Showing 75001 words to 78000 words out of 133548 words

Chapter 26 - YAR AIKIN KARUWAI BOOK COMPLETE by Asma Baffa .txt

04 Dec 2024

6577

munyi da sauki,suna fita aka Kira Ango da Amarya Muka mike muka shiga sabo da iyayin Nawwar Wai a filin rawar za a sa Masa kujera kamar wani sarki ya zauna a tsakiyar wajen Yana Shan ruwan roba,ni kuwa rawata na dinga yin cin koshi ka rantse ba Amaryar bace,mikewa yayi ya dinga zuba min ruwan Yan dubu dubu, ana ta dauka a wayayi,Sera ce tazo ta min rada kuyi kiss zamu dauka a waya nace bazai yarda ba,sai kace ba mace ba ai karuwancin Zaki tuna,dariya nayi Ina dan takawa yana min liki,na dora hannuna daya a kafadarsa na maida dayan ma a kafadar na dora yace ta ya Zan Miki likin Wai bakya Jin kunyar mutane ne fa abokaina zasu ce baki da tarbiyya nace sai yanzu suka sani kiss zamuyi dauka za ayi zai zame nace Allah kana guduwa sai na kunyataka a wajen nan ka sanni, ai Kai kace kaji ka gani ka aureni, mu bama Jin magana ka bani hadin kai,yace to kiyi sauri na gaji,Yatsa na dagawa su saira su dauka haushina yaji Yana ta fada bai Dace ba wannan a musulunci Wanda yanzu ya Zama ruwan dare mutane da yaran masu kudi gani suke birgewa ce wayewa ce,a hankali nace kaine fa zaka min Ido ya zaro tare da furta na shiga Uku nidai,please karka kunyata ni Zan kunyataka wallahi, Ido ya rufe aka canja slow music a hankali na dora bakina a saman nasa ya min kiss a nutse ana dauka na rungume shi sai aka dauki tafi da ihu yeeeeeeee Yan kauyen Suka Fara cewa yeee ya tsotsi bakinta alquran,billahillazi bakinta ya lasa kunga sun rungume da gani sun Saba tun a waje,Yan matan kauyen shewa Suka dauka yau Muna ganin bariki yehoho ahayye chasss...,Khaleel bai taba zaton abokinsa ya fetse haka ba sai yau dariya ya dinga yi, sai da Muka gama likawa juna kudi Yana min Ina Masa sannan Muka fita,Khaleel yace Lover boy,Nawwar ya hade rai tare da Zama,abokai su abin ya birge su sosai dama duk gasu Yan gayu yaran masu kudi,Wise bata gajiya sake shiga tayi tana yiwa kanta da kanta liki tana cashewa,Autan su Nawwar yaga duwawuka sai tsalle suke yace wow ya radawa Nawwar irin wannan Zan Aura nima Yaya idan na girma da wuri za a min aure,Nawwar yayi dariya a ransa a fili yace sai kaci ubanka wlh ni ban San ma ya akayi ka biyo mu ba,Mami ce tace nazo yaci gaba da cewa Auren Kauye za a min da wuri ni wallahi ba sai na girma ba,na daina kula Yan class dinmu wajen Aunty Rabiah zanzo ta hadani da kawarta,Nawwar yace sai na zaneka bari mu koma gida tunda baka kunya,Shuru yayi bai sai sake magana amma ya zurawa Mata ido.


