Showing 69001 words to 72000 words out of 133548 words

Chapter 24 - YAR AIKIN KARUWAI BOOK COMPLETE by Asma Baffa .txt

04 Dec 2024

6594

ke muce lallai idan bai amince ba sai mun kawo video dinsa gida mun nunawa Amaryarsa Ummyn Haidar,sai Mun nunawa Dan Uwansa Baban Sabreen da Sabreen da Iyamami har Nawwar sai ya gani da kowa nasa sannan dole ki zauna gida daya da Sabreen da wannan gidan duniya ne Aljannar duniya ne,sannan idan yayi Masa baki ko ya saka Miki Ido a aurenki zamu saki video,tafawa mukayi su Santana Yan daudu Suka saki shewa,Sera tace Miracle da aure mu Kam aure sai dai a lahira waye ma zai aure mu sai dai muyi Ashawon mu,nace nima na dan wani lokaci ne zan dawo bafa son auren nan nake ba dole yayi min,Wayar Nawwar ce ta shigo,na daga da sauri yace yanzu Zan shiga ciki na Tara kowa Zan fada Kiyi addua,Murmushi nayi nace an gama, Yana datse Wayar Muka dauki shewa.


Nawwar Yana shiga ya zauna,Papa yace Muna jinka Nawwar mene ka tara mu sai kace zaka raba Mana kadararka,Nawwar yace zuwa nayi na fada muku dan Allah kuyi hakuri ku yafe min Zan Kara aure,da sauri Sabreen ta shide tare da dagowa da sauri,Iyamami tace Yar gidan wace a dangi tunda ka damu uwarka ta zugoka ka nuna mana bamu Isa ba,dama ya tsaneni Iyamami cewar Sabreen ta fashe da kuka,Nawwar yace banyi Dan na batawa wani ba sai don na raya sunna,Kuma Allah yace ayi idan kana da Hali zaka iya adalci, Mama ce tace Kai dalla rufe mana baki zaka Kara aure dai sabo da baka son Sabreen jininka,Baku da aiki ku maza iliminku baya tashi da hadisin ku da Jan aya sai zaku Kara aure duk maza haka suke ba yau Muka taba ji ba,Papa yace zaka samu a gaba ka Raina mana hankali sai shegiyar Isa da mulki da mallaka da izza ana fada uwarku tace ai Kun gaji sarauta kakanta ne fa ya taba rike me unguwa tun irin sarauta ta kauye karka Zo Mana da gadara a nan wacce ka gada a wajen uwarka,Mami tace ai dai jininmu daya,yace ke ba Yar uwar mu bace can kisan danginki,Baffa ransa ya baci ya nuna Mami yace kece munafuka karki ce komai ke Kika zuga shi algunguma Ina jinka cikakke isasashe wacece a dangi kasan mu babu bare a cikin aure, fada mana wace,Nawwar ya gyara zama dan rainin hankalin Nawwar sai Kawai ya dakko musu labarin Rabiah yanda ta bashi tiryan tiryan sai da ya Kai aya yace wannan ba abar a taimaka bace wannan ba abar da za a tsaya a duba lamarinta bane,Ran Baffa idan yayi dubu to ya baci, yace na farko kasan a tsarinmu babu auren bare,amma dan ka maida mu wasu Yan Iska sai ka dakko bare a baren ma ba Yar asali ba sannan ma Yar tsuntuwa,karshen muni Kuma itace wace Muka sani ka Kai gidanka muke zarginta da karuwa,ai ba zargi bane karuwa ce cewar Sabreen tana kuka wiwi,ba a San Yar waye ba,Yar shege ce,mayya ce,jininsu babu na kirki,Basu da Nasaba bata da kowa, komai babu Kawai sai mu kawota cikin zuriarmu ta haifa mana mugun iri yaran zina cewar Baffa, to ka sani ni Sulaiman....kirrrrrrrr Wayar Baffa ta dauki ruri ya dakata da magana ya dauki Wayar sai ya ga Star ce take kiransa dama yau ma Yana so su hadu sabo da Amaryarsa bata nan ta tafi ganin gida,dagawa yayi ya mata Sallama tare da furta Ina meeting Zan nemeka anjima ya Kira star da Namiji Wai zan nemeka anjima dake Karuwan sun San irin wannan,sai tace bani minti daya hope ba a Jin maganata a fili yace ae da sauri


