Showing 66001 words to 69000 words out of 133548 words

Chapter 23 - YAR AIKIN KARUWAI BOOK COMPLETE by Asma Baffa .txt

04 Dec 2024

6580

tayi tana mamaki sigarin da take Sha ta kashe tace lafiya fada min menene? nace cikin kuka Sera korata yayi Wai karuwa ce ni Kuma Ina sonsa da gaske wallahi na sake fashewa da kuka,Sera ta fashe da dariya tace heyyyyy Hajiyar love me na fada miki,me na fada Miki karuwa bata aure ko kinyi baki Zama lafiya Sabo da zarginki zai ta Yi,danginsa baza su taba sonki ba,kowa zai kyamaceki ko da kin shiryu baza a fahimci hakan ba,rayuwar mu ba Daya bace data kowa bamu da kunya bamu da tarbiya,Kuma daga Namiji ya Gama cinyeki karshe korarki zaiyi karya yake ba son Allah yake Miki ba,gashi kin kashe abinda Kika tara a gidan marayu sai kiyi hakuri a sake sabon lale karki Manta karuwa bata taimako abincina bazan baki ba so kin Saba dare yayi tunda ke kullum tasallah ce sarkin Sallah sai kiyi Sallah a fara Shirin fita Neman customers,nace bazan iya fita ba ni in Banda tunaninsa babu abinda Zan iya hasalawa,kin San Allah ba Wasa nake ba abincina baki ci jiya Kika ce min dubu biyu gareki,nace yanzu ma Saura dari biyar Sera tace to gwara ki tashi.


Ba yanda na iya tashi nayi bayan munyi wanka nayi sallar Isha nayi adduoi nace Allah ka daidaita tsakanina da Nawwar ka sa Masa salama a zuciyarsa,shiri nayi sosai na saka guntun Bumshort da riga me dogon Hannu me santsi gabanta da botin Fara da zanen fulawa baki,wandon Kuma Baki,takalmi da jaka bakake na saka hular gashi na me tsada Dana barsu a dakinmu,Muka shirya tsaf 11:30pm Muka fita,na tsaya a cikinmu gamu nan reras damu Mata iri iri daasu kyau da munana ana ta dauka,Ni Kuwa na tsaya a wajen kamar gunki Ina tunanin Nawwar,Seraline ce ta daki kafada tace love no dey tire you? Haba ki saki ranki fa Hmmm, hayyacina na dawo na daga hannu Ina cewa customer,Nyash dey,big breast dey, duwawu for sale,local government for sale,come with your cash hot lady dey,Su Seraline duk sun samu customers Ni Kuwa na gaji na tsuguna a wajen na hada Kai da gwiwa na saki kuka,sauran matan ko wacce ta tabe baki basu kulani ba,mota ce ta tsaya a gabana fyalleliyar da ban taba gani ba na mike wani dattijo me Kamala ya sauke glass yace shigo,kallonsa nake Yi kamar na sanshi,yace Yan Mata kinyi min,nace Alhaji dama harda irinku Kuna lekowa nan? Yace jefi jefi mukan zo,a tsorace na bude gaban mota na shiga,yaja muka tafi,Yana kallon cinyoyina Yana lashe baki,Hannu ya Kai zai shafa na rike hannunsa da sauri,na bata rai,yace lafiya? nace farashi na da tsada,yace Nawa kike? Nace na Kai million daya, na baka kaina saida million idan baza ka iya ba saukeni,Alhaji ya kyakyace da dariya yace na Kara Miki 2million nace good Man,har ga Allah tsoro nake ji sabo da ban taba yi ba,ganin haka sabo da ya sauke ni sai ka Kara min million daya,yace an gama ai kin min ni ko nawa ne Zan biyaki Yana dariya, wani rantsatsen hotel ya kaini cikin lafiyayyen daki, Ina zaune nayi tsuru tsuru Nawwar Kawai nake tunani jira nake yi na gudu