A wajen muma muke cin take away dinmu har Yan Kauye Suma sun samu da yawa sun samu, tare zamu tarkata da angwaye mu koma can Anambra, duk munfi yin rawar wakokin Yan kudu su Muka iya Kamar kannen Naira merly, 2pm aka tafi Sallah wanka Muka sake tare da canja Kaya wannan karon ba make up Kawai dauri mukayi kowa tayi wacce zata iya, muka fito na sha shadda dark purple nayi kyau, su Kuma ankon Atamfa Suka saka me kyau sunyi kyau daga nan aka dora da kida da rawa tare da sabon liki, babu Wanda zai so ya bar wajen nan,sai lokacin muka raba waina da miya aka sake ci da ruwa da lemo, bamu Ankara ba har 5:30pm sai Inna ce tazo tace Yan Kai Amarya sun shirya,sannan Muka tashi daga kida,masu kida Suka hada kayansu da motarsu suka tafi abinsu suna murna sun Sha kudi.
A gurguje nayi wanka sabo da zafi na canja cikin Net less fari yasha hadadden dinki na Sha takalmi da jaka fari aka min dauri na yafa mayafi me kyau fari da adon silver,turaruka na shafa Wanda kayana komai an tattara su tuni sunyi gaba Angwayen da Suka Fara tafiya su aka bawa Suka tafi da komai dama kayan lefe ne, Wanda na cire Kuma Sera ta ninke ta tattara komai a jakata da na zubo kayan sawa na biki suna wajenta tsinke namu bamu bari ba, Jangudo ne yace tunda Kai Amaryar ba addini bane iya kawayen ma sun Isa ga angwaye ai sun Isa Kai Amaryar


Ba sai an sake wahalar da Ango ba Watarana idan ta haihu sai aje Mata,Inna tace hakan ma shawara ce shike nan aka fasa a Raina nace da ace Ina da iyaye Dole sai an rakani dakin miji amma ya zanyi haka Allah ya tsara min wannan yasa zuciyata ta karye na fashe da kuka,duk sun zaci kukan Kai Amarya nakeyi Suka dinga dariya Yar bariki da kuka za a kaita dakin miji suna ta tsokanata, Nawwar ganin Ina kuka dariya ta Kama shi yace Amma Yarinyar nan ba karamar Yar rainin hankali bace lallai Ina ganin Yar duniya,ki gama tikar rawa gata dama zaman kanta takeyi ta Gama sanin da Namiji me yayi Saura.


Muna jikin Motar da Ango yake tsaye mu da kawayena kaf Inna tana cewa Allah ya tsare kinji Allah ya kade fitina,a zauna lafiya kinji dai nasiha ta to Allah ya bada sa'a ya bada zuria dayyiba na manta ma kuka nakeyi nace Ameen Ameen Allah ya bani me hankali,Inna sai da tayi dariya da su Star ana ta dariya har angwaye, Inna tace aure sai hakuri kiyi hakuri da mijinki komai yace to banda musu da gardama da taurin Kai,ba a jayayya da miji,Miji yafi Gaban Wasa,Nawwar Yana gefe yace dama ta rainani Kuwa Inna,Inna tace wallahi idan kina so ki gama da duniya lafiya kibi Allah kibi mijinki yanzu ba da bane baki da kamarsa,yanzu mulkinki ya Kare shi zai haye karaga shi zai Fara nasa mulkin sai yanda yayi dake,Nawwar yace ai tuni ma na fara Inna,Inna tace lokacinka ne banga laifinka ba dan nan kayi abinka,Amma mace dai ki sani Rabi bata da wani yanci Matukar a gidan miji take,ta kalli Nawwar tace wallahi kai Kuma idan ka zalunci marainiya ubanka zaka ci a wajen Allah yo Allah ba ruwansa,ka kula da ita ka Zama gatanta ka Zama mijin marainiya,kaga Allah Kai ya damkawa amanarta Amana fa aka baka banda banbanci tsakanin matanka ka kamanta adalci, Kar kaji Daya tafi daya iya kwanciyar aure ka wulakanta daya,su Star suka kaure da shewa, Nawwar ya kalli Inna da sauri,Inna tace ae zaka zuba min Ido ku maza imaninku a nan yake da kunji ba bayani to mutunci ya Kare abinda kuka iya kenan soyayyarku kwanciya da mace ba uwar da kuka iya a nan kuka iya soyayya musamman hausawa sai a lokacin za a fara Ina sonki bani da kamarki,kece gwanata,jarumata,dausayin raina, kece tekun zuciyata,ya turmin dakan dake lugude a zuciyata Nawwar ya sheke da dariyar da bai shirya ba,kowa dake wajen motar dariya yake su Seraline harda ihu,Inna tace yo ai mun sani muma zamaninmu munyi soyayyar nan tsiyar maza wacce ce bamu gani ba,sai kana haihuwa shike nan an juya ma baya sabuwa ake nema Allah yasa kai a kudu kake Allah yasa dai ka koyi halin arziki,dariya na dinga Yi a boye cikin mayafi,Nawwar ma Dariya ta kume shi Khaleel dake Gaban mota da Driver sai dariya suke Kamar ba gobe,Nawwar yace mun gode Inna za a kiyaye,Inna ta furta ato kun girma dai idan Kun gyara ruwanku idan baku gyara ba ruwanku Inna tana gida tana baccinta.