Star ta furta ka tuna wacce jiya ka dauka a titi street din da muke tsaiwa? yace kwarai,tace to itace wacce danka ke son Aure Kuma kawata ce wallahi ka yarda tun wuri a daura aure Kuma idan an daura ba ruwanka da safgar Aurenta da mijinta Kuma tare zasu zauna da Sabreen din Kuma kaje kayiwa danka walicci idan ba Haka ba wallahi Muna da video dinka Wanda muke sex tare na dauki wasu Ina da su Matukar baka amince kawata aminiyata ta auri danka Nawwar ba wallahi kaji na rantse har gida sai nazo da kaina na nunawa Ummyn Haidar Amaryarka,Iyamami,Papa,da Nawwar Kai da dukkan family dinka kuma kasan Zan iya idan kana musu kazo mu hadu a hotel din jiya yau na nuna Maka videos din ka gani da idonka,yanzu ma ka bude WhatsApp dinka zaka ga wasu,Baffa gumi ya Fara hadawa da kyar ya iya magana yace Zan Kira anjima ya datse Wayar ya kalli Nawwar yace kowa ya tashi ya tafi na sallami kowa zanyi magana da Nawwar akan aikin gidan gonata da Zan bude Zan sake tara meeting,tunanin kowa har Nawwar a Kamfani aka Kira Baffa yayi asarar wata kadara yanda ya gigice yake hada zufa,har Iyamami fita Suka Yi da yakinin aure baza ayi shi ba,Baffa WhatsApp dinsa ya bude yaga videos dinsa guda uku tun daga Kansa har kafa tsirara Yana Sex da Star,bai sani ba Su Star Indai zasu kwanta da mutum sai sun saka wata camera a boye Kuma baza ka gani ba,komai sai ta dauka incase ko zasu hadu da wani shege ya Raina musu hankali sai suyi blackmailing dinsa da shi,har su Sera duk haka suke yi,Baffa hankalinsa ya tashi da sauri ya goge na wayarsa gaba daya,ya kalli Nawwar yace na yarda ka aureta abinda Allah yace ba yanda za ayi idan na matsa karshe Allah zai iya dauke ni Kuma ayi abin bana raye,Kuma na duba naga abar taimako ce tabbas na yarda Zan Shige gaba Allah yasa Albarka amma da sharadi daga ni sai Kai Sai Mami zasu sani a gidan nan bayan haka ko kannenka Kar su sani gudun Kar Iyamami taji ta hana,idan an Riga an daura sai nace Nima ban sani ba munafuntata kayi na maka fadan karya nace lallai sai ka sake ta to karka saki abarka kuyi zamanku,jeka abinka yaushe ne bikin muje wajen waliyyin nata? Nawwar Kamar an dasa shi haka mamaki ya kamashi jiki a sanyaye yace Baffa ka Zama waliyyinta,Ni kuma Zan karbi aurena da kaina kaga shike nan tuwon mu man mu ya furta Yana dariya,Baffa a ransa Kamar ya fashe da ihu amma haka yayi yake yace acan kauyensu zamuje a Tara mutane a daura, yace an gama mun shirya Nan da 2weeks yayi? Baffa yace ai sati daya ma me kake jira tunda a shirye kake kana da gida da komai,Nawwar ya dinga mamaki maimakon murna sai da Suka gama tsarinsu sannan ya koma Yana bawa Mami labarin abin mamaki,ita kanta tace to lafiya kuwa anya lallai akwai wani abu a wayar da Baffa ya daga,tabbas Wayar nan ce da yayi akwai wani abu a kasa babba,ko ma mene Rabiah zata fada maka Watarana,yace tabbas daga nan fa Nawwar direct gidanmu yazo,Ya same mu Muna shirya gagarumar dinner da zamuyi har kala biyar Kuma shi zai biya ,sanye yake cikin shadda sky,na karaso jikin motarsa cikin abaya Ina karasowa Ina murmushi nace barka da zuwa Angona, Ido ya lumshe yayi Murmushi,nace ya kuka Yi? yanda Kika ce ya faru,nace Alhmdllh shike nan,Wai meke faruwa ne me kuka ce masa? nace karka damu Indai nice ana zuwa gabar da zaka ji Zan sanar da Kai kasan bana boye maka,nacewa yayi lallai sai na fada Masa nace tunda ka damu sai kaji to wata kwangila ce Suka fara da Saurayin star,Baffa ya Gama kashe kudinsa yayi domin wajen billions ya kashe shine Muka saka Saurayin muka ce yace idan bai yarda ba lallai zai janye kwangilar yasan shine da asara Kuma mutumin Sakataren gomnati ne na federal,shine ya yarda kaga munyi sa'a, Nawwar dai Yana mamaki yace Naga Baffa ne ya Saba da asara Kuma shi bai fiye son kudi haka ba akan kudi ba a tursasa Baffa yayi abinda baiyi niyya ba,nace to a nan sai yaso kudin Kam domin munyi nasara dan sai da mutumin yace ma Sai yasa EFCC ta bincike shi tunda Yana hada harka da gomnati kaga Kuwa kudin gomnati ba Wasa,Nawwar yace idan wannan ne Zan yarda dan Yana harkalla da gomnati sosai,Murmushi nayi dan Kuwa na tsara yanda star tace Yana harkalla da gomnati suna bashi kwangila, sabo da bai kamata dansa ya San ubansa yana Neman Mata ba,sannan bai Dace mu iya fadawa Nawwar ba in munyi haka ba Amana,da ace Baffa gonarmu ya shiga to zamu iya keta shi ta ko Ina ba ruwanmu da duk Wanda zai sani mu dama bamu hada Hanya da arziki ba bamu sanshi ba bare mu kyale.


