Showing 12001 words to 15000 words out of 133697 words

Chapter 5 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt

yanzu zan shiga ciki nashirya Insha Allah, to shikenan sai ka shirya ga breakfast dinka nan na jiran ka a dinning, to Ammy ya fada hadi da nufar part din sa.............


✨ _Victoria_ . ✨


Anguwace ta christianity irin ta masu kara min Karfi, destiny naga ni ta fito da ga wani gida ta nufi wan da ke opposite din inda ta fito jikin ta sanye da gown iya gwiwarta purple color kanta da kitson kalaba na attachment ka farta sanye da flat shoe, gidan dan karami ne, ko ina ya sha cement dakuna biyu ne a gidan nufar daya daga cikin kofofin tayi knocking hadi dacewa" excuse" daga cikin dakin naji ance "come in" tura kofar tayi hadi da shiga Victoria ce acikin
dakin tana ta faman jan straight gown taki shigar ta destiny ce tace " lallai Victoria a she bakima shirya ba kin kuwa san nisan da wurin ya ke da shi sai fa munfita Lagos kuma fa kinsan yau ana zuwa church da yamma, sorry destiny yanzu zan shirya mu tafi, abun da yasa ma nayi late bari nayi sai momy ( mahaifiyar ta ) ta tafi market sannan domin in tasan inda zamu ba zata bari mu tafi, Victoria naga ma shiryawa suka fita gidan tafiya sukayi sai da suka hau kan titi tukun suka tsai da mai mashin suka hau, tafiya su kayi mai dan nisa sannan suka kawo wani dan karamin kyauye duk duwatsu suna kawowa inda mashin bai wuce wa suka sauka, kudin sa suka bashi su kuma suka cigaba da tafiya nanma sai da su kayi tafiya ba laifi tukun suka kawo wata yar bukka ita kadai a wurin sai mutane jere a bakin bukkar suna karaso wa suma suka bi layi, sun jima a tsaye layi bai zo kansu ba, victoria harta gaji da tsayuwa ta duƙa, lokacin da layi ya zo kansu shiga sukayi tare cikin bukkar, wani mutum ne zaune gaban sa wasu kahuna ne sai kawunnan mutane kwaran gwal jikin sa sanye yake da jajayen kaya fuskar sa duk ta sha digedige fari sai idanun sa kewaye da bakin fenti gaishe dashi sukayi dawani irin yare mara dadin ji shi kuwa kwashewa yayi dawata irin dariya sannan ya tambaye su meke tafe dasu, destiny ce ta kora masa bayani a kan abun da yake tafe dasu, dariya ya sake kwashe wa da Ita sannan yayi yan surkullen shi wani magani ya dauko cikin wani bakin tulu ya basu destiny tasa hannu ta karba ita kuwa Victoria sai zare idanu take kudi suka dauka masu yawan gaske suka ajiye a gaban bokan sannan suka fice daga bukkar ta hanyar da suka biyo ta nan suka bi sai da suka kawo cikin kyauyen tukun suka samu wani mashindin ya dawo dasu gida, gidan su destiny suka wuce dan lokacin kafe 4:15 dakin destiny suka nufa zama sukayi suna huce gajiyar tafiya destiny ce tace" ina zuwa" tana fada ta fice daga dakin batafi 1 minute ba ta dawo da kwano a hannun ajiye shi tayi gaban Victoria fita ta sake yi sai gata ta sake shigowa hannun ta rike da pure water guda biyu zama tayi hadi da bude kwanon sakwara ce da miyar okra ( kubewa) suna cikin ci saiga wani namiji ya shigo dakin sanye ya ke da crazy jeans sai singlet gashin kansa kuwa yasha dada ( yanda yan iska keyima gashin su ya koma kamar lagwani )da kaga yana yin sa zaka san a buge yake, ya na ganin Victoria ya kama washe baki daure fuska Victoria tayi tana ganinsa , kusa da Ita ya matso kamar zai yi hugging din ta ba shiri ta mike tsaye hadi da daka mashi tsawa tana cewa" which kind of this nonsense samuel " bangane wulakanci ba Victoria you are my wife ya fada yana washe baki, destiny dai na gefe tana kallon su bata ce masu kala ba sai da taga Victoria na niyyar fita da ga dakin sannan taba Victorian hakuri shi kuma Samuel ce mashi tayi "ya fita ya basu wuri tun da shi ba shi da hankali , Victoria tace bata son shi to mi yasa zai ta kura ma rayuwar ta, Komawa Victoria tayi ta zauna sai wani cika take tana batsewa, suna kammala cin a binci fita su kayi bakin wani fanfu suka wanke hannu Victoria ce tace "destiny zan tafi gida domin nayi shirin zuwa church din kuma kin ga momy bata san nafita ba kar ta dawo bata ganni ba, kawai dai kinson zuwane amma aikin san bata dawo ba, da ta dawo da mun iske momy ( mahaifiyar destiny ) a gida itama ta dawo tun da wurin business din su daya, kuma tare suke fita su dawo tare, to kawai Victoria tace, komawa su kayi dakin, destiny tace " kinsan fatan da nake kuwa Victoria, Aa sai kin fada Victoria ta fada tana sauraron mi destiny zata ce, so nake wannan wawuyar hidaya ta taya ki bama dr hakuri kamar yarda da tace, a samu sa'a shi kuma ya maida ki uhmmm zata sha mamakin abun da zamuyi mata dan sai munrabata da eko ma gaba daya yan da ba zata sake ganin dr ba, nima haka nake so zata sha mamaki In dai ya mai da ni wuri na, dariya sukayi harda ta fawa suna nan suna shirya yan da za su yima hidaya sai ga mahaifiyar destiny tashi go , suna jin shigo warta suka fito daga dakin gaishe da Ita su kayi yayin da destiny ke amsar kayan da momyn ta ta shigo dasu, Victoria ce tace "ni na tafi" to saina shigo destiny ta fada tana fita gida ta shiga momynta ta samu a dakin zaune cewa tayi" good afternoon momy , afternoon daga ina kike na shigo baki nan momyn tafa da , ina gidan su destiny ne momy, ok kawai momyn tace, wurin 5:00 suka shirya domin zuwa church ( suna zuwa church su duk ranar Asabar domin gyaregyre sbd lahadi ) gidan su destiny , Victoria taje daga chan suka wuce church din.........


