Showing 90001 words to 93000 words out of 133697 words
Chapter 31 - Doctor Shazim season one by Kainaat .txt
a ɗakin fatima ta kwana.
Shazim bedroom ɗin shi ya shiga yayi wanka ya canza kayan da ke jikin shi zuwa na bacci parlor ya dawo wurin Abdallah dake zaune yana latsa wayar shi shima sanye yake da pajamas, kallon shi shazim yayi yace " ka shiga ka kwanta ni zan kwana wurin fatima dan ina kyautata zaton zata iya farkawa a kowane lokaci "
"bana jin bacci, kai idan kana ji zaka iya kwanciya ni sai na zauna na jira ta farka " murmushi shazim yayi dama ya san in dai yace zai haka to Abdallah bazai kwanta ba
"ko ina jin bacci dole na haƙura"
"kai kana ma ji ke nan "
"na san kai ma kana ji sai dai ka ƙi kwanciya "
"to ina ji bazan kwanta ba"
"to ai shikenan " shazim ya faɗa haɗi da miƙewa ya ɗauki laptop ɗin shi, tashi Abdallah yayi ya bi bayan shi, medical room ɗin su ka nufa kan sofa suka zauna, shazim na aiki a laptop yayin da Abdallah ke aikin latsar waya......
_Episode 46_47_
..........Medical room ɗin su ka nufa kan sofa suka zauna, shazim na aiki a laptop yayin da Abdallah ke aikin latsar wayar shi,suna ɗan taɓa fira jefi jefi, har shazim ya gama abun da yake a laptop fatima bata farka ba, wajen Asuba ta fara mutsu mutsun farkawa, da sauri su ka ƙara sa wurin ta, sai kiran sunan Ammy take da shazim,sai ƙoƙarin tashe take mai da ta yayi ya kwantar "ya shazim ina Ammy " fatima ta faɗa
" Ammy tana ɗaki bacci take, ya jikin naki "
"ya shazim ina nake "
"kina gida ya jikin "
"ya shazim ina ta kiran ka amma baka zo ba "
"yanzu ai gani a kusa da ke "
"ya noor ma da Ammy duk na kira su amma basu amsa man ba, ya luqman so yayi ya kashe ni ya shazim " ta faɗa hawaye na bin idanuwan ta, sosai ran Abdallah ya ƙara ɓaci da abun da fatima ta faɗa
"kiyi haƙuri kinji, bazan sake bari wani abu ya faru dake ba insha Allah, ki kwantar da hankalin ki "
"dan Allah ya shazim kar ka bari su Aura man shi wallahi bana son shi "
"bazan taɓa bari su aura maki shi ba karki damu "
"ya ina son ganin Ammy "
"Ammy bacci ta ke fatima, dare ne yanzu ki bari sai da safe zata zo kinji "
Abdallah na gefe ya ƙira mata ido ji yake kamar ya mayar da ciwan a jikin shi tsabar yan da yake jinta a cikin jikin shi
"zaki sha ruwa ne " shazim ya faɗa ganin tana miƙa hannu alamar wani abun zata ɗauka, girgiza mashi kai tayi
" Eh ya shazim " hannun yasa ya ɗauko ruwan da ke kan table ɗin da magungunan ta ke kai cire marfin jirkar yayi da kanshi ya bata a baki, bata wani sha sosai ba ta kauda kai, ajiye jikar shazim yayi yana cemata " ki koma ki kwanta " da to ta amsa haɗi da komawa ta kwanta drip ɗin da ke jikin ta ya cire mata
"zaki sha tea ko " ya tambaye ta, ɗaga mashi kai tayi alamar eh
"Ok bari na kawo maki sai kisha maganin ki daga nan " ya faɗa haɗi da tashi ya bar gaban gadon kallon Abdallah dake tsaye ya zuba ma fatima ido kamar ya cinye ta yayi " lafiya dai ko?" ya tambayi Abdallah haɗi da tsare shi da idanu, kawat kawata hankalin Abdallah na kan fatima bai ma san shazim na mashi magana ba, har sai da shazim ya ɗan taɓa shi tukun ya dawo cikin hankalin shi, zuba mashi ido yayi yana kallon shi
"malam lafiya ka wani tsare ni da idanu " Abdallah ya faɗa yana wani shana mur
"kai zan tamabaya ai wannan " shazim ya faɗa yana zuba mashi harara, jin muryar Abdallah ne yasa fatima jutuwa da sauri ta kalli inda suke tsaye shi da shazim
"Ya dr " fatima ta kira sunan shi cikin kasalelliyar murya ta marasa lafiya, matsawa yayi kusa da ita yana faɗin " "na'am fatima, ya jikin ki" hawaye ne su ka taru a idanuwan ta tace " ya dr, yaushe kazo "
"tare muka zo da ke, ya jikin " ya faɗa haɗi da neman wuri bakin gadon ya zauna, fita shazim yayi zuwa part ɗin shi .