Muryarsa na tsinta yace bari nayi wanka ko nace to,wayarsa ce tayi Kara ya daga da sauri naji yace sorry zanyi waya da Dana,karaf naji yace Nawwar wallahi kaji na rantse idan har ka sake dukan Sabreen sai na tsine maka,akan Kawai ta sake daukan kudinka tayi cefane,baka bata ne shi yasa,Nawwar yace yanzu Baffa ta daukar min 2million ban sani ba dollars Dina fa ta kwashe tasan na mene,to kaji me nace kayi hakuri akan million biyu sai na biyaka tsiyarka banza sakarai ya kashe wayar,gaba daya zufa ce ta lullubeni duk kuwa da ac din dake dakin,naji har muryar Nawwar a waya wallahi shine,Baffa ya shige wanka bai kula da halin da nake ciki ba,Yana shiga na tashi na dauki jakata na lallaba na bar dakin a hankali a nutse Kar ace wani abu nayi na rashin gaskiya na bar hotel din da sauri Ina barin hotel din na shiga taxi sai gida.


Baffa Kuwa Fitowa yayi tsirara haihuwar uwarsa Yana cewa Baby na fito yaga wayam ya duba ba kowa bakin ciki ya Kama shi yace ya zata min haka gashi yau bazan iya jurewa ba ga Amaryata bata nan,akan ya kusanci Mami gwara ya nemi karuwa dama haka yake Yi mutum ne me tsananin sha'awa da bukata ko yaushe baya iya jurewa ko kadan,haka ya rasa ya zaiyi sai waya ya bugawa tsohuwar karuwarsa Star,tabbas Star ta gidanmu ya Kira tasan akwai kudi ai da gudu ta bar motar Wanda ya dauketa tace a gida ake nemanta ta tafi wajen Baffa a hotel din Dana bari tirr da masu Hali irin na Baffa na dawo gida na kwanta Ina ta mamaki amma ya damu sai na bar gidan dansa ashe shima dan hannu ne.


Ina kwance a dakinmu nayi lamo abin duniya ya min zafi Banda tunanin Nawwar ba abinda nakeyi na kwanta Ina ta sharbar kuka,kofa naji anyi knocking sai ga Malika ta leko tace kunyi bako gashi zai shigo Kawai naga Nawwar ya shugo,kaina na maida saman katifa naci gaba da kukana,Murmushi yayi yace to kukan fa? Nayi masa banza,baza ki kulani ba,yace bari na bar Miki dakinki,da sauri na dago Ina hawaye nace ba...ba...bakina nane ya jawo min,da me? da nayi maka kiss,dama kace na daina na daina naki ji Ni ban San me yasa nake maka ba,na daina kaji kayi hakuri na fada cikin kuka,Bai ce komai ba na sake cewa ka yafe min na fashe da kuka tare da tashi na rungume shi ta baya,yace wayyo Allah ya rintse Ido da karfi ya furta zata kasheni a ransa a fili yace yanzu fa Kika ce kin daina a haka zan yafe miki,jikina na janye da sauri ya juyo muna facing juna yace fada min Rannan da bana nan Ina Kika je min da mota Kika Yi kwana biyu?