Nawwar na mikawa paper nace gashi mun tsara yanda bikin zaiyi,karantawa yayi yaga uban miliyoyin da Muka tara Masa,yace ku duk harkarku ba sauki a ciki yasa biro yayi cancel dinner yace guda daya za ayi tal bana son wannan shirmen party din Ni ba Dan bariki bane,nace to ai dai za ayi dayar ko? yace Inshaallah,nace sai lefe gidan su Sera za a Kai a Kauye,yace ba damuwa,karanta paper din ya sake yi yaga na rubuta kudin gyaran nono ba wani sakayawa sai lokacin ya kula ma,dariya yayi a ransa, yasa biro ya rubuta Boobs ki bar wannan a hannuna Ni Zan gyara shi da kaina,ya duba kasa yaga na rubuta Local government Kar a manta da kayan shaving dinsa,sai Kuma kudin siyen kayan gyara wajen sabo da wajen ya Kara lipton duk da wajen cewar yaji Lipton dama,Ya rubuta ke ga Lipton a wajen ango ai Yana nan zai tsoma shi a ciki,a ransa yace Yarinyar nan tayi balain rainani gani takeyi Kamar ban San komai ba ma irin ga wani ajawo,kwafa ya ja Ina jinsa nace Wai rubutun me kakeyi Kai? In kin karba Zaki gani, ya gama soke Wanda zai soke ya bani takardar yace zanyi transfer hole Kuma za a kama,karba nayi nace thanks ya shiga mota ya tafi,ni Kuma na koma na zauna a saman bench din da muke zaune Muna shirin biki.