Zamu Shiga mota tace ban Gama ba ke Rabi na sanki da zafi yanzu ba a wa miji Fushi,ba Kuma a juyawa miji baya ke gaki Allah ya albarkace ki da Ido kamar Madara ki dinga sanyaya Masa zuciya da kallo,ke bakisan da kallo ma idan mace ta Isa sai tayi juya Miji ba,Nawwar Yana ta dariya yace banda ni Inna,Inna tace wane mutum karya kake yaro baka hadu da tsohon Hannu bane mu irinmu muka sa Namiji a gaba ai ya shiga Uku,Muka sake kwashewa da dariya kaji tsohuwa wa zai kalleta ma harda yabon kai, Rabi nace Na'am tace kuka bazai fishshe ki ba sai kin tashi sosai gidan kishiya zaki, ba a kishin fada,duka ko zagi gasa ake a wajen me gida,idan ta bashi Onga Kinga kayan Miya ne dai ko to karki sake kuyi abu iri daya a'a ke karki bashi Onga ki bashi Madara,Idan ta bashi Milo ke ki bashi farfesu,haka akeyin tsere Nawwar kunya ta kamasu Ni Kuwa ko a jikina nace to Inna tace yawwa dare nayi kuje sai munyi waya,muka shiga mota kowa ya shiga Driver yaja mota dariya Kawai muke Yi Kamar me,Allah sarki Inna na bata Atamfa da leshi da sabulai cikin kayan lefena,sannan na bata kudi su Wise ma sun bata kudi akwai dadin Zama.


Sauran duk sun rigamu zuwa airport muna zuwa dama jirgi na kasa Muka shiga da kayan mu Nan ma an Mana pics duk an watsa a media,har Muka sauka lafiya na Kira Inna nace mun sauka ta Mana fatan Alheri na rufa mayafina a Kai Amarya sosai,Mami da kawayenta su Uku da Maman Khaleel da Sufia a Airport suka tarbemu cikin shigar su ta Alfarma, sauran abokan Ango da Ango bayan an sake pics suka tafi kowa sai Khaleel da Nawwar Suka shiga mota driver ya ja su zuwa gidan Khaleel can suka Yi wanka a part dinsa Suka canja Kaya sannan suka Yi Sallar magriba da Isha suka zauna suna kallon pics suna Hira da labarin irin dadin da bikin yayi.


