Showing 102001 words to 105000 words out of 133548 words
Chapter 35 - YAR AIKIN KARUWAI BOOK COMPLETE by Asma Baffa .txt
cin abinci safe rana da dare,sannan baka da nutsuwa duk ka rame na rasa gane Kan abin sannan naji wajen su Iyamami suna min dariya Wai ka saki Rabia ta kawo kwarto gida,murmushin yake yayi yace ba haka bane Mami Kawai dan fada Muka Yi bata Jin maganata shine fa na Mata fada sai tayi yaji ta tafi ni Kuma banje na dawo da ita ba,Mami tace Kana da hankali Kuwa Nawwar ya zaka bar matarka ta tafi Kuma baka je ba,kuma kasan bata da kowa sai Yan duniya bariki dai zata koma tunda can ne gidan nasu,ashe karya kakeyi ba taimakon nata zaka Yi ba,Mami ita fa tayi tafiyarta,Nawwar baka da hankali gashi nan ka damu kana son Yarinyar nan kaki ganewa ne Kawai,Allah ya kiyaye ya furta, ni bana sonta Kuma bazan so ta ba ni na gaji ma bazan iya taimakon ba na fasa Kawai a bar zancen,Murmushi Mami tayi tace wai me tayi maka ne? yace ba sai kinji ba,tace to ai duk so ne gashi nan baka so aji laifinta Kar wani yayi tunanin wani abu a kanta anyway yanda ka gani koma mene Watarana zaka fada min ni dai na baka shawara ba dai dai bane baka saki matarka ba ka barta ta koma bariki ba Allah zai tambayeka.
Shuru yayi ma Mami Yana cin abinci Yana tsaki har ya gama ya tashi ya fice ya bar gidan,layinmu na bariki ya nufa Yana zuwa ya samu Sera a waje,taje Suka gaisa tace Ina kawata? Kansa ya daure yace wacce kawar taki bayan satinta guda da yin yaji Kuma nasan nan zata zo,Sera tace bata zo ba gaskiya to Ina Kuwa Rabia zata tafi bata sanar min ba,Nawwar ya zaro Ido yace Wai da gaske kike ba nan tazo ba idan Wasa kike ma kin San dai bana Wasa dake, Sera tace tab ai kuwa ita tasan inda ta tafi bata nan gidan wlh,Nawwar yaga fa da gaske ne hankalinsa ya tashi matuka,yace kira Inna kiji ko can ta tafi,Inna aka kira tace bata je ba ko kauyen ma ba Wanda yaga Rabi a can,Nawwar ya rasa inda zai saka Kansa gashi an wuce sati Ina zai neme ta,haka ya koma gida jiki a sabule,Sabreen tana Shan kallonsa sai Dadi take ji burinta ya cika ga mijinta baya cikin farin ciki, Addua da sallar dare ya Fara ba ji ba gani,har aka sake kwashe sati shi kadai ya fara hawaye shi matarsa yake so,a Daren ya tafi wajen Mami sai ganinshi tayi duk ya fada Yana zuwa har da kwalla Ya shiga bawa Mami labarin komai da ya faru tsakaninsu karshe yace Ina ji a jikina akwai wani Abu a kasa gaskiya Rabia baza tayi haka ba shi yasa ban dauki mataki ba ita Kuma Kawai sai tayi tafiyarta ya karasa da marairaicewa yanzu Mami ya zanyi wallahi karya nakeyi Ina sonta ban taba son wata ba Kamar ta kawai na kasa yarda da ita ne ganin a inda na dakko ta farko,Mami dariya tayi sosai tace tun ba ayi nisa ba ka fadi gaskiya,Nawwar yace Mami kina dariya Allah ni Ina sonta bazan iya rayuwa ba sai da ita,Mami ta zuba Masa Ido tare da furta Nawwar In love Rabia ta ciri tuta,yanzu mafita daya kaje ka lallaba kawayenta zai wahala Basu san inda take ba,Mami kije wajensu zasu fi Jin maganarki please,ka bani number Sera din Kawai yace bani da ita,tace to bari na shirya muje da Kai yaji wani sanyi a ransa.