Takardar Muka karanta Muka ga abubuwan da ya rubuta shewa mukayi da ihu nace yeeeeeee shima Dan duniya ne yeeeeyyyyyyyyyy Muka tafa da su gaba Daya Muka hada hannaye waje Daya harda Santana Dan daudu yace Warrrrrrrrrr inji gwanja za a daki ganga wallahi aci uwar gayu ranar sai na saka bra katuwa ko na samu mashinshini,dariya ya bamu Muka kalle shi,ai ba jira washe gari tuni mun buga gate pass,gyaran jiki kuwa munyi shawara kayan kamshi da sauransu za a min a dafa Ni da kamshi yanda duk inda na zauna ma to fa kamshi zaiyi kwanaki bai bar wajen ba,sai gyaran skin sai maganin infection kawai,shi na Fara gaba daya Sera ce ta biya kudin Wai gudun muwarta gashi komai namu me tsada muke Yi dan mu ba garorin Yan bariki bane kucakai layinsu daban,kafin kace me kowa yasan zanyi aure a barikin duk shiri akeyi Mata da maza Wanda muke harka,duk Wanda ka gani dan wanka ne da karya da kashe kudi sune a bikin,anko ma wani materials me tsada aka fitar kala hudu kowanne agroup da Kalar nasu a wajen,maza Kuma shadda Muka fitar kala hudu irin na kalolin material din,sea blue,milk,purple sai silver,su Star nasu Sea blue Suka zaba, duk wata karuwa sai da ta gayyato Saurayinta data fi good time da shi Kuma yayi ankon Kalar na group din da take,Karuwan sun min Kara akwai hadin Kai ko wacce da kudin data bani sun tara min kudi sosai har maza.


Tuni mun fadawa Inna a waya ta sanarwa Dan uwanta Jangudo me tausayina sai Murna yake shi ya bawa dattijai da su liman Alawar daurin aure ya fada musu ranar,shi Kansa Dagaci sai ji yayi an Kai Masa gida ana gayyatarsa a masallacin Juma'a na garin, yace ashe za ayita asirina bai ci Yarinyar Nan ba aure ma zata yi,to wallahi ko anzo sai na sa Iyayen yaron da kansu sunce sun fasa yanzu haka basu San Yar tsuntuwa bace,Gwaggo tace ai nima nan sai inda karfina ya kare,Aunty Amarya mamaki da bakin ciki ya hanata magana Sam,mu Kuwa ana jibi daurin aure ranar Friday zamu Yi dinner Saturday ana gobe aure zamu tafi Kauye idan an daura daga can za a dakko Amarya,Saura kwana hudu biki Nawwar ya hada lefensa Mami ce ta hada komai akwatuna set biyu guda goma Sha hudu ko wacce da kyar take rufuwa, Abin a sirri ake yinsa dole Mami da Seraline suka tafi can Kauye a jirgi,suka sauka a airport dake kano taxi Suka shiga me kyau har Kauyen Suka Kai Lefe,ai Kuwa Sera har gidan su Gwaggo taje tace an kawo lefen Rabi kuzo ku kalli abin farin ciki ko yarinya me iyaye bata isa ta Kama kafar Rabi ba, kawai ta juya tayi tariyarta,su Kuma da son gulma da wuri Suka fice har Mairo ita da Aunty Marya ga Gwaggo Suka je tun daga ganin Mami Suka tsorata sun San ba talaka ne ba yaron,suka ga Kaya iya Kaya Saratu tana daga musu tana cewa Kudirar Allah ta sauka a kauyen nan idan da hankali ya Isa izina,Rabi yanzu tafi karfin mota sai dai yawo a jirgi, Gwaggo hassada ta motsa kasa karasa gani Suka yi harda cewa komai sai anyi karya ai Zamanin nan ba lefen ba ciyarwar shine aikin,Mairo tace uhmm ayi mu gani Suka juya Suka fice,Mami Murmushi tayi tace sune Suka rike Rabiah lallai dole taci wahala, da Yamma Suka koma a jirgi aka bar lefen a dakin Inna.
Dagaci sabo da bakin cikin Jin labarin ya nemi Yara Yan daba ya biyasu kudi yace suje cikin dare su zarewa Inna wuka su sato Masa kayan lefen tas,Kamar Inna ta sani a daren tasa Jangudo yazo da yaransa maza samari Suka kwashe lefen tas aka maida gidansa,tana bacci cikin dare sai gasu sun banko kofarta dama bata rufe ba,makamai Suka zare Mata,Inna ta saki Salati tana hawaye suka ce Ina lefen da aka kawo wani ya shaki wuyanta,Inna ta rafka salati tace ai sun koma da abinsu inda Amarya take me za a bar lefe a nan ayi da shi,ku duba dakin,dakin gaba Daya Suka caje ba komai sakinta suka yi Suka koma a daren suka sanarwa Dagaci Suka Kara gaba abinsu.


