Showing 6001 words to 9000 words out of 133548 words

Chapter 3 - YAR AIKIN KARUWAI BOOK COMPLETE by Asma Baffa .txt

04 Dec 2024

6563

Shuru bata fito ba duk ihun da akeyi dakinta ya koma da sauri ya sameta a saman gado tana ta shakar bacci,mamaki ya kamashi yanzu yanzu ta bar dakinsa amma har tayi baci,ke...ke..ke...ya furta Shuru inda kasan gawa ya sake bubbuga gadon duf Hannu yasa ya dagata Shuru a hankali ta Dan bude idonta ta lumshe ta koma baccinta tashin duniya taki tashi har Yan kwana kwana sunzo ma sun kashe wutar kitchen dai ya kone kurmus,Mama tace Oh Allah ya takaita wahala,Nawwar ya fito yace Mama kuzo kuga Sabreen irin baccin da takeyi ban sani ba ko ta mutu ne,Mama da Papa suka ruga cikin dakinta,Suma yin duniya sunyi ko motsi ko ta Bude Ido sai ta lumshe,Mama cikin mantuwa tace Ni Kam papan Sabreen ko cocaine dinne ta Sha yau,da sauri Nawwar ya kalleta,Papa ya kyaftawa Mama Ido nan take Mama ta canja zancen tana wayancewa ai nufina sai kace me shaye shaye cocaine Naga a turai itace ke sa Haka,Papa yace no Sabreen bata Shan komai Suka canja zancen,Nawwar tunani ya shiga sai Kuma Kawai ya basar bayan komai ya lafa a ranar ya Kira masu aikin gini Suka rushe kitchen din ba garen da yaci wuta akayi sabo cikin kwana uku aka Gama komai aka gyara ka rantse ba ayi gobara ba ko daya,daga ranar Kuma Nawwar ya hana Sabreen girki yasa Mami ta samo Masa dattijuwa Uwale da Ladidi me aiki dama akwai maza masu kula da compound etc,Daya ita zata dinga shara da mopping da duk wani tsafta,Uwale ta kware a girki iri iri itace me abinci Kawai.


Waye Nawwar da Sabreen.








Sabuwar Number ta
08061929616








AsmaBaffa
[7/15, 5:48 AM] +234 912 082 5656: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼

LITTAFIN KYAUTA NE




6-10




Official


By
AsmaBaffa




08061929616 sabuwar Number ta fans




LITTAFAN DANA RUBUTA SUNE


CIRANIN AMANA
MA'AIKACIYAR GOMNATI
KASUWANCINA
GASKIYA CE
KAMARSU CE DAYA
DUK INDA TA FADI
ME MAGANI
TUBABBIYA
HADIN KAI
JIN DADI SABO
MAFARKIN FARIDA
WARE BAIKO
AUREN MU


NA KUDI SUNE


RASHIN SA'A
TA GYARU
ADDUAR KAWA
YAR KWANGILA
GIDAN GWAURO
DANGIN RABI
DUNIYATA AMNAH
JIKAR MAGUZAWA
BABU KAUNA.