Ni Kuwa zuwansa na farko Sera ta Kirani a Wayar Hajiya Abida ta fada min na dinga murna Ina murna farin ciki nake ji marar misaltuwa amma Jin Shuru bai koma ba naji na koma gidan jiya,Bayan Mami ta shirya har layin Suka je yaci sa'a ya hadu da Star, Bayan sun gaisa ta gaida Mami wacce ta fito ta jingina a jikin motar tana kallon barikin da yanayin mutanen Dake wajen,tace lallai wannan bariki ce ta kirki,Star ai Sera ta samu tace dan Allah kizo mijin Miracle sun zo da Maminsa,wlh tausayinsa nake ji naga Kamar shima ya rame irin Miracle mu hadasu Kawai ko dan halin da Miracle ke ciki,Seraline Fitowa tayi Suka zo wajen Mami bayan sun gaisa Mami tace dan Allah Saratu idan Kun San inda Rabia take ku fada mana kunga harka ce ta aure ba abin Wasa bane please,Star ce tace mun sani amma mufa gaskiya baza a dinga dukar Mana Yar uwa ba,miji ya dinga dukanta yana Mata wulakanci sabo da bata da gata ya sameta a bariki a bagas shike nan da me zata ji da kishiya ko da su Dagaci ko kuwa da halin Dangin miji zata ji ga kuma uwa uba miji haka Kawai wlh baza mu yarda ba idan ba a sonta a kyaleta mu Muna son a barmu, Nawwar ya harari Sera sai da tayi dariya ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa Kika ce baki sani ba,Sera tace tuba nake amma Kar a sake taba mana Yar uwa Suka shiga bayan mota har gidan Hajiya Abida mace me Kamala da mutunci,yayi farin ciki ganin ba a bariki ta zauna ba yaji wani Karin kaunarta a ransa,Suna shiga Haj Abida ta fito Suka gaisa shima Yana palon,tace shine mijin Rabia akace ae,tace Kai mashaallah tayi dace bari na kirawota tana dakinta,tana Shiga ta samu Ina bacci,Fitowa tayi tace ai bacci takeyi,Nawwar yace bari na ganta ya mike tare da shiga dakin Kawai kayana ya harhada a kwati ya fito da su ya saka a mota ya dawo har inda nake kwance ya daukeni Kamar jaririya ya kaini gaban mota ya ajiyeni,Sera tace su a nan zasu yini gidan Hajiya Abida,Mami tace wato mace tafi uwa ni sai dai na zauna a gidan baya tana dariya ta shiga ta zauna Ina ta baccina sanye nake cikin doguwar Riga marar nauyi ta yadi me santsi kaina da hula a Kai me kyau,Mami ya sauke a bakin gate tare da cewa thanks sai nazo,ciki ta shiga tana Masa tsiya,Yana Hawa titi Kamar Zan farka Kuma ban farka ba sabo da na tara bacci Kuma ni Ina da nauyin bacci sosai, a hankali yake tafiya gudun Kar na tashi
A hankali na bude idona bacci bai sakeni ba gefena na kalla na hango Nawwar Kamar a mafarki na zaci mafarki nakeyi idona na murza sosai naga dai ba bacci nake Yi ba a hankali na furta Ina yini,Tsaki ya ja ya kalleni Kawai tare da maida Kansa ga tukinsa,nace baka sakeni ba dama? Kafadarsa na dafa nace Wai Kaine Nawwar ba mafarki nake Yi ba? Shuru bai kulani ba,na sake cewa Wai kaina so nane da yawa haka baka Fushi da ni,Nawwar ne kuwa? Fuskarsa na leka tare da furta Nawwaru...Muka dinga Addua a kanka rabona da nayi Addua tun a Makkah sai da na bar gidanka,su Seraline Suka dinga taruwa irin yanda ake adduar rokon ruwa suna ta Mana Addua zo kaga yanda fuskar mu ke kyallin musulunci sabo da tsabar Addua wani haske goshin mu yayi na musulunci su Seraline Suka Yi wani hasken musulunci adduar da Suka min kaiiiiii gaskiya munyi addini Addua Kamar ba gobe kalli yanda nayi wata Kamala sai fa da na Zama wata Yar kwarya kwaryar waliyya gaskiya na Sha Addua ji nake wani fresh sabo da tsoron Allah