Kayana da ango duk mun dinka na fitar biki kaf, ba Wanda yasan ana biki a gidan Baffa sai Mami sai Baffa,yau ta Kama ranar dinner tunda aka sa bikin banga Nawwar ba komai Khaleel yake aikowa,ya Sha tsiya wajen Khaleel Kawai share shi yake yi, itama Sufia tace ai Dole nabi Mijina Khaleel musha kallon bikin Yan bariki dole akwai show,yace ai komai shigar dai hausawa za ayi inda kisan kina Kano, ranar 8pm za a fara sabo da haka wajen make up kowa cikinmu da inda ya tafi, nikam tawa inda sai wane da wane ke zuwa nan naje Wanda Ango ne ya biya,su Sera suna can tasu,abinka da masu samari kala kala dukkan matan kusan kowacce ta karbo shegiyar mota a wajen samarinsu,mota ce da mota ke tashi sai wadda ka gani,har wasu masu abota da yaran masu kudi duk an gayyato su sunyi anko Kuma Yan Mata na kece raini ba a magana Sabo da masu kawaye ma sun gayyace su, Kai kace bikin wata Yar wani ce da, waje ya hadu dama na manya ne, 8:30pm an gama min make up, munsha kayan namu Kalar decoration din wajen da aka yi Fari da dark pink sai Silver gaba Daya wajen walwali yake, ni rigar Amaryar tawa gown ce daga kasar waje yayi order online dark pink tana Jan kasa daga baya,sama ta kamani me dogon Hannu Net,sai gogoron da aka daura min Silver da takalmi da jaka silver Kalar shaddar jikinsa,hularsa da takalminsa duk Kalar shaddarsa Yar gaske an Masa babbar riga ta matasa dai dai shi, Khaleel ke driving dinsa a bayan sabuwar motarsa ta bugawa a news fara duk ta Sha adon flower da zare pink kana gani kasan ta Amarya da ango ce, daga wajen makeup din na fito wacce ta min ta rike min kasan rigar har motar na shiga ta rufe tana mana murna Khaleel yaja Muka wuce,hannuna wata a layinmu bahaushiya ta iya lalle tana yiwa hausawa karuwai, ita ta zana min ta gani ta fada ja da baki hannu da kafa nayi kyau abin ba a cewa komai, Khaleel yace Amarya kinyi kyau sosai wlh dama me kyau ce,nace na gode Friend


Nawwar yace mu ganki na juyo sosai harda fari na lumshe Ido dan Wai yaga gashin idon da aka saka min sosai, hannayena da ya Sha lalle da abin hannu na amare na daga Masa ya gani na juya Masa tafin hannun ya gani,Khaleel yace kaiiiiii gaskiya lallen yayi,Nawwar yace Wai mene haka bana son munafunci,dariya yayi yace to sai ka bari a daura sai mu daina fada amma yanzu bata zama taka ba,Murmushi nayi na zare takalmin kafata tare da dago kafar daya nace ka gani, Khaleel ya leko da Kansa ya maida Kansa wajen tuki,Nawwar yace Allah ya kyauta maka Khaleel,kafar ya gani tayi kyau yace good, maidata dan Allah kin dameni,sai da na maidata yace muga hannun naki na Miko na dama,yace na hagu,na Miko masa hannunsa yasa a aljihu ya saka ya zaro gidan zobe ya bude naga zoben gold me tsada Dan karami hannuna ya rike ya saka min zoben a yatsana na kusa da karamin yatsan da kyar ya shiga yayi min cif cif,na washe baki nace yayi kyau thanks gidan zoben ya saka min a jaka tare da kudin liki masu yawa Yan dubu dubu sababbi,Khaleel yace gulmamme abinda kakeyi kenan,Bai kulashi ba, tun kafin mu karasa wajen event din muke jin kida na tashi Kamar hauka Yan gayu ana ta Shiga Su Sera Amarya suke jira suna waje wajen su goma sauran Kuwa an gama cika ana cashewa rawa suke ta rashin kunya ta fitsara Amma da aji ake yinta ba hauka ba yau ranar nutsuwace da yanga da aji, Yar zabil tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login