hannun ta Abdallah ya kamo yana faɗin "fatima ina tambayar jikin ki kinyi shiru "
"ya dr da sauƙi "
"Allah ya ƙara sauƙi "
"Ameen" shazim ne ya shigo hannun shi ɗauke da cup ɗin tea sai turiri yake,kusa da gadon ya matso, amsar cup ɗin Abdallah yayi yana faɗin
"tashi ki zauna kisha tea ɗin " yunƙurin tashi tayi, aje cup ɗin yayi kan table domin ya tai maka mata ta tashi tun kafin ya ajiye shazim ya kamata ya tayar da ita zaune,
" thanks" Abdallah yace, harara shazim ya zuba mashi murmushi kawai Abdallah yayi da kanshi ya shiga bata tea shazim kuma na duba mata magungunan da ya kamata ta sha, da ta kammala sha amsar magungunan Abdallah yayi ya miƙa mata da kanshi tasha, matsowa shazim yayi da allura a hannun shi yana faɗin " to malam matsa " juyowa Abdallah yayi yana kallon shazim dake tsaye hannun shi riƙe da allura,
"ka matsa nace bawai ka kallan ba "
matsawa Abdallah yayi yana faɗin
"ka dai yi a hankali dan nasan halinka, ban da mugunta"
"ka san Allah zanyi maka ita idan baka yiman shiru ba ɗan rainin wayau kawai " shazim ya faɗa yana nuna ma Abdallah allurar da ke hannun sa
" zaka iya " Abdallah ya faɗa haɗi da nufar kan sofa ya zauna, fatima dai sai binsu take da idanu abun ba ƙaramin burgeta yake ba, matsowa shazim yayi kusa da ita yana faɗin "miƙo man hannun ki " hannun rigar da ke jikin ta taja haɗi da miƙa mashi hannun, a damtsen hannun ta yayi mata alurar yana tsirawa ta rintse ido da sauri Abdallah yace "wai Allah, dan Allah kayi mata a sannu "
" ka takura man fah, ai da zuwa kayi ka amsa kayi mata da kanka " shazim ya faɗa
" bana iya yi mata allura ai " tsaki shazim yaja " aikin banza da na wofi "
" kai kaga aikin banza " fatima sai murmushi take dan ba kaɗan su ke sata nisha ɗi ba, lura da hakan ne ma yasa shazim biye ma Abdallah har sai da wani baccin ya sake ɗaukar ta tukun su ka bar ɗakin dan lokacin sallar asuba yayi, alwala su kayi a part ɗin shazim su ka nufi masallaci tare da noraiz su ka tafi, lokacin da su ka dawo Ammy da sa'ada su ka samu a medical room ɗin tare da fatima da ta sake farkawa, gaishe da Ammy su kayi haɗi da zama kan sofar da ke ɗakin har sai da gari yayi haske tukun su ka tashi su ka bar Ammy da sa'ada Innah Asabe ma ta shigo ta duba jikin fatima,da ta tashi tafiya kitchen bin ta sa'ada tayi ta shirya ma fatima lafiyayyen breakfast, duk da bakin nata ba daɗi haka Ammy da sa'adar su ka tasa ta gaba sai taci, ganin sun damu taci ne yasa ta daure badan tana jin da ɗin shi ba taci sosai sa'ada taji daɗin ganin taci, fatimar ma daɗi taji ganin yanda kowa ke nan nan da ita ta kuma ji daɗin