Page naki ne
MRS CHIEF










NAWWAR SULAIMAN RAJ shine cikakken sunansa asalin Shuwa ne,Sulaiman Raj iyayensu su biyar Suka haifa Sulaiman shine na farko sai kaninsa Yusuf Raj, Sunusi Raj,Fatima wacce ake Kira da Binta sai Autarsu Rukayya,Allah yasa suna da wadata irin ta da suna da arzikin dabbobi da noma,sun taso cikin gata amma basu Yi ilimin boko ba sai na addini Kawai,sun girma sun Kai shekaru 27 lokacin tuni an aurar da Binta da Rukayya suna auren masu kudin gaske Yan kasuwa a cikin garin maiduguri,mazan Kuma da girmansu Suka koyi karatun hausa da rubutu harda turanci suna dan iya karanta wani abin sabo da Business da sukeyi, gaba daya mazan Rana Daya aka daura musu aure irin na gata Kuma cikin family aka zabo musu matayensu Sulaiman aka hada shi aure da Yar uwarsu Salma Mami kenan wacce ke da yara biyar Nawwar shine na farko,Sultana,Nasira,Hamra sai Autansu Nawaf suna ce Masa Autan Mami, daga baya bayan Nawwar ya gama degree na farko sai ya karo Amaryarsa itama Yar dangi shuwa ce dukkansu jininsu daya Safarau suna ce Ummin Haidar, tana da Yara biyu Haidar dan 8yrs sai Ahmad 5yrs, Yusuf Papa kanin Baffa kuwa aka aura Masa Mariya Mama kenan Wanda yarsu daya tal Sabreen Allah kuma bai sa ya Kara aure ba har Suka manyanta sai Sunusi aka hadashi da matarsa Zuwaira wanda shi baiyi tsawon rai ba Allah ya masa rasuwa wanda matarsa ko haihuwa bata yi ba, daga Baffa sai Papa sai Kuma kannensu da suke gidan Aurensu Binta da Rukayya, gaba Daya sai kasuwanci yasa Sulaiman Baffa ya tattara da matarsa Suka koma can kudu garin Inyamurai da Zama Onitcha inda take bakin ruwa a Anambra state shekara daya matarsa Salma ta haifo danta Najimiji katon gaske kyakyawa na nunawa sabo da su din jinin kyau ne,ranar suna yaro yaci suna Nawwar, Yusuf lokacin matarsa tana da tsohon ciki bayan watanni kadan ta haifo yarta mace zankadediya taci suna Sabreen, Bayan Mahaifinsu ya rasu, ganin haka Sulaiman ya dakko Mahaifiyarsu da suke Kira Iyamami ya dawo da ita gidansa nan Onitcha suna zaman su lafiya.


Nawwar kuwa tun Yana yaro Baffa ya koya Masa kasuwanci ya dorashi akan harkar sosai har ya tara dunbin dukiya da tarin kadarori.


Bayan an raba gadon Sunusi Wanda ya rasu papa gaba daya ya handame dukiya har ta Kannensa mata yace zai dinga juyawa,shi yasa dukiyar shi sai taki albarka wannan yasa ran Yusuf ya baci bakin ciki ya kamashi ya tura Yan Daba har gida Suka yiwa Baffa fashin milliyoyin kudi babu Wanda ya sani ya ci gaba da bushasharsa,Babarsu tayi bakin ciki amma bata San danta bane yayiwa dan Uwansa turen yan fashi ba,Yusuf sai kukan karya ya samu dukiya ya tattara duka yaci gaba da juyawa Yana samun kudi a ciki yake biyawa Sabreen kudin makaranta da komai nata bayan Baffa shi ke masa komai ,Iyamami bata San komai ba ganin danta Namiji Daya Yana da kudi na fitar hankali duk da Yusuf shima yana da nasa rufin asirinsa sai tafi tausayin Yusuf ya koma dan gwal a wajenta sai abinda yace,duk abinda yace shine dai dai part dinta guda a gidan,sai Yusuf shima Baffa a gidansa ya warewa dan Uwansa part guda shi da matarsa Mama,Arzikin dai baya ci gaba kullum sai karewa suke,ganin haka tun Sabreen tana primary ya hada milliyoyin kudi ya kaita Italy tare da matarsa Zuwaira Mama ya kaisu can Kan ta kula da Sabreen ta samu Ilimi me kyau zai dinga zuwa musu ziyara,bayan sun tafi shi Kuma Nawwar a nan kasar can maiduguri aka maida shi wajen Rukayya can yayi makarantar secondary sabo da ya samu tarbiyya da ilimin addini tunda arewa ba Kamar kudu ba.


Har Nawwar ya gama Secondary Sabreen tuni ma a Italy ta dora da degree lokacin Mama ta dawo Nigeria shi Kuma Yusuf ya siyar da wani katon gidan Baffa a Abuja million dari a ciki yake turawa Sabreen kudi na hauka Baffa bai sani ba sam,Sabreen kuwa bata da aiki sai shaye shaye makarantar ma da kyar take zuwa tana gidan Saurayinta Lorenzo sune shekewa.
A wajensa ta koyi shaye shaye,sai club sai wajen Lorenzo tana sonsa shi yasa ta bashi kanta yake lalata da ita.
Shi kuwa Nawwar da bai San komai ba akan Sabreen sai Allah ya dinga hada shi da turawa masu kudi Suka Fara aiki a kamfanunuwa daban daban ya Fara samun mahaukatan kudade na shigo da Kaya da fitarwa ta fannin jirgin ruwa,Yana gamawa ya dora da masters yana Kuma Harkar business Allah ya sa Masa albarka,abokinsa kwaya daya ne dan gidan wani Sanata,guy ne hadadde shima dan masu dashi shima a kudu suke da Zama tare sukayi Secondary Suka tafi Uk tare Kuma amma shi Khaleel bai dora da masters ba babansa ya sama Masa aiki a NNPC,ya dawo gida Nigeria ya auri matarsa Sufia.