Mu kuwa Mami tana gefe na a mota da sauran kawayena a wasu morocin Muka nufi gidan Sabreen,Mami a mota tana ta min Nasiha sosai akan zaman aure karshe tace dan Allah ki kiyaye ki farantawa Nawwar shima ya samu farin cikin da duk wani da Namiji ke samu karki biyewa rudun duniya da kawaye ki kula da aurenki ba abin Wasa bane shine darajar duk wata mace, rayuwar waje da Kika Yi wannan ya wuce da ba yanzu bane a manta da waccen rayuwar a Kama wannan kinji Rabiah dan Allah kiyi hakuri da halin kowa ku zauna lafiya,Kar naji ba daidai ba,nace Inshaallah,Mami tace ke ba yarinya bace Rabia kin San komai a kiyaye,Nawwar ya nuna Miki gatan da ba kowane zai iya ba,nace na sani Mami karki damu Inshaallah tace yawwa Yar Albarka Allah ya muku Albarka a haka Muka karasa gidan an canja tsarinsa gaba daya komai anyi sabo abin ya bada citta, Sabreen ta tashi a bacci tayi wanka ta fito Palo tana kallon furniture din da aka canja komai na gidan an canja an gyara ko Ina Yana kamshi mamaki ya kamata tace nasan dai anyiwa gidan nan gyara to waye yayi shara da mopping ko Ina na kamshi,wayarta ta tuna da ta kashe yau kwana kusan biyu bata tuna kowa lokacin ta sha kwaya da yawa,wayarta ta kunna ta kunna Data ta shiga WhatsApp Kawai taga wasu duk sun cire status din wasu sun saka bikin sabo da an kashe kudi musamman Dinner din,taga pics farrrr jamcy ta turo da videos ta bude nan ma Nawwar ta gani da Rabiah da kawayenta kamar ango da amarya,Pics din maza ta gani a masallaci alamar wajen daurin aure,sai ga pics din Amarya da ango a wajen daurin aure ga kawaye sai rawar Dj,tana bude wani taga Nawwar yayiwa Rabi Kiss a filin rawa suna ruwan kudi an ci uwar Naira,ihu ta saki tare da mikewa tsaye Zumbur tace na shiga Uku na,guda taji a gidan motoci suna ta shigowa,da gudu ta fada dakinta ta cire atamfar da ta saka ta canja Riga da wando tace yau za a kwashi bala'i kafin na sanar da Baffa da Iyamami,dama ba samu damar daukan Baffa a pics ba shi Yana daura aure ya fice ya bar kauyen daga nan ma kasar ya bari ya wuce US Dan karma a dame shi,yace wa Iyamami da Yan Uwa da matansa ya tafi Us su basu San ma daga wajen daurin aure ya wuce ba yayi haka ne Dan ace ai baya gari ma aka daura.


Sabreen wuka ta dakko a kitchen ta rike tana huci Yan kawo Amarya Suka shigo Mami ce a gaba sai kawayenta da Kuma su Sera,ai Sabreen tana ganin gayyar su Sera sunfi ashirin suna guda suna cewa wata tara a zubo Mana twins,Wise tana shewa tace a bawa ango local government sosai,yau Ango zaiji banbanci ya samu GRA masu kirji fanko a ja baya,Allah ya taimaki ango an kawo masa me kirji a cike,Mami kunya ta kamasu gashi sunki yin Shuru sai fitsara suke suna cewa ayi magana mu naushi bakin mutum, da sauri Sabreen ta wayance wukar data dakko ta ajiye a Center table tace daga kitchen na fito Ina girki ashe kune ta juya salin alin ta maida wukar inda ta dakko,sai ta zagaye ta bayan kitchen ta fice waje tare da tare taxi ta fada motar ta bar gidan a million, tana fita a gidan ta fashe da kuka sai gidansu tana yiwa me taxi bala'i yayi sauri.


Mami tace Sabreen fito Ina da magana da ku,Shuru shuru,Sera tace ta gudu fa ta bar gidan Naga fitarta,Mami tace Allah ya kyauta to,Sama aka haura da ni cikin hadadden dakina nima,sabo da a saman ma part uku ne,part din Nawwar,Nawa sai na Sabreen,kowa sai kallon gida yake ana yabawa,dukkan kayan lefena da tarkacen kayana har na gidan Karuwai da kayan gyaran jikina duk an kawo suna part dina su Misha su Muka bari tunda baza suje kauyen ba su suka shirya min komai na part dina har kayan Suka goge Suka gyara gidan ko Ina Kal Kal dama dakin ogan yasa key,Basu shiga part din Sabreen ba,sun Sha mamaki irin yanda suke karaf karaf a gidan amma bata tashi a bacci ba,ko Ina kamshi yake na musamman sunyi aiki babba na gyara gidan.