Dariya yayi a ransa Wai a haka shine abin proud adduar tasu ta Dan lokaci a fili ya furta karki dameni ni,nace a hankali yanda bazai ji ba na furta almasifatu kanwar azaba,Ashe yaji ya tambaya me Kika ce? Cewa nayi ka jawo na rame kalleni rama har nono sun dawo wasu gasu nan Allah ya taimakeka baka tabawa da kaga ta kanka ji zaka Yi Kamar ka tsinko dan lemon zaki karami,dariya ta Kama Nawwar ya kasa dannewa sai da ya murmusa,nace tsaya a siyi pad matar taka an jima kadan Zan Fara yoyo na kusa,slow yayi yace ta Kare ne duk yawan wacce na siya Miki? nace ai kyauta na yiwa su Sera Kawai ka siya min wata sannan accnt dina ba kudi ka tura min sannan dinkuna na an dinka ban karbo ba,yasan halinmu da kashewa Kai kudi Kawai parking yayi a wani Shopping mall,nace ka taho da ice cream,kamar bai ji ba sai gashi ya siyo min har ice cream din, ya kawo min,tun a motar na Fara Shan abina,Muna tafiya Wai a Dole haushina yake ji,dariya ya bani nace dinkunan kala uku ne Dan fake fake ne 20k,yace sai kace ke aka zana a jikin kayan,dariya nayi nace ka dinga kyautatawa iyalinka Allah zai Kara buda maka duk nasan komai kanayi karka ji komai kayi komai ba komai duniya ce dole mu baza mu bita a Sannu ba da gudu zamu bi a barmu, nace Addua ta karbu, kunnawa min kida yanzu na warwasa,hmm yace Kawai Yana kallon na kunna kidana.
Sabreen tana Palo ita daya gidan duk dirty kaca kaca amma ko a jikinta sai sallamata taji mun shigo tare da Nawwar, Nace Honey Kauye tayi na gode da barina da kayi naje unguwar nan kaga ko ba komai na gaisa da iyayena da Suka rikeni,naji dadin tafiyar nan kaga ai nayi zumunci,Sabreen a ranta tace wato dama ba sakinta yayi ba unguwa taje Kauye ashe Kuwa akwai bala'i wlh Zan iya kisan kai bari nayi sabon shiri,kwafa ta ja Ina kallonta bata ko kalle mu ba sai da kyar ta kalli Nawwar ta dauke kanta,ice cream Dina naci gaba da tsotsa na Mika Mata roba daya tare da furta uwar gidana ga roba daya nasa hannuna a saman kanta nace wannan gashin ai sai a zaci dambu ne mu rufa Masa wawa,kutmar....keda ice cream din ta kutuntuma min ashariya ko a jikina,shi kuwa tuni ya wuce samansa nima bangarena na wuce.
Ina hutawa Fitowa nayi na zage na Fara gyara gidan,Da dakinsa na Fara lokacin hankalinsa ya kwanta Yana zaune gefen bed dinsa Yana latsa system dinsa na wanke toilet kal kal na fito nasa Hannu tare da dauke system din daga gefen bed din na matsar da ita gefe sannan nazo na riko hannayensa biyu nace Yi hakuri ka tashi,mikewa yayi Yana Jin sanyi a ransa,bed din nake gyarawa Yana Kare min kallo kamar zai cinyeni sabo da sanye nake da guntun wando da kyar ya rufe min duwawu da rigata t-shirt peach wandon Maroon,Shi kuwa sanye yake cikin dogon wando da riga iri daya farare tas rigar me dogon Hannu harda hularta yayi kyau sai kamshi yake,Yana kallona Yana ganin girmana sabo da Ina da tsayi da Yar kibata normal komai yaji,sai da na gama da gadon nasa sannan nace zauna tare da rungume shi na zaunar dashi a haka na dawo Masa da system dinsa inda take sannan na share nayi mopping ko Ina ya dauki kamshi sannan na fito ko Ina sai da na gyara banda bangaren Sabreen,kitchen na Shiga na fara girkina gida ya dauki kamshi,Nawwar ya dade rabon da yaji kamshin nan sai ya dawo Palo ko Ina Yana shining ya zauna a nutse,su Sultana ne Suka shigo da sallamar su,na fito Muka gaisa na zauna Muna surutu Nawwar yace yunwa nake ji fa,tashi nayi na koma dakina na dauro zanin Atamfa akan dan gutun wandona,hakan ya Masa Dadi yace a ransa lallai kin Fara hankali.