ganin ƴan uwan ta a tare da ita, ko da Ammy ta kira malam ta sanar da shi farkawar fatima hamdala yayi ma ubangiji kuma da safen ya sa driven shi ya kawo su shi da ummy, da shazim bari yayi sai anjima yaje ya ɗauko su da kanshi sannan ya sanar da su farkawar fatimar, amma sai Ammy ta riga shi kiran malam sai dai kawai ya gansu sun zo, majeed ma ya zo shi da mamar shi sun daɗe gidan sosai sannan su ka tafi,shazim da har ya shirya zai je Abnoor sai ga kabir ya zo duba jikin fatima, tun jiya ya kira wayar shazim bai ɗauka ba shine ya kira noraiz, shine noraiz ɗin ya sanar da shi ai sun dawo da rashin lafiyar fatima, shine daya fito daga gida zai je eko ya fara zuwa nan dan ya duba jikin ta,da kabir ɗin zai wuce ne ya shirya su ka tafi tare ba yanda bai yi da Abdallah ba akan ya bishi su tafi amma yace zai tsaya idan lokacin shan maganin fatima yayi zai bata har ce mashi shazim yayi ai Ammy na nan amma ƙiri ƙiri ya ƙi binsu, tafiya shazim yayi ya bar sa shima bai wani jima ba ya wuce Abnoor can ma ana yi sallar asr ya dawo, Abdallah da ya zauna gida kulawa sosai ya ba fatima da tace kaza jiki na rawa zai yi mata shi tun yana ba Ammy mamaki har ya dai bata mamaki, dan sosai ya cire duk wata kunya daya ke ji ta Ammy,su malam kuwa ba ƙaramin daɗi yaji ba ganin yanda Abdallahn yake kula da fatima a gaban su, har kiran Abie da mom yayi ya ba Ammy da malam har da ummy su ka gaisa su ka kuma yi ma su ya mai jiki, sai da daddare su malam suka tafi akan gobe ma zasu dawo su sake duba jikin ta.
haka fatima ta cigaba da samun kulawa daga wurin kowa a cikin su har ta ɗan samu sauƙi ta ma koma ɗakin ta da zama yanzu ba'a mata allura magunguna kawai take sha, kwanan Abdallah huɗu ta wuce katsina dan tun tuni uncle ahmad ya tafi, ya tafi ne akan zai dawo ya sake duba jikinta shi da su Abie, kamar tayi kuka da zai tafi taso ace ya ɗan yi kwana ki da yawa cematan da yayi zai dawo ne yasa ta haƙura.
Shazim kullum kafin ya tafi aiki sai ya tabbatar da taci abinci kuma tasha maganinta, noraiz ma ya fara aiki
kulawa kowa yake bata hakan yasa ta ƙara jin daɗi kuma jikin ta Alhmdllh masha Allah dan ba inda bata zuwa, kuma taji daɗin da sa'ada ta biyo ta.
Satin su ɗaya da dawowa lagos su uncle Ahmad su ka zo da uncle Ibrahim, kairiyya, feenah, gwaggo Halima , luqman har da momy da mama, mansoor bai samu zuwa ba saboda aiki amma yace insha Allah yana nan zai zo idan ya kammala, ba yanda ba su yi da innah da gwaggo Uwani su zo ba amma tace wallahi ita ba zata zo ba ta so ma ta hana su uncle Ahmad ɗin ma zuwa amma su kace su sai sunzo sun gaishe da fatima.