Alhaji Yusuf sun San komai abinda yarsu ke aikatawa na shaye shaye da bin saurayinta da sauran abubuwa marasa kyau sai Alhaji Yusuf Wanda Nawwar suke Kira da Papa yaje wajen Iyamami tare da matarsa Zuwaira yace tunda kowa yasan Sabreen ta lalace Babu me iya auranta a haka Kawai a hadata aure da dan uwanta Nawwar nasan Nawwar bazai ki jininsa ba,abin yayiwa Kaka Iyamami dadi a ranta tace ka kawo shawara ai tunda ya kusa dawowa sai a fara Shirin aure,Nawwar shi kuwa sai da ya kafu ya Zama me kudi na kirki ya Blbude kamfanunuwansa a nan Nigeria can Onitcha da wasu state sannan ya dawo ba zato Mami da Baffa sai ganinsa suka yi babban abokinsa Khaleel ya dakko shi,abinda ma basu sani ba Nawwar ya mallaki gidaje da abubuwa da dama a nan Nigeria Maminsa da Baffansa sun sani su, sai Murna su Papa sukeyi lokacin Sabreen taki dawowa rabonta da Nawwar tun suna Yara,bayan Nawwar ya cika wata Daya da dawowa ya Fara zuwa Office Yana ta kasuwanci gidansa da ake kera Masa Wanda zai zauna da matarsa idan yayi aure wannan na musamman ne,Papa hankalinsa ya tashi ganin Nawwar ya Zama me kudi shi Kuma Wanda ya handame sun kare ga Baffa dan Uwansa arziki sai abinda yayi gaba duk da kuwa irin zaluntarsa da yake yi yana siyar Masa da kadara ba tare da ya sani ba,sai ya dage da son lallai Sabreen ko tana so ko bata sai ta auri Nawwar ta nan zai samu ya mallake dukiyar Nawwar, Haka ya Kira Sabreen Yana masifa yace wlh idan baki dawo gida Nigeria ba ban yafe Miki ba, Mama zaune take kusa da Papa tace ka dinga binta a hankali ita kadai ce garemu,Papa Yana fada yace to kina ganin ni naki yin arziki gaba daya kamar bakin uwa duk gani a tsiyace kina gani dan uwana Sunusi uwar mu daya u abanmu daya yazo yayi kudi ni kuwa na roka na roka Shuru,akan haka fa ganin lokacin Sunusi har ya kusa fin Sulaiman kudi hakan yasa na tura aka kashe Sunusu ya bar duniya,da Sauri Mama ta rufe masa baki tana furta ka rufa mana asiri Kar wani yaji tunda ba Wanda ya sani to muyi shuru, yace to nayi shuru,Sabreen masifar papa yasa ba shiri ta tattara ta dawo,Papa da Kansa ya dakkota a airport,tana shigowa part din Mami a Palo ta iske Nawwar Yana dining Yana cin abinci
Mami tana ta zuba Masa surutu,dake Allah yayi ba me son magana bane Kuma shi bai fiye fara'a ba ga kafirin Isa da mallaka da son girma sai ya Mata shuru sai jefi jefi yake furta uhm hakane, har Sabreen ta kwala sallama ta shigo ta Sha tsadaddijar gown golden ga takalmi da Haka tayi kyau matuka,Mami ko murna bata yi da dawowarta ba ,Nawwar ko kallonta baiyi ba yaci gaba da uzurinsa itama bata kulashi ba sai da Mami tace ga yayanki Nawwar ku gaisa,sai lokacin tace Ina yini ta Kara gaba bai ko amsawa.