Waina da miyar da na Fara Yi na zubo musu da kemo da ruwa sannan na kawo musu chin chin,kitchen naje Ina aikina har na gama suna hira abinsu sai da na gama na zubo Masa nasa wainar inda yake na kawo gabansa a manyan flasks na koma kitchen Ina cewa da Kannensa kuci fa kun San dai nan ba bakon gida bane,idan bata Isa ba sai na Kara musu dan Allah kar ku ji kunya,Su Sultana sai Murna sukeyi sun samu aunty me kirki,sai da na kawo Masa komai gabansa sannan na zauna,sai da suka ci Suka koshi nace Mami tana son Masa?Suka ce ae nace to na zuba muku sai ku Kai Mata,shi kanshi yaci wainar nan sosai fiye da zato na,da zasu tafi haka na cika musu flask sannan miyar daban suka tafi da ita,suna tafiya na cire zanin na fito kusan tumbur dani, kallona Nawwar yayi kawai Ina mamaki a raina wai ya akayi bana birge shi ne,Sam baya sha'awata,cinyoyina na tale yanda Muka saba zaman mu na Yan kwalta,Muka sake hada Ido ya maida Kansa ga tv,gabansa na dawo na tsaya tare da furta ban gane ba fa,yace what? Nace Kai billahillazi sai kayi sha'awata na gaji koma yane Kawai kayi sha'awata yawwa ehe Indai ana so a zauna lafiya Kawai ayi sha'awata haka Kawai sai gana min azaba akeyi,Dariya na bashi ya dinga Kuwa kyalkyalawa Kamar ba Nawwar ba,tsayawa nayi Ina kallonsa,sai da ya gama yace dama wai dan ni kike yi? baki na turo nace ban sani ba,Hannu ya miko min na kalli hannunsa na Mika masa nawa hannun nayi a hankali ya jawoni na zauna a hannun kujerarsa ya Kare min kallo ya sake tuntsirewa da dariya,Fuska na kwabe cike da shagwaba na mike a fusace Zan bar wajen ya sake riko hannuna naji wani yarrrrr a jikina, jikinsa ya jawo ni na fado saman cinyarsa bayana yake karewa kallo ko Ina fari luwai luwai,a saman dokin wuyana ya dora bakinsa a hankali cikin wata irin murya me rikita mata ya furta me kike so? nace ba komai Kawai,oya Ina jinki me ya faru naga gardi rungume da matata? Sannan Wanda ya Kira fa Yana Miki ya gajiya? Nan take idona ya ciko da hawaye na zame a hankali na koma kasa na zauna sosai sannan na dago idona Ina hawaye,yace ba kuka nace ki min ba,nace idan na rantse zaka yarda? Kasan bana karya wallahi duk abinda nasan nayi shi Zan fada maka,ban San komai ba akan Wanda ya kirani a waya Kai sheda ne da ace Ina da maza masu kirana da ka sani amma Inshaallah very soon zaka fahimta,sannan Wanda yazo gidan kawai ganinsa nayi a Palo ya fado Ina kokarin guduwa ya damko ni Kawai na barwa Allah duk Wanda ya min haka Inshaallah asirinsa sai ya tonu,Kawai kasan mu a baya an San mu a duniyanci ko yaushe a zargi muke shi yasa da anga irin wannan za a yarda kasan a inda ka dakko ni Kuma na yarda na zauna da kai Kuma bana boye maka komai tsakani da Allah nake zaune da Kai,mu yanzu ba Wanda bazai Mana sharri ba sai ka Kai zuciyarka nesa fa sannan akwai abinda nake kokari ka samu shine shedata lokacin zaka yarda dani .