Fatima gaba ɗaya hankalinta tashi yayi da ta ga luqman dan ta tsorata da shi,bawan Allah duk ya sha jinin jikin shi ganin yanda take ɗari ɗari da shi, ga wani kallon tsana da shazim ke binshi ga Ammy kwata kwata ta ƙi bashi fuska ko da ya gaishe da ita kadarn kadaham ta amsa mashi ƙarshe ma tashi yayi ya bar parlorn ya nufi parking lot ya zauna a mota , haɗa kan shi yayi da siti yarin mota duk ji yayi ya tsani kan shi yayi kuma daya sanin abun da yayi mata, ganin duk ya damu ne ya kuma ware kanshi ne yasa Ammy ta ɗan saukko tanuna ba komai komai yawuce har ta sa noraiz ya kira mata shi, ko da yazo haƙuri ya bata akan abun da yayi fatima, ta kuma ce ta yafe mashi amma a zuciyar ta ɗauki alƙawarin ba zata bari ya auri fatima ba
Fatimar ma ba yanda ba'ayi da ita ba akan ko magana tayi ma luqman ɗin ko da bazata yafe mashi ba amma taƙi.
Fennah sai ƙoƙari take taga shazim ya kula ta amma ya ɗure fuska ko kallon banza bata ishe shi ba,da su uncle su ka tashi tafiya ƙin binsu feenah tayi dole ita a nan zata zauna, ganin ta dage ne yasa Ammy cewa a barta idan mansoor yazo sai su koma tare harda kairiyya ma, sa'ada daman ba mai maganar ta dan cewa tayi tun da fatima baza tai karatu abuja ba to ita zata yi lagos , ko da tace haka dady bai yi musu ba ya amince mata.
da zasu wuce sai da suka je gidan malam,su ka kuma roƙi afuwar shi akan abun da luqman ɗin yayi, ya kuma haƙura yayi masu Allah ya kiyaye hanya.
Shazim fa har su ka tafi ban da gaisuwa babu abun da ya haɗa shi da su har su ka bar garin.
Abdallah kamar yan da yace kwanan shi biyar da tafiya, ya dawo shi da uncle Ahmad mom da ummh, abie bai samu zuwa ba saboda wani uziri daya tsare shi, hakan yasa su ka zo su ka ɗai ban da shi, Ammy taji ɗadi sosai ta kuma yi masu godiya, fatima kamar tayi dan bata taɓ gaini mom ba a zahiri sai dai photo da waya sai ga shi yau taga mom ido da ido.
wani abu da na lura da shi kallon da mom ke ma ammy da wanda ammyn ke ma mom kamar sun taɓa ganin juna ko, duk da sun kasa tuna inda su ka taɓ ganin juna.
A ranar su mom su ka koma katsina Abdallah kuma sai da yayi kwan biyu tukun ya koma.
_* to masu karatu kar ku manta an tafi an bar Feenah da kairiyya akan idan mansoor ya zo za su tafi tare da shi , yanzu wasan zai fara amma kafin nan ina so na sanar da ku waye shazim*_
_*WANENE DR ABDULƘADIR ABUBAKAR NURADDEEN ( SHAZIM) *_
Dr shazim ya ka sance ɗane daga zuriar alhaji nuraddeen ahmad sharani.
Alhaji nuraddeen sharani, mutum ne mai rufin asiri, ya ka sance ɗan kasuwa ne mai sayar da kayan masarufi, alhaji nuraddeen yana zaune ne a garin kurfi dake jahar katsina, anan cikin garin yake gudanar da harkar kasuwancin shi da ƙauyakun da ke kusa da garin kurfi.