Itama sai bayan ta cika sati biyu da dawowa sannan Papa ya kirata ya sanar Mata cewar ya hadata aure da Nawwar ita Kuma Saurayinta Dan Italy take so Lorenzo,Zata Yi Musu papa ya dakatar da ita yace wlh idan baki yarda da auren nan ba sai na tsine Miki muna so muci arziki kina hauka kudi ne fa da shi kina gani arzikina ya Kare shi yake mana komai yanzu ci Sha sutura idan Kika aure shi ai dukiyar ma zai mallaka Mana wata Kuma mun samu damar Shiga jikinsa tunda shi Sulaiman busy ya Masa yawa, Mama tace ana Neman arziki kina hauka idan kika aure shi ai kinyi dace, Sabreen ba yanda ta iya haka ta amince Kawai,sannan Baffa ya samu Nawwar har dakinsa ya zauna yace Nawwar magana nake so muyi Jin haka Nawwar ya gyara zama sabo da shi mutum ne me biyayya, sune Suka kula da shi Suka dauki nauyinsa har ya zama abinda ya zama yanzu,Baffa yace dan Allah na rokeka Nawwar ka auri 'yata Sabreen sabo da Kaine kadai na yarda zaka riketa da Amana ko bayan ba raina dan Allah karka ce a'a ka amsa min,Murmushi Nawwar yayi yace ni ai bance bana son Sabreen ba na amince Baffa bani da abinda zan biya ku iyayena,sannan na gama gina gidana na gama komai sanda kuka shirya ayi bikin,Yusuf Papa yana gefe a zaune shima ya dinga murna yace an gama dan albarka Allah ya baku zaman lafiya Kamar gaske bayan a ransa yana ta saka tsiyar da zai hadawa Nawwar ya gaje wannan kudin nasa da ya tara.


Baffa tunda ya auri Amaryarsa Ummin Haidar gaba daya ya tsani uwar gidansa Mami haka su Iyamami ma Suka tsani Mami basa sonta kullum sai zagi da cin mutunci,duk abinda danta yayi to ita zasu Zo su zage tasss bata da iko tayi magana Baffa sai ya sake ta gaba daya igiyar auren Saura daya jal,bai bata kwananta sai dai ranar girkinta tayi girki ta Kai Masa part dinsa amma Kuma Ummin Haidar ce zata kwana da miji,tun Mami na zuwa Yana wulakantata ya koreta har yace ta daina zuwa Masa da dare,a gidan daga ita sai yaranta su Nawwar da su take rayuwa,Abu na gaba gaba ma abinci ya daina zuba Mata a part dinta ganin haka Nawwar ya koma siyen komai a gidan na abinci Watarana ma har bangaren Iyamami da Papa, basa kaunar Mami ko kadan a gidan,Ko bata je wajen Baffa ba idan yaga dama har bangarenta zai Zo ya zazzageta ya fita,tayi kuka har ta Saba ma da rayuwar.


Bikin su Nawwar wata daya kacal aka saka sabo da gaggawa nan da nan biki yazo ba wani shagali Kawai aure za a daura a Kai Amarya cewar Sabreen tunda ba auren soyayya bane ana gobe daurin aure Yan Uwa da abokan arzuka sun ciga gida, ga kawayen Amarya sai Nawwar Wanda bai kaunar auren Sabreen baya sonta Sam haka suka raba Iv,Hajiya Binta da Rukayya kannen su Papa sun iso da yaransu samari wasu Kamar Nawwar wasu Kuma kasa da haka,akwai ma Mus'ab babban dan Binta ya girmi Nawwar,Washe gari aka daura auren Sabreen Yusuf Raj da Nawwar Sulaiman Raj Kan sadaki dubu dari, kudi dama ya basu da kansu Suka je kazar waje suka hada lefe, bayan Sallar Isha Papa da Mama suka Kira Ango da Amarya,Baffa,Mami,Ummin Haidar suna gefe Papa ya fara Nasiha me shiga jiki kamar gaske har zuciya sannan Suka ce su tashi su tafi shine Suka tafi gidan aurensu yayin da Ango ya dandana Amarya yaji ba kanta.