_Katsina......_


Mom ce zaune a main falo suna fira da baaba larai abdallah ne ke saukowa daga stairs case jikinsa sanye da jallabiya wurin su mom ya zu hadi da cewa fira kuke ne nagan ku zaune, wlh kuwa sai ina haka naga kasha jallabiya mom tafada amsa ya bata da cewa zan danje wani wuri ne daga nan zan tsaya sai angama sallah sannan zan dawo, mom tace" ah kace wurin diyata za'a amma sai kaje mata da jallabiya sai kace wani limami, murmushi kawai yayi hadi da cewa " mi za kiyi da wata diya keda kike da yan biyu duk mata a gaban ki, mom ce tace " duk da ina dasu kari ai bai kin dadi koh baaba larai" haka ne kuwa hajiya baaba larai ta bata amsa, Mom ce ta kuma cewa" ni dai yau she zaka kawo man surukata gidan nan" abdallah ne yace " ki bari mom dana samu wacce ta dace dani zan kawo maki Ita har gida, uhmmm Allah ya shirye ka abdallah wata kan har yanzu baka samu wacce tada ce da kai ba ko, nasan maganinka ai sawa xanyi abie dinku ya zabo maka mata tun da kai ka kasa Mom ta fada, abdallah yace" haba mom kamar ni za'a za boma mata, ai kuwa dana bani , yo ai sai abokaina suyi man dariya, mom tace" to In dai baka son auren dole to ka fito da mata kayi aure, kai ko kunya bakaji shekara 30 fa amma ace baka da mata haba ina amfani ' dan Allah mom kibar batun auren, dolenan , In dai aure ne very soon zanyi in Allah ya yarda, Allah ya yarda mom ta fada, ni na wuce sai na dawo ya fada hadi da nufar kofar fita, a dawo lafiya mom ta fada , fira mom suka cigaba Ita baaba larai suna nan zaune sai gasu Aaimah sun shigo da'a lama daga Islamiyya suke dan jikin su sanye suke da hijabi blue color gaishe da su su kayi sannan suka nufi bedroom din su wanka su kayi hadi da alwallar magrib sannan suka sanya kaya marasa nauyi a daki suka zauna har sai da su kayi sallah isha tukunnan suka fita falo fira sukeyi a kan Islamiyya anan mom tasa me su har da abie wanda baijima da dawowa ba daga masallachi nan sukai ta fira har 9:00 sannan su kayi dinner kowa ya wuce dakin sa suna shiga daki wayar Aairah na ringing dauko wayar tayi dake ajiye kan bedside murmushi tayi data dauki wayar taga mai kiran Aaimah ce tace " halan ya mus'af ne, daga mata kai Aairah tayi to sai da safe domin nasan ke ba yanzu ba Aaimah ta fada hadi da hayewa kan bed taja blanket Ita kuwa Aairah zama tayi bakin bed ta cigaba da waya ba Ita bace ta gama wayar nan ba sai wurin 10:55 sannan ta haye bed adu'a tayi ta shafa hadi da shafa ma Aaimah sannan taja blanket Ita ma bayan ta kashe bulbs da bedside lamp.....
Asuba ta gari yan biyu 😴