Alhaji nuraddeen yana da mata ɗaya tilo mai suna habiba ana kiran ta da ruma, ita ma yar cikin garin kurfi ce, barumiya ce kyakyawar gaske, shekarar su goma cif da aure Allah bai basu haihuwa ba, ruma kullum cikin tashin hankali take saboda tsangwamar da iyah ( mahaifiyar nuraddeen ) ke mata ita da ƴaƴen ta, har ta kai ko hidima suke ruma bata zuwa saboda kyara da tsangwama da suke mata, ganin yanda hankalin ruma yake atashe yasa nuraddeen ya shiga kwantar mata da hankali yana nunamata cewa Allah yana sane dasu kuma zai basu haihuwa karta damu da duk abunda ƴan uwan shi ke cewa, sosai yayi mata nasiha akan su cigaba da adu'a kawai, kwantar da hankalin ta tayi ganin mijinta bai damu da rashin haihuwar ta ba, mahaifiyar nuraddeen ta takura ma shi akan dole fah sai ya ƙara aure tunda matar shi bata haihuwa, nuna mata yayi baya buƙatar ƙara aure, indai haihuwa ce Allah zai ba ruma, sosai ran iyah ya ɓaci jin abunda ya ce ta kuma ɗauki fushi da shi akan ƙinbin umarnin ta da yayi, har gida taje ta samu ruma tayi mata cin mutunci, duk a tunanin ta ita ta hana nuraddeen ƙara aure saboda ta shanye shi, sosai tsanar da yan uwan nuraddeen kema ruma ta ƙaru saboda ƙin ƙara aure da yayi, ruma ba ƙaramar wahala take sha ba awurin iyah , dan kusan kullum sai ta zo har gida ta ci mata mutunci, hakan yasa tayi ta roƙwan mijin nata akan ya bi umarnin mahaifiyar shi da nuna mashi mahimmanci bin umarnin nata, da farko ƙin amincewa yayi sai da ruma ta rinƙa tasa shi gaba tana yi mashi kuka akan ya ƙara auren, haka nan ba dan ya so ba ya amince da ƙarin auren, iyah da kanta ta nema mashi auren ɗiyar aminiyarta, ba a ɗau wani lokaci ba aka ɗaura auren nuraddeen da amayar shi hauwa'u ana kiran ta da maijidda, ranar da aka kai hauwa'u gidan shi ya haɗa su ita da ruma yayi masu nasiha akan suyi haƙuri su zauna lafiya, hakan ce ta faru dan sosai ruma da maijidda ke zaman lafiya, ruma ta ɗauki maijidda kamar ƙanwarta uwa ɗaya uba ɗaya........
_Episode 48_49_
........... Watan maijidda ɗaya da satittika a gidan nuraddeen Allah ya albarka ce ta da samun ciki , zo kaga murna wurin nuraddeen da ruma, da iyah taji labarin cikin maijidda har gida ta zo tayi ta sakar ma ruma habaici tana ce mata juya, ita kuwa ruma babu abun da ya dame ta tasan Allah da ya bama maijidda yana sane da ita, sosai take kula da maijidda, cikin na kaiwa wata biyar ta hana maijidda aikin komai a gidan daga sallah sai bacci da cin abinci take yi,da cikin ya isa haihuwa iyah ta mai da maijidda gidan ta, a cewar ta a gaban ta zata haihu, watan cikin maijidda tara da kwana goma ta haifi ɗa namiji kyakyawa mai matuƙar kama da nuraddeen, zo kaga murna wurin angon jego da iya, ruma ma ba'a barta a baya ba tayi murna da farin ciki sosai, da ranar suna ta zagayo yaro ya ci sunan mahaifin nuraddeen Ahmad ana kiran shi da magaji, sai da maijidda tayi arba'in ta koma ɗakin mijinta,ruma ta cigaba da kula da ita da yaron ta har yayi ƙwari, shekarar magaji biyu maijidda ta samu wani cikin ta haifi ɗiyarta mace wacce taci sunan iyah watau maryam suna ce mata uwani haka maijidda tayi ta haihuwa amma ruma shiru bayan uwani maijidda tayi halimatu daga kan halimatu ne ta ɗan dakata bata ƙara haihuwa ba, yaranta sun taso cikin soyayyar mahaifin