Hannuna na yarfe Kamar wacce ta Kama wuta a hannun nace baza ka min fada ba? Yace yeah,nace karya Muka yi da motar Muka je kauyen Kano can inda na girma,Ido ya zaro yace Kano a mota? Nace ae Ina murmushi,kin iya mota dama nace kaji ka Ina Yar bariki ai mu komai mun iya ko Dan karya,ai mu Yan karya ne,In fada maka a motar Wise Muka koya itace ta koya min,da Seraline Muka je,Muka Yi dinkuna masu tsada kala uku,Muka tafi Kano Saurayin Sera ya Kama mana dakuna biyu ni Daya na kwana ita Kuma tare suka kwana,ya ganni yace Nima Yana ciki Wai ta bashi ni ya shiga local government dina zai biya Mata Makkah,Dan majalisa ne amma nace idan taje Makkah da kudin bariki to ba lada,tace ai Dan tayi show zata je tayi pic ta saka a media,in fada maka da Yamma na Kai mota wajen wanki taci wanka na Sha shaddar nan ka ganni kamar Yar gomna wanka ya Kai wanka, nace dole muyiwa maza kwalele masu zaman banza,a birnin nan Muka dinga burga da motar nan naci glass munyi pics a iPhone din Sera Zan tura maka kaga wankan ko Kai wallahi sai kace Excellent, Muka dinga bi majalisa Muna dan yin parking mu fito mu dan shiga shago muyi Yar siyayya mu fito,kaga idon maza duk an zanci yaran masu Hannu da shuni ne basu San da zasu ji tarihinmu to wallahi jefe mu ya kamata yayi,dariya ta Kama Nawwar Jin shirme Muka tafi Muka yi,Ina bashi labari nima Ina dariya cinyarsa na dakawa duka Kamar kawata mace Ina cewa sai da Muka girgiza maza masu zaman banza sannan Muka nufi kauyen,wayyo na saka hannuna na sakalo ta wuyansa nace zo kaga Rabi a Kauye ta waye dariya Nawwar ya saki ba shiri nima nayi dariya tare da dan dukan cinyarsa kadan da sauri nace sorry Ina dariya Ina sake dukan cinyarsa kadan Kamar dai yanda akeyi da kawa mace,yace to Ina ji nace haba na dinga fyalla Naira Ina yiwa Dagaci da su Gwaggo kwalele,Kuma nace Ina nan sai nayiwa Dagaci fidiyar dan akuya sai na koma Zan fita da fitata.


Kudin da ka bani na cefane naje nayi karyata a Kauye Dagaci ya turo su Gwaggo suzo suga yanda na koma a gabansu ko kallonsu banyi ba ban ma nuna na sansu ba,nan dai na bawa Nawwar labarin komai har zuwan mu gidan marayu nace Naga Yan Uwana na fada Masa abinda Muka siya Muka kai,Yana Gama ji yace uhm ta wani bangaren kunyi dai dai ta wani bangaren Kuma Baku yi ba me yasa kuka je kauyen? nace karya ta kaimu,yace ai zarginku za ayi Kuna karuwanci za ace zaman kanku kuke yi tunda an San ba miji ne gareku ba,nace ai basuyi karya ba,mu abin kunya baya Muka bashi ba gaba ba,ransa ya bata sosai ba Wasa yace yanzu kaf kudinki sun Kare? Nace ae yace good tunda a gidan marayu Kika karar ko ba komai kinyi abin kirki,kayi hakuri abinda nake maka ban San Sanda nake Yi ba sai naji kamar ana ja na,ya sake daure fuska yace kina so na hakura? da sauri nace ae,yace ki min alkwari duk abinda nace Zaki Yi babu musu Kuma dole kiyi,nace nayi Alkawari,yace in na furta ba musu ya Zama Dole,nace komai na yarda Indai zaka hakura,yace Marry me,Ina ji na furta kace me? Nace ki aureni,ji nayi kamar ya zuba min wuta a jikina ni bana son zancen aure a duniya sai naji tsananin damuwa daga lokacin na rasa farin ciki,nace ai ban San aure zaka ce ba ni bana son aure ko mene na yarda zan baka a duniya banda aure,taya Zan taima miki taya Zan zauna dake babu aure kina rungumeni kina min kiss ba aure tsakaninmu idan munyi aure Kuwa babu damuwa sannan ni karki tunanin sonki nake bazan taba iya rayuwar aure da karuwa ba,bazan iya saduwa da Karuwa ba inda maza da yawa Suka Shiga ba bazan iya Kai kaina nan ba,sannan magana ta Allah zai wahala na yarda da Yar bariki ko yaushe Ina zarginta,Kawai Ina so ne ki taimaka min kawai na karya dokar gidanmu daga kaina a daina auren dangi auren dole shike nan in kin min haka muka dan zauna komai yayi settling Zan iya sakinki in kina so,sabo da haka ko kin aureni ba sex ba feeling karki ji komai a kaina so ko wani sex bana so kisa a ranki babu wannan Kawai ga abinda nake so ki yarda ki bada Amanna na aureki shike nan