A gefen bed dina na zauna komai nawa na dakin milk and brown ne,Ina zaune mayafi a kaina,sauran Suka ce to Amarya sai munzo nan da sati asha amarci lafiya,na dinga musu godiya Suka tafi,su Mami ma da Sufia tafiya sukayi ya rage daga ni sai Sera,Star da Wise,na cire mayafin Muna ta hirar bikin Muna kallon pics,nace in ya bari na siyi waya Zan tura please ,Sera tace wallahi Indai sun tabaki ki Kira mu,nace ya zama dole,ki kula sosai Kinga ta Fara daukan wuka Kar ta shammaceki cewar Wise Nace Allah dai ya tsare, Sallah nayi abina, Suka Shiga kitchen Suka Sha Madara da lemuka Suka dawo Muna zaune har 10pm sannan Suka min Sallama zasu tafi nace zanyi kuka karku tafi,Muka kwashe da dariya har ni, nace sai na biku ni Muna ta dariya,nace wayyo first night ya zanyi tsoro nake ji,Muka fito tare Muna ta dariya sai ga Sabreen ta dawo a compound ta ganmu har Amarya tace Yan bariki tayi ciki da gudu,shareta Muka yi Amarya ce da rakiya har waje kofar gida,Nawwar ne ya karaso da motarsa da mamaki glass ya sauke ya musu godiya sosai yace a fadawa sauran Yana godiya Suka ce zasu ji Suka Shige Napep din da Suka Kira sai gidan bariki, kirji na dafe nace Allah sarki Kwalta,Stree ohh duniya Ashawo work me Dadi da yanci ai Zan dawo ne soon ana sakina Zan dawo Yan Uwa Ina nan zuwa ba da dadewa ba nace bye bye Street Ina daga hannu,Nawwar Yana kallona Yana ji tunda a saitina yake glass dinsa a sauke yake,Kai ya girgiza yace in kin gama sai ki koma ko,ciki na shiga na koma dakina da sauri na rigashi shiga na zauna saman bed na jawo mayafina na rufe kaina zuwa fuskata na nutsu,ya shigo lokacin tsaki ya ja ya ajiye min ledata cike da nama da abin dadi,Daya ledar hannunsa dakin Sabreen ya nufa.


Ya isketa ta dora Kai a jikin mudubi tana rusa uban kuka,shi dariya ma ta bashi yaushe ta Fara kishinsa,Kafadarta ya dafa tare da furta Babyna lafiya bai taba kiranta da Baby ba sai yau,mikewa tayi tsaye Zumbur tare da daga masa Hannu tace dakata Malam me zaka ce dani zakayi aure ka fada min baza ka fada min ba sabo da cin amanarka sabo da zaka auri Karuwarka ai ka Dade kana cin Amanata tun kafin ayi aure ka Gama da ita dole ka boye min Kuma kaje gobe Iyamami tana nemanka,Murmushi yayi yace karki sake Kiran matata da karuwa ya Zama last idan ba haka ba Zaki ga abinda Zan Miki Kuma Iyamami ta Isa dani ne bazan je ba ki fada Mata kice nace baza a zo ba duk abinda zakiyi kiyi, aure kuma na kara ke kin Isa wace ke da sai na fada Miki tunda bacci Kika zaba kije ya isheki yaja tsaki tare da jefar mata ledar namanta ya fice abinsa.


Part dinsa ya shiga ya kalli ko Ina kaca kaca duk dirty babu me gyara Masa shi kyankyaminsa ma yaji a haka yayi wanka ya fito ya shirya cikin kayan baccinsa ya kwanta sai bacci,ni kuwa ganin yaki shigowa na bude naci abinda zan iya na ajiye sauran nayi wanka da brush nayi Shirin bacci cikin gown Yar guntuwa ko cinya bata rufe ba peach nayi adduoi sannan na kwanta baccin gajiya ko farkawa banyi ba sai asuba,na tashi Ina saman Sallaya ya dawo daga masallaci ya bude kofata a hankali tare da lekowa ya ganni saman Sallaya juyawa yayi ya wuce abinsa ban ma San ya leko ba,part din Sabreen yaje ya duba tana ta bacci tashin duniya yayi taki tashi hakura yayi ya koma dakinsa ya koma baccinsa.


8am na tashi na gyara ba garena Kal Kal Yana kamshi,fitowa nayi na gyara ko Ina har Palo dama ba dirty sabo da jiya an gyara,masu kula da compound sunyi nasu,part dinsa na shiga Yana bacci, toilet na fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login