Ci Gaban Labari


Karasawa nayi a nutse Ina zuwa nayi sallama ya amsa,nace Ina yini ya amsa min Yana kallona yana zuba Murmushi ni dai daga haka bance komai ba,da Kansa naji ya fara magana yace Rabi na dago da kaina a hankali na maida kaina kasa Ina Wasa da yatsuna yace ba Wasa ne ya kawo Ni ba,kamar yanda na fada Miki sunana a farko to hakane Ina da mace guda Daya da yarana uku ,da gaske nakeyi wallahi harga Allah sonki nakeyi da aure bada Wasa ba,Amma bance sai kin Soni yanzu ba Sanda Kika ji kina so na sai ayi komai,nace to kawai,yace Ina Harkar shigo da Kaya da zannuwan gado daga kasashen waje Zan dinka baki bedsheet kamar guda ashirin zuwa sama ki dinga Kara ribarki kina siyarwa Kinga kin samu Sana'a ko tunda naga da shekarunki,Mamakinsa ya kamani na zaci karya ne ashe da gaske yake haka Muka rabu,sati Daya ya sake dawowa Allah bai sa Yan gidanmu sun San me kudine ke zuwa wajena ba har sai da Muka shaku sosai na fada son Alhaji Kutama,muka tsunduma a soyayya daga nan ya Fara min Wasa da kudi a haka ma Ina kin karba,har dai yace zaizo ya gaisa da iyayena,wani zuwa na fadawa Gwaggo Saurayina zaizo ya gaishe su sai dariya suke min tunannsu talaka ne Yana zuwa Gaji ta leka taga irin motarsa ta koma gida tace jama'a kuzo kusha kallon Saurayin Rabi,dukkan matan gidan Suka leka waje abin ya tsorata su Mairo tace tab ko mu da mukayi ilimi bamu samu irin wannan Saurayin ba ko me lifan bamu da shi sai Rabi wlh da sake,Dagaci ya gigice yace Kar Wanda ya damu Kansa Rabi baza ta aure shi ba Amma a kyale shi muyi amfani da damar mu sai mu samu kudi,Haka ya lallaba su Basu nuna min komai ba na Masa iso har ciki Suka gaisa sun Sha Alheri na kudi Dagaci ma dubu dari biyu ya bashi ya bawa su Gwaggo dubu ashirin ashirin,Gaji da Mairo dubu goma goma sannan yace za a kawo kayan abinci, a ranar ya siya min waya me tsada Ranar murna ta cika gida sai basu kulani ba Muka ci gaba da soyayya da Alhj Kutama ya dinga kashe min kudi kamar hauka kayan sawa masu tsada iri iri takalma jakankuna,mayafai etc,Dagaci ne ya kwace iPhone Dina ya siyar ya siya min Tekno keypad Yar dubu bakwai yace baza ki rike babbar waya ba, Haka kayan kwalliya duk su Mairo da Nawa suke amfani da turaruka,gashi ya Fara kawo min yadin gado Ina siyarwa iri iri a garin,Dan ma a Kauye muke ban waye ba tunda ni ba ilimi nayi ba iyakata primary a Jss1 Dagaci ya hanani zuwa,Dagaci ya fada Masa gaskiya cewar Ni Yar tsintuwa ce duk da haka Alhj Kutama yace yaji ya gani yana so, Haka Dagaci yace ya kamata Kutama ya turo da manya,ba Wasa ya turo manya Suka kawo kudin aure aka tsaida aure wata hudu.


Abu Yana ta karasowa Ni Ina ta Shirin biki Kutama Kuma ya tafi Dubai business dinsa yace bazai dawo da wuri ba sai dai a daura aure baya nan idan an daura zai min visa na bishi kasar waje can Dubai Haka akayi magana da Dagaci.
Haka biki yazo komai ya turo danginsa tunda baida iyaye kanin babansa da sauran Suka Zo da yawa aka taru aka daura Aurena da Kutama akan sadaki dubu dari biyu,ga lefe an hada na gani na fada,to bayan an gama ba wani shagali akayi ba tunda bani da gata ba Wanda ke shiga lamarin auren nawa idan ba Dagaci ba,Ina jira muji me Ango zaice Muna waya kullum har sati daya da biki, Gwaggo tana zaune tare da Dagaci Ina dakina Basu San Ina Jin hirar tasu ba sun manta Ina dakina Kuma a jikin dakin Nawa suke,yace karku damu kanku Gwaggo na Gama daukan mataki malamin yace bazai taba Zama tare da ita ba kwana nan zamu ji labari me Dadi,Gwaggo ta rangada shewa tace Alhmdllh ai nafi so Gaji da Mairo ta suyi auren su Allah dai ya kawo musu Miji me kudi Wanda zamu huta cewar Dagaci, Ni dai bance

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login