Sai lokacin naji sanyi a raina nace tunda ba Zama zanyi ba ai da sauki,yace Kuma sai kinbi dokar aure abinda Allah yace kin nutsu,sannan auren nan yaki ne sosai kafin ma Baffa ya amince ayi shi,nace Baffa ne matsalar auren? Yace kwarai sai kinyi hakuri,Murmushi nayi nace wallahi yafi komai sauki Kuwa karka damu ka kwantar da hankalinka kaje gobe direct kace aure zaka kara idan ka fada masa Kawai ka kirani ka sanar dani, dariya yayi ya zaci shirme na ne a ransa yace wannan bata san waye Baffa ba,ai shi baya Wasa da kowa baida lokacin kowa ma daga aiki sai amaryarsa,a Raina ni kuma nace oh Namiji ba a mallakarsa dole ta wani bangaren Amaryarsa ta mallake Baffa akan Mami ta Zama ita ce on top amma bata mallake shi akan karuwai ba,ta zaci ita daya ce,ta hanashi kula matarsa ta sunna amma gashi Yana bin na banza,yace kin amince? Nace tabbas Ina da waliyyina a Kauye can kano, Kawai ka shirya ka fada Masa sannan ka sanar min,yace mun shirya to,Murmushi nayi yace wannan Yan iskan kayan da Kika saka fa? Nace shakatawa nake kafin na koma prison gidanka,yace bikin nan fa bazai wuce nan da sati biyu ko Uku ba Kawai ku shirya abinda zaku shirya ku fada min Baffa ko ya yarda ko bai yarda ba za a daura bai sani ba,nace karka damu da Kansa zai karbi aurenka,duk Wasa yake gani,skert na dora a saman wandon Nawa na rako shi har jikin wata motarsa red, kudi ya dakko 50k ya bani yace kudin abinci na sanki da shegen zuwa Saloon,nace to ya zaka Yi ka hadu da Yar duniya Yar bariki Local government guda muke siyarwa fa,yace jeki ni kudin na rike Ina fifita da su Ina ce masa Saurayina Dan dolo ya bada kudi ko nono bai tabawa ehhh ehhh ahhh nabi wani kida dake tashi a layin Kamar zai fasa dodon kunne da kyar ake Jin magana,na koma gaban motar Nawwar na dinga karkada masa mazaunai ina fifita da kudin,naki matsa Masa yayi reverse ya fita a haka ya bar layin,Malika ce tazo ta dana min duka ta Kara gaba dariya nayi nace yanci dadi, Santana yace kekam Karuwanci ya taimakeki kinfi kowa sa'a a gidan nan har yaushe Kika Zo garin nan da tsumman kayanki kina warin Kauye Wai gashi kinfi kowa samun me kudi kowa yazo neman ki sai me kudi Kuma sai kinwa kowa yanga,nace haka lamarin Allah yake wani baya sonka ya jefar da Kai wani sai yayi kuka akanka na wuce daki na kwanta sai bacci.