Har na gama bashi cikakkiyar amsa Yana kallona yace na gamsu da ke,nace na gode da fahimta da wani ne da tuni ya dade da sakina,me zance da Kai sai godiya,Ni Kuwa me zance da kai ai a duniya bani da kamarka Kuma na gode Allah ya saka a Aljanna firdausi,Ameen ya furta Yana Jin sanyi da wata nutsuwa a ransa,ya akayi kika daina min kiss? nace Naga Kamar baka so,ki daina daka tani ni kunya ce dani ba iya komai nayi ba yayi min wayo ban gane ba,dariya nayi na koma saman cinyarsa na zauna nace ka daina Jin kunyata nifa ba kunya ce dani ba zan iya tubewa a gabanka,yace Allah? nace ae to mu a fada Mana fitsara shi yasa nake so kaji dadi kaki Kai Kuma,Ni mene ma zaka ji kunyata ni ba malama ba bare ace Ina kwarjini,yace to ku ai Kun waye da irin wannan harka ni ai sai dai ki koya min,duk ban gane wayo bane,nace Kai da kake da mata bata baka ne? Yace to ita kunya ni kunya bama iyawa sosai, dariya nayi tare da furta ba wani ka iya kowa fa a fagen nan dan iskane Allah nayi kasa da muryata cikin rada na furta harda ubana tunda yayiwa uwata cikina,baki ya rufe da hannu yace Kika zagi Daddy,nace waye Daddy din ni bani da kowa gashi nan ana cewa Yar shege ce ni,mikewa nayi nace good night na wuce part dina,wanka nayi tare da tsaftace lungu da sakona yanda na Saba sannan na fito nan haka bayan nayi shirin bacci cikin wata guntuwar rigata pink,Ina Shirin kwanciya naji wayata tayi kara na duba Nawwar ne,Ina dagawa yace zo ki kawo min green tea, Fitowa nayi naje na hada Masa na nufi dakinsa Sabreen an Sha kwaya ana ta uban bacci.
Shiga nayi daga shi sai boxers jikinsa ne me kyau ya dauki hankali na ina satar kallonsa na ajiye masa Zan juya yace Kun rainani a gidan nan ko wacce ranar girkinta sai tayi tafiyarta part din ta to daga yau nan kwana,Dadi naji amma na danne,kallona yake yi na zauna a gefe nima Ina kallonsa,muryarsa na tsinta yace kina son hakkinki ne a baki? Kai na girgiza alamar a'a,yayi mamaki yanda da nake roko amma yanzu nace a'a, Ido ya tsura min yace da gaske? nace da gaske na furta babu alamar wasa,to ni idan Ina so fa? dariya ya bani na danne sannan nace ni bana so yanzu,Zan iya tayaka kwana kamar da yanda baka taba ni,Amma yanzu ni harkar ciye ciyen nan ba so nake ba,ba kalau kike ba to infection ya kamaki,dariya na dinga yi nace akan me Infection zai kamani a toilet dinku ta gidan yawa da kike zuwa kina shiga ya Miki illa baki sani,3days Indai Kika ci gaba a haka asibiti zan kaiki dole kina da infection matar da kullum kike roko sai an lalata ki,pillow na dauka tare da rufe fuskata,baki ya bude yace ahhhhh gaskiya ba kalau ba ruqiyya kike bukata yau kece da kunya? harda rufe Fuska? Saman gadon na kwanta tare da kife kaina a Kan katifar Ina dariya kasa kasa yace Wai da gaske kike kunyata kike ji yau? mikewa nayi zaune duk na rasa inda Zan saka