Episode 7_8


Mom ce zaune a main parlor suna fira da baaba larai ya abdallah ne ke saukowa daga stairs case jikinsa sanye da jallabiya wurin su mom ya nufo hadi da cewa "fira kuke ne nagan ku zaune? "
"eh , sai ina haka nagan kasha jallabiya" mom ta fada amsa ya bata da cewa zan danje wani wuri ne daga nan zan tsaya sai angama sallah sannan zan dawo, mom tace" ah kace wurin ɗiyata za'a, amma Sai ka je mata da jallabiya Sai kace wani limami," murmushi kawai yayi hadi da cewa " mizakiyi da wata diya ke da kike da yan biyu duk mata a gaban ki, mom ce tace " duk da ina dasu ƙari ai bai ƙin daɗi koh baaba larai? " haka ne kuwa hajiya baaba larai ta bata amsa, Mom ta kuma cewa" ni dai yaushe zaka kawo man surukata gidannan? " abdallah ne yace " karki damu mom, dana samu wacce ta dace dani zan kawo maki ita har gida, uhmmm Allah ya shirye ka abdallah wata kan har yanzu baka samu wacce tada ce da kai ba ko, na san maganin ka ai, sawa zanyi abie dinku ya zabo maka mata tun da kai ka kasa Mom ta fada, ya abdallah yace" haba mom kamar ni za'a zaɓo ma mata , ai kuwa dana ji kunya, yo ai sai abokaina suyi man dariya, mom tace" to In dai baka son auren dole to kafito da mata kayi aure kai ko kunya bakaji shekara 30 fa amma ace baka da mata, haba ina amfani ' dan Allah mom kibar batun auren dolen nan In dai aure ne very soon zanyi in Allah ya yarda, Allah ya yarda mom ta fada, ni nawuce sai na dawo ya fada hadi da nufar kofar fita, a dawo lafiya Mom ta fada , fira mom suka cigaba Ita baaba larai sai gasu Aaimah sun shigo daga Islamiyya jikin su sanye da hijabi blue color, gaishe dasu su kayi sannan suka nufi bedroom din su , wanka sukayi hadi da al'walar magrib sannan suka sanya kaya ma rasa nauyi a daki suka zauna har sai da sukayi sallah isha tukunnan suka fita parlor,kan sofa suka zauna suna fira islamiyya a nan mom ta same su harda abie wanda baijima da da wowa ba daga masallachi nan suka zauna suna fira har 9:00, sannan sukayi dinner kowa ya wuce dakin sa , suna shiga daki wayar Aairah na ringing dauko wayar tayi dake ajiye kan bedside tana murmushi ganin mai kiranta, Aaimah ce tace " halan ya mus'af ne, daga mata kai Aairah tayi, to sai da safe domin nasan ke ba yanzu ba Aaimah ta fada, bed ta nufa ta kwanta taja blanket , Ita kuwa Aairah zama tayi bakin bed ta cigaba da waya, ba ita bace ta gama wayar nan ba sai wurin 10:55 sannan ta haye bed, adu'a tayi ta shafa ta shafa ma Aaimah sannan taja blanket Ita ma bayan ta kashe bulbs da bedside lamp.....


_Washe gari........_


Zaune suke kan sallaya suna adu'a da tasbihi, tashi Aaimah tayi daga kan sallayar ta nufi inda suke Ajiye Alqur'ani , guda ɗaya ta ɗauko, kusa da Aairah ta dawo ta zauna hadi da mika mata tana cewa" sister amsa in karanto maki haddar da nayi, inda nayi kuskure saiki gyara man,"
to in dan na gama maki nima sai ki amsar man"to Aaimah " karatu ta fara cikin ƙira'a mai daɗi ,Aairah na sauraron ta inda tayi kukure sai ta gyara mata, sai da suka gama amsar ma junan su hadda tukunnan suka mai da qur'anan wurin da suke a jiye su , fita suka yi daga bedroom saboda gari ya waye Ƙarfe 7:00 na safe, main parlor suka nufa a kitchen suka samu mom da baaba larai suna hada breakfast gaishe dasu sukayi , amsa masu su kayi cikin kulawa Mom tace " ina fatan dai kungama hardar ku ta yau, eh mom , to masha Allah, baaba larai tace " kace muna da bikin hadda dana kammala makarantar gagarumi gidan nan, to Allah ya taimaka ya nuna mana lokacin lpy" har hada baki suke wurin cewa ameen, kama masu aikin su kayi harsuka gama sannan su Aairah suka jera kan dinning, bedroom din su suka koma domin shirin zuwa Islamiyya ( Islamiyyar harda suke, in suka tafi tun safe sai yamma duk ranar weekend, Idan kuma ba weekend bane karfe 2:30 suke zuwa sutaso da yamma, amma ban da ranar Friday in kuma an yi hutun school to kullum ne ban da friday .)
Aaimah ce ta fara shiga toilet domin yin wanka ita kuma Aairah uniform dinsu na Islamiyya ta dauko masu tare da bags dinsu , Aaimah na fitowa itama ta shiga shaf shaf Aaimah ta shirya cikin uniform din san da Aairah ta fito har Aaimah ta gama shirin ta ita ma cikin kankanin lokaci tashirya suna gamawa suka fice zuwa main parlor dinning suka nufa domin yin breakfast suna gamawa part din abie da na mom suka nufa domin ce masu zasu tafi , a dawo lpy suka yi masu , fita su kayi harabar gidan anan suka samu mudi na jiran su dan shine ke kaisu, sai wurin 10:00 su mom su kayi nasu breakfast din saboda weekend........


✨ _SHAZIM_ ✨


Yau sunday baya zuwa aiki , kwance yake kan sofa a bedroom din sa ya baje papers da laptop din sa yana, tun da ya gama sallar asuba ya ke nan wurin yana aiki har bacci yayi awan gaba da shi, jikin sa sanye yake da jallabiya, wayarsa ajiye saman cikin sa yayin da ya sa ɗayan hannun sa ya rufe fuskar sa, wayar sa dake saman cikin sa ce ta fara ringing, hannun sa dake kan fuskar sa ya janye yana ya tsina fuska alamar an katse mashi baccin sa , daukar wayar yayi "Brother" shine sunan daya bayyana akan screen din wayar picking call din yayi hadi da Kara wayar a kunne " hello Yaya na cikin wayar ya fada, "ba zaka chanza ba ko noraiz , ina amfanin wani hello kana muslim "
" a fuwan big bro noraiz ya fada, Allah ya shirye ka, ameen Yaya ka tashi lpy yasu Ammy da fatima? , lafiya lau suke kaifa, Ina fatan kai ma kana lafiya? , ina lpy Yaya, oka Masha Allah shazim ya fada hadi da cewa ya maganar da wowar ka yau, domin da naga kiranka nayi tuna nin kace man ka iso dan nasan halin ka da chanza lokaci idan zaka dawo , A'a ba haka bane Yaya ina nan zuwa yau din Insha Allah , kawai dai ban samu biyo jirgin safe bane shiyyasa nakira ka na fada maka sai dai da yamma insha Allah, ok Allah ya kawo ku lpy, ameen Yaya sai an jima, ok kawai shazim ya faɗa hadi da kashe wayar ya ajiyeta kan center table, sai da yayi 5 minutes a kan sofar sannan ya mike, papers din da ya baza ya kwashe da laptop ya saka cikin din briefcase, cire jallabiyar dake jikin sa yayi ya koma da gashi sai shorts toilet ya nufa ya jima a toilet din sannan ya fito ya nufi dressing mirror anan ma ya jima yana yan shafe shafe sai kace mace sannan ya nufi clothes dinsa shiryawa yayi cikin jeans and T_ shirt fita yayi daga bedroom din part din Ammy ya nufa a parlor ya same ta Ita ka dai, fatima na Islamiyya, gaishe da Ita yayi , amsa mashi tayi wuri ya samu ya zauna kusa da ita, Ammy tace " ga breakfast dinka chan kan dinning tun dazu har nayi tuna nin yau baka fitowa a daki za kayi weekend , wane ni Ammy , kina a gida na zauna daki, ai dole na fito na tayaki fira, tun da auta na Islamiyya kuma rigimenmen ki baya nan duk da yau zai dawo , murmushi kawai Ammy hadi da cewa kunyi waya da shine naji yace da safe jirginsu zai taso, kin dai san halin ka yanki Ammy da chanza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login