Amarya Gaji Kuwa amarci Kawai suke Sha da Danbinni,angon bata wani so da kaunarta yake yi Yana Jin bazai iya rabuwa da Gaji ba,itama ta dan hakura ganin yanda yake bata kulawa,Zayya Kakarta da kanta tazo gidan ta kwantar Mata da hankali tace ba a kishi da fada baza kici nasara ba ai kwantar da Kai Zaki ki dinga hada Mata tsiya ta karkashin kasa cikin tuggu,sannan sai a hada da malamai ayi Mata Wanda zata bar gidan nan ai baza mu taba Zama ba baza mu barta ba Amma karki sake takalarta da fada ko ta kulaki da fadan ki maida abin Wasa zata ci ubanta,Zayya taji dadi tun daga ranar Gaji ta samu lafiya da Zayya ta zaci ta hakura,shima Danbinni haka har Yana murna, Kakar Zayya Kuma wani rubutu ta kawo wa Zayya a boye tace gashi kin ganshi sai kinyi wanka Zaki shafe jikinki da shi ki tabbatar ranar ya sadu dake in kinyi shike nan ita da miji shike nan,Gaji Kuwa washe gari Mairo tazo wani abin Hannu Kamar awarwaro na guru tace gashi inji Baba yace a hannunki Zaki daura babu ke babu masu tsafi ko me kishiya zata Miki a banza,yace karki Wasa da shi sai da ya siyar da gonarsa ya iya karbo shi tsada gare shi kusan dubu dari biyu ya kaiwa Malam sai da aka yanka rakumi,Gaji nan take ta daura abinta a hannu, duk akan miji suke sunnawa kansu tsafi,Zayya tana ta faman kashe kudi magani yaki cin Gaji sai amarci da love akeyi Kamar ma Kara kaunar juna suke yi,ganin haka Zayya ta gaza hakuri ta dawo da bala'inta,Gaji ma ba jira,Haka Kawai Zayya tayi girki Gaji ta fito ta bude miyar ta dandana tace gishiri yayi yawa ga shegen yaji ke a gidanku haka aka koya miki taki tarbiyyar kenan? Oh no wonder goyon kaka ce tasa kafa ta daki tukunyar Miya ta watse a kasa zayya ta taso Suka kaure da kokawa har waje kofar gida suna kokawa,mutane sun cika damkam ana kallo anyi anyi su bari sunki ji,Gaji harda ja da baya kamar wata rago ta taho da gudu Zayya ma ta taho Suka hade gwaraf Kara Suka saki zafi ya ishe su ko wacce tana sosa goshi da hanci,aka kwashe da dariya da ihu Suka sake rukumuwa Gaji tace sai na kashe ki nice ajalinki,Zayya tace nice ajalinki kafin ki Gama dani zan gama Dake bazan yarda ba Danbinni ya dinga Kwanciya dake Yana cika gida da ihu ba Ni Kuwa sai yayi Shuru a dakina,gaji tayi tafi tace heeee ba Maggi baki da Maggi Ni Kuwa ajino moto ce harda curry,Mutane da Yara sai ihu da shewa akeyi ana dariya zamani na waya ana ta musu video kafin kace me Abu ya cika tik tok sai gani akeyi har WhatsApp wasu sun saki ko waccensu ba mayafi suna ta fada kamar kaji anci dariya ganin Gaji tana dukan kirji tana cewa itace Maggi ajino moto harda curry ana ta yanko wajen ana sawa a media,Haka ana saka wajen zayya da tace ita Danbinni baya ihu da kuka idan Yana kwanciya da ita sai Gaji,Danbinni ransa ya baci ganin matansa sun baza media a ranar da kyar manyan Mata suka sasanta fadan.


Nawwar ne ya samu Mami da zancen aurensa,tace mashaallah Allah yasa ka Zama sanadin shiriyarta amma ka dakko da zafi zaka jawo min bacin rai,Matukar Baffa yaji zaka auri bare to mun shiga Uku ba zai yarda ba watakil ma ya sakeni,Nawwar yace Wai Rabiah tace na fada da Kansa ma zai daura auren ban San dai mene ba amma na yarda da ita ko ma mene gwara Kawai ayita ta kare,Mami tace tab Nawwar bari na hada kayana nayi Shirin barin gidan Yana cewa tafi sai tafiya, Sultana suna Jin labarin Nawwar zaiyi sure Kuma bare wai ma karuwa Rabiah wacce akan zamanta a gidansa Kawai an kusa ayi yaki a gidan su kansu sun San zaman Maminsu ya Kare a gidan tunda komai danta yayi a kanta yake karewa tuni Suka Fara kuka suna addua.
Nawwar Kuwa sai da ya tara kowa na gidan har Sabreen sai da ya Kira ga Baffa,ga Papa,Mama,Iyamami,ana jiran aji Nawwar me yazo da shi ya tara kowa haka, Mami tayi Miki Miki kusa da yaranta,Nawwar Kuwa Yana gaf da palon ya kirani a waya lokacin na tara su Sera na sanar musu komai har daukana da Baffansa yayi zaiyi sex dani,Star tayi shewa tace ai ni na dade da sanin Baban Nawwar Yana bin Mata tsohon kwartona ne shine ma ya siya min gida a Kaduna ya kaini makka,na more shi sosai Kawai fada Miki ne banyi ba,wannan ta kwana gidan sauki blackmailing nasa zamuyi mu biyu ni da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login