kwashe ba,yo Yar tsuntuwa ai kowa yasan Yar shege ce oh anyi gado,anyi gadon iyaye ta juya tare da haurawa sama.
Nawwar ya zauna a gefen bed ya rasa inda zai sa Kansa bacin rai ya Masa yawa sai tunanin maganganun da gayen ya fada yake yi,Ni Kuwa a nan na zauna Ina mahaukacin kuka Kamar raina zai fita har na gaji na tashi na haura sama dakina na fada saman gadona in kuka ranar ban iya bacci ba shima Nawwar haka,da safe ban fasa aikina ba nayi duk abinda nake Yi har abinci,dakinsa Kuwa ban leka ba gudun wulakanci,steps na hau shi Kuma ya taho zai sakko ya Sha wanka ta jikinsa na raba Zan wuce ya bangaje ni nayi baya na rike karfen steps din da kyar tsaki ya ja ya wuce ya fice abinsa ko abincina bai kalla ba.
Sabreen ce kawai ta fito ta danni abincin da na dafa tace an gaisheki me gidan bai so yanzu,bata ita nake yi ba,dakinsa naje Zan gyara naji ya kulle gam,dakina na koma na zauna Ina ta tunani har ga Allah tunda Muka je Makkah naji Kamar an yaye min komai naji Ina son aurena bana son barin gidan sannan naji rayuwar bariki bata birgeni ko kadan bazan iya bada kaina ba,ko asirin ne na Dagaci ya karye oho.
Ina zaune a gidan kullum Nawwar baya ko kallona har ya gaji ya bani wayata amma baya ko kallona,damuwa ta min yawa kullum a Addua nake da sallar dare kuka Kuwa baya yankewa a idanuna.
Ina gida yau Sabreen ta fita unguwa shi Kuma ya fita aiki da yamma likis Wanda nasan gaf yake da dawowa, Ina zaune kawai naji an turo kofar Kamar Wanda ya shigo yasan code din kofar,wani saurayi ne matashi baki da shi ya shigo na mike tsaye Zumbur a tsorace Ina cewa waye kai Malam,My love ya furta,ihu na saki Ina cewa dan girman Allah na rokeka ka fita karka kashe min aure wlh Ina son mijina Ina son aurena yanzu, ban sanka ba Kawai kace min your love Dan Allah,Karar motar Nawwar naji hankali na ya tashi na taka zan gudu,mutumin nan ya damko ni ban San waye ba ya rikeni Kam tare da jawoni jikinsa yana kissing din dokin wuyana dake baya na juya Ina kokarin guduwa Ina dura Masa ashar,Hannu yasa ya toshi min baki yane cewa Ina sonki Baby kina da Dadi bana iya rabuwa dake,Nawwar Yana shigowa mutumin Yana furta shekaran jiya fa kin jiyar dani dadi me yasa yanzu Kika ki,kafin mijjnki ya dawo munyi mun gama ko kin manta yanda muke yi, Yana Jin motsin Nawwar ya sakeni da sauri tare da ja baya,ni nasan Nawwar ya shigo tunda naji kamshinsa,shima ya sani da gani kasan turo shi akayi amma Nawwar bazai gane ba,a wajen Nawwar ya sandare,Ni Kuwa zubewa nayi a kasa na rushe da wani irin kuka, Saurayin tsayawa yayi Yana kallona tausayina ya kamashi shi kanshi sai yaji bai kyauta ba, Amma tuna kudin da aka Masa Alkawari sai ya bar gidan da gudu Nawwar Yana tsaye Kawai ya haura sama,nima ban ce Masa komai ba Kawai kuka nake yi sabo da bani da abin fada, Gajiya nayi na tashi a wajen Kawai na nufi dakina Ina share hawayena sabo da zargina da akeyi dole kowa ya yarda shi yasa Kawai na zabi wasu kayan na cika akwatina na fito na ja Allah yasa ba kowa a palon na fice na,Masu aiki suna kallona na fice na bar gidan ina kuka.
AsmaBaffa
08061929616[7/17, 3:09 PM] Yar Aikin Leemah❤️: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼
LITTAFIN KYAUTA NE
76-80
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA DUKKAN YARAN TSUNTUWA
Page naki ne
Mom Sani
Gaisuwa ga
Ummu Lateefah
Washe gari da rana abinci na gama Nawwar baya nan sai na zuba nawa a plate Zan ci Ina sauri naji wayata tana Kara ashe Sabreen tana leke na tana ganin na haura sama ta fito lokacin yazo dai dai da shugowar Star gidan ita kadai unguwa taje ta biyo gidana zata ci abinci,taga Sabreen Sanda ta fito ta nufi kitchen yanda take kalle kalle ya nuna bata da gaskiya,Kawai sai Star taji bata yarda da Sabreen ba wayarta tana hannunta ta bi bayanta da Sanda itama ta leka kitchen din,ganinta tayi ta fito da wani garin magani fari tas,da Sauri Star ta fara daukanta da waya sai da ta Gama dauka sannan ta shigo kitchen din,Sabreen a gigice ta juyo tunaninta Rabiah ce, gumi ne ya Fara keto mata jikinta ya Fara mazari,Star gwanar daukan abu ne a waya,wayarta ta dannowa Sabreen video dinta tana zuba magani,tsoro ya kama Sabreen a kasa ta zube tana rokon Star dan Allah ki rufa min asiri
Star Murmushi tayi tace kina so na rufa Miki asiri? tace dan Allah,to fada min maganin mene kike zubawa,Sabreen ta tsaya inda inda tace to bari naje na nunawa....kafin ta rufe baki Sabreen tace ta kisa ce idan an ci a hankali take kashewa mutum kayan cikinsa sai ya Fara cuta slowly slowly har ya mutu,Star tace oh my God yanzu rashin imanin naki ya Kai na kisa? Akan kishi Wai me yasa mata muke haka ne akan kishi sai mace ta kashe kishiya,miji,ko yaran kishiya banda Wanda ake haukatawa,tace to wannan bayanin da Kika Yi na maganin shima nayi recording sabo da hujja,Kuma wallahi duk abinda ya samu Rabia kinji na rantse kema se ya same ki mark my word in dai Yar uwar mu ta mutu wallahi Wallahi sai kin mutu yanda kika dauki hukunci haka zamu dauka a kanki,Kuma Ina nan zuwa kanki wannan abin da Kika yi ba banza ba,Sabreen ta mike ta fice sum sum,Fitowa nayi na iske Star a kitchen ta juye abincin da na zuba a plate cikin Leda baka tana wanke plate din,nace wai dama har kin karaso? Ae tace min kawo ,nace ya naganki ranki a bace? Naga wucewar Sabreen itama Kamar ranta a bace zaginki tayi naci uwarta,ke